Daɗin Zama Page 1 Complete by Saliha Ahmad Na'ibi Seemahwrites


DAƊIN ZAMA🍁

Book 1

   Saliha Ahmad Na'ibi Seemahwrites

Women of Words Writers

THE TRIO OF TALES

(Three minds, Three stories, One journey) 

Disclaimer: Ban amince a sauya min littafi ta ko wace irin siga ko a ɗaura min a wani channel na youtube ba tare da izini na ba, yin hakan babban kuskure ne kuma zai sanya na ɗauki tsatstsaurar mataki domin haka a kiyaye

Any resemblance to any figure or event, deceased or living is purely coincidental

Special thanks to Addah Ramlah (Mai dambu)

Lubna Sufyan 

Sanah S matazu 

Abdulaiimar

And my pen sisters Janafty and Maryamkitty💕

Sincerely, To Aunty Hauwa Yarima. Allah ya so ki da rahamar sa🤍

بسم الله الرحمان الرحيم

*Ga wanda ya rayu a cikin kalamaina tun kafin na rubuta, wanda ya kasance tsakanin kowani layi na wannan labari. My dear Brother Muhammad Inuwa Ahmad, wanda Allah ya jarabta da nakasar kurmanta ba don bayi ƙaunar shi ba. You’ll always remain an irreplaceable treasure in our lives, a beloved person in our hearts*

 01….Lokaci ne da rana take baza hasken ta a sararin samaniya, zafinta kuma ya sanya wa’inda Allah ya horewa na’aurar sanyaya wuri kunnawa, tare ɗage gilashin motocin su domin samun sauƙi. 

Saidai irinta wa’inda ke cikin napep, da ma wa’inda suke kan mashina da kekuna a cikin cunkoson, har yakan kai su saka hannu a kan fatar jikinsu su sharce zufan da yake tsatstsafowa, bayan zafin da abubuwan hawan su ya ɗauka a dalilin tsayuwa na tsawon lokaci.

Hayaniyan da ake yi na buɗe hanya bayi samun shiga kanta saboda damuwan da ya riga ya cika shi fall. Idanunta suna kafe a kan wasu yara da aka sallamo daga makaranta, suna tafe tana bin su da kallo yayin da suke hira da ƴan uwan su cikin nishaɗi da ƙoshin lafiya. 

Har saida suka ɓace ma ganinta, sannan ta mayar da ganin nata kan wani ƙaramin yaro dake sanye cikin sabon uniform riƙe da blue ɗin lunch box shima sabo, yana tsalle-tsallen shi a harabar ƙofar makarantar su. 

Murmushi ne ya suɓuce mata ba tare da ta sani ba, a hankali ta furta “kaman Muftee na.” tana da tabbacin ba zai wuce shekaru uku zuwa huɗu ba.

Ta rungume envelope ɗin da take riƙe da shi a ƙirjinta, tana cigaba da kallon yaron cike da sha’awa har wani mutum ya nufo shi. Yaron kuwa yana hango shi ya fara murna da tsalle, daga inda take tana iya jiyo sautin ƙaramin muryar shi yana faɗin “oyoyo Abba!”.

Mutumin ya ƙarasa ya ɗauke shi ya cilla shi sama ya caɓe farin ciki bayyane a kan fuskarsa. 

A gaban mashin ɗinsa ya ɗaura shi, yaron yana ɗaga hannu ma sauran ƴan makarantar su baban ya kunna mashin ɗin suka juya hanyar da zai kaisu gida wanda shi babu cunkoso a kai, suka tafi cike da farin ciki wanda zafin rana bai kai ya narkar da shi a cikin zuƙatan su ba.

Ɗumin hawaye ta ji a kan fuskarta, bata damu ta goge ba ta maida dubanta gaba domin ganin yaya cigaban ɓude hanyar yake tafiya. Saidai cece-kucen da ake yi tsakanin mai babban motar da ya biyo hanyar da ba tashi ba da nufin sauƙe kaya a gaban wani babban shago, da kuma mai mashin ɗin da a garin kauce masa ya bugi napep ɗin wani har ya cire masa madubi bai nuna alamun mai sasantuwar yanzu bane.

