ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.
*SHAFI NA ƊAYA*
*SHIMFIƊA*
Farar mota ce mai matsaikacin kuɗi ƙirar lexus ke tafiya cikin natsuwa babu gudu bare rough driving, daga gani matuƙin ba yaro bane ko kuma ya iya kasancewa yaron amma mai tarin sani akan harkar tuki da kuma dokokinta, idan ka tsananta nazari kuwa zaka fahimci ana bin motar a hankali ne saboda wanda ake tuƙawan ba abin wasa ba ne ko na ganganci.
Daga cikin motan mutum huɗu ne, ɓangaren mai zaman banza akwai wani matashin saurayi da ya fi yanayi da ɗalibin neman ilimi, sanye da jumpa mai sauƙin kuɗi har da hula rungume da wasu tarukuce na briefcase, Laptop da sauran gadget.
A baya ɓangaren hagu nan ma wani matashin ne amma da alama zai iya girmewa wanda ke zaune daga gaban a shekaru, fari ne sanye da baƙar Thobe (jallabiya), ya ɗora hular taɓani-ka-ji-hadisi fara a kanshi mai matsaikacin gashi, fuskarshi cike da saje haka kuma hankalinshi gabaɗaya na ga gefenshi da magana mai sanyin amo ke tashi cike da wani irin natsuwa da waenda ke cikin motan ba don sun natsu kuma sun kasa kunne ba babu abin da zai sa su ji me yake cewa.
Mai maganan dake zaune daga ɓangaren dama ya ɗan muskuta, tare da ambaton Allah ya yi shiru tamkar mai nazari sai kuma ya cigaba da magana a hankali.
Duk inda kake neman natsuwa da kamala a kallo ɗaya da zaka yi wa wannan bawan Allah ka same su ka gama, daga yadda yake zaune za ka fahimci dogo ne, yana da matsakaicin jiki amma da alama ƙarfaffe ne, yana da haske fari ne fat, fuskarsa da cikakken gemu wanda da alama ba'a taɓa shi iyakaci gyara, idanunshi sakaye da wasu fararen madubi amma hakan bai hana bayyana natsuwa da zurfinsu ba.
Sanye yake da Grey Thobe ya ɗora baƙar shara sharan alkyabba irin ta Larabawa wanda ake kira (jubba) a kai, kanshi akwai Ghutra(wannan gyalen da aka san Larabawa da ɗora wa a kai mai kalar ja da fari da ya zauna mishi sossai a saman ta kuma akwai Agal (wannan baƙin abu mai yanayi da gammo wanda ke hana Ghutra faɗuwa idan ana iska) agogo mai sauƙi amma tsadar a bayyane take ɗaure a tsintsiyar hannunshi, hannunshi ɗaya jikin motar ɗayan na daga kan kafafunshi yana cigaba da yi wa na gefen magana.
"Ammar ina fatan ka fahimta?"
"Eh Shehi, In shaa Allahu za'a yi komai yadda ka ce"
Kai ya gyaɗa kan ya mayar da idanunsa kan titi ya cigaba da azkar cikin natsuwa don shi ma'abocin yawan zikiri da salatin annabi ne hakan ne kan katangeshi da duk wasu surutai marasa dalili.
Wani kalar wawan birki matuƙin motar ya ci. Ammar da yake danna waya ya ɗago da ɗan hanzari.
"Ya dai Malam Bala?"
"Malam Ammar ina ga fa 'yan fashi ne a gabanmun nan, gashi sun rufe hanyar"
Malam Bala ya faɗa sai dai ko ɗarr dukkansu babu wanda ya ji don ba yau suka saba encountaring irin waennan ɗin ba tunda aikinsu ne na kai wa dare wurin wa'azi da karatuttukan Shehi na dare.
Ko kan wani daga cikinsu yayi yunƙuri an fara bubbuga musu glass kuma tuni Matasa har huɗu sun zagaye motar da Malam Bala ya dannawa General lock.
"Ka ga irinta ko Irshad? Sai da na faɗa maka securities are very important to you amma ka ƙi aminta, yanzu idan wani abu ya sameka fa?"
Ammar ya faɗa duk tashin hankalinshi na bayyana Dukda adduna ne da sanduna yake hange hannayensu, alamunsu duk sun bayyana tsananin maye da ficewar hayyaci.
Sai a lokacin Shehi da Ammar ke yi wa magana ya buɗe idanu ya kalli situation ɗin cikin natsuwa.
Ya kalli Ammar
"Rayuwa da mutuwa duk na Allah ne Ammar"
Jarumtakarshi da tsantsar tawali'unshi na sake bayyana tsantsa a kalaman bakinsa.
