Karfe Daya Baya Page 4 Amo Na Fatima Muhammad Gurin


ƘARFE ƊAYA BA YA AMO


✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN 

(GUREENJOH)


@Gureenjo on Arewapen

@Gureenjih6763 on Wattpad 


ADABI WRITERS ASSOCIATION


TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. 


GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.


NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.


*SHAFI NA HUƊU*


Kaman yadda ta yi alƙawarin hana kowa zaman lafiya a yankunan haka suka yi, sun zubar da jini har da waenda basu ji ba basu gani ba, sun ja wa mutane dayawa asarar kayan sana'o'insu kuma basu samu yaron da suke nema ba.


Sanda ne maƙale a wuyanta ita ce gaba suna take mata baya har gaban mota ta shiga su ma duk suka ɗuru sai asibiti inda Pascal ɗin ke kwance, nan ma sai da suka yi rigima amma ta hana a taɓa kowa, daga nan bayan sun duba shi suka yi gida.


Magrib ne ta shigo gidan bayan ta yi parking ko oho ta sauƙa, a cikin motar ta bar key ɗin kofar ma bata rufe ba ta nufi cikin parlor, jagaban ta gani zaune yana shan tabar wiwi.


"Baaba"

"Zo nan 'yar baba"

Don niyyar wuce shi ta yi, dawowa da baya tayi ta zauna kan kujera tana harɗe kafafu.


"Daga ina kuka fito haka? Ya na ga yanka a hannunki?"

Ta ɗaga hannun ta kalla.


"Nima ban san ya aka yi na yanke ba... Chan Dorayi muka yi muka ɗaga musu hankali, Pascal nawa fa suka taɓa!!"


Pascal kusan idan basu yi sa'anni ba to bai wuce ya girme ta da shekara ɗaya ba hakan ya sa tana da shakuwa sossai da shi a click ɗin nata, bata manta sanadiyar haduwarta da Pascal a nan gidan ne ya zo sayan Tramadol wanda oganninshi suka aike shi a sadda ta tambaye shi shima yana sha? Ce mata yayi


****


"Ban taɓa sha ba amma Oga Sanusi ya ce watarana da kanshi zai ɗandanamin wai yana hana gajiyar aiki. Kin san aikinmu ba na rago ba ne"


Ta yi dariya tare da kallonshi 


"To Meyasa kake zuwa gidan bredin aiki ba ka zuwa makaranta?"


"Diva idan ban zo gidan burodin ba ina zan samu kudin da za mu ci abinci da kanwata da mahaifiyata? Babanmu babu ruwanshi da ciyar da mu a gidan ya auri mata sama da biyar kuma kowacce ta ajiye 'ya'ya amma kowani ɗaki su suke ciyar da kansu, tufatar da kawunansu da kuma kula da lafiyarsu har ma da makaranta idan suna so su saka kansu shi ya ce ba'a yi mishi ba yana ƙarami shima ba zai yi wa kowa ba"


A lokacin tausayinshi ne ya kamata a yadda yake magana, ya taɓa ce mata babanshi na da gidajen haya kaman Babanta haka kuma yana da gonaki a kauyuka da gaske baƙar mugunta ce kawai zai sa ya watsar da nashi da uzurin cewa shima nashi uban bai mishi ba alhali shi ba jalihi bane da iliminshi boko da arabi sai dai ɗan aƙida ne..


Bayan kwana biyu da ya dawo sayan Tramadol ɗin yake sanar mata ai ya sha kuma yayi aiki sossai ya samu kuɗi har kifi soyayye ya sayawa mahaifiyarshi, daga nan rayuwar shi ta lalace daga wannan sanadiyar ya zama addicted to drugs, ya zamana idan bai sha ba baya aikin bredin, idan ta ga mahaifiyarshi da natsuwar ta ta kan tausaya wa rayuwar Pascal amma bata bari ya bayyana ba, tun samuwar click ɗinta yake na gaba gaba a dukkan lamuranta sai dai idan faɗa bai tashi da Diva ba yana ciki hakan ya sa take kaunarshi tamkar ciki ɗaya suka fito.



