Joda page 1 Complete by Sadi-Sakhna

 


_____👑 *JODA* 👑_____

Na 

*Sadi-sakhna*

Ƴar mutan Jama'are

*JINJINA*

THE TRIO OF TALES 

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey) 

JODAH by sadi-sakhna

DAAƊIN ZAMA by seemawrites

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by gureenjoh

Wannan tafiya da zamuyi Allah ya haɗa kawunanmu ya kaɗe fitina da Sabani a tsikanunmu. Jinjina my Triple tales.

*GAISUWA*

Ga ɗaukacin Iyaye sannunku da ƙoƙari Allah yaƙara haɗa kan zuri'armu bisa hanya madaidaiciya.

*GARGAƊI*

Ban yarda a yanki wani sashe na littafina ba,ƙirƙiratace ni naje nayi bincike na tara bayanai na,dan haka ɗaukamin wani yanki na littafina bada yarda ta ba ban amince ba.

*ƘARIN HASKE*

Wannan labarin zai aukune a wasu shekaru da suka wuce a nahiyar africa,zan ambaci gurare masu ban mamaki,saidai bawai ƙirƙira nayi ba face dama sun wanzu a lokacin iyaye da kakanni. Ba shaci faɗi nayi ba.Domin gudun rashin fahimta ga kaɗan daga labarin waɗannan Dauloli (empire) da zasu zo inshaallah a cikin wannan labari na Joda.

Ƙasar africa a wannan ƙarnin nahiya ce data riƙe kambu na ƙarfin mulki da tashen arziƙi,wanda mafi yawan abinda ya kasance abin tunƙahon wannan nahiya shine zinare,da Allah ya albarkaceshi a ƙarƙashin ƙasar wajen.

Wannan nuna mulki da isa na ƙarfin izza ya wanzune a tsakanin jiga jigan dauloli guda Huɗu.

👑 *DAULAR MASAR (EGYPT EMPIRE)* 👑

Daular Masar Daɗɗiyar daulace data Wanzu cikin izza ƙarfin kasuwanci,noma da sauransu. Inda ta zaba babbar cibiya na gudanar da kasuwanci tsakanin Sin(china),Indiya da kuma Yamen. 

Masar ta shiga Daular Musulunci ne a shekara ta 640-642 Miladiyya, lokacin da rundunar Musulmi ƙarƙashin Amr ibn al-ʿAs ta kwace ƙasar daga Roma (Byzantine). Wannan ne ya sa Masar ta zama ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin Daular Musulunci.

👑 *DAULAR GHANA* 👑

Daɗaɗɗiyar daulace data kafu Tun a shekarar 300C.E, Mutanen soninke sune suka kafa wannan daula,Tayi tashen fitar da ɗanyen zinare daga ƙarƙashin ƙasa na tsawon lokaci da zamani,inda har tasamu mulki daga sarakuna 144 a lokacin.

Addinin wannan yanki shine bautar gumaka,sai daga baya wajen 740CE aka fara samun yaɗuwar addinin musulunci a cikinta.

Mutuwar Daular Ghana ta farane wajajen 1328CE inda Daular mali mai biye mata baya ta mamayeta bisa jagorancin sarki Abu bakr, a ƙarni na 11th.

👑 *DAULAR MALI* 👑

Daular mali itace ta biyu bayan Daular ghana,duk da cewar daular ghana tafita daɗewa tana damawa da ragamar iko,saidai itakuma tafi daular ghana yawan arziƙi da kuma tashe a faɗin duniya.

Daular mali ta wanzune a ƙarƙashin jagorancin Sarki Mansa Fasih,wanda yakasance mutumin daya riƙe kambun wanda yafi kowa a ƙudi a zamaninsa,wanda har a yau ana ganin masu kuɗin yanzu basu kama ƙafarsa a dukiya ta zallan ɗanyen zinare ba.

Daular mali daula ce ta musulinci,wacce tayi babban aiki wajen yaɗa addinin musulunci a yammacin africa da kewaye. Saidai itama tayi ƙasane sakamakon Mutuwar Sarki mansa Fasih,wanda Sarki Sunni Ali wanda yakafa Daular Songhay ya cita da yaƙi a ƙarni na 16th.

👑 *DAULAR SONGHAY* 👑

Wadda itace daula da ƙarshe,duk da batakai sauran taka madafun iko da daɗewa ba saidai itama ta taka muhimmiyar rawa wajen mallakar dukiya da kuma iko mai ɗumbin yawa.