"Duk da hakan wani sa'in ba mutuwar ce abin tsoro ba wahala ake ji wa"
Ko kan Ammar ya gama rufe baki an bugi glass na gefen Malam balan sai da ya daddatase, innalillahi wainna ilaihi rajiun duk suke maimaitawa, kan su ajiye ma an sake kaiwa glass ɗin duka da sandar gora tuni ta tarwatse.
"Kai Tsoho me ya biyo da kai hanyarmu a lokacin farauta?"
Wata kakkauran murya marar daaɗin ji ta faɗa tana haske su da tourch light, maganan su ya sa hankalin Ammar ya ɗan kwanta da alama zaune gari banza ne, 'yan daba masu kwacen waya da sauransu, wayanshi yake kokarin kunnawa ya kira 'yan sanda cikin dabara aka bugi glass ɗin ɓangaren shi ma ya rushe har yana ji mishi ciwo.
"Hasbunallahu wani'imal wakeeel.."
Kalmar da ta fito a bakin Shehi kenan don idan akwai abin da ke zama weakness ɗinshi to cutar da makusancinshi ko masoyinshi, yana ƙoƙarin buɗe kofar ya fita don basu duk abin da suke nema ya ji wata murya ta shiga ratsa kunnuwanshi.
Mace?
Ya raya a ransa yana juya fuskarshi inda sautin Muryar ke fita bayan ya kai idanunsa kadan ya ga time wurin karfe ɗaya da wani abu na dare.
"Kaiiiii....wasu ƙananun ƙwarin ne nan?"
Yadda Muryar ta fita babu abin da zai hanaka fahimtar mammallakiyar Muryar a Buge take, kuma cikin wani irin salo na dabanci sai dai zaƙin Muryar bai ɓuya ba sam.
Waenda suke jikin motan ne suka juya gareta suna hasketa idanunsa suka samu nasarar sauƙa a kanta.
Ya subhallah!
Ya ambata a ransa, wani cargo baggy trouser, sai sweeter hoodie mai hula jikinta baƙake, kanta sanye da facing cap da ya rufe rabin fuskarta sai ta ɗora hulan rigan a kan facing cap ɗin, hannunta wani coke ne da ba tantama a surke yake da wani abin.
Abin da ya ɗaga mishi hankali tabarbarewar tarbiyar wannan zamani, mace ta tsinci kanta cikin wannan kazanta ba ƙaramin abu bane ga malamin addini irinshi.
"Ke!"
Ɗaya daga cikin waenda suka tare su ya faɗa yana sa hannu a baki alamun mamaki kan ya cigaba.
"Babawo... ka ga wata gara chan wai da mu take?"
Tsaki ta ja tsiriri ta matso sossai kan ta sa hannunta ta ja hoodie ɗin kanta idanunta dake a lumshe cikin maye amma tsaff kanta ya gama ɗauke wa don tana cikin hankalinta suka bayyana ta kallesu.
Zare ido ɗayan yayi
"Kaiiiii.... Gayuuuu wallahi DIVA ce..."
Bata ce komai ba wasu gayu huɗu da mata uku a bayanta duk cikin shigar da zai tabbatar maka thugs ne, kowa kuma ka bincike shi ba ka rasa mugun makami a tare da shi suka bayyana.
"Ku bar nan...!"
Ɗaya daga cikin mazan ya faɗa cikin kakkausan murya.
"Tuba muke uwar ɗaki, ai ja da ke sai ɗan wahala ko mai kararren kwana! Allah ya taimaki shugaba..."
Hannu ta ɗaga kaɗan ta nuna musu hanya fuskarta babu digon fara'a ai tuni suka yi gaba don babu ɗan daban da bai san sunan DIVA ba da click ɗinta waenda suke tamkar yayyunta amma kaman bodyguard suke a gareta umurninta suke bi a komai, kuma su ne ƙawayenta abokan hiranta, yana wuya ka ga Diva na magana idan ba da su bakwan nan ba to Babanta... shiga komarta dai dai yake da yanke kauna da rayuwa, ko bata ɗauki mataki ba Jagaban Uban daban gabaɗaya garin Kano shi ne Babanta dole ya farauceka ko ina ne ya yanke maka mummunan hukunci, bare ita kaɗai ta ishi gayya, wargaza taro ce da idan tayi juyi sai an bata wuri Dukda matsayinta na mace wasu kan ƙirata kwaruwa don fitinanta ya fi ƙarfin giwa.
Idanu ta zubawa Malam Bala.
