*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites*
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
04…“Subhanallah Fidela!” Maama ta ajiye wuƙar da take firan doya dashi ta miƙe, ganin yanda suka shigo tana ɗingishi, ga farin ƙyalle mai jini riƙe a hannun Aliyyu.
“Yaya Ka kaini ciki” Ilham tayi magana tana numfarfashi kaman mai naƙuda a tsaye.
Buge hannun da ta riƙe sa dashi yayi “dalla sake ni” yace yana watsa mata harara. Sai ta koma jikin Maaman ta lafe a jikin hannunta tana ajiyar zuciya.
Maama da zuciyarta ke cike da zullumin abinda ya samu yarinyar da yanzu aka turata makaranta ta dubi Aliyyu tana tallafe Ilham a jikinta tace “me ya same ta ne?”
Cike da takaici yace “Tuntuɓe fa tayi Aunty!.” sannan ya mayar da dubansa kan Ilham yana ɗaga hannu sama “Wallahi yanzu sai na kikkifa miki mari ki samu dalilin kuka da tushe.”ya jefar da farin socks ɗin a wurin, ɓacin rai ma ya saka ya manta ya wuce bai gargaɗeta kada ta labarta ma Maama abinda ya faru ba don ya san halinta da barbaɗen zance.
Maama ta kalli safa mai jinin da ya jefar a ƙasa da kyau, sai a lokacin ta fahimci menene. ta sauƙe ajiyar zuciya domin tayi tunanin wani cutarwar ne mai girma ya samu Ilham.
“Sauran kaɗan fa da na fasa kaina a jikin dutsen Maama, saboda yanda yake ja na kaman zai tashi sama. Kuma ciwon da zafi sosai ai kinga yanda yayi jini sosai ma” tayi maganar tana jan hanci tare da matsar ƙwalla.
“Sannu ki shiga ki cire hijabinki ki kwanta, bari na soya doyan baban ku sai a saka miki”.
Bata bari farin cikin da ya cika zuciyarta ya saka murmushi ya bayyana a leɓen bakinta ba, domin Maama tana ganin fara'ar ta fa toh shikkenan ta warke. Don haka ta fara ɗingisawa har ƙofar parlourn Maaman, tayi sallama ta ɗaga labulen ƙofar ta shiga sannan ta saki yanayin fuskarta.
Dogon kujera ta ɗale ta miƙe a kai bayan ta zame hijabin wuyanta, tana jin wani yanayi mai daɗi yana shigarta jin yanda gidan yayi shiru kowa na makaranta, ba kamar kullum ba da su Ihsan ke takura mata.
Har barci ya fara ɗaukarta zuwa garin nisa, ƙamshi ya ziyarci ƙofofin hancinta lokacin da Maaman ta shigo riƙe da ɗan bowl mai ɗauke doya, wanda aka dafa sannan aka naɗe shi a cikin ƙwai aka soya.
Muƙut taji ta haɗiyi miyau, daman yunwa ya fara ƙwaƙular cikinta.
“Fidela Tashi”
Bata bari Maaman ta maimaita ba ta miƙe zaune ta saka hannu biyu ta karɓi bowl ɗin.
Maama ta koma saman fridge ta ɗauko roban yaji sannan ta dawo tana faɗin.
“Sauce ɗin da nayi bayi da yawa ne na juye ma Taa aka kai mishi office, ga yaji”
Hannu ta saka ta karɓi roban tana furta kalmar Godiya, ga yawunta dake kan tsinkewa. Babu ɓata lokaci ta fara dandala ma doyan Yajin Maama mai ƙamshin tafarnuwa tana saita ma cikinta.
“A wani chemist ne aka wanke miki ciwon?” Maama ta tambaya tana zama a gefenta, idanunta a kan yatsar dake naɗe da bandeji.
Langabar da kai tayi “Na gefen makarantar mu, kuma Sunce wai kada nayi dogon tafiya sai nan da sati ɗaya” ƙaryar da ta gama shiryawa tun a hanyar dawowar su gidan ya biyo bayan amsar tambayar Maama.
Maama ta jinjina kai “Allah ya sawwaƙe. Daga gobe sai Taa yana sauƙe ki idan zai wuce”
Ta waro idanu “Maama tun kafin 7 fa yake tafiya, Taa da ko karyawa baya yi a gida?, idan naje makaranta ƙarfe 7 Wallahi saidai ayi ta saka ni shara tunda ba'a fara zuwa ba, kuma ma baya nan lokacin islamiyya, Gashi a lungun da muke bi shortcut Wallahi akwai ƴan shaye-shaye, yau har haɗuwa muka yi da wani ya tsare yaya Aliyyu ya bashi kuɗi ya siyo masa wani abu a shagon malam Sama'ila ya dunƙule a hannunsa ya koma ya bashi.” bata shaƙi numfashi mai tsayi ba saida ta samu ta dire.
