Daɗin Zama Page 2 Complete by Saliha Ahmad Na'ibi Seemahwrites

 DAƊIN ZAMA🍁

Saliha Ahmad Na’ibi

   Wattpad and arewapen *@Seemahwrites*

#THE TRIO OF TALES 

_(Three minds, Three stories, One journey)_

Sincerely to Aunty Hauwa Yarima, Allah ya so ki da rahamar sa🤍

02… Sauƙa Ilham tayi daga bayan mashin ɗin da ya kawota.

Ta zaro kuɗin da ya rage mata a cikin purse ɗinta sabuwar naira ɗari biyun da Khausar ta bata da kuma wata tsohuwar ɗari, ta miƙa wa mai mashin ɗin ya karɓa ya soke a aljihu sannan ya juya da kan mashin ɗinsa yayi tafiyar shi. 

Juyawa tayi ta fuskanci asibitin lokacin da ta shaƙi dogon numfashi, a hankali ta furzar kana ta sake jan wani. Nutsuwa ce take so ta sameta ko yaya ne, kada ta daburce idan Hajiya surayyah ta tuhume ta dalilin biyota da tayi.

Girman asibitin da tsaruwar shi tun daga waje ya isa ya shaida mata asibitine ba na jinyar irin su ba, Allah yasa dai kada a tambaye ta abinda ya kawo ta don ta gaji da mako ƙarairayi.


Ta fara takawa tana jin kaman a kan ruwa take tafiya amma wannan zaɓin kawai ita da Muftee suke da shi.

Bata samu nutsuwa ba har saida ta hango kanta a farfajiyar asibitin. Abinda idanunta suka fara cin karo da shi kuwa motar Hajiya Surayyah ce fake a wurin da aka tanada domin adana motoci. Har murmushin jin daɗi saida ya bayyana a kan fuskar ta, sannan ta nufi inda ƙananun gravels suka lulluɓe ƙasan wurin cikin jin daɗi, sanin cewa idan ma ta shiga cikin asibitin ba sanin inda zata same ta zata yi ba. Amma babu yanda za’a yi tana zaune a wurin har ta fito ta tafi bata lura ba.


Saima ta samu bakin interlock da aka kewaye shukokin dake zagaye da duk kusurwan asibitin ta zauna, bata damu da cewa matsugunin ya kasa ma mazaunanta ba tunda dai ta samu tana fuskantar motar hajiya Surayyan dake tsakanin wata baƙar highlander da jan honda.


Ta shiga jira da daako cike da fata. Tabbas Allah bayi ɗaura ma bawa abinda ya fi ƙarfin sa, don haka tayi imani jinyar Muftahul khair bai fi ƙarfin ta ba, kuma zai kawo mata mafita.


Abinda bata sani ba shine mafitar zuwan shi a kusa yake ko a nesa? Da sauƙi zaizo ko da sadaukarwa? Abu ɗaya kawai ta sani; zata iya yin komai a kan yaronta matuƙar ba saɓon Allah bane ba zata yi. Shiyasa bata gaji da jira ba har duhun maghriba ya lulluɓe gari sanin cewa indai hajiya Surayyah tana ciki to zata fito, amma tana tsoron ta matsa da niyyar gabatar da sallah ta dawo ta samu babu motarta. Shiyasa ta cigaba da zama har hasken solar ya maye gurbin rana wurin haske farfajiyar. 


Babu haske a wurin da take daɓashe, kuma a sannu sauro suka samu matattara a jikinta suna zagaye ta saboda duhun hijabinta har ma da fatar jikinta, kukansu suke rerawa a cikin kunnenta tare da kai mata cizo ɗaya bayan ɗaya.


Lokaci ɗaya kiran sallan isha da ringing ɗin wayarta suka shiga kunnenta. Ta buɗe purse ta ciro wayan tana kallon ma’ajiyin caji da yayi jaa yana nuna buƙatar wutan lantarki da wayan yake da shi, kana ta mayar da dubanta kan sunan mai kira.



Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe, ta ɗora murmushi a kan fuskarta kaman mai kiran na zaune a gabanta, sannan ta ɗauka ta ƙara a kunne.


“Maama nah!” ta ambata tana kwaikwayon muryar ɗoki domin ta ɓoye mata damuwarta.


“Na’am Fidela ta. kina lafiya” aka amsa cike da karsashi irin nata ta ɗaya ɓangaren.


“Lafiya ƙalau maama. Ina Filiyan da Fitami.?”


“Ihsan tana hostel, Jawad kuma zuwa yayi ya ajiye mun uniform ɗin shi mai datti shine ana kawo wutan nepa na saka ya ɗauka ya fita ya wanke.” ta ambaci yaran nata da inkiyar su na ainihi a maimakon na yare, kana ta ɗora da “yaya jikin mai gidan. Kin samu ganawa da mutanen kuwa, na ji shiru tun safe baki kira ba.”