A ƙarni na 14 daular Songhay tana ƙarƙashin daular mali ne,bayan da tayi raunine itama ta samu nata madafar ikon a ƙarnin 15, bisa jagorancin Jarumin sarki Sunni Ali,ɗan addinin musulunci ƙarƙashin koyarwar Sunni. Wanda kafin haka kuma mutanene su masu yarda da bautar magabata ko kuma iskokai.

Daular Songhay tayi tashenta ne ta ƙare a tsakanin ƙarni na 15 zuwa na 16,hakanne yasakata zama daular mai gajeren Zango in an dangantata da sauran daulolin.


Daular Songhay shine yammacin africa a yanzu wanda ya haɗa dasu Nigeria,Niger,Chadi,Cameroo da sauransu.





...................👑*Sharar fage (prologue)*👑



Nahiyar Africa a shekara ta 728AH. Bayan hijira na fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) wanda yayi daidai da 1327-1328CE. Na miladiyya haihuwar annabi isah (AS).



.......A rayuwa Allah yayiwa ɗan adam baiwa, baiwa ta yayi tunani,yayi nazari sannnan yayi tafiya a tsaye batareda ya kifa gwiwoyinsa da hannyensa ba,domin ɗaga darajarsa fiyeda ta sauran halittu. Ya fifitasu akan komai daya halitta,ya basu ikon yin mai kyau domin ya saka musu,haka kuma shi mai yafiyane idan suka saba masa kuma suka dawo gareshi....... To amma mai zai faru idan su wannan halittun a cikinsu suke ƙasƙantar da wasu sashen daga cikinsu zuwa matsayin da yafi na dabbobi ma muni...!!

Shin sun manta cewar idan Allah yatashi yin baiwarsa da ɗaukakarsa yakan ɗaukaka wanda yaso koda kuwa ku kuna ganinsa a bakomai ba, sai hakan kuma daga karshe yazama hassada da tabewa.



******



Hantsi mai haɗeda shuɗin launi na sararin samaniya,garine mai ɗauke da gini na laka da akayi su da ɗanyar ƙasa da kuma itacen giginya domin ƙara karfin ginin.



Cikin Garin Adik wanda Babban garine a ƙarƙashin Mulkin Soghay, kuma shine na biyu bayan Garin Goa inda Daular Songhay take.



Babbar fadar sarki a cikin garin Adik tafi kowanne fada girma ƙayatarwa dakuma girman mamayar ƙasa. A cikin fadar wani bangare dayake ɗauke da fili mai dauke da farar ƙasa mai laushi an shareta abin gwanin ban sha'awa.



Yarane ƙanana da bazasu wuce shekara bawai ba zuwa takwas,dariya suke suna bulawa wata yarinya a gefensu ƙasa wacce zata kai shekara goma sha biyu ita,domin ta ɗan girmesu a tirinyar jiki amma kuma daga yanayinta hankalinta ma bai kai nasu ba.



Idan suka ɗebi kasa suka watsamata sai ta saka kuka tamkar asara,su kuma hakan sai yasa su sheƙe da dariya cikin farinciki. Tana gefe a zaune gabaɗaya sun wanketa da ƙasa itakuma ta bare baki tana ta kuka.



Can bayan wani ɗan lokaci fuskarta tayi kaman dodo,hawaye ya haɗu da ƙasa tayi buju buju da ita.



Ɗaya daga cikin yaranne tace.



"Joda Aga agaaaa"



Tana cikin kuka tayi maza tace "Aga" cikin wauta.



"Agah waye zata iya shiga cikin jejin can ta ɗaukomin takalminaaa ?"



"Niii Coɗa"



"To jeki ki ɗaukomin sauri ki dawo yanzu zan baki kifi na idan babana yakawomin daga ruwa"



Da sauri ta tashi ta kaɗe jikinta ta nufi inda yarinyar ta nuna mata bigizim bigizim. Jeji ne inda ake noman su giginya kwakwar manja da sauran manya manya bishiyoyi irin Goro da sauransu saboda niimar wajen yana kusada kogin Niger,sai hakan yabawa yanayin garin sanyi da lumshi.