"kai dattijo! ka kiyaye fita a irin wannan lokaci na dare da duk karnuka suke waje, idan yau ka taki sa'ata gobe zan iya wucewa tamkar ban ga me ke faruwa ba...gayun nan kuma...ehh ya nee...ina fata kana fahimta?"
Tana maganan ne cikin wani salo idanunta suna lumshe wa da buɗewa da kansu.
Tsantsar mamaki ya kama su, amma Malam Bala ya daure ya ce
"Ɗiyata mun gode, amma don Allah da za ki yiwa kanki faɗa wannan rayuwar bata kama...."
Muƙuttt haka maganan ya koma tamkar an tura shi jin sauƙar wata kyakyawar WUƘA mai sheki saman maƙogoronshi.
Muryarta ya ƙara kaushi, tana mishi wani jan kallo da har Ammar da Imam sun razana ta ce
"Ko da kuskure ka sake buɗe baki da niyyar min wa'azi sai na tsinke maƙogoronka na rantse da Assamadu!! Naaa daɓa ma wannan wukar na ga gatanka"
Bai yi magana ba hannunshi dake kan stiring ne ke wani irin rawa, tayi tsaki tare da janye wukar ta nuna hanya
"Ware..."
Idanunsu ne suka sarƙe saboda shi mamaki da tsoron Allah duk ya rufeshi, wani ɓangaren tausayi ne, idan yana jin labarin akwai 'yan ta'adda bai san abin ya kai har mace ma ta zama shugaban 'yan dabar ba don daga reaction na waenda suka soma tare su zaka san sunanta ya jijjigasu.
Kallon seconds biyu yayi mata saboda wani irin mamaki na iya dorawa mutum kaman Malam Bala dattijo wuka a makogoro ya rufe shi.
Ita kuwa ba zata ce ta ga na bayan motan ba, bayan wucewansu ta cigaba da tafiyanta da gayunta yadda ta saba na maza kuma 'yan daba kaman yadda take'yar daba itama, cikin unguwar su ne don basu yi tafiya mai nisa ba suka isa wani gida matsakaici, gini ne na block amma babu plaster haka babu penti sai dai akwai gate mai girma da ƙarfi kalar Ja, karamin kyauren ta tura babu wuta solar ne kunne hakan ya haska mata tsakar gidan da kaman rana ne maza ne kala kala a ciki ana shaye shaye da cha-cha.
"Barka DIVA! Barka KWARUWA!"
Kalaman da ke ta tashi kenan bakunansu cikin yanayin tsantsar dabanci.
Hannu ta ɗaga tayi crossing suka amsa
"Chauchauuu... Eeeyyy mana"
Tayi murmushi ta juya ga gayunta
"Sai Allah ya kai mu"
"Mu kwana lafiya Diva"
Suka haɗa baki wurin faɗa don sun san ba sake fitowa zata yi ba kenan, ta nufi karamin barandar ta haye ta tura kofar parlorn ta kutsa kai babu ruwanta da sallama.
"Baaba"
"Ƴar Baba!"
Wani rikakken murya ya amsata ta riga ta ga abinda yake ɓoye wa don haka dariya kawai tayi.
"Babana na kaina... A cigaba da sana'a"
Tana kai nan ta wuce su don zaune yake da wasu mutane biyu diloli ne da suke zuwa karbar kwaya wurinshi, ɗakinta ta tura ta shige bata damu da rufewa ba don ko kuda ne Jagaban ba ya bari ya sauka kanta bare ita kanta hatsari ce.
Ba rayuwar da ya so zaɓa mata ba kenan amma bahaushe ya ce barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba.
Gado ta faɗa ko boots na kafafunta bata cire ba ta shiga bacci irin na maye.
****
Allah ne ya kawo su gida lafiya don Malam Bala ko uffan bai sake cewa ba yana ji Imam da Ammar suna tattauna batun wacce aka kira da Divaa amma ya kasa furta ko A shi da ya gama ganin mutuwa ganin idanunshi.
Irshad Al-Noor kuma dama sun san ba tankawa zai yi ba shiyasa Ammar ya kama Imam suke ta maganan, Horn nasu shi ya tado mai gadi ya zo ya buɗe tamfatsatsen kyauren gidan na Alhj Omar Al-farouq mai kamfanin Twins Enterprises, gida ne mai Girman gaske, gida ne da kallo daya zaka mishi ka fahimci daɗɗaɗden kuɗi ne ciki ba sababbin arziki ba, an zuba kayan alatu iya ganin ido.