****


"Shi ne kika bari aka ɗauki hotunanki ana yamadidi da su duniya? Bana son kalar bakin da ake yi miki Sohana bana jin daaɗi, ba rayuwar nan na so ki yi ba"

Yayi maganar da iyaka gaskiyarsa don yayi iya kokarinsa amma abin da rayuwa ta zaɓa mata kenan karatun ta yi shi iya secondary ta shiga FCE ta fara karatu ya ƙi dadi don ko ɓata mata rai aka yi ta dawo to su Pascal sai sun shiga sun ɗaga hankalin kowa a makarantar bata je ko ina ba aka koreta ita kuma ta ce ta gama karatun tunda ba dole ba ne babu yadda ya iya ya zuba mata idanu.


Jin ya kira asalin sunanta ya sa ta tabbatar da gaske ya shiga yanayin damuwa.


"Kuttt to na rantse da Allah duk gidan jaridar da suka poster ni har suka yi sanadiyar bacin ranka sai na tarwatsa su..!"


"Ba maganan kenan ba, idan wanchan ne ni da kaina zan yi maganinsu ɗaya bayan ɗaya, ina dai so ki rage wasu abubuwan ne ki bar wa su Obafiya ba sai kin fita da kanki ba"


"Baaba ba zan iya tura yarana bakin daga in kwanta in yi bacci ba, yadda nake jagabarsu kuma shugaba a garesu dole ni ce kan gaba a duk wani tarzoma da ta shafe mu... Bacci ai sai rago ni kuma babu ragwantaka a tsarinaa"

Kallonta kawai yake ta miƙe 

"Ka huta Baaba"

Tana kai nan ta yi ciki.


Tana jin shi yana kiran hajjo, wanka ta shiga tana fitowa ta samu abinci ne aka ajiye mata a shirye, ta san aikin hajjo ne kuma da umurnin Baba don haka sallah ta yi ta zauna ta ci codein ta sha ta ƙara da ice, anan ta bar komai don ta san hajjo za ta zo ta tattare, tun ta buɗi ido ta ga dattijuwar hajjo ne ke kula da komai da ya shafe ta, bata taɓa cire ƙaya ta ɗauke da kanta ba sai hajjo ta zo ta ɗauke, bata taɓa sa hannunta kan tsintsiya da sunan shara ko wanke bayi ko gyaran ɗaki ba, kayan jikinta ma idan ta cire bata san ta tsuguna ta ɗaga ba anan zata barshi karshe zata zo ta same shi a goge a shirye cikin wardrobe ɗinta.


****


"Ina za ki je ba ki bada kuɗin cefane ba?"

Malam Iron yayi magana yana kallon Zubash da ta fito a shirye.


Tsaki ta ja ta fiddo dubu biyu ta jefa mishi.


"Yaya Zubaida"

Ƙanwarta ta ƙirata.

"Ya?"

"Wai fa waec ne za mu fara kuma kin ga ke ce kike biyan kuɗin makarantar an ce zuwa karshen watan nan idan ban biya ba za'a rufe karɓa sai kuma wata shekarar"


Ta lumshe manyan idanunta ta buɗe.

"Na ji"

Tana kai nan ta nufi kofa, saura kaɗan Salmanu ya hankadeta yayi saurin matsawa gefe.


Shi karan kanshi ya san yanzu ba da bane, a da ne ya daka ya zalunta kuma ya zaga amma a yanzu idan ya gwada hakan sai ta bazar da shi kuma a banza.

Harara ta zabga mishi tana tsaki ta fice.


Mota ce dake Parke a kofar gidan ta buɗe ta shiga.

"Ya aka yi?"

