ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.
*SHAFI NA BIYU*
Ƙarfe uku da rabi ya buɗe idanunsa, a hankali lips ɗinsa ke furta
"Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma amatana wa ilaihin nushur"
Cikin natsuwa ya miƙe zaune ya ɗan jima a zaunen kaman yadda sunna ya nusar akan samun cikakken natsuwa bayan farkawa daga bacci kan miƙewa.
Ya zura kafafunsa ƙasa ya sauƙa ya nufi toilet, wanka yayi tare da alwala, ko da ya fito sai da ya shirya tsaf cikin farar thob da baƙar jubba mai gold a aikin hannu da kuma gaban daga wuya zuwa ƙasa, ya saka oil perfumes nashi na Oud da har sun kama jikinshi ba kayanshi kaɗai ba, duk kuma inda zai zauna ya tashi sai ya bar kamshin na lokaci mai tsawo, don shi ɗin ma'abocin son kamshi ne kwarai da gaske musamman turaruka irin na Larabawa, ya ɗora farar Ghutra a kanshi ba tare da ya nemi Agal ba don ba buƙata, a natse yake ajiye kafafunsa cikin tattausan rug ɗin ɗakin har zuwa wurin sallarshi, burner ya kunna sai da yayi zafi sossai ya kashe sai ya ɗora turaren wutanshi a kai, a kan sallaya ya daidaita natsuwarshi kan ya fara ganawa da ubangiji cikin kankantar da kai da sallamawa.
Sai da ya jima yana nafilfili kan ya zauna ya ɗan yi wasu zikirori anan ya ji an fara ƙiran Sallar farko bai motsa ba, ya karanta shafuka biyu daga cikin qur'ani kan ya miƙe yana gyara Ghutra ɗin shi har wurin fuska ya nufi ƙasa, wata farar mage da bata yi yanayi da na ƙasar Nigeria ba ta taho da gudu ya duƙa ya ɗaga ta zuwa jikinshi fuskarshi na sakewa a hankali daga a kame zuwa murmushi mai sanyi har fararen hakwaranshi na bayyana yana shafata a hankali ya furta.
"Sabahulkhairrr yaa humayrah!"
Tayi miyauuu ya saki murmushi, ya duƙa ya ajiyeta ya nufi wani locker ya fitarda canfood ta bi shi da gudu zuwa gefen dining inda anan yake saka mata abinci ya juye mata a kwanon ta shiga ci shi kuma ya fice, sai da yayi rakatanil fajir kan ya isa matsayar limami babban masallacin nashi mai suna Al-Noor Mosque ya shiga gabatar da Sallar asuba duka unguwar ya ɗauki tattausan muryarsa mai tsuma zuciya da sanya salama ya kuma tada tsikar jikin duk mai saurare.
Bayan sun idar bai motsa ba yana nan zaune yana adu'o'i da azkar har bayan mintuna talatin kan ya juyo gabaɗaya, duk wasu mamun da suka bi Sallar tashi sun fice ya saura dalibanshi ne na kusa su wurin Ashirin da biyar, matso wa suka yi suka yi musabaha kaman yadda yayi musu nuni da hakan suna kuma gaishe shi da Fatan ya tashi lafiya.
Bayan gama gaisuwa suka shiga ba da karatu yana nan zaune yana saurare idan ka yi kuskure zai gyara har su ka gama kowa iya abin da ya iya ɗauka ya bayar, idan sun bayar kuma za su shigar a gabanshi su karanta na gobe da Kur'ani a buɗe idan da kuskure ya gyara kan su tafi don koyan haddar.
Har sai da suka gama tass kan ya samu ya karanta shafuka uku again, rana na fitowa ya miƙe yayi nafila yadda sunnah ta tanadar kan ya fice daga masallacin ya nufi gate ɗin gidansu dake daga jikin masallacin hannayensa goye a baya bakinsa na ambaton Allah a hankali.
"Barka da safiya Baba lawan"
Ya faɗa a natse, mai gadin da bai ma ji tahowarshi ba yayi saurin Miƙewa cikin ladabi Dukda Shehi yaro ne da zai iya haifa martabarshi na addini da tarin baiwa da ubangiji ya mishi ya sa har manya kan bashi girma wannan na daga cikin kamalar kowani malamin addini.
"Barka da safiya Shehi, mun tashi lafiya?"
Cikin girmamawa ya mayar mishi da gaisuwan.
