*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na’ibi
Wattpad and arewapen *@Seemahwrites*
#THE TRIO OF TALES
_(Three minds, Three stories, One journey)_
3... Haɗuwar Sati Ɗaya.
KANO.
*Talatin ga watan Maris, shekara ta Dubu biyu da sha huɗu(31/3/2014)*
Riƙe take da tsintsiyar hannun shi, ruko tayi mishi sosai da iya karfinta idanunta yana maiƙon hawaye, amma sanin kanta ne bata isa ta buɗe baki ya ji kukanta ba, kasancewar itace dalilin da tasa aka ɗaga shi da sanyin safiya a lokacin da yafi jin daɗin barci domin ya rakata makaranta. Don haka bin takun dogayen sawayen shi take yi da gajerun nata, tana haɗawa da sauri-sauri gudu-gudu ta samu su daidaita tunda ba rage saurin tafiyan nashi zai yi ba.
Tsoron ta ne ya ƙaru ganin sun fara hango gate ɗin makarantar. Dukda rakiyan yayan nata kuwa yanzu idan suka ga dama sai su saka ta wankin banɗakin su mai shegen wari da kashi a kasa kafin su bari ta shiga, kuma ta san shi ba cewa komai zai yi ba, Allah dai yasa babu prefects on duty kuma babu wasu ɗaliban da aka tsare idan kuma ba haka ba Allah ya Isa zata yiwa Addah Iman tunda ta san ta ɗan koma barci bayan an ɗaga su suyi shirin makaranta kuma har suka fita bata sake tashinta ba, gashi yanzu ta fito ko karyawa bata yi ba.
Hanyar da suke bi a matsayin shortcut baya da faɗin da mota zai iya wucewa, mashin ma sai tuƙin kwararre a rakubewa ta gefen kwatami da buɗaɗɗen sokawe. shiyasa wani lokaci yake zama daba na yan shaye-shaye da masu busa sigari, domin sune zarnin fitsarin dake lungun bayi damun su.
Har sun kusa fita bakin titi suka ji anyi Fiito daga bayan su tare da kwala kiran “Hey!"
Shiga ukunta ya sanya ta waiwaya zuwa ga inda sautin muryan ya fito, idanunta suka shiga cikin nashi na tsawon daƙiƙa guda.
Saidai kafin ta kai ga fayyace kamannin shi taci wawan tuntuɓen da ya sanya ta kusa kifawa.
hannun yaya Aliyyu da take riƙe dashi ne abinda ya ceci haƙwaranta daga zubewa a kan dutsen da ta buge babban yatsar ƙafar ta a jiki Dukda saurin yake bunkawa kaman mai zuwa karɓan sadaka a masallaci. shima yatsar bai ɓata lokaci ba wurin aman jinin da ya rina jikin farin sock ɗin da yake lulluɓe a ciki.
Ƙarar da ta saki cikin azaba ya sanya Ya Aliyyu da tsayawa da tafiyar, ya juyo ya fuskance ta yayin da ta durƙusa ta riƙo ƙafan tana baiwa ƙwallar da ya taru a cikin idanunta damar saukowa saman fuskar ta.
Tsaki ya ja “Mtsww kina da azababben raki wallahi. Mu gani?” shima ya durkusa tare da amsar kafar daga rukonta ya zame sandal da safan jiki, ya shiga duba ciwon.
“Farce na ya tumbuke ko?” ta tambaya cikin sheshshekar kuka “wayyo Allah na”
Fatan yatsar ne kawai ya kuje sosai shine yake fitar da jini don haka yace “zaki tashi mu karasa ne ko kuma in yi tafiya ta?”
Ta dago ta kalle shi tana ƙara kwabe fuska “Haba yaya Aliyyu! Ta yaya zan iya zuwa school a haka, ka kai ni chemist sai ka dawo ka fada musu na ji ciwo ba zan iya zuwa makaranta ba sai next week” ta ƙarasa tare da jan hanci.
“Tuntube ne zai saka ki zaman gida har na tsawon sati guda Fidela?” ya tambaya yana tamke fuska.
Ƙasa tayi da kai ganin mugun kallon da yake watsa mata tana kara matsar kwalla kana ta amsa da “shima tuntuben ana kamuwa da ƙwayar cutar tetanus aka fada mana a class din inter science”
Ya jinjina kai, kafin ya mayar mata da martani sai ji yayi wani abu ya daki kafadan shi har saida yayi taku biyu da baya, kana ya samu ya daidaita tsayuwar shi ya dago duban shi don ganin menene.
Idanun shi ne suka sauƙa a cikin na wanda ya daidata a cikin nashi kasancewar tsayin su ya kusan zuwa ɗaya.
“Baka ji bane lokacin da na kira ka?”
Duban shi na kan Aliyyu amma nata yana kan bakin shi da ya maƙale toothpick a tsakanin hakorin shi, wanda take da yaƙinin shine dalilin da ya sanya hausan nashi ya fito wani iri.
Wani iri ba yana nufin babu dadi ba A’a, wani iri dai kaman daga bakin da bai saba da Hausar ba.
Wani iri da bata san da cewa zai yi mata tasiri nan da shekaru masu yawa fiye mamakin da tayi a wurin ba kawai.
“Ka kira sunana?” Aliyyu ya tambaya don sarai ya ji fiiton da yayi ɗazun.
Bai amsa shi ba sai miƙa mishi sabuwar naira 500 da yayi yana masa alaman ya karba ya tafi da kai.
Aliyyu bai karba ba, ba don bai fahimci nufin shi ba tunda ba yau bane gamuwar su na farko, sai domin yau ɗin bayi da niyyan aikata yanda yake so.
“Ko na bata ne ta siyo a madadin ka?” ya tambaya ganin ba zai karba ba, lokaci daya yana dawo da dari biyar din gareta sannan duban shi ya biyo baya.
Suka sake yin ido hudu, a cikin hausar tashi ya soma fadin “kara biyu zaki ce a bak..”
Saurin wafce kudin da yaya Aliyyu yayi ya katse masa sauran zancen sa. ya dube shi da dan karamin murmushi tare da fadin “idan kaine kuma kwalin zaka karbo mun”
Bai yi musu ba kaman yanda yayi tsammani, shiyasa da ya gan shi tare da yarinyar da yake da yaƙinin kusanci a tsakanin su yaji dadin kiran shi.
Tunda yana sanye ne da uniform ɗin makaranta idan ya je ba zasu yarda su siyar mishi ba, haka itama yarinyar.
Saidai yayi yunkurin tura ta ne don yayi mishi barazana kuma hakan yayi aiki.
Ita dai dubanta ne yake yawo a tsakanin su bayan ta hadiye kukan ta, cikin rashin fahimtar abinda yake faruwa ko kuma abinda wannan yake nufi da ‘sanda biyu’ da kuma ‘kwali’ .
“Tashi mu tafi” cewar yaya Aliyyu.
Ta yunƙura zata dingisa ta jiyo shi yana fadin “ka barta a nan ka karbo mun sako na tukunna zan yi maka gadin ta.”
Da sauri ta mike ta tusa kafar da babu safa cikin baƙin sandal dinta lokaci daya ta manta da raunin wanda jinin da ya fitar har ya bushe.
“A’a Ya Aliyyu mu tafi dan Allah” tace tana komawa bayan shi ta ɓuya tare da sake riƙe damtsen hannun shi gamm.
Sai ya taɓe baki kawai ya juya, hannun shi zube cikin aljihun wandon shi yake takawa ya koma dakalin kofar gidan da yake zaune dazun yayi zaman jiran dawowar su.
Suna karasawa bakin titi Yaya Aliyyu yace ta tsaya daga inda zai iya hangotanta jira shi saboda babu yanda za’a yi ya je siyo sigari da ita.
Ya karasa shagon da yake tsallaken makarantar su, akwai mutane biyu a gaban shi don haka ya jira saida aka fara sallaman su tukunna ya mika dari biyar ɗin yana fadan abinda za’a bashi.
Mai shagon ya kalle shi a kaikaice. “Aliyyu kai da nakewa kallon mai hankali kai ma bushe-bushen zaka fara”
Saurin kare kan shi yayi da “A’a malam Sama’ila ba nawa bane, aiko ni aka yi”
“Waye ya aiko ka”
“Uncle Rabe” ya samu kan shi da mishi karya don da kunya ya fadi ainihin wanda ya aiko shi kuma har ya yarda yazo.
“Jiya-jiya na gama mishi gargadin kada ya sake aiko ku idan ba haka ba zan hada shi da baban ku. Bai ji ba kenan?”
