Joda page 2 Complete by Sadi-Sakhna

 


👑 JODA 👑

Na 

Sadi-sakhna

Ƴar mutan Jama'are

THE TRIO OF TALES 

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey) 

@sadisakhna on Arewapen

@SAKHNA03 On Wattpad

09035784150 on Whatsapp

LITTAFI NA 1

*Harƙa ta (2)*👑

"Dan Allah kici abincinnan kada yayi sanyi kinji"

"Nakoshi ko naci ma amansa zanyi Aban Joda,zuciyata ta kasa sukuni ji nake kaman zata buga ta fashe. Bantaba sanin inason Ɗiyata ba duk da lalurar datake ɗaukeda ita sai yau,ita kaɗai ce wacce nake gani a matsayin cigaba na zuri'h ta,babu wanda yake ɗaukeda jini na sai ita,amma inaji inagani saboda dogaro da jahilci da kuma Al'ada za'a binne min ita tana numfashi,dama haka umman zakir taji da aka kashe mata ɗanta?"

"Dan Allah kidaina wannan sambatun haka,nace miki babu wanda zai kashe mana ita ki kwantar da hankalin ki kinji"

"Uhmm tohh mai zakayi,wanne mataki zaka ɗauka ka faɗamin ko raina zaiyi sanyi"

"In lokacin yayi zaki sani kedai ki tashi kici abinci ki tafi aiki kar a zargi wani abu,naji su Umman Sule ma sun zunɗenki ɗazu jiyama bakije aiki ba"

"Wanne aiki akeso naje ƴata tana wannan halin mai kamada mutuwa,wai mu ba mutane banene,ko dabba ƴar ta batada lafiya inaga ba'ayi mata adalci ba idan akace ta tafi aiki,ni ba inda zanje"

"Meyasa kikeda rikicewane Aminatou,nasan halinda kike ciki babu daɗi,amma bazaki yarda dani ba kiyi abinda nace,kinfiso ki sake jawo hankalin kowa kan abinda muke ciki ne. Idan kin yarda dani kitashi ki tafi aikinki,kekanki kinsan dabba ma tafimu a wanann rayuwar,Allah ne kaɗai yake kallonmu a matsayin bayinsa masu daraja,amma ba ƴan adam yan uwanmu ba."

A haka jiki kaman babu laka tana waiwaye tana kallon Joda dake kwance kaman mai bacci har ta fice daga cikin ɗakin.

Cikin harabar Fadar ta shiga,kana tabi wani lungu dazai kaita Turakar Garka (Gimbiya)Hamdiyyah. Matace Mai haƙuri da Sanyayawa na ƙasada ita,saidai Jakadiyarta kuma batada mutumci ko kaɗan,duk inda tasan inta bi zata taka wani to nan take bi. Yauma a tsaye take da jajayen kayanta anyi musu ado da kalar baƙi irinna sauran bayi,itakuma nata da ja ajiki yana nuni da shugabanci.

Tunda suka haɗa ido da Aminatou daga nesa gabanta yabada sautin dummm domin tasan ita da ita Allah ne kaɗai zai rabasu. Cikin sanyin jiki ta ƙariso inda take a tsaye tana sunkuyar dakai,yayin da itakuma take binta da wani kallo kaman taga ɗan tsako.

"Da izininwa baki zo aiki ba jiya,kodan kunga uwargijiyarmu bata damuwa shiyasa kuke cin karenku babu babbaka. Da akayi mana alfarmar zama wani sashe mu ƙirashi da namu sannan mu taho aiki da safe shine yabaku damar yin yadda kukeso? Wata ƙasar zaku samu hakane. Zakuwa ki fuskanci naki hukuncin"

"Kiyi haƙuri Jakadiya wlh ɗiyata ce batada lafiya,shiyasa bansamu damar zuwaba dan Allah kiyi haƙuri kiyimin rai"

"Dan ƴarki batada lafiya shine bazaki zo wajen aiki ba,kin manta da ko kece bakida lafiya dolene kizo ballantana wata ƴarki? Lallai kun samu ƴanci bayinnan."

Kallonta Aminatou takeyi cikeda ƙunan rai,saikace itama ba baiwar bace,wannan da itace sarauniya da tuni ta gasa kowa ta cinye.