"Alhamdulillah Baba, ba wani matsala?"
Girgiza kai yayi kan dai ya ce
"Babu matsalar komai sai dai na kula iyayenka sun jima jikin motarka da Shi Malam Ammar da Malam Bala don tun bayan fitowansu Sallar asuba suka ga aika aikar da 'yan daba suka yi muku"
Girgiza kai yayi, ya san aikin Ammar ne, shi a wurinshi wannan duk ba abin mayar da magana bane ko don shi yana da tsatsauran tsari da ra'ayin shanye koma menene a cikinshi ne oho, yana shirin nufar sashenshi ya ji wayanshi na ƙira sautin larabci marar kida na shiga kunnenshi, zaro ta yayi ya ɗaga tare da makalawa a kunne hannunshi ɗaya na goye bayanshi kanshi na kallon ƙasa
"Assalamu Alaikum warahmatullah Abiey"
"Wa'alaikassalam warahmatullah ka fito masallacin kenan, same mu sashen Daddah"
Ya amsa cikin girmamawa.
Yana sauƙe wayan ya nufi ɓangaren kakarsu mace dake cikin gidan, duk suna zaune ana ta tattauna magana jin sallamarshi ya natsar da dayawa har wasu na muskutawa kwarjininshi bai bar har manya ba, Uncles ɗinshi biyu ne a parlorn Twin brother na mahaifinshi wanda shine baban Ammar sai cousin ɗinsu da ya girma ne ma wurin Daddah ɗin tare da su Ishaq sai sisters ɗin Abbiey ɗinshi mata guda biyu da wasu 'yan mata uku waenda yaran aunties ɗinshi ne da duk su biyu suka rasa mazajensu kuma tun sannan a gidan suke wurin Daddah ɗin, su ne zaune parlorn.
Yaran matan ganin shi ya sa duk suka tashi suka fita suka bar iyaye, Daddah na zaune daga ƙasa.
"Shehi!"
Abba ya kira shi.
Ya ɗan ɗago sai ya nuna mishi gefenshi ya taka yaje ya zauna kan ya shiga gaishe su suna amsawa.
"Ashe kuma Abinda ya faru kenan? Yara ne duk sun lalace in ba lalacewa ba abin wani ne zai tsone maka ido har ka nemi kwacewa? Kai duniya! Allah ya takaita ya tsare mana kai Shehi"
Daddah ta faɗa cikin jimami sanye da hijabinta dattijuwa ce da kallo ɗaya zaka mata ka ga cikakkiyar bafulatana, don hausarta ma ba wata nuna tayi ba.
Murmushi Irshad Al-Noor yayi kaɗan cikin natsuwarshi ya ce
"Daddah Adu'a suke buƙata, Allah ya shirya mana su"
Abbiey ya ce
"Amma ya kamata ku yi reporting irin wannan lamarin ba abin kawar da kai ba ne, ko ɓarnar da suka yi wa motar ka ya kamata a ce an binciko su an yi musu hukunci daidai da laifukansu idan yau kun tsira gobe Allah kaɗai ya san wanda za su cutar ko su illatar tunda idan suna cikin mayen nan ba sanin me suke aikatawa suke ba"
Har lokacin da ɗan murmushi kan fuskarsa idanunsa na a ƙasa ya ce
"A'a Abba babu buƙatar hakan tunda Allah bai ba su nasarar yi mana wani ɓarna ba"
Uncle Ishaq ya ce
"Har da laifinka Irshad, kana da daman daukar masu tsaron lafiyarka amma hakan ya gagara gashi yanzu maganan ya gama bazuwa a media makiya sai su yi amfani da irin wannan daman don ganin bayanka"
Ya ɗaga idanunsa masu cike da wani haske da kwarjini ya kalli Uncle Ishaq a yanzu ba murmushi yake ba.
ya ce sharply
"Babu mai yi mini abin da Allah bai rubuta ba, bana buƙata Uncle"
Ya ƙarasa yana dauke kai don zuwa yanzu ma ya fara gajiya da maganar.
"Toh Allah ya tsare mana kai ya cigaba da kiyayewa, Amma dai kaima ka sake kiyayewa idan akwai yadda zaka rage commitment ɗinka na dare sai ka yi samun ka dinga shigowa gida kan lokaci"
Abba ne yayi wannan bayanin
Kai ya gyaɗa bai amsa da baki ba.