Kafin Maama ta gama sarrafa zancen a cikin ƙwaƙwalwar ta Aliyyu da ya dawo kashe wa Ilham warning ya faɗo ɗakin ko sallama babu.
“Munafuka annamimiya, laifi na ne da na ɗauki kuɗina na bayar aka suturta kuturun ƙafar ki ban bari ya ruɓe aka guntule ba, amma babu damuwa akwai gaba. Kuma na siyo ɗin zo ki dake ni uwata, makira kawai.” Ya galla mata harara kafin ya saki labulen parlourn ya juya yayi tafiyar shi.
Da ya shigo ko kallon Maama bai yi ba, amma a cikin kalaman shi ta fahimci saƙon da nata ne kuma ta ɗauka, don haka tunda ita ba uwar shi bace babu ruwanta da abinda yake yi ko menene.
“Kinji shi ko Maama”
Ta juyo ta kalli ƙwallar da ya taru a cikin idanun Ilham. “Kema ina ruwanki? Ba na hana ki shiga uku da faɗi ba'a tambaye ki ba?”
Daman ta sani sai ita kaɗai Maama zata yiwa faɗa. Ko tayi daidai ko bata yi daidai ba idan ya shafi sauran yayyenta saidai tayi mata faɗa ita kaɗai su ba zata ce musu komai ba.
Cikin kasashshiyar murya tace “Maama har bani kuɗi ɗan shaye-shayen yayi fa kafin yaya Aliyyun ya karɓa ya siyo masa”
Ta waro idanu cikin tashin hankali tace “kuma kin karɓa?”
Sauyawar yanayin Maaman lokaci guda ya sanya ta saurin ajiye bowl ɗin a gefe ta shiga girgiza kai da sauri. “A'a Wallahi ban karɓa ba”
“Toh daga yau ban yarda ba ban amince ke kaɗai kina bin hanyar ba. Ko ki koyi shiryawa da wuri kina bin sauran ƴan uwan ki ko in faɗa ma baban ku.”
zaburowa tayi ta riƙe hannunta tana ƙara girgiza kai “wallahi ba zan sake ba, dan Allah Kiyi haƙuri kada ki faɗa mishi”
Yanayin kallon da take mata da wannan raunin a cikin idanunta ya tuna mata da shekaru tara baya, lokacin da aka kawo ta wannan gidan a matsayin amaryar mahaifinsu. Yayin da bata saka sauran yaran shi a cikin idanu ba sai bayan kwanaki, Ilham yarinyar shekaru uku a lokacin ne kawai tazo jikin gadon da take zaune a wannan daren, ta samu wuri ta zauna daɓas a saman carpet da aka lailaye ƙasan ɗakin da shi tana leƙowa ta kasan mayafin da aka lulluɓe ta, koda suka yi ido huɗu a lokacin da irin wannan kallon a fuskarta.
Shiyasa bayan duk wani rikici da tashin hankali da ya biyo bayan karɓanta da tayi ta ƙi ta haƙura da yarinyar. Ba domin zallan jinta a rai da take yi kaman ƴar da ta haifa ba, harda dalilin raunin da take gani a cikin idanunta.
…..
“Idan kuka samu abun nan yayi popular kuka san irin kuɗin da zaku samu?. Kuma daga nan baku buƙatar biyan kuɗin recording, saidai ma studios suna niman ku suna biyan ku tun kafin kuyi musu waƙan su sake ma duniya.
Amma dubu goma zallan recording zai muku gaskiya, banda sabon sauti shima tunda kun ce tape har biyu kuke so.”
Fire dake faman zuƙe sigarin da ya zara a aljihun wandon uniform ɗin Abdulhameed yana sirka musu iskan wurin da hayaƙi jira yake yi ya samu inda zai kashe wutar sigarin a goshi ko ƙeyar mai studio ɗinnan.
“Amma yaya batun wanda kace idan muka haɗo kuɗin zaka haɗa mu yayi mana advertising na music tape ɗin?” Abdulhameed yayi tambayar cikin lalama, tunda ba zai fara waƙa bane don ya kunna a ɗaki yaji shi kaɗai.