Aliyyu sai ya daburce ya fara kame-kame “D… daman fa.. Daman…”
Ganin mutane suna tunkaro shagon, malam sama’ila ya amshi kudin ya fito da kwalin sigarin ta kasan kantan shagon ya dunkula masa a cikin hannun shi yana fadin “ka tafi, kada ka sake dawowa. Idan ba haka ba kuma a kunnen mahaifin ku.”
Da sauri Yaya aliyyu ya bar shagon ya ƙaraso inda take yace su tafi.
Da suka koma wurin mai fiito shima yace ta jira shi daga nesa, ya ƙarasa wurin da yake zaune sai taga ya dunƙula masa abinda ya siyo din yana waige-waige, alamun rashin gaskiya duk sun bayyana a jikin shi, ya dawo ya fisgi hannunta suka bar lungun.
Chemist ya kaita aka wanke ciwon ƙafarta sannan suka koma gida fuskarta shabe-shabe da hawayen kukan shagwaba, don ta samu a lamunce mata ta sha zamanta a gida na tsawon sati guda kaman yanda ta kuɗurta a ranta.
…..
*Abdulhameed*
Duba agogon dake maƙale a tsintsiyar hannun shi yayi ganin tara da rabi ta gota, ya saka sigarin a cikin jakar makarantar shi tare da mikewa yana da yakinin zuwa yanzu Nne ta isa wurin aikinta.
Ya saƙala hannun jakar shi ta saman kansa ya raba shi a kafadar shi na hagu kana ya gyara ma jakan zama a jikin kunkumin shi ta bangaren dama sannan ya karasa bakin titi ya tsari mashin ya hau.
Da key din shi ya bude kofar dake jikin farin gate din ya shige tare da sake murzawa kofar key ta ciki ya rufe.
Haka ma kofar parlourn yana shiga ya garkame. Durƙusawa yayi ya shiga warware igiyan cover shoes ɗinsa ya watsar da su a wurin kana ya karasa ya kunna socket ɗin Tv sannan da shi da jakan shi suka zube a kan dogon kujeran dake fuskantar talabijin.
Lighter ya fara cirowa daga aljihun wandon shi, ya cire tsinken sakace hakorin dake bakin shi ya luma hannu a jaka ya fito da kwalin sigarin ya zari guda ɗaya ya makala a tsakanin labban shi ya kunna masa wuta.
Kafin shirin da yake son kallo ya gama loading a DVD har ya zuke rabin kara hayaƙi ya buɗe madaidaicin parlon.
A lokacin da ANIME mai taken BLEACH ya fara playing sai ya kishingida ya cigaba da zukan kayan shi hankali kwance.
.
.
“Biko sir, ana m abia obere oge. I forgot some papers at home” A tsakanin kunne da kafadarta ta makala yar wayar da take magana a cikinta, yayin da take kokarin zura key a jikin kofar farin gate din da nufin bude shi.
“Yanzun nan zan dawo nace maka mota na ma a kunne na barta” ta cigaba da faɗi cikin wayar tana shigewa ta cikin kofar bayan tayi nasarar budewa, bata tsaya ko tura shi tayi ba ta wuce cikin gidan tunda yanzu take saka ran fitowa.
Kife murfin ƴar NOKIA ɗinta ja tayi bayan ta gama magana ta tusa cikin jakar hannunta, sannan ta canza makullin da take rike dashi cikin jerin gwanon mukullan tun daga na gate zuwa na gida, shima ta zura a ramin shi, ta murda, ta bude, tayi Shigewar ta ciki kanta tsaye, yayin da taja taci birki a tsakar parlon lokacin da idanunta suka sauƙa a kan abinda ya kaɗa mata hankali.
“Nwam?!” ta kira cikin kaduwa.
Kara hade fatar idanun shi yayi yana sauke numfashi a hankali kaman mai barcin gaske. Ita kuma ganin bai motsa ba ta sake kiran
“Abdulhameed!”
Tana karasowa kusa da kujeran da yake mike, hannun shi a saman kirjin shi da yake dagawa a hankali, ga plate din abinci da kwalban 7up da aka gama sha a wurin.
“Nwam(my son).” ta kira a karo na uku tana dan bubbuga kafadan shi.
“Hmm?” Sai a sannan ya bude idanun shi sannu a hankali yana mayarwa ya rufe kaman wanda barcin bai ishe shