ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
THE TRIO OF TALES
THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY.
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.
*SHAFI NA UKU*
Ƙarfe Tara da rabi ta farka kaman koyaushe yau ma dai Sallar asuba ya wuce ta dama ɗaiɗaikun ranaku ne take samun sallah kan lokaci amma sai dai tayi daga baya wani sa'in ma ya wuce da haka kenan.
Wanka ta yi ta zo tayi Sallar, wani material da aka yi wa ɗinkin garari don a yanke yake ko ta ina ta saka da wando Jean, scarf ne ta ɗaura kanta don bata cika barin kanta ba ɗankwali ba muddin zata fita daga cikin ɗakinta.
Parlor ta fito ta samu Baba a inda ya saba zama.
"Barka da safiya"
"Sarauniyata kin tashi?"
Kai ta gyaɗa.
Yayi murmushi.
"Barka da tashi dama su Pabloo suna chan suna dakonki"
Ta miƙe tsaye
"Bara na karasa, hajjo ta dafomin indomie yadda na saba ci Baaba"
"an gama ɗiyar Baba"
Ta fice daga parlorn.
Murmushi ta saki ganinsu duka zaune kan plastic chairs suna jiran fitowarta, Shaly da Obafiya ne suka fara ganin Fitowarta don hankalin Pabloo ya ɗauku ne wurin neman jijiyar da zai tsira wa kanshi allurar pentazocine.
"Barka da fitowa Diva"
Ta ƙarasa tsakiyar su suka bata kujera ta zauna tana karbar allurar don taya Pabloo duba jijiya, su ne 'yan uwan da ta buɗi ido ta gani, su ne ƙawayenta kuma su ɗin ne shaƙiƙanta.
Pabloo ta kalla bayan ta gama mishi allurar Penta ɗin idanunsa lumshe ta koma ta jinginu da kujerar tunaninta na komawa wani lokaci chan baya.
****
"Pabloo menene wannan?"
Ta yi tambayar ne da zuciya ɗaya saboda kwata kwata a lokacin bata haura shekaru bakwai ba, Pabloo ɗin kuma zai iya kai wa sha uku zuwa sha huɗu kuma a lokacin ma da kanshi yake yi wa kanshi allurar.
"Sunanshi Penta"
"Shi ma Baba na sayar da shi?"
Kai ya gyaɗa mata.
"Meyasa kake jin daaɗin yi wa kanka allurar bayan na san da zafi? Kuma dama don kawai a bugu aka yin shi?"
Yayi murmushi
"Za ki fahimta ne daga baya sohana amma bana miki Fatan zama ɗaya daga cikinmu, ina so ki yi rayuwa mai kyau"
Ta ɗan tura baki
"Ka ba ni amsa Meyasa ka ke yiwa kanka wannan allurar?"
"Na fara shi ne saboda Baba ya ce shi ne zai sauƙaƙa min damuwata, shi zai mantar da ni matsalolina kuma da gaskiyar shi tunda na fara bana tunani ko fargabar komai"
"Menene damuwar?"
Ta Yi saurin tambaya.
"Sohana Mahaifiyata ta haifeni ne da wani irin baudadden talakan mutum, talauci irin mai tsananin nan da abin da za'a ci ma wahala yake bare a shayar da ni, suna zama ne a ci yau gobe a kwana da yunwa, a haka kuma ya ƙaro aure ko watanni uku ban rufa ba duk malnutrition ya gama bayyana a siffata, sun yi rigima sossai don ɗan kudin da ya samu ne a gado maimakon ya yi amfani da su wurin gina mu sai ya zaɓi ƙaro aure, ita kuma mahaifiyata ta zuciya sanin irin kangin talaucin da ta juri zama ciki, ganin ba zata iya ba ya sa ta ajiye mishi ni tayi tafiyarta, ba zan ce miki ga yadda na tashi har na shekara bakwai wurin Stepmother na ba, Baaba Salame ta fahimci irin talaucin Baba da rashin makamarshi ne bayan 'yan kudin gadon sun ƙare, ɗawainiyar gidan ya dawo kanta a dole tunda tana sana'a amma fah ko baban kwaryarshi a wulakance, talaucinshi ya ja mishi wani irin raini kuma bashi da bakin magana saboda idan ta bar gidan ma bai san ya zai yi ya ci da mu ba.