Jimm tayi cikin rasa tacewa. Ta ga ci ta ga rashi, ta kuma samun hope duka a yau kawai. 

Hala dai hajiya Surayyah ba mai fitowar yanzu bace ba ko kuma ma kwana zata yi a cikin asibitin tunda gashi dare har ya gama rufawa shiru. Awannin da suka rage mata basu wuce a ƙirga ba kafin a fara rabon tallaffin da safiyar gobe.


“Rabon mutum bayi wuce shi Maama, zan jira idan rabon mu ne duk daren daɗewa Allah zai kawo shi gare mu. Ki mana addu’a” tayi maganar cikin karyewar murya.


“Addu’a kullum a cikinta muke Fidela. Allah ya tallafa miki, ya tashi kafaɗun Ibrahim. Ke kuma Allah ya karɓa miki hakkin ki”


Ji tayi kaman kuka zai ƙwace mata da zancen Maaman, saboda ta taɓo mata inda yake mata ciwo. 


“A ce ka haifi mutum amma ka gagara ɗaukan ɗawainiyar shi bacin kana da halin hakan Maama? Ya Hashim ko tausayin yaron nan bayi ji? Ni ba abun ya tausaya mun bane tunda ya san ba wani sana’a nake da shi ko wani hanyar samun kuɗi ba, amma ya sake mun jinyar yaron shi babu kunya ba tsoron Allah?. Wallahi da zan iya da bari zanyi Muftee ya mutu saboda uban shi ya gagara sauƙe hakkin da ya rataya a wuyan shi in ga yanda za’a yi. Amma ɗana shine zuciya da jini na, nima ba zan rayu ba idan babu shi” ta ƙarasa kukan na cin ƙarfin ta saboda ɗamewar da zuciyarta keyi.



Ta ji lokacin da Maaman ta sauƙe numfashi kafin muryarta ya sake fitowa ta cikin wayar. “Kiyi haƙuri ki cire damuwar shi a ranki Fidela. Gani nan jira nake yi ɗaukan adashe ya juyo kaina in turo miki ki rage wani abun. Filiyan ma idan tayi hutun makaranta sai ta ɗan zo ta taya ki da ɗawainiyar asibitin kema ki samu ki huta”



 “A’a Maama, na san kema kina buƙatar kuɗin, tunda Allah ya ɗauke mana Taa bani da mai kula mun da ku yanzu. Ni daga wurina zan cigaba da ƙoƙarin wani abu har Allah ya kawo mana mafita. Amma kin yi naki ƙoƙarin Maama, baki haife ni ba amma ko kusa ban tashi da maracin uwa ba har bayan ran Taa kuwa, babu komai tsakani na dake sai addu’ar alkhairi da ƙauna mai tarin yawa. Shi kuma Ya Hashim Allah ba zai barshi ba, tunda bayi zalunci kuma bayi son mai yin ta, da taimakon shi ko babu Muftee zai rayu Insha Allah.”


Rarrashin ta Maaman ta cigaba da yi da bata baki har ta rage kukan kafin tayi mata sallama da cewar duk halin da ake ciki ta sanar da ita.


“Toh Maama na cinye miki kati ma”


“Kin jiki.” Tace da sautin murmushi.


Itama sai ta samu kanta da murmusawa. “Allah ya saka da alkhairi Maama ina ƙaunar ki”


“A gaida mai gidana”


“Zai ji in sha Allah”


Da haka Maama ta datse kiran, sai itama tayi tunanin ya kamata ta kira taji jikin Muftee ɗin gashi Khausar tayi mata yakanar rashin kira ta tambaye ta lokacin da zata dawo.


A agogon wayan ta ga lokaci karfe 8 har da minti 40. Ga jan layi na cikin akwatin cajin ma ya dauke ya dawo empty.


Haka dai ta danna kiran layin Khausar ɗin da fatan katin wayan ya basu daman yin magana mai tsawo.


“Hello Aunty Ilham.”


“Khausar kun wuni Lafiya?”


“Alhamdulillah aunty, an samu nasara?”


“Tukunna Wallahi khausar, har yanzu ban samu ganawa da ita ba”


Khausar ta amsa da “hasbunallahu wa niimal wakeel. Toh Allah yasa jinkirin ya zamo alkhairi”


Jin ana mata kashedin ‘one minute remaining’ ya sanya ta cewa “ina yarona?” Bayan ta amsa addu'ar da ameen.


“Gashi nan” cewar Khausar tana cire wayan daga kunnenta ta mayar nashi.


“Mimi!”