"Wai ma wacce ƴar kike tunani,badai wannan tunkiyar ƴar taki ba da batada maraba da mutumtumi,wannan idan tamutu ma aikin huta zakiyi aikinki cikin nutsuwa,nima kuma zan huta dajin uzurinki a kullum"

Wani ɗaci Aminatou taji ya ziyarci maƙogaranta, babu abinda ta tsana irin a ƙira ƴar ta da wannan ƙasƙantaccen sunan,shin meyasa mutane suka manta da cewar itama uwace,idan suka ƙira ƴar ta da sunan zataji babu daɗi?

Cije bakinta tayi idanunta sun kaɗa sunyi jawur,gabaɗaya kunnuwanta sun daina ji ballantana tasake jin wata kalma daga bakin Jakadiyar. 

Firgit ta dawo hankalinta jin ihun da Jakadiya take mata.



"Wannan kallon da kikemin fah,ba tunkiyar bace ko ƙarya akayi ai gwara tunkiya ma za'a kaita kasuwa a sayar ko yanka,itakuwa fah dakike ta ɗawainiya da ita wani amfani zatayiwa kanta balle kema ta amfaneki,sai wahala dakike akanta wasu ma kina damunsu"



"Jakadiya duk abinda zaki faɗa dan Allah ki daina ƙiran ƴata da wannan sunan banaso,kuma da kike zancen amfani sai ɗanka yanada amfani zaka soshi,sannan akwai wanda in Allah yayi niyyar azurtashi da ɗa yake zabar wanda zai bashi ne. Abinda Allah ya jarabci ƴata dashi Jarrabawata ce kuma na karba hannu bibbiyu,na yarda Allah yanada kallona kuma zaimun Fasihnya da mafi kyansa a duniyarnan ko kuma a lahira"



"Iyeee lallai ke kinsan wanne kuskure harshenki yake faɗa,lallai kin ƙira mutuwarki ko kuma azabarki,ke zo nan je ki ƙiramin Sarkin zagi yanzunnan . Kice yazo yayiwa wata baiwa hukunci na bulala hamsin,ya taho da dorinarsa"



Da rawar jiki wata mai kaya irinna Aminatou ta matso jinjina kai alamar karbar saƙon kafin tasaka gudu zuwa wani bangaren.



Ita dai Aminatou tana tsaye a wajen ga rana tana cikinta ta haɗa gumi,ga tunanin halinda ƴar ta take ciki sannan kuma ga kallon zakici ƙwal ubanki ɗinnan yau.



Duguzun duguzun ya shawo kwana da wata Jar babbar rigar saƙi a jikinsa yana jijjiga wata ƙatuwar dorina a hannunsa,bayansa kuma wacce aka aika ta ƙirashi tana binsa da sauri sauri. Taraddadin dayake cikin zuciyar Aminatou na tunanin halinda ƴar ta take ciki ya zarce cin wata fargaba da hukuncin da Jakadiya ke shirin yi mata. Ji take idan da in anyi mata wannan dukan ƴar ta zata tashi to ashirye take ta ƙarbi ninkinsa ma.



Yana isowa wajen ya washe baki da suka haɗa ido da Jakadiya,itakuwa ganin kallon dayake mata yasa tayi fari da ido sai kace wata yarinya sannan tayi wata ƴar rausaya. Don kowa yasani Sarkin Zagi na ɗaya daga cikin wanda suke zawarcin Jakadiya bayan mutuwar mijinta a fagen yaƙi.



"Jakadiya sai anganki aga Gimbiya,idan ba a ganki ba babu mai ganin gimbiya,taka lafiya idaniya Mikiya mai kulada dukkan komai"



Ƙirarin duk da mai cika ma'ana ba amma babu laifi yataka rawar gani wajen fasa kan jakadiyar,take kuwa taji ta kamar a saman gajimare.



"Kaga ba wannan ba, wannan baiwar nakeso ya saitamin ta dawo kan hanya,wai har ni nayi zafin da zata dunga maidamin magana akan wata shanyayyar ƴarta da ko kaɗan bata kama hanyar shiga sahun mutane ba"



"Ehhh lallai ta tafka babban kuskure dole a ladabtar da ita tagane iyakarta"



Jijjiga bulalar yasakeyi tareda zare ido ya turbune fuska kaman bashine yake kafa fadarsa a wajen Jakadiya yanzu ba. Tsawar daya dakawa Aminatou ne yakasa hantar cikin ta ta kaɗa jikinta yafara mazari. Kafin tayi wata wata taji ya zage ya zuga mata bulalar hannun nasa.