Suka cigaba da tattaunawa baya cewa uffan sai da ya gaji ne ya miƙe yayiwa Abba da suka fi kusa sallama ya fice.
Sashen Maamah ya nufa yana tafiya ne ba tare da waige waige ko kallon baya ba kanshi ƙasa har ya isa ya shiga parlorn da sallama, kan carpet ya hangi Ammar na karyawa ya girgiza kai ya nufi wurinshi ya zauna daga kan carpet ɗin yana tankwashe ƙafafu.
"Sai yanzu Ya Sheikh?"
Shirun seconds biyu har Ammar ya zaci ba zai ce mishi komai ba kan ya ji yana cewa
"Meyasa kake da baki ne?"
Ammar ya kalleshi ya kai loma
"Saboda in ci abinci"
Murmushi kaɗan Irshad yayi.
Bai sake magana ba sai ma motsa lips da yake kaɗan kaɗan Ammar ɗin ke faɗa mishi yayi mamaki da daga Safiyar Allahn nan media ta ɗauki dumi har wasu na cewa an ji wa Sheikh Irshad Omar Al-Noor rauni, wasu na cewa yana cikin mawuyacin hali har wasu na ikararin an kashe shi, ba yau ne farau ba duk wani motsinshi kaman jira media take za ta ɗauka, ba da sonshi hakan ke kasancewa ba amma bashi da yadda ya iya.
"Ka san me? Wlh har yanzu ina mamakin wannan yarinya da aka kira da DIVA wani irin nisa tayi haka? Ta wani ɓangaren kuma rashin tsoronta ya burgeni"
Idanu Irshad ya zubawa Ammar ɗin shi kuma daga ganin hakan ya san bai fahimci ma a kan waye yake magana ba.
"Ina magana kan wannan yarinyar da ta kori waenda suka tare mana hanya, ƙaddararta yayi gi..."
"Yar daba!"
Ammar yayi shiru yana kallon Shehi don da ya kira hakan bai kalleshi ba, seconds kadan tsakani ya ce
"Sai na fi gane wa, har me abin burgewa a wanchan kazantantaccen rayuwar? Wuƙa fah ta ɗorawa Malam Bala da niyyar illatasa, Allah kaɗai ya san alhakin da ta tarar wa kanta na bayin Allah, wannan ba kaddara ba ce kar ka ɗora mata ba komai ne yake kaddara ba, a shekarunta da wayonta a yanzu na tabbatar ta san daidai da akasin hakan"
Ammar ya ce
"Amma Irshad ka fa fi ni sanin babu kyau judging abu daga gani ɗaya, ba mu san background ɗinta ko environment da ta taso ba, definately akwai abinda ya jefa ta cikin wannan halin ruwa bai taɓa tsami banza ba amma dai hali ne kam mai matuƙar muni da hatsari"
Shehi bai ce komai ba, da Ammar ya gaji da magana shima yayi shiru ya san ba wai Shehin ya yarda ba ne, yana da wannan idan ya kafe kan ra'ayin shi bai cika uziri ba.
Maamah ce ta shigo parlorn a lokacin fuskar Shehi ta sake sossai itama da murmushi ta ƙaraso ta zauna kan kujerar da Shehin ke zaune gabanshi ta ce
"Barka da shigowa Babban malami"
Kanshi ƙasa ya ce
"Maamah mun tashi lafiya?"
"Alhamdulillah mun gode Allah"
Kan ya sake magana ta kalli Ammar.
"Kai kam ban san wani irin dan uwa ba ne kuma aboki, yanzu ka bar min yaro da yunwa kana ta cin abinci yana kallonka?"
Ammar ya ce
"Toh Maamah ai bai ce zai ci ba kin san shi ba'a mishi gwaninta"
"Au dama ban faɗa maka abincin tun asali don shi na yi bane ka zo zaka cinye masa?"
Shi dai Irshad murmushi yake don ya saba ganin wannan rigimar ta Ammar da Maamah, Maamah ita ce mahaifiyar Ammar amma kuma shi a wurinta ya tashi don ita da mahaifiyarshi da suke kira Ammiey twins ne kaman yadda Abba da Abbiey suke twins, Ammiey da Abiey suna da wani irin kawaici a kanshi hakan ya sa ragamar rayuwarshi duk a wurin Maamah ne, haka sauran sisters ɗinsu they are mixed up wasu yaran Maamah gabaɗaya a wurin Ammiey suke har mutane daga waje basa gane ma su waye ne yaran wane su waye yaran wance, wasu sun ce kamannin zuri'ar na asalin Fulani baya ɓuya.