“Komai na rayuwar nan fa ɗan haƙuri ne. Da sun buɗe ma mutane hanya ne mu wuce uzururrukan gaban mu” 

“Hajiya toh ke zaki biya shi ne idan bai tsaya ya karɓi hakkin shi ba?” mai napep ɗin da suke ciki ya juyo ya fuskanci dattijuwar dake zaune a tsakiyar su yana sosa kunnen shi da wani ƙaramin kara da ya ɗauka a ƙasa.

“Toh mu menene namu a ciki da za’a tare mana hanya?” ta mayar mishi da da martani. 

Budurwar dake ta ɗaya gefen dattijuwar kuwa hankalinta a kan wayar hannunta sai faman jero tsaki take yi.

Rayuwa kenan, kowa da abinda ya dame shi.

Ta sake maida dubanta kan envelope ɗin dake hannunta. Ita kuwa da sun san girman uzurinta, da shi kaɗai zai sanya su yayyafa ma zuciyar su ruwan sanyi su bude hanyar nan.

Ba abin tace zata sauƙa daga nan ta ƙarasa da sawayen ta ba saboda akwai sauran tafiya a gabanta sosai. Kuma bata da kuɗin tare wani abun hawan a gaba, wannan ma saida ta haɗa da canjin hannun Khausar kafin ta samu wanda zai ishe ta zuwa da dawowa.

Fatan ta bai wuce idan ta samu ganawa da wa’inda zata je wurinsu ba su amsa buƙatun ta. Da sun ceci rayuka har biyu kuma zata ƙare rayuwarta tana gode musu.

Daga wani ɓangaren kuwa, akwai wanda da gaske yana da tabbacin cewa nashi uzurin, idan aka haɗa na duka mutanen dake da niyyar bin wannan hanyar a wuri guda, ba zai kai kaso ɗaya bisa goma cikin nashi ba.

Shiyasa bayan faman danna horn da yake yi yana cika musu kunne, har wasu na haƙura da sanyin na’urar motocin su na ɗan lokaci su fito cikin zafin ranar domin ankarar dashi gajen haƙurin shi, ta hanyar rage nasu ɓacin ran a cikin muryoyin da suke ɗaga masa.


Ko a jikin shi, domin ba jin su yake yi ba. kasancewar shima kamar su, gilashin motar shi a rufe yake.


“Da ana filfili a wuce da baka saka wa taka motar fuka-fuki ba?” cewar wani yana ƙarasowa ɓangaren da yake saka ran hango matuƙin motar, ya ga wani mai ido da tozalin ne.


A ɗan tsakanin aka samu nasarar lallaɓa masu rikicin da su koma gefe a sasanta, hanya ta fara buɗewa, wa’inda ke ta gaba-gaba suka fara kunna abun hawan su da shirin barin wurin da zaran sun samu dama.


Saidai su jiran daman suke yi ya iso gare su da kan shi. Amma ga wanda yake ganin duk wani daƙiƙa da ya ɓata a hanyar tazara ne mai yawa yake ƙaruwa tsakanin shi da isa ga zaren da ya ɗinke rayuwar shi, ya hana shi yagewa filla-filla a lokacin da yake tunanin asirin shi ya gama tonuwa duniya ta yi mishi tsirara. Mutum irin wannan ƙirƙiran dama yake ma kan shi, koda kuwa a lokacin kowa ya tabbatar masa da ba zai yiwu ba.


Hanyar da faɗinta ya bada damar wucewar mashina da kekunan yara ƴan makaranta ne kawai, ta cikinta ya hango faragar da shima Highlander ɗin da yake ciki zai wuce. Don haka bai yi shawara da kowa ba ya bawa motar wuta tare da matse horn, a lokacin da ya zugi gudu sauran ƙadan yayi ciki da mutumin da ya tunkaro motar, shikuwa ya saka kai ba ji ba gani.


Ba zallan na tsakiyan cunkoson wa’inda har iskar wucewar motar tashi saida suka jita a fuskokin su, ga ƙirjin su dake luguden farbaga, da godiya ma Allah da ya sanya bai bi ta kansu ba. Har su da suke gafen hanya saida suka bi ƙurar da ya rufawa motar baya da kallo baki sake, tuni ya riga ya ɓacewa ganin su.


 “Ku ga wawa jahili” “ga wani banza mara hankali” 


Kaɗan kenan daga cikin kalmomin aibantawa dake fitowa daga bakin wasu kafin ƙurar ta kai ga lafawa. Amma marasa lokacin ɓatawa su ma sun bi jagorancin shi ne sau da ƙafa suka ɓulla hanyar da ya buɗe musu don ɗorawa a kan sabgogin rayuwar su bayan ɗan tsaikon da aka samu.