Salame macece mai baƙar zuciya da mugunta ban samu wani katabus ba saboda irin abusing ɗina da ta dinga yi, physically, emotionally and mentally na azabtu irin azabar da bana yi wa ko makiyina fata, almajiri ya fi ni gata da kima a gidan uban da haifeni, wata rana ta saka ni wanki sai ta aikeni ban dawo da wuri ba na tsaya wasa a hanya har kudin suka ɓace, tsoron hukuncinta ya hanani komawa tunda ita ke ci da mu da ni da mahaifin nawa shima bashi da say a gidanshi, ko da na tattara courage na koma tayi min dukan da ban yi tunanin zan rayu ba saboda mutuwa ya ratsa idanuna a lokacin, ko da ta kyaleni washegari ta ba ni tallarta yadda ta saba na ƙwai dafaffe a kasuwa wani mai babur ya kaɗe ni.
Hankalina ya tashi ba ciwon kafafu na nake duba ba sai asarar kwan Baaba Salame, ganin irin kukan da nake da halin da na shiga ya sa wasu dattijai suka raka ni gida don yi wa Baaba Salame bayani tunda mai babur ɗin ya gudu bai tsaya ba, bayan ta gama jinsu tayi godiya suka tafi suna fita ta fusgo ni ta shiga kirba tana tsine min kaman wacce Allah ya aiko daga ni har mahaifina da na tabbatar yana jinmu tunda ya gama kashe zuciyarsa ba neman yake ba bare ya sa tunanin samu, ta ja ni ta rufe a ɗaki kwanana biyu sai ruwa kawai take ba ni wai na ci kwan da na mata asara ba dai abincinta ba, a kwana biyun mutuwa ne kawai ban yi ba Sohana.
Kwana na ukun ta buɗe ni na yi furu furu na firgice, ciwon kafafuna basu samu kula ba kudaje ke bi haka ta sake ɗora min tallah a akan idan ban sayar ba yau ma haka zan kwana da yunwa in na ga dama in mata asara.
Nayi kuka na ji na tsani kowa da komai zuciyata ta kitsa min irin muguntar da zan mata, har tunanin buga mata tabarya na yi, nayi tunanin kwarara mata rufan zafi haka dai na gama sake sake na har na sayar na dawo ta ban abincin da bai taka kara ya karya ba, tana shiga ɗaki na zuba mata manja a tiles tana fitowa ta shiga wurin wanke-wanke ta zame ta yi mummunan fasa kanta da har aka yi tunanin ta samu brain injury tsoron hukuncin da za'a dauka a kaina ya sa na gudu. Allah ya haɗa ni da Jagaban ya ɗauke ni tamkar danshi, a wurinshi na samu dukkan kulawa, ya ja ni a jiki inda yake ba ni abinci har sau uku a rana kuma bai saka ni aikin komai kan ya ba ni, shine mutum na farko da ya fara yi min kirki hakan ya sa na ji kome zai faru zan mishi biyayya kuma zan zauna da shi har in gina kaina.
Na shiga matsanancin damuwa da tsoro haka kawai sai in firgita shi ne Jagaban ya fara yi mini wannan allurar da nufin zai sa in manta duk wani damuwana da tsanar da na yiwa iyayena daga haka na saba da shi har ya zama ina iya yi wa kaina da kaina, allurar na rage raɗaɗin ciwo ne (narcotic) musamman ga masu ciwon sikila ko wani ciwon ƙashi mai tsanani... Tun jagaban na yi min a kyauta har ya sakani a sana'ar gyaran machine ina kawo mishi kuɗin shi a lissafe na yawan allurar da nake karɓa.
*****
"Diva!"
Shaly ta ƙira sunanta tana taɓa ta ta ɗan yi firgigit tana dawowa daga tunanin da ta tafi, ta sake kallon Pabloo zuciyarta na karta a hankali, a yanzu sana'ar machine yake mai kafa biyu amma duk inda kuɗin ya zo na Jagaban ne ko biyan gidan hayan da ya gina a gefensu da dakuna masu yawa yake accomodating thugs da suke under drug addicts ko kuma ya biya kudin pentazocine da ya zame mishi addiction ƙarfi da yaji.
"Me kike tunani ne haka?"
Ta girgiza kai
"Ga shi Diva maganin damuwan kenan ko ma wace iri ce"
Zee baby ta faɗa tana miƙa mata coke mai sanyi da ta juye codein ciki, karɓa tayi ta kalla kaɗan kan ta kai Bakinta ta shiga sha.
"Zubash fah?"
"Bata shigo ba bai wuce tana chan suna rigima da Mijin Asawanyarta ba"
Kai ta gyaɗa
Suna ta hiran su tsakaninsu bata tanka ba bata ce uffan ba har sai da ta bugu sossai aka kawo mata breakfast ta ci sossai saboda yanayin shaye shaye da ke saka jin yunwa, daga nan ɗaki ta koma ta zube kan gado sai bacci.