Cikin gigita ta tsugunna a gabansa ta ɗaga kanta sama tana kallonsa,hannayenta dukka suna gadon bayanta tana ƙoƙarin sosa inda bulalar ta kwanta a jikinta.



"Kwanta kwanta!!! Ki ƙarbi hukunci ƴar jakar uba,daga kunga anayi muku sanyi sanyi saiku fara raina na gaba daku ko?"



"Kai kai la'ilah mai nene haka mai tayi maka kake mata wannan dukan kaman kasamu gardi ɗan uwanka"



Denti Hamdiyyah ce take maganar tana leƙowa ta turakarta jin hayani a ƙasan tagarta.



Cikin sauri yaja da baya ya tsugunna jikinsa yana mazari yana zazzare ido.



"Ranki yadaɗe Jiminar ƙasar Adik,wannan baiwa rashin kunya tayiwa na gaba da ita,wanda idan aka barta ta hanyar zuba mata ido zata iya fara maidawa manyan na sama sosai magana"



"Wannan ba Aminatou bace,a sanina tunda tatashi a masarautar nan bantaba kamata da rashin kunya ba,ko kuma naji labarin wani yakamata tayi masa ba.....saidai idan wani abunne yafaru daban. Kuma an faɗamin tunba yau ba kuna ƙiran ƴar ta da sunaye na ƙasƙanta,idan yau ma abinda kukayi ne to kuwa babu wata uwa dazata jure hakan. Ke Jakadiya ki gyara wajenann komai yakoma yanda yake.



Ke kuma Aminatou mai yake faruwa?"



Tsayawa tayi da murje murjen bulalan da sarkin zagi ya shimfiɗamata a baya jin Denti Hamdiyyah tayi mata magana. Allah yagani jininta ya haɗu dana matar,wannan dalilinne ma yasa sauran bayin suke hantararta ganin ana bata Abubuwa su ba'a basu. Kuma tafisu gaskiyane da riƙon amana,sannan ga aiki tsakani da Allah shiyasa Uwargijiyar tasu takeson aikinta har taki yarda ta saida ita ko kuma kaita wani bangaren daban. Da ƴarta tayi aure ma taso tafiya da ita,amma ta hana saboda tanajin daɗin aiki da ita,kuma tasan Aminatou bazata so hakan ba,tunda tanada aure kuma ga ƴa mai laluri.



A cikin nutsuwa ta zayyana mata abinda yafaru,duk da kuwa tana cikin halin ciwon bulalun data farasha.



"Ayya Allah sarki Allah yabata lafiya,ki tashi kije maza ki kulada ita harta samu lafiya saiki dawo na baki dama. Kekuma Jakadiya kishigo ciki inkin gama inada magana dake,sannan karki sake ɗaukan hukunci a hannunki a sashena,idan wani abu yafaru kizo ki faɗamin,bawai ki ƙirani wani can da baisan ciwon kansa ba yazo yana yiwa bayina hukunci ba."



Da sauri jin abinda Denti Hamdiyyah tafaɗa Aminatou tatashi tsaye zumbur takaɗe jikinta tareda yin Godiya sosai sannan tayi hanyar gida da sauri,ko takan su Jakadiya bata ƙara bi ba. Kamar kaza mai ƴaƴan daka ɗaure kuma aka saketa tabi bayan ƴaƴanta.



Tana gama faɗar hakan takoma ciki bayan taƙarewa Sarkin zagi kallon kaman taga mahaukaci,badan mugunta da shiga sha'anin bayi bata dameta ba ta tuni ta sutaleshi shima tasaka na gaba dashi sun hukuntashi. Dandai batason bayi suyita yamiɗiɗi da sunan ta kaman sauran abokan zamanta ne.



Tana wuce kuwa sarkin Zagi yaja ajiyar.



"Ke Jakadiya wannan wacce baiwa ce da uwargijiyarki ta muzantamu a gabanta haka?"