Har zuwa lokacin da suka isa wurin da ta kwatanta mishi, bayan sun sauƙe budurwar nan a ƙofar wani shagon kwalliya, mai napep ɗin da ya ɗauko su bai fasa mita a kan motar da ya wuce su ɗazu ba. A ko wani layi na cikin zancen sa kuma sai ya zagi masu ƙudi da iskar da ya ɗebo su.


Da a cikin nutsuwarta take, da ta ce mishi ba don wasu masu kuɗin ba, da wasu da yawa daga cikin wa’inda Allah bai horewa wata mafita ba baza su rayu ba. 


Irin su Muftee.


Sauƙa tayi ta biya shi hakkin shi, kana ta juya ta nufi masu tsaron wurin da ya dace da kwatancen da aka yi mata, tana ƙoƙarin ciro takardan dake cikin envelope ɗin da tayi dakon shi.


“Sannu da aiki officer” ta gaida su cikin girmamawa.


Dukkan su suka amsa da “yauwa” kana suka bata hankalin su domin sauraron abinda take tafe da shi.


Matsawa tayi wurin wanda ya fi kusa da ita, tana miƙa mishi ɗaya daga cikin takardun hannunta take faɗin “Hajiya Surayyah Kagarko nake son gani, tace in zo in same ta a nan” 


Duban takardan yayi a tsanake, takardan asibiti ne da bayanan lafiya na majinyaci mai suna Ibrahim Hashimu Baniza, mai shekaru huɗu. 


Ta ɗan cize leɓenta na ƙasa tana jiran amsar da zai bata, ko idan zai gane ƙarya take yi. Domin maƙwabciyar ta a children ward wanda itama take kwance da ƴarta a gadon dake gefen nasu, ita ta bata shawaran idan ta zo ta nuna cewa kiran ta suka yi ba niman allfarma tazo ba. 


Shiyasa ma ta bata sunan matar da tazo asibitin, a ranar da aka yi rashin sa’a ta tafi gida da muftee tayi mishi wanka ta samu ta huta kafin likitan shi ya zo duba shi da yammaci, saboda a ranan babu wani a kusa da shi bayan ita ɗin kuma an cire mishi ƙarin ruwa.


Su kuma duk yanda aka yi dasu su saka ta a cikin list ɗin wanda za’a tallafawa da jinyan yaransu sun ƙi. Da cewar ba zasu yi amfani da information ba kawai ba tare da sun ga patient ba, sanin halin damfara na mutanen mu. 

Kafin a kirata ta dawo asibitin kuwa har sun tafi.


Tun daga wannan rana take ta fafutukar yanda za’a yi su dubeta don tana buƙatar taimako matuƙa. Da tallafin su ne kawai muftee zai samu jinya mai kyau ya kasance cikin ƙoshin lafiya na tsawon lokaci. Har ɗan wani abu ta haɗa ta bayar wa mutanen da suka yi alƙawarin mata hanya zuwa ga masu A&I support organisation amma abu yaci tura, gashi gobe ake zancen zasu fara rabon tallafi.


“Kin san inda zaki same ta ai?” tambayar tashi ya bata mamaki domin tayi tunanin zasu nemi ƙarin bayani kafin su barta ta shiga, shiyasa bayan addu’o’in da take ta nanatawa a cikin ranta take ƙoƙarin haɗa kalaman da zata gamsar da duk wanda ake buƙatar ta fuskanta kafin ta kai ga hajiya Surayyan. 


Sai ta samu kanta da gyaɗa mishi kai a lokacin da yake maido mata da takardan. 

Bata maraba da wani tsaiko da zata samu koda na daƙiƙa ɗaya ne idan ba ya zamo dole ba. 

Ta sani duk rintsi idan ta shiga wurin ta tambaya ba zata ɓata ba.


Ya saka hannun shi ta baya ya tura ƙofar dake Jikin gate ɗin ya wangale mata “wuce Allah ya sawwaƙe ya bashi lafiya”.


A lokacin da take amsawa da ameen tare da godiya tayi rabin ƙulewa ciki.


Tsayuwa tayi tana ƙarewa harabar wurin kallo. yana da girma amma ba sosai can ba, kaman private school ko hospital. Ta juyar da duban ta daga jerin motocin dake fake a gefe guda zuwa ofisoshin dake ta waje kowanne da tambarin sunan shi a jikin ƙofar da yawanci a rufe suke. 

Sannan ta ɗaura idanunta a kan Babban ginin da yake tsaye curr a gabanta kaman mai jiran isowarta kawai, yana ɗauke da tambari wanda aka kafe a saman ginin da manyan baƙaƙe A&I SUPPORT ORGANIZATION.


“A&I” ta maimaita harufan guda biyu a kan harshen ta a lokacin da wayar dake cikin ƴar purse ɗinta ya shiga ruri.


Babban envelope ɗin ta mayar gefenta na dama ta riƙe a ƙasan hammatanta, kana ta buɗe purse ɗin ta ciro waya ƙirar itel mai keypad, madannin amsa kira ta latsa bayan ta karanta sunan mai kiran sannan ta ƙara wayar a kunnenta.


“Hello khausar”


“Na’am Aunty ILHAM.” dake wayar ba mai sirri bace sai amsar ɗaya ɓangaren ya fito tarr daga cikin ta.


“Yaya aka yi?”


“Kin samu zuwa ɗin?” ta furta dalilin kiran nata.


“Eh, yanzu na iso, Amma ban samu ganinta ba tukunna. Yaya jikin Muftee?”


Ta amsa da “da sauƙi.” sanna ta ɗaura da “ Toh Allah ya bada sa’a, yasa a samu abinda ake nima”


Da “ameen” ta amsa tana mai jin daɗin addu’ar. “Bari na shiga, Sai mun yi magana. kice ma yaro na Mimi tana gaisuwa”


“Ya samu komawa barci ma amma idan ya farka zai ji in sha Allah.”


“Nagode Khausar. Allah ya biya ki da gidan aljannah”


“Ameen Aunty” da haka ta katse kiran, ta mayar da wayan cikin purse ɗinta, kana ta durfafi wani mahaɗi na ƙaddararta da zai kamo baya da gaba ya ƙulle su a wuri guda ba tare da kowa ya taɓa tsammanin yiwuwar hakan ba. Har da ita kanta.



A gaban teburin reception ta tsaya ta miƙa musu takardun hannunta kaman yanda tayi a gate, sannan suma ta sanar da su Hajiya Surayya Kagarko ne tace ta zo.


Ba zallan hanta ba, harda hanjin cikin ta kaɗawa suke yi a lokacin da aka ɗaga waya aka kira ita Hajiya Surayya ɗin.


“Yaya sunan ki?” receptionist din ya tambaya yana ɗan kawar da wayan daga kunnen shi.


Da sauri ta amsa da “Amina Usman Jen. mother of Ibrahim Hashim Baniza”


Ya mayar da wayan kunnen shi, ya maimaita duk abinda ta faɗa kana yayi shiru yana sauraron abinda ake faɗa na yan sakwanni, kafin ya amsa da “toh” ya ajiye wayar.


“Ta ce ki jirata tana da baƙi”


Hamdala tayi a zuciyarta, ta amsa a bayyane da “toh” tare da mishi godiya sannan ta nufi ɗaya daga cikin waiting chairs dake jere a reception ɗin.


“Yi haƙuri malama akwai baƙin da zasu zo inspection yau, ki ɗan jira a waje.”


Bata damu ba ta gyaɗa kai cikin fahimta. Dukda har ta fara jin daɗin sanyin AC dake aiki a cikin wurin saidai biyan buƙata ya fi dogon buri.


Wajen ta fita, ta samu wuri mai inuwa a ƙasan wani bishiyar neem, kuma daga wurin zata iya hango mai fitowa da kuma mai shiga ciki.


Awa ɗaya, biyu, uku… tun tana iya tsayuwa har ta nemi wuri a saman interlocking ɗin dake wurin ta zauna daɓas. A lokacin da kiran sallan la’asar ya shiga kunnenta sai ta miƙe ta sake komawa reception ɗin a ɗarare, da tunanin ko dai shanya ne aka yi mata.


Receptionist ɗin yana shirin tafiya masallaci ta riske shi domin gashi tattare da alamun alwala. 


“Nace dan Allah bata fito ba?” ta tambaya tana matse fatar bakinta dake a bushe.


Shi shaff ya ma manta da tana nan tana jira.

“Meeting suke yi ne, shiyasa. Amma tunda lokacin sallah yayi na san ba zasu daɗe ba zasu fito”


Ƙara kwantar da murya tayi tace “toh ni a ina zan yi alwala in yi sallah dan Allah?”


“Bari na baki darduma, sai ki zaga baya daga ta waje akwai banɗaki da famfo.”


“Toh Nagode” murmushi ya bayyana a saman fuskar da zafin rana da gararin rayuwa ya gama koɗarwa.


“Ah babu komai” ya amsa tare da ɗauko mata darduman ta karɓa tana sake masa godiya sannan tayi kaman yanda yace, ta samu ta sauƙe farali.


Da ta idar, sai ta cigaba da zama a kan abun ibadarta tana ƙara kai kukanta ma Allah da yi masa kirari, tare da roƙon cikin rahaman sa ya sanya abubuwa su tafi daidai.


Wata farar mata, doguwa, mai ɗan jiki ta fara hangowa tana fitowa cikin hanzari da waya ƙare a kunnenta. Sannan ta hango wannan receptionist ɗin ya biyo ta a baya yana ta baza idanu a ƙoƙarin shi na hango ta.


Ya kuwa yi sa’a idanun shi suka sauƙa a kanta daga inda take zaune. Da yatsa yayi mata nuni da matar da ta nufi ɗaya daga cikin motocin dake fake, bakin sa ya furta mata “ita ce.” ba tare da ya bari sauti ya fito ba. 


Aka ci sa’a kuwa ta fahimta, don haka tsugul ta miƙe ta durfafi matar kafin ta kaiga faɗawa cikin motarta, domin ta san daga wannan kuma shikkenan bata da wani daman.


“Hajiya dan girman Allah ki taimaka mun yaro na” tace tana niman zubewa a kan guiwowinta tare da haɗe hannunta wuri guda cikin sigar roƙo.


Matar da itama yanayinta yake nuni da damuwa ko tashin hankali tayi saurin ɗagota tana cewa “Baiwar Allah kiyi haƙuri nima emergency ne ya taso mun. Amma ki dawo gobe da safe ƙarfe goma. Nayi alƙwarin zan saure ki ko me kike tafe da shi”


Da haka ta faɗa mazaunin driver tana mayar da wayar da daman ba katseta tayi ba a jikin kunnenta tana tambayar “A wani asibiti ne aka kwantar da ita?... Medi-plus?... gani nan zuwa” Bayanan da Ilham ta ji kenan kafin ta janyo ƙofar motarta ta rufe.




MEDI-PLUS HOSPITAL, KADUNA.




 “Idan har bayan duk wani ƙoƙarina hakan zai faru to ina amfanin shi?” ya wasa kaifin tambayar tashi ta hanyar ɗaga hannu a iska, a hankali kuma idanun shi suke zagawa kan duk wani mai rai da numfashi dake tsaye a wurin, domin su fahimci amsa yake nima.


Babu mai ƙwarin guiwar tanka mishi, dukda a wurin akwai wa’inda da kallo ɗaya zaka fahimci ba zallan rata na ƴan shekaru bane kawai a tsakanin su, a girme sun kai su haife shi. Saidai hakan bai basu ƙwarin guiwar cewa komai ba saboda ko sun faɗa ɗin ba jin su zai yi ba. 


Ba zai saurare su ba, zai yi amfani ne kawai da abinda kuturun zuciyar shi ta ayyana mishi, ko wani irin uzuri suka kawo suka tsayar a gaban shi in dai a kan Ikram ne ba zai kalla ba.


Addu,a kala ɗaya yawancin su ke yi a cikin zuƙatan su, shine Allah ya kawo Surayyah da wuri don ita ƙaɗai take iyawa da shi wani lokacin.


A yanda yake jin zafi a ƙirjin shi game da yanayin da Ikram ta kasance a ciki ɗazu a gaban idanun shi, babu wani abu da zai iya sirka wannan zafin a halin yanzu idan ba hannun agogo ne zai koma baya a samu wanda zai kare faruwar wannan hatsarin ba. Amma ganin yanda suka mishi shiru sai ya ƙara tunzura.


“Idan ɗawainiyar mu ne yayi muku yawa sai ku faɗa mun in ɗauki ƴata mu bar muku gidan”


“Wallahi da mun huta da bala’i da masi..” ɗane mata baki da matar dake tsaye a gefenta tayi da yatsar ta ya sanya tayi saurin haɗiye sauran zancen, ta kai hannunta wurin da zafi ya shiga ratsa fatar lebenta tana shafawa a hankali. 


“Ki bari ya gan ki mu shiga uku Huda” cewar matar cikin ƙasa da murya tana kare bakinta da tafin hannunta kada ayi katari ya hange ta ya fahimci abinda take cewa.


Turo baki gaba Hudan tayi ta cigaba da sauraron masifan da yake zazzagawa a babin babu yanda ta iya. Don kowa ya sani bayan komai ya lafa idan ya fahimci akwai wanda bayi wurin a wannan lokacin tsaf zai iya saka ka a blacklist ya cire maka tallafi. Samm baya yi da duk wanda baya yi da Ikram.


Hamdalan su saida ya fito fili a lokacin da suka hango Surayyah tana tunkaro su, Allah ya gani sun gaji da faɗan da yaƙi ci yaƙi cinyewa kaman cin ƙwan makauniya.


Saida ta ƙaraso gaban shi ta tabbatar ya sanya ta a idanu kafin ta riƙo hannun shi biyu da suka yi ɗumi, fatar su ta tamke ga jijiyoyi sun fito raɗa-raɗa har zuwa wuyan shi da kan shi da babu hula, kuma a yanzu babu yawan gashin da zai ɓoye hakan.


A hankali bakinta ya furta “kayi haƙuri Abdulhameed.”


Ta sani a duk lokacin da ta riƙi hannun shi bayi iya ƙwacewa no matter what. Saboda a lokacin da yake tsananin buƙatar mai riƙon hannun nashi da ta kama bata sake ba har yau.


“Aunty Surayyah yarinya guda ɗaya kawai, roƙo na guda ɗaya babu ƙari. Amma mutane kusan 20 sun gagara kulawa da yarinya guda ɗaya mai shekaru 3 da watanni 8 da kwana 4. Bayan lalular da Allah ya ɗaura mata sakacin mu ya ƙara mata wani. Shin mun yiwa mahaifiyar ta adalci?”


Surayyah ta ji dogon tsakin da wani a cikin su ya ja, amma bata kula ba gudun kada shima hankalin shi ya tafi wurin ya fahimta, don haka ta ƙara ƙarfin ruƙon da tayi ma tsintsiyar hannun shi dukda tsawon yatsun ta basu kai su zagaye shi baki ɗaya ba.


“Akwai sakaci tabbas amma wannan ma ƙaddarar ubangiji ne Abdulhameed. Ko da dukkan mu mun taru a kanta a wannan lokacin idan Allah ya riga da ya rubuta Kiki zata faɗi ta targaɗe a hannu to sai hakan ya faru. Kayi haƙuri don Allah”


Tana kallo wani abu ya motsa a maƙogwaron shi, ɓacin ran shi yake ƙoƙarin haɗiyewa. 


A karo na babu adadi ya tabbatar mata da a duniyar nan wani yana cin albarkacin wani, sannan ɗan halak da ya amsa sunan shi bayi manta alkhairi. Kuma daga nan bai sake cewa komai ba, itama a hankali ta saki hannayen shi suka koma ma’ajiyin su a ɓangaren shi na hagu da dama. Sai kawai ya juya ya ƙarasa ƙofar ɗakin da ya baro cikin ta ba da daɗewa ba, ɗakin da aka kwantar da rabin ran shi cikin wani hali. Ya murɗa hannun ƙofar, ya tura a hankali, kuma yana shiga ya maido shi ya rufe saboda bayi buƙatar rakiyar kowa. Amma haƙuri tunda ta roƙa ya haƙura.


Bayan shi aunty Surayyah dama sauran suka bi da kallo har ya ɓace ma ganin su, tana ayyanawa a ranta cewa Madaran waken suya ne ya siya mata wannan alfarmar. 


Madaran waken suya.



~•~•~•~•~•~•~•~•

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....


1. ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh 

2. DADIN ZAMA by Seemahwrites 

3. JODA by Sadi-sakhna 


*A whatsapp 

One 1k

Two 1800

Three 2400* 


 *Telegram 

One 700

Two 1200

Three 1500*


Account details 

0545475847 

Gt bank 

Fatima Muhammad Guri

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post