Matashin dake zaune ciki ya ce 

"Wani deal ne ya samu, akwai wani babban dan siyasa da ya sa na samo mishi mace da irin siffarki shiyasa na neme ki kai tsaye Dukda a raina kam Uwar ɗakinki ne Diva"


"kulll ka sake ambatan sunan DIVA, zan iya yin komai a kanta Jibril.. Sai in shemeka kuma babu abin da aka isa ayi na rantseee...Na sha gayamaka Diva ba haka take ba ni karan kaina da nake wannan harkar babu yadda ta iya da ni ne amma babu abin da ta tsana irin Biye biyen maza...har ka mutu ba za ka iya kawalcin Diva ba"

Yadda take magana ya sa yayi shiru Dukda ba a Buge take ba sai ta illata shi akan wannan Diva ɗin.


"Za mu je ne ko na sauƙa?"

"Ki yi haƙuri, ai ba zan bari mu yi asarar makudan kudade ba daga ni har ke"

Motar ya ja suka nufi wani rantsatsen guest house tabbas akwai kudi wurin don karan kanshi kamashonshi ya fi dubu ɗari da hamsin don Alhjn ya ruɗe akan kyaun Zubaidah na cikakkiyar bafulatana, harkar da ta saba ne da shi kowa ya dogara a gidansu don haka babu shakka ko fargaba suka shiga holewa.


Sama da awanta biyu wurin wannan Alhjn kan ya sallame ta.


"Zubash!"

Ta ɗaga ido ta kalleshi yana kallonta yace 

"Kina da kyau mai ɗaukar hankali"


Tayi murmushi 

"Shi ya zama jari na! Wannan kyaun shi ya ceceni daga rayuwar wahala"


"Da za ki yarda da na aureki, ba za ki gane irin features ɗinki ba, baki san baiwar da Allah yayi miki ba ne...amma rayuwar nan bata kamaceki ba"

Tayi dariya.


"Aure?? Har Aure wani abin alfahari ne? Ka ga malam Sallameni in tafi"


Har zuciyarshi ya ji soyayyarta, ta haɗu ne ko ta wani ɓangare amma ya kula rayuwar bariki ce kawai gabanta.


Kudadenta ya mata transfer chass kan ta miƙe ta fice.

Riga da wando ne jikinta kanta manyan kalaba da bata ko damu da rufe su ba, tafiyarta take hankali kwance ta ji wayanta na ƙara.


"Shaly!"


"Kina ina? Diva na nemanki tun safe...har tarzoma muka tayar baki nan"


"Diva ta fita da kanta faɗa? Me ya faru?"


"Pascal ne aka soka a injin biredi"


"kuna ina? Gani nan zuwa"

Tana jin suna gidan Jagaban ta tari machine ta haura.


"A gafarceni Diva ban san abin da ya faru ba"

Zubash ta faɗa tana ɗan rankwafawa kaɗan.


Diva da ke shan ice ta ɗago idanunta da suka ji kwalli suka kara haske ta kalleta.

"Daga ina kike?"


Sosa kai kadan tayi bata ce komai ba.

Tsaki Diva ta ja ta tura mata kujera.


"Zauna"

Zama ta yi.

"Me yake burgeki ne da maza Zubash?"

Diva tayi tambayar ba tare da ta kalleta ba sai lumshe ido take ice ɗin na hawa har kwakwalwarta.


Kai tsaye tace 

"Sulallah... Idan ban je garesu na samu kudade ba wa zai cigaba da kula da gidanmu?"


****


Haka ne lallai Zubaidah ɗiyar kwarai ce a farko tana iya tuna ranar da ta fara karɓawarwa Zubaidar faɗa Ɗan mijin mamanta Ya biyo ta da wani ƙarfe har kofar gida yana dukanta har hannunta ya karye, wucewa kawai suke amma zaluncin da aka yi mata ya sa Diva taimaka mata, sai da ta rama mata kariyarta.


Bayan kwana biyu Zubaida ta zo mata godiya har gidan Jagaban da dayawa a unguwar suka tsani ko wucewa ne yaransu su yi ta wurin tabbas da akwai dama da sun jima da korar Jagaban a unguwar amma ya riga ya zame musu ciwon ido. Diva ce  ta biya komai aka mata gyarar kariyar don haka ta ji dole ta shiga tayi mata godiya saboda Salmanun har tsoronta ya fara ji shima kuma yana fama da Azabar nashi kariyar, da ta zo ta samu Diva ɗin da su Pabloo a harabar gidan suna ta shaye shaye.