"Hmmm kaima ka faɗa,ai inaga bakaga komai bama,mu nan bayinda muke sashennan muna ganin abu,nice da kujerar Uwar bayinnan amma in a gaban Denti ne waccar munafukar har ta fini,kanaga hukuncin da akayi mata yasa da samu sassaucin da kowacce ta haihu bata samu ba? Ni kullum bincike nake na kamata da laifin da zaisa na kawar da ita dukkama,gata da iyayin addini kaman ta ɗauro masallaci a kanta,ko abu muka raruma aka raba da ita sai taƙi ƙarba wai ba haƙƙinta bane,da alama ma zuwa take tafaɗi mun ɗiba,shiyasa itace da gaban goshi,komai mukayi ba'a kallo sai nata"



"Ehh naga zahiri kam,gashi an muzantamu muna shugabanninta a gabanta,gaba ta ganmu ma dariya zata farayimana...dolene mu ɗauki matakin maganinta a masarautar nan,dan irinsu barazana ne ga ɗan matsayinnan da Allah yabamu ya ɗoramu akansu"



Wata baiwa ce da suke danga ɗaya da Aminatou ta matso inda suke tana ɗan sosa kai alamar rashin gaskiya,Sarkin zagi ne ta kulada ita yace.



"Ke kuma miye kike sussunne kai kaman an kama tsohuwa tana satar itace?"



"Uhmm Ran sarkin Zagi ya daɗe,dama nace nasan wani labari da in kukaji zai taimaka muku kuyi maganin Aminatou muma ko zamu samu mu samu shiga idan batanan"



"Lallai shiga manya ke asuwa,kedai faɗi ko hakan zaisa na fara ɗan ɗagamiki ƙafa a wani abun,ko kuma in labarin yanada matuƙar amfani a wajenmu na iya maidaketa wajena"



Jin abinda Jakadiya ta faɗa yasa da sauri kaman an sakawa recorder memory tafara zayyano labarin halinda su Aminatou suke ciki. Shuru sukayi suna saurarenta harta kai aya.



"Kai Sarkin Zagi wannan fah babbar damace dazan kawar da wannan baiwar,tabbas wannan labarine mai daɗi. Dan kuwa indai wannan magana ta kai kunnenta Uban doka dolene a zartar da hukuncin binneta indai har bata tashiba a gobe. Kai bama ga ita kaɗai ba inmunyi wannan aiki babbar shahada fah mukayi na kubutar da garinmu daga iftila'i,dan barin yarinyar nan a kwance dama ga tabin hankali babu motsi kaman gawa na tsawon lokaci babbar matsalace,kuruwarta yawo zata dunyi mana a saman gari tasaka a hanamu ruwa,dama ga damina ta gabato"



"Kaii kumafah zancenki haƙƙun,wannan ai ba abin boyewa bane,koma waye ba itaba dolene a zartar masa da hukunci kaman yanda akeyiwa kowa,kema menene ma sunanki idan wannan hukunci ya tabbata kinada babbar kyauta. Yanzunnan zanje ga Maga ɗaki,shi suna shiri da Uban doka,zai mika wannan lamari kotu a gobe ba sai an jinkirta ba."



"Shikenan kaga muma mun huta bibiyar da take yiwa yaƴanmu kalan ta koya musu dolantaka,ƴa kaman an toshe mata ƙofofin hankali,tana tafe tana haɗa hanya da dalalar yawu"



A bangaren Aminatou kuwa wani daɗi ne yajiyarci zuciyarta jin an bata damar taje tayi jinyar ƴar ta batareda tazo aiki ba.



A zaune ta iske kamaluddeen yana shafe jikin Joda da tsumma mai damshi,idanuwansa cikeda damuwa da zullumi,bashida burin dayawuce ƴar tasa ta tashi,koda kuwa zatayi masa wannan dariyartata da dukkan ƙarfinta,yayi kewarta sosai.



Ɗaga kai yayi ya kalli Aminatou wacce take tsaye a bakin kofa hannunta riƙeda asabarin(labulen da akayishi da zana) dayake rataye a jikin ƙofar saboda yakare hasken rana shigowa ciki.



"Yana ganki kin dawo harkin gama aikin?"



Kwashe abinda yafaru tayi tafaɗawa mijinnata,yana jinta har saida takai ƙarshen bayaninnata kafin ya numfasa kana ya haɗa da cewa.



"Wani lokacin kina da zuciya Aminatou kuma hakan yakan kaiki ki aikata wani abu da in yajuyomiki baxakiji da daɗi ba. Sanin kanki ne mutanennan ƙiris suke jira su tozartamu saboda damar da Allah yabasu akanka,yanzu badan kin samu uwargijiya mai Mutunci ba mai kike tunanin zai faru?........."