Yanda ake saka na wasu a Radio kowa yana ji haka yake so shima a saka nashi. Yana da burin har wata rana a haska shi a gidan talabijin domin haka gajen haƙuri ba nashi bane, sanin cewa waƙar su ba shi zai tallata kan shi ko ya siyar da kan shi ba sai sun kama ƙafar masana wa'inda suka fisu experience a music industry.
Mutumin ya dube shi a cikin idanu “A moher! babu abinda baya yiwuwa idan akwai kuɗi. Kai idan kuɗin ka sun isa har Lil Wayne idan kana son gani zaku gana har kayi collaborating da shi ma. Don haka kuje ku ƙaro kuɗi ku dawo indai da gaske kuke kuna so ku zama manyan rappers a san da ku a ko ina.”
Fire zai yi magana ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mishi hannu.
“Nawa zamu ƙaro?”
Mai studio ɗin ya ɗan tsuke baki yana tunani kana yace “kun ga tunda ga na recording yanzu sai a samu na sound kaman dubu biyar na advertisement ma dubu biyar”
“Amma hidiman ka akwai rainin hankali a ciki. Ba kai kace mana 10k zai yi mana komai da komai tunda ba babban production bane ba daga farko?” Cewar Fire a harzuƙe.
“Abubuwa ne suka canza, idan ba zaku iya ba ga kuɗin ku kuje ku nemi wani studio”
Fire ya miƙa hannu zai karɓi kuɗin. Lallai bai san yaya ma aka yi suka haɗa wannan ɗin a cikin kwana biyu kacal bane yake kawo musu wani maganar banza. Bayan Abdulhameed da yayi ƙuru ya haɗo dubu shida, ya san mahaifin shi na can yana niman sabon wayar shi da ya salwantar a dalilin sauran dubu huɗun da ya cika musu.
Dakatar da shi Abdulhameed ya sake yi, shi ba mai zuciyar haƙura da abinda yake so cikin sauƙi bane.
“Shikkenan, idan muka kawo wani dubu goman ka tabbata zaka cika alƙawarin ka?”
Ya gyaɗa mishi kai yana lumshe ido cikin tabbatarwa da kuma jin daɗin damfaran samarukan da yake shirin yi cikin sauki.
“Zamu kawo, ka cika alƙawari ko kuma zaman shagon nan ya gagare ka. Bani daba amma shi zai fara gwadawa a kan ka” ya ƙarasa magana yana nuna Fire wanda ya ɗaga rigan jikin shi karamin wuƙan da ya soke a kunkumin shi ya bayyana.
Abdulhameed ya juya ya fice daga studio ɗin Fire ya rufa mishi baya bayan ya gyara zaman rigan shi.
“A moher yanzu kam saidai mu fasa gari ayi a nemo kuɗaɗen nan”
“Ba zaka yi abinda bayan mun shahara zaka ɓata mana suna ba.” Ya amsa da harshen turanci idanun shi kafe a kan baƙin canvas ɗin ƙafar shi.
Tunanin ta inda zai fara yake yi, bai san ta ina zai fara nimo dubu goma ba tunda babu wani hanya na neman kuɗi da ya sani bayan idan yana da kowani irin bukata ya tambayi Nne ta bashi. Amma tunda ta nuna mishi bata amince yayi waƙa ba babu yanda za'a yi ta ɗauki har Naira dubu goma ta bashi, kuɗin school fees ɗinshi na term kenan, kuma makaranta mai tsada Nne ta saka shi a hakan.
Ya luma hannu cikin gashin kanshi yana furzar da numfashi. Ba zai sake ɗauka mata kuɗi ba, wannan ma da amincewarta kuma bata masa iyaka ba shiyasa ya ɗauki daidai abinda zai biya mishi buƙata, amma ba zai taɓa yiwa Nne sata ba, bayan duk ƙoƙarin da take yi a kan shi.
Ita kaɗai tana mishi gatan da masu uwa da uba basu dashi, ba zai mata sata ba bayan yasan irin wahalan da take yi a kansa shi kaɗai.
Sai ya zaro blackaberry ɗin shi a aljihu ya miƙa ma Fire “Lukman nawa za'a sayi phone ɗin nan?”
Karɓan wayan yayi ya jujjuya a hannun shi sannan ya mayar mishi yana faɗin, idan tayi daraja ne dubu 3, da kwalinta kuma zata iya kaiwa 3500 ko dubu 4 idan an samu mai so kai tsaye.
Bayi da wani zaɓin da ya wuce ya tambayi Nnen dai, Ko wayar shi ya siyar ita ɗince zata nemi kuɗin siya mishi wani, kuma yana da tabbacin ta siye wayan nan ninkin kuɗin da zai siyar sau uku.
“Ka san me? mu haɗu a wurin da muka saba, zuwa gobe zan yi ƙokari inzo da kuɗin.”
….
Suna saka ƙafa a cikin gidan dariyar da Ilham take ƙyalƙyalawa ya fara shiga kunnuwan su, kafin suka hango ta zaune a kan farin kujerar roba ta ɗaure tray ɗin silver a kan cinyarta tana taya Maama tsintar wake.
“Nidai ba zance a siyo kaji saboda ciwo a ƴar yatsa ba ahtoh, tunda ciwon bai kama bakin ki ba idan ya dawo sai ki faɗa mishi da kan ki” muryar Maama ya fito daga kitchen ɗinsu na tsakar gida wanda ta shiga ɗaura sanwan abincin dare.
Saida Ilham ta ƙara ƙyalkyala dariya saboda son lallaɓa ta take yi kana tace “kema fa zaki ci idan aka yi farfesun Maamana”
“Ba sai a hana ni ba?.” Tayi maganar lokacin da ta fito, sai taga Ilham ko rabin gama gyaran wake bata yi ba.
“Har yanzu kuma baki gama tsince ɗan wannan waken ba Fidela?. Mijin ki sai ya fara gyangyaɗi kafin ki dinga kai mishi abinci ko?”
Baki ɗaya hankalin su bai kai kan mutanen da suka shigo musu gidan kai tsaye babu sallama ba.
Sai wucewarta suka gani fuuu janye da akwatinta bayan ta ja dogon tsakin da yayi nasaran tattaro duka hankalin su ya dawo kanta.
Ita ta fara wucewa ɗakinta sannan masu rufa mata baya suka biyo sawu.
“Duniya daɗi, tunda an samu an kori ƴar uwar mai gida sai bararrajewa kawai.” cewar ta biyun su tana ƙarewa simintin dake lailaye a tsakar gidan kallo yanda yake a share a wanke.
Basu ishi Maama kallo ba sai karɓan tray ɗin hannun Ilham tayi ta koma ɗakinta dashi ta bawa Iska ajiyar su.
Ganin haka Ilham ma ta miƙe zata bi bayanta. Ɗan ɗaɗin da take ji na yau hayaniyar gidan ya ragu na ɗan wani lokaci yana gushewa, daman su Iman da Ihsan suna dawowa daga boko basu daɗe ba lokacin Islamiyya yayi suka tafi banda ita, yayyenta maza kuma ba masu zaman gidan a ko yaushe bane dama, suna da wani matsugunin a family house ɗin Baniza. Shiyasa yanayin sosai yayi mata daɗi sai gashi wannan matar da idan ba'a ji muryar ta a maƙota a kowace rana ba bata jin daɗi ta dawo.
“Ke! Baki iya gaisuwa ba ko? Saboda Jamila ta koya miki raina iyayen ki.”
Ta ɗan turo baki “A fa fiyan goggo Fatu, a fa fiyan goggo Halima” ta gaida su ina wuni da harshen jenjo.
Fatun bata amsa ta ba sai harara da ta watsa mata, tana riƙe da sabon kwali mai zanen keken ɗinki ta wuce ɗakin da matar farko da zura key ta buɗe daga gefen na Maama.
“wuce muje ki taya mu shigo da kaya” goggo Halima ta umarta.
Sai tayi saurin nuna mata yatsar ta “Ƙafa na akwai ciwo, Taa yace in huta shiyasa ko makaranta ban je ba yau”
“Babu wanin nan lalaci kawai kike fama dashi, Ni zan so ganin wanda zai kai zuciya nesa ya tattare ki a ahalin Baniza” ta ja tsaki ta koma wurin shigo da sauran shirgin da suka zo dashi, itama Ilham sai ta saɓule jiki ta koma parlourn Maama ta cigaba da kwaciyarta.
Duk kaiwa da komowa kuwa sai sun yiwa Maama habaici ta hanyar aibanta Ilham. Har yarinyar ta ƙare ta fara zubar da hawaye.
Maama Bata kula ta ba saboda itama zuciyar ya iso wuya.
Freezer ɗinta ta buɗe ta ɗauki ƙullin naman miya guda ɗaya wanda ta tafasa ta saka yayi kanƙara, sai kuma ta ƙara wani saboda Ilham da taji ciwon da take riritawa da kuma kishiyarta da ta dawo a yau tunda yanzu sanwar harda ita, ta haɗa da waken da ta ƙarasa tsincewa ta fita dashi.
Kaya sosai suka baje a tsakar gidan har jikin bangon ɗakin Maama, A dakalin shiga parlourn Taa kuma suka samu matsuguni ana ta ɗaura sabon keken ɗinki.
Tayi musu kallo daya ala dole sannan ta juya harƙan gabanta.
“Ahalin Baniza dai muna da tushe da asali sai Usmanu mai idon gane-gane da ya je ya ɗibo mana tsintacciyar mage. Ina fatan dai kina kwana da tashi da sanin ko da aure ko babu Shafa’atu dai jinin Usman ce, duk aikin sihiri da tsafi baki isa ki raba su ba wallahi.”
“Halima kin san dai ko bayan ran Usman baki da gado a gidan nan ko? Toh ɗaga hankalin na menene?” Ta tanka ganin shiru ba zai fishsheta ba tunda sun ƙare sun shigo da ita kai tsaye.
“Au ke har ta rabon gado kike tun da rai da lafiyan shi shiyasa kika shiga kika fita sanda kika shiga tsakanin shi da Shafa ko?, toh da mu kike zancen Jamila dan Allah kada ki fasa”
“Ku dai zauna ku tambayeta dalilin da yasa tayi yaji. Lokacin da suka warware abar su ina nawa ɗakin ina kula da tarbiyyan yara na, don na samu darasin cewa girma da hankali abubuwa biyu ne mabanbanta. Fidela kuma in sha Allahu rabbi yanda sauran ƴammata suke auren soyayya itama shi zata yi, ba wanda yaranku zasu dinga koro mana ita ko su gagara zuwa biko ba sai ta dawo da kanta”
Idan sun jawo tayi musu gori Laifin su ne da basu bar rikicin su a iya tsakanin su yanda suka saba ba sai sun taɓa mata yarinya.
“Wa ma zai ɗauki tsiyarki? Ai tun ranar da ta fara kallon ki a matsayin uwa muka cire ta daga cikin mu, bamu maraba da mugun Iri.” Sai yanzu Fatu ta magantu.
Shafa da ta zare ɗankwalin kanta ta ɗora a ƙugu ta ƙaraso gabanta tana faman hura hanci “Kuma dai soyayyar ita ta sanya na shigo gidan nan ko shekara baki rufa ba gida ya dawo nawa yara suka dawo nawa. don haka duk wani taggu da munafurcin ki nan gani nan bari ɗumamen mayya, Usmanu ya ɗauko kainuwa dashen Allah.”
Maama bata ji ko ɗarr da yanda take faman muzurai da hura hanci ba, domin idanma ta kai ga kacamewa Shafa’atu shaida ce a kan yanda zata ɗagata ta nana da ƙasa.
“Ai soyayya idan ya wuce wanda yayi sanadin raba Usman da ahalin Baniza ƙarya ce” ta faɗa da murmushi a saman fuskarta, wanda yayi nasarar cusa ma Shafa takaici tayi kururuwa ta ruƙo wuyan riganta, suna shirin kaurewa suka jiyo muryan shi.
“Kai! Kai!”
Maama da take fuskantar ƙofar shigowa idanunta suka sauƙa a kan shi cikin fararen kaya da ya fita dasu a jikinsa riƙe da briefcase ɗin shi.
Girma da kuma shekarun shi sun nuna ƙwarai a kan fuskar shi dake bayyana rashin jin daɗin yanayin da ya dawo ya riski gidan a ciki.
Shafa da ta bashi ƙeya ta juyo ta fuskance shi a lokacin da zuciyarta ya shiga bugawa da karfi.
Ya faɗa mata idan ta tafi kada ta dawo masa cikin gida tunda ita bata da sirri, kuma koda a waya bai taɓa kiranta ba tun bayan samun saɓanin su har zuwa yau, shiyasa da zaman jira ya isheta ta nema wa kanta mafita ta tattaro ta dawo in yaso sai ayi yanda za'a yi.
“Sannu da dawowa” Shafa ta gaida shi kanta a ƙasa tana ƙoƙarin kada muryarta ya bada ita yayi rawa a gaban kishiya gashi ita ko iya gaishe shi bata yi ba sai wucewarta da tayi ta cigaba da harƙan gabanta.
Koda ace ran shi ya ɓaci da banzatar dashi da Maama tayi toh bai gwada a kan fuskar shi ba, sai ma share gaisuwar Shafa da yayi, ya amsa nasu Fatu da “lafiya” kawai yana kallon yanda suka baje kolin su a hanyar wucewar shi sai ya wuce ɗakin Maama kawai ya duba Ilham da aka kira shi a waya aka sanar mishi ta samu rauni, dalilin shi na dawowa gida da wuri kenan.
````````````
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