Musamman Shehi da yayi rayuwa cikin Larabawa har ma ya saje da su don ko hausa yake za ka zaci larabci ne saboda yadda harshenshi ya karye zaman sama da shekaru Ashirin cikin Larabawa ba wasa ba
Maamah taje ta shiryo mishi abincin ta kawo da kanta, yayi mata godiya ya miƙa hannu ya wanke cikin bowl na wanke hannun da ta hada mishi da shi don da wuya ka ga yana cin abinci da cokali ya shiga ci da bismillah.
Bayan ya gama daga nan sashen Ammiey yayi anan ya gaisheta, ta amsa cikin kamalarta tana kallonshi, a koyaushe ta ɗaga idanu ta ga kyautar da Allah yayi mata sai ta ji natsuwa da sanyi na ratsa zuciyarta, ta kan tsinci kanta cikin yi wa Allah godiya da kuma yi mishi adu'ar samun mace ta gari ta ƙwarai mai halayya da dabi'u irin nashi su cigaba da haifar tsatson ƙwarai, jaje ta mishi akan abin da ya faru ya nuna mata adu'arta kaɗai zata cigaba da yi Allah ya katangeshi da duk wata fitina, sisters ɗinsu sun ta shigowa suna mishi gaisuwa da jaje amma a gajarce ya ke amsawa.
Daga nan sashenshi ya koma, ya zame jubba ɗin ya bar thob kawai da Ghutra ya nufi study table ɗinshi ya cigaba da research akan littafin da ya fara nazari don Asabar ne yana da sauƙin commitment.
****
Daga gidan Jagaban bata zauna ba ta yi wa sauran click ɗin sallama ta fice, cikin rashin tsoro da sabo da dare ta cigaba da tafiya sai da ta wuce akallah gidaje biyar ta tsaya jikin kofar wani gida da bashi da kyaure, zaure ne kawai a buɗe ciki ta shiga ta cigaba da tafiya hannayenta a aljihu tana isa tsakar gidan aka hasketa da toci hannu ta sa ta kare idanunta kan ta lailayo zagi ta buga.
"Wani ɗan abu kazan ne wannan?"
"Ubanki ne! Na ce Ubanki ne marar kunya fitsararra, wallahi na gaji na gaji da ganinki cikin gidana kina abin da kika ga dama, rumfar kasuwa ce gidan da za ki fita sadda kika ga dama ki dawo sadda kika ga dama? Ko da shi ke ba laifinki ba ne, laifin Zaliya ce uwaki ba? laifinta ne da ta kasa baki tarbiyar da ta dace"
Ta zuba mishi idanu na seconds.
"Malam Iro na fa sha gargadinka akan idan kana abin ka ka daina saka mahaifiyata a ciki yawwa, yawo kuwa yanzu na fara shi rashin tarbiya ai kura ba zata ce da kare maye ba..."
"Ke Zubaidah!"
Wata murya daga cikin ɗaki ta fito tana daka mata tsawa.
"Ashe baki da kunya? Ba mahaifinki ba ne?"
Taɓe baki tayi tana layi kaɗan kadan
"Mahaifina? Allah ya kyauta mijin Asawa ai ba uba ba ne da kanshi ya faɗa ya fi a kirga"
"Eh laifina ne a kullum ina ganin laifina tunda na auroki Zaliya kuma na ce na ji na gani zan riƙe miki yaranki, ni Iro ni ne mai laifi..."
Ya tashi ya shige wani ɗaki yana cigaba da mita.
"Kin kyauta"
Ɗakin da ta fito ta juya ta koma.
Wacce aka ƙira da Zubaida ta bi bayan mahaifiyartata ta dage labule ta shige, Maman za ta sake magana kenan ta ji an jefeta da kuɗi da sauri ta ɗauka.
"Ashe da abin arziki kike shine kika tsaya kina ta fitsara tsakar gida. Sai ki samu wuri ki kwanta"
Maman ta faɗa fuskarta fesss tana kirga kudaden babu ruwanta da tambayar inda ta samo.
******
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
Ƙarfe ɗaya ba ya amo by Gureenjoh
Daaɗin zama by Seemahwrites
Joda by Sadi-sakhna
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a tura shaidar biya ta
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