Da misalin ƙarfe uku da 'yan kai wani irin hayaniya ya farkar da ita, tsaki ta ja tana mutsitsike idanunta da suke a lumshe farare da su, bata da aukin kirki sai hatsari, doguwa ce mai matsakaicin jiki, tana da albarkatun sama da ƙasa don shape ɗinta mai kyau ne, bata da ra'ayin maza shiyasa duk wanda ya tinkareta da sunan soyayya ma sai ta zubar masa da jini wannan alkawari ne hakan ya sa kowa ke gudunta, ita ba fara ba ce ba...irin wannan warm golden brown complexion ce, bakinta ya ɗan yi duhu daga ƙasa tsakiya kuma da haske saboda shaye shaye da take yi.
Miƙa ta yi tana ɗan sosa idanunta, ɗakin har lokacin duhu ne dulum kaman ba rana tsaka ba, ta janyo wayanta ta kunna ta ga time kan ta dira daga kan gadon taje ta kunna hasken ɗakin da kaman na wata princess ya bayyana sai dai komai baki da fari ne don kalar da ta fi so baƙi ne...
Toilet ɗinta ta nufa tana zubar da kayakin jikinta a hanya kan ta gama shiga ba komai jikinta tayi wanka Sharp Sharp ta fito da Alwala gefe chan ta nufa akwai sallaya da doguwar riga da ƙimar ta saka ta haɗa sallar azahar da la'asar hakan ya bi jikinta Dukda ba ya mata dadi yawanci in ta bugu sai ta gwamutsa salloli wasu ta rama wasu kuma sun shige daga haka kenan.
Wardrobe ta nufa babu abinda ta ɗaga a kayakin da ta zubar ta saka wani wando dogo da trench coat a kai ya kai mata har gwiwa duk baƙake sai a lokacin ta zame ɗankwalin ɗazu tulin gashinta ya bayyana ta aske har ta gaji ta daina don kwana kaɗan zai dawo har ya fi wanda ta asken, tufkeshi tayi kan ta ɗauki vintage scarf fara ta ɗaura sau ɗaya ta baya ta saki jelar gefe da gefe, wukakenta da duk akwai sunanta jikin kowanne ta ɗauko, daya bakinshi ma ziz-zag ne irin wannan tana so idan ta soki mutum da shi ta zaro da tsokokinshi ya fi bata kwanciyar hankali sai ɗayan plain ne ta saka su jikinta.
Har lokacin gidan na cike da hayaniya da sauri ta nufi kofa ta fito, ba kowa a parlor ta nufi waje, yaran gidanta ne tsaitsaye suna ta hayaniya.
"Wai ya aka yi ne? Me ke going?"
Muryarta da suka ji ya sa suka daddare.
"Barka da fitowa Shugaba!"
Suka hada baki suna miƙa mata gaisuwa.
"Pascal ne aka sokaaa ya kusa warewa chan kiyama amma dai bai ware ba..!"
Obafiya ya faɗa cikin yanayin maganansu.
Lokaci ɗaya fuskarta ya chanza, idan kana kaunar ɓata mata rai ka taɓa daya a cikin mutane bakwan nan da suka zama rabin jikinta.
Pablo, Pascal, Skipo, Obafiya, Shaly, Zee da Zubash.
Jar uban chann! kayyasaa...Wasu ƙananun fitsararru ne da wannan gangancin na tarar aradu da ka?"
"Eh shugaba yaran chan sabon titi ne"
Skipo ya faɗa a daddare.
"Chan dallah! kun zo kun tsaya kuna menene yaran basu riga sun shiga kogin jini ba? Ku wuce mu je daga Dorayi zuwa Sabon titi kowa bacci dole....."
Fitooo mai ƙarfi ɗaya ya yi daga ciki wani ya ja addaa kan dakali ya ba da ƙiiiiiiiii
"kowa ya zaburo a bar shi ya kawo... Kafin a yi dare akai kwan, Kuma komin lalacewar masa ta fi karfin kashin shanuuu...kowakkwana lafiya shi ya so... Wallahiiii"
Skipo ya zaro mata key ɗin motarta don bata yarda a tukata, da hanzari kusan su goma sha wani abu da suke gidan a lokacin suka chusu cikin SUV baka wuluk ta zagaya ta shiga ɓangaren driver, tun fitowanta mai gadin ya wangale gate don ya san yau ba zaman lafiya yayi mata garaje ma shima kwana zai yi jinya.
Da wani irin reckless driving ta fita, matasan suna ta ihu da kirari rike da adduna da sanduna...
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a tura shaidar biya ta
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