Tasan abinda yafaɗa gaskiya ne,ita kanta tasan bata iya rike fushinta indai akan zagin da akeyiwa ƴar tane,ita dai tunda tasamu am bata wannan ƴancin babu wanda yakaita farinciki a yanzun,gabaɗaya ta nemi zogin bulalar da sarkin zagi ya naɗa mata ma ta rasa. Dan kar a yita jan maganar yasa ta ɗaukowa kamaluddeen wata hirar daban.



"Dana shigo na kalli kana kallonta cikin damuwa da alamar kamar mai nazari kuma,shin wani abune yafaru dana tafi?...."



"Ahah ko ɗaya,kawai dai ina tunanin wacce mafita zan samu ne,nace ki barmin komai a hannuna zanji dashi amma alamu yana nuna zan gaza karbar yardar dazaki ɗoramini,lokaci dai tafiya yakeyi,ji nake kaman idan dare yashiga to karya waye,idan kuma gari ya waye to kar dare yakuma lullubeshi,duk wasu sa'o'i da daƙiƙu da suke wucewa ji nake kaman na jawosu su tsaya cakk a taredani. Banajin zuciyata zata iya jure saka ƴata da ranta a cikin rami na binneta kawai domin abinda wani ya yarda dashi na jahilci Aminatou. Hakan ba daidai bane kuma son kaine,mutum mutum ne miyasa in fushin kar wani bala'i ya afkune bazai hau kan kowa ba sai bawa.? Akwai ɗa sarkin garinnan da yayi jinyar doguwar suma babu wanda ya binneshi har saida ya shekara biyu ya mutu dan kansa,sai mune idan muka samu wannan matsalar za'a kasa haƙuri damu a kawar damu. Bamu ɗorawa jinyar Joda kowa ba,mun yarda zamuyi abinmu meyasa zasu rabamu da ita koda bamason hakan. Jiya da daddare naje wajen Abokaina nakejin Ashe Babawuro ya faɗawa kowa zancen ƴata sauranta kwana biyu a duniya,na yarda dashi har hakan yasa yasan halinda muke ciki,bansan miyasa ya zabi yayimin haka ba. Bamuda ishashshen lokaci komai ma zai iya faruwa."



Zuwa lokacin kuka Aminatou takeyi shabe shabe kaman mai zaman makoki. Matsowa tayi ta dafa mijinnata tareda sako kanta ta kafaɗarsa tana kallon jodan itama,wacce take kwance kaman mai bacci,amma ta gagara farkawa yau kwana shida. Tunda ta kalli halin karayar zuciyar da mijinnata yake ciki tasan abin ba ƙarami bane,yanemi mafita iya iyawarsa ya rasa.



"Aban Joda to yanxu yazamuyi kenan,shikenan muna gani za'a binneta gobe idan bata tashi ba?"



Shuru ne ya ratsasu,babu abinda yake tashi sai sheshsheƙar kukanta da kuma ajiyar zuciyarsa. Wasi wasine a zuciyar mai bata amsar,wanda lalume yake da neman shin wacce mafita kwakwalwar tasa zata miƙo masa domin yasamu yabata?.....kwatsam wata kalma ta fito daga bakinta wacce ta razana shi har saida hantarsa ta kaɗa,bai taba tunanin zata faɗi hakan ba.



"Aban Joda mu tattara kayanmu mu ɗauki ƴar mu mu gudu daga garinnan a darennan"



Diff yaji kamar kunnensa sun daina aiki,mai take cewa? Guduwa? Ko kaɗan shi hakan baizo ransa ba,zatonsa roƙo zayyi tayi har a jishi a karba a ƙyale masa ƴarsa da ranta.



"Ya ilahi Aminatou kinsan mai bakinki ya furta kuwa,guduwa fah......idan aka kamamu fah dukka zasu kashemu mu ukun,sannan a rataye gawarmu ana jifanta a tsakiyar gari har rana ta narka namanmu da kitsenmu ya zagwanye yabar kashi"


*********


Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....


DAAƊIN ZAMA by seemahwrite

JODA by sadisakhna

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by gureenjoh


*A whatsapp 

One 1k

Two 1800

Three 2400* 


*Telegram 

One 700

Two 1200

Three 1500*


Account details 

0545475847 

Gt bank 

Fatima Muhammad Gurin 

Sai a tura shaidar biya ta

09035784150

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post