"Na zo ne na miki godiya"

Ta faɗa a ɗarare saboda yanayin gidan da 'yan dabar da ke cike da shi.


"Meyasa za ki zauna ana zaluntar ki ba za ki kwatarwa kanki 'yanci ba?"


"Ya zan yi? Ba ni da wani 'yancin kwatar saboda alfarma ne muke kai, Ba gidan mahaifina ba ne, mahaifiyarmu ta haifemu mu biyu a chan Taraba kauyen Gassol da aure ya kai ta, bayan mun fara girma da wayo suka rabu da mahaifinmu, ta ƙi barinmu wurinshi ta tattaro mu ta dawo da mu Kano, shi kuma ya rantse cewar idan bata mayar masa da mu ba ko sisin kobo ba zai tura mata don kula da mu ba, ta zo ta sake aure muka zama mu ne bayin manyan yaran mijin da mijin shi karan kanshi.


A ƙarshe kin san me mahaifiyata take cewa?"


Diva da ta zuba mata ido a lokacin ta girgiza kai.

"Ta gaji da ganinmu a gabanta haka mu fita mu nemi kuɗi, babu ruwanta da inda za mu samu, babu ruwanta da ta yadda za mu samu, ina da haddar izu ashirin anan na ce mata zan samar mata kudin amma ta bar khadija kanwata tayi karatu ni kaɗai na isa samar mata da kuɗin haka na ajiye karatun alqur'ani na, na bazama aiki neman kuɗi karantarwa ne na samu na kananun yara tunda ina da ilimin na fara koyar da su daga safe har yamma ana ba ni salaries karshen wata, a haka idan na kawo mata ɗari biyar dubu ɗaya ta kan zara daga ciki ta ba ni matsayin wahalar da nake sha na rana da koyarwa. A haka babu mai godiya Salmanu abu kadan na mishi zai kamani gabanta ya daka to ya zan yi? Agolancin kenan"


"Samari na yi na gari har wurin huɗu amma Mahaifiyata ita ke nuna min hanyoyin da zan bi na ci kudinsu a karshe na ƙi aurensu da sunan basu kai su sameni ba, har ga Allah rayuwata tana cikin garari ban san ya zan yi ba ban kuma san ta ina zan fara ba..."


Diva ta dafa kafadarta 

"Zubaidah Bashir, haka sunan yake?"

Kai ta gyaɗa mata.

"Zubash"

Diva ta ƙira da hakan tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sun fahimta.

Obafiya ya ɗauki coke me surke da codein ya miƙa mata

"Ki sha wannan za ki samu sassauci"


Da farko tayi kokonto amma daga baya ta karɓa ta sha ɗin, wannan shan da ta fara shi ya zama kofar shaye shayenta, matsi sai ya ƙaru mata don an koreta a makarantun da take karantarwa saboda fahimtar ta fara shaye shaye, Maama ta uzzura mata saboda sun daina samun kudi daga wurinta har tana barazanar tura ƙanwarta waje neman kuɗi saboda tseratar da khadija da sharrin shaye shaye ya sa ta faɗa harkar bin maza wanda har yau Diva bata farin ciki da hakan.


****


Miƙewa kawai Diva tayi bata sake ce mata komai ba ta shige ciki idanunta na lumsuwa saboda bacci.


"Shaly ya jikin Pascal ɗin?"

"Da sauƙi"


Daga nan suka cigaba da hirarrakinsu.


Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....


*A whatsapp 

One 1k

Two 1800

Three 2400* 


 *Telegram 

One 700

Two 1200

Three 1500*


Account details 

0545475847 

Gt bank 

Fatima Muhammad Gurin 


Sai a tura shaidar biya ta

09039206763




                       🖤Gureenjoh🖤

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post