A wuni guda kawai da bata ji muryar shi ba a yanzu sai take jin kaman wani ɓari ne a jikinta da ya shanye ya dawo aiki da siririyar muryar shi ya shiga kunnenta.


“Mufteen Mimi yaya jiki?” Ta amsa tana daɗa kwantar da murya saboda jikinta da take ji kaman ana zuba mata ƙanƙara.


“Mimi kin….” Ɗiff taji maganar ta ɗauke. Ta ciro wayan daga kunnenta ta kawo shi gaban idanunta don ganin ko katin ne ya ƙare amma hasken wayan ya ƙi kawowa koda ta danna.


Sai ta ji duniyar ta sake mata zafi, komai ya sake tsayawa, a hankali kuma fatan ta ya fara narkewa kaman daskararren kitse a ƙasan rana.

….


Ƙarasowa tayi jikin gadon da ya kifa kan shi. A hankali ta kai hannunta ta taɓa saman kafaɗan shi don haka ya ɗago ya fuskance ta.


A maimakon ta buɗi baki tayi magana sai ta nuna rigan jikin shi da yatsar ta, kana ta mayar da manuniyar kanta ta ware sauran yatsunta tana goga tafin hannunta sama da ƙasa a jikinta alamun ya je yayi wanka. Sannan tayi hand movement yanda mutum keyi idan zai cire riga kana ta haɗe tafukan hannayen ta biyu ta saka a ƙasan habarta na dama ta ɗan langabar da kanta ta ɓarin tare da lumshe idanunta na abinda bai fi daƙiƙa guda ba.


Ya fahimci abinda take nufi tunda communication method ɗin shi ne dama. Amma ya fi fahimtar dalilin da ya saka tayi amfani dashi wajen isar da saƙonta, sanin cewa ya tsani ana mishi magana da sign language. 

Saboda Ikram dake barci ne, kada maganan su ya tashe ta, dukda kuwa bata sanye da hearing aid ɗinta amma sautin zai iya damunta. 


Da hannu shima yayi mata bayanin zai jira har sai ta tashi tukunna, domin sign ɗin da tayi masa na nufin yaje yayi wanka idan yana da niyyan kwana a asibitin ne.


Ikram dake barci da ɗaurarren hannu ta nuna wannan karon sannan ta sake maido da hannun fuskarta ta ware idanunta kaɗan, ta bi ta nuna kirjin ta kana ta gwada kujeran da yake zaune a kai.


Tana nufin zata zauna a nan har ya je ya dawo koda ikram ɗin zata farka.


Tunani ya tsaya yi na ƴan daƙiƙu yana jin kaman ba zai iya ba dukda shima nauyin kayan jikin nashi ya dame shi, kuma tun safiya yake sanye da su, amma idan Kiki ta buɗe ido ta buƙace shi fa?.


Wannan karon da baki ta ambata mishi “ina nan, ba zan motsa ba har sai ka dawo” maganar tata ya fita ba tare da sauti ba ko kaɗan amma tunda idanunsa na kan laɓɓen ta tana da tabbacin ya fahimta.


Ya miƙe cike da sanyin jiki idanun shi a kan ƴar shi. 

Aunty Surayyah ta nuna kanta ta nuna shi kana ta nuna ƙofar fita ma'ana suje ta raka shi.


Sai ya girgiza kai Alamar A'a. Ya gyara mata kujerar a gaban gadon ta zauna Sannan ya juya fita. Ya kuma yi namijin ƙoƙari da bai juyo ya sake kallon Ikram ba har ya janyo ƙofar a bayan shi ya rufe.


Ƙaran shigowar saƙo da ya shiga kunnen Aunty Surayyah bayan fitanshi ne ya sanya ta miƙa hannu ta ɗauko wayan dake gefen flask ɗin ruwan zafi dake ajiye a saman drawer tare da magungunan Ikram.


Wayan shi ne ya manta, amma ta san bai yi nisa ba idan tayi sauri zata cim mishi kafin ya bar asibitin. A saboda haka sai ta ɗauka ta fita daga ɗakin da sauri.


“Yauwa kun gan shi, Wannan da ya wuce, shine sarkin masifan ɗazu da rana” wata nurse kenan take gwada ma ƴan uwanta Abdulhameed da ya wuce ta gaban su yanzu, domin su samu fuskar da zasu ɗora ma labarin da suka samu tun shigowar su dutyn su na night.


“Haba! Gashi kaman ba zai yi magana ba ma” ɗaya a cikin su ke miƙa wuya kaman zata tsinke shi don ta samu idanunta su sake ɗauka mata fuskar Abdulhameed sosai.


“Kutt kin ji bala’i? Ai yanda suka mayar da asibitin nan kaman gidan biki, shi kuma yana tsaye sai zazzaga yake yi kaman lawyern da aka bawa cin hanci” hannunta duka biyu a ƙugu tana ɗan girgiza take tabbatar musu da gaskiyar ta.