Batareda shayin komai ba ta nufi dajin,burinta tayi abinda aka sakata yazama ita tayi nasara,kuma za'a bata kifi. Ta manta kargaɗin da akayiwa yaran karsu bar cikin masarautar. Saboda hatsarin faɗawa hannun masu kamen bayi da kuma naman daji masu hatsari.



Tun tana shiga tana kallon bishiyoyi da sukayi kama dana kowanne daji,har ya zamto ta fara yin karafkiya da duhuwar daji mai ɗauke da bishiyoyi masu launi kala kala. Abinka da ƙananun shekaru haɗeda yarinta da wauta maimakon hakan yabata tsoro ko ya ɗarsa fargaba a cikin ranta,saima ya ƙara ƙayatar da ita tareda saka shauƙi a cikin ranta.



Tafiya take da sassarfa tana ƙara gudun tafiyarta. Wata akwalkwala (malan bude littafi) ne ya iyo ƙasa ƙasa yana walwali a samanta daidai yanda hannunta zai iya tabawa. Aikuwa hakan yayi tasiri wajen jan hankalinta matuƙa,inda tafara binsa da gudu tana ƙyalƙyala dariya,shikuma yacigaba da janta izuwa zuciyar dajin.



Takai wani lokaci tana bin Akwalkwalar zata kama,amma sam taƙi bata damar yin hakan, sai ta kusa kamata sai ta sake yin sama da kaɗan. Dariyarta ta fara sararawa alamun gajiya sun fara bayyana a jikinta. Waigawa tafarayi da alamun tanason komawa da baya. Rau rau tayi da ido zata fara kuka,jin dajin tsit babu sautin bil'adama ko guda ɗaya,sai kukan tsintsaye,rausayar bishiyoyi da kuma sautin ƙananun halittu masu ban al'ajabi da babancin Halitta fiyeda na waɗanda muka saba gani.


Wani haske tagani a cikin wani kogo da kuma sautin motsin mutum,da sauri kuwa batareda ta sake tunani na biyu ba ta nufi wajen.


Kai tsaye shiga tayi tana ƙarewa wajen kallo. Abincine akan tebur an ajiye tamkar ana jiran baƙo yazo yaci. Cikinta ne taji yayi ƙara alamun yunwa ta gara mata,domin rabonta da abinci tun gurasar da suka hau layi aka raba musu. Da sauri ta nufi wajen zata saka hannu itama taci. Saidai taji an riƙe hannunta caff. Juyawa tayi da mamakin waye? .....Wata mace tagani dattijuwa a matakin ƙarshe na shekarunta,tana sanye da farin saƙi amma kuma fess da ita. Ba kaman ita ba da takeda baƙar fata da kuma ƙayan saki masu matuƙar dauɗa.



Murmushi tayi mata wanda baya bayyana ƙyama ko kaɗan. Jan hannunta tayi zuwa ƙuryar ɗakin,inda wani kofin Duma yake ajiye da tsimi a cikinsa. 



"Sam abubuwan dasuke wajennan bakya buƙatarsu a yanxu,keɗin makulline wanda sai yayi tafiya mai nisa da take cikeda ƙalu bale kafin yakai ga buɗe ƙofar ƙaddarar da take gabansa. An haifeki da baiwa ta Fasihmman wanda wani ƙashi ya tosheta sanadiyyar haihuwarki da Mahaifiyar ki tayi a tsaye saboda firgici na halin yaƙi. Karbi wannan ruwan kisha,zai taimaka miki wajen warkar dake sannan ya taimakawa ƙarfin tunaninki. Wannan shine iya abinda zan iya biya daga taimakon da Mahaifinki Yayimin batareda yasani ba"


Hallau da murmushi akan fuskarta ta tsiyanyo ruwan ta miƙawa Joda. 



Batasan mai take faɗaba ballantana tasan mai take nufi,sakamakon an haifeta da shanyayyen tunani,sai anyi magana goma kafin tagane ɗaya. Karba tayi kawai tashanye saboda ƙishirwar da takeji. 

Yana shiga cikin bakinta ta zefar da kofin tareda tsallara wata ƙara mai ƙarfi,dafe kanta tayi tana kallon matar wanda a hankali take Dusashewa daga idonta,a wani bangare kuma wata duniyar tana bayyana. Muryar mahaifinta take jiyowa sama sama, daga nan batasan mai yasake samun ganin ta da jinta ba....

*********

09035784150

Sadisakhna ce ❤

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post