Yana da gine gine manya manya kuma hakan bai tare faɗi da girman gidan ba, gaban wani building suka yi parking Imam ya fito da sauri ya buɗewa Shehi kofa, sai da ya ɗan ɓata lokaci kadan yana kamalla Adu'a kan ya zura kafafunshi dake cikin simple shoe na maza na kamfanin Gucci da ya bayyana kyaun kafafunshi da kaman baya taka ƙasa ya sauƙa, sai da ya tsaya da kyau ya gyara jubba ɗin jikinshi kan ya taka cikin natsuwa ya isa wurin Malam Bala da ya fito yake shan Iska Ammar kuma na kallon barnar da suka yi musu.
"Malam Bala kana lafiya dai?"
Muryarshi mai cike da natsuwa ya fita cikin kulawa.
"Ba dai ƙalau ba Shehi yau na ga abin da ya fi ƙarfin kakata"
Cikin jimami da tsoro yayi magana don Allah ya gani ya ji tsoro, cikinshi wani irin ƙugi yake ba zai manta da mutuwar da ya ga gilmawarta kan idansa ba, 'yan daban nan zare musu imani ake don ta kashe sa da wannan kaifaffen wuƙar ba komai ba ne.
"Tsoro halal ne! Amma karka manta da ambaton Allah a yayin da wannan tsoro na abokin hilitta ya ɗarsu a ranka"
Ya faɗa yana kokarin wucewa don shiga ɓangaren shi.
"In shaa Allahu Allah gafarta malam, Mu kwana lafiya"
Ammar ma ya iso yana ce mishi
"Sai Allah ya kaimu Shehi"
Kai kawai ya gyaɗa, Imam ya bi shi da abubuwanshi.
Malam Bala fita yayi ya nufi gidanshi dake nan cikin Layin, Ammar kuwa ciki ya wuce don anan sashenshi yake kasancewar shi Cousin kuma amini na kut da kut da Irshad Al-Noor.
Imam kuwa bayan ya zube mishi abubuwan daga parlor ya juyo ya fito, shima waje yayi yana yin sallama da mai gadin don gidansu na dalibai na nan gefen gidan wanda akwai su dayawa daliban ilimin Shehi da kan zo daga garuruwa daban daban saboda ɗaukan karatu, nauyin su da komai a wuyan Shehi yake zama bai taɓa bari sun shiga yanayi ba, kuma suna kwasan ilimi daidai gwargwado ya kan ce musu yana hidimta musu ne saboda kanshi ba don su ba saboda duk wani ilimi da suka koya daga gareshi muddin sun isar to ladan shi a wurin ubangiji ya fi abin da ya basu suka ci a cikinsu har bayan ranshi.
Bai zauna a parlorn ba ya wuce sama, wani parlorn da ya fi yanayi da study room saboda tarin littatafan addini da kuma qur'anai Dukda yana da study room amma ya fi gane parlorn saman tunda shi kaɗai yake rayuwa sai hidimtawa addini da ubangijinsa.
Kai tsaye ɗaki ya wuce da sallama kan lips ɗinshi, a hankali yake zame komai na jikinshi sai da ya saura doguwar farar cotton wando da farar singlet kan ya nufi toilet.
Ya jima ciki kan ya fito a kimtse cikin fararen kayan bacci masu fadi kan dresser ya je ya fesa turarukanshi na Oud masu sanyi da nauyi wurin shaka.
Parlorn ƙasa ya koma ya ɗauko laptop ɗinshi ya dawo saman a kan gado ya zauna tare da saka glasses ɗinshi ya buɗe ya fara nazarin wani littafin addini, komai nashi cikin natsuwa da kamala yake yinsu, ya san idan da zai duba parlor akwai abinci da Maamah zata aiko amma babu abin da zai iya ci a yanzu don haka dabino da ruwa ya sha bayan tsawon lokaci yana duba littafin da harshen larabci kan ya rufe.
Suratul Mulk da Rahman ya karanto da kai cikin wani irin Muryar qira'arsa mai sanya natsuwa da tada tsikar jiki kan yayi sauran adu'o'in bacci ya kwanta ta hannunshi na dama, dama ba wutan ɗakin ya kunna ba dim light ce ya barta kunne kasancewar ba daidai ba ne kwana cikin duhu mai tsanani da ba'a iya kallon tafin hannu.
Babu bata lokaci yayi bacci don kwakwalarsa babu space na wani tunani a lokacin tsantsar gajiya ce da jiki kan yi bayan doguwar hidima na yau da kullum barin ma irin nashi.
********
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a tura shaidar biya ta
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
https://chat.whatsapp.com/KYfUvRMZrw25zbahNgj4SC?s=cl&p=i&mlu=4&amv=1