“Uhmm ni naji ma wai wasu a cikin ƴan uwan nasu suna cewa wai Yarinyar Shegiya ce, basu yi aure da uwarta ba aka haifa masa ita.”


“Ke haba?!” Suka riƙe baki cikin mamaki.


“Walla….”


“Ku gode ma Allah da baya ji, tabbas da kun gane kuran ku.” cewar Aunty Surayyah tana tsayuwa a gaban su.


Sosai suka firgita har suna niman hanyar watsewa kowa taje ta kama abinda ke gabanta.


“Gashi”


Dake a tsarge suke, duka sai suka juyo a tare suna kallon wayan da take miƙo musu ƙirar samsung z Flip dake a rufe.


“Karɓa ki kai mishi.” Ta bawa ta farkon sannan ta juya ta koma ciki. 


Da sassarfa ta bi bayan shi don har ya fice daga reception ɗin asibitin ya nufi wurin da ya faka motar shi.


“Malam.. Hey… ka ji….” Irin kiran da take masa kenan tunda ba sanin sunan shi tayi ba har ta cim masa amma yana kan tafiya bai tsaya ba kuma bai waiwayo ba.


Tunawa da tayi matar ɗazu tace baya ji ya sanya ta sha gaban shi tana fitar da numfashi. Irin kallon da yake mata gashi ya haɗe gabas da yamma yasa kawai ta miƙa mishi wayar ba tare da tace komai ba.


Ya kalli wayan, kafin ya miƙa hannu ya karɓa ya buɗe ta. 

Hoton Kiki da ya cika screen ɗin ya tabbatar masa da nashi ne. 


Bai saki fuskar ba yace “Nagode” sannan ya raɓa ta ya cigaba da tafiya, ta bi bayan shi da kallo har ya buɗe ƙatuwar motar shi ya shiga sannan ta juya ta koma ciki kafin a nime ta.


Kunna motar da yayi ya sanya hasken fitilun gaba da suka kunnu Suka dalle mata idanun da suka yi luhu-luhu ga hawaye dake kwaranya daga cikin su.


Tayi saurin saka bayan hannayenta ta kare fuskarta.


Saidai ya riga da yaga fuskar.


Kuma ya gane ta.


Ilham ce.


A cikin kanshi sai yaji kamar an kirashi, da muryar nan


"A Moher..."


Muryar da itace karshe wajen kiranshi da wannan sunan.


Akwai wasu mutane da kan shigo rayuwar mu kaman da kuskure. Wasu bayan kallo ɗaya ba zamu sake ganin su ba har ƙarshen rayuwar mu. Wasu kuma zamu yi ta gamuwa da su a hanyar wucewar mu na yau da kullum amma bamu taba magana da juna ba.

Wasu wani abu zai haɗa mu na ɗan lokaci, daga nan kuma shikkenan anyi rabuwar karshe.

Akwai kuma wa’inda a ajiye zancen sabo ma a gefe, su ɗin ɓarin rayuwar mu ne, ko bugun zuciyar mu, ko bangon jinginan mu madafan mu, ko kuma sune gishirin rayuwar tamu baki ɗaya da babu su babu ɗanɗanon rayuwa. Amma haka a lokacin da muke musu kallon ƙarshe a duniya sai muga kaman zamu sake.


Su kuma wa’inda suka shigo rayuwar mu kaman da kuskure sai Allah ya ƙara haɗa mu da su a gaba, mu fara tunanin a ina muka san su?.


Saidai Ilham tana cikin Ɓarin memories ɗin da ba zai taɓa mantawa ba har zuwa ranar da ƙasa zata rufe idanunsa. Kuma bayi fatan ya manta ɗin, bayi ƙoƙarin mantawar, saboda memories ne masu matuƙar ciwo da kuma muhimmanci a rayuwar shi.


Daga wannan sati ɗayan ne ƙaddara tazo da bargonta mai nauyi ta lulluɓe shi, bata bar mishi ko ramin shaƙar numfashi ba. 


A sati dayan ne yake iya tuna farin cikin Nne, ɓacin ranta, tashin hankalinta, damuwarta, dariyarta da kukanta duk cikin sati ɗaya kacal. Kuma a lokacin Ilham ta faɗo ciki from nowhere, daga nan kuma bai sake ganinta ba sai a yau. 


Bayan tsawon shekaru goma sha biyu.



~•~•~•~•~•~•~•

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....



ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh 

JODA by Sadi-sakhna 

DAƊIN ZAMA by Seemahwrites 


*A whatsapp 

One 1k

Two 1800

Three 2400* 


 *Telegram 

One 700

Two 1200

Three 1500*


Account details 

0545475847 

Gt bank 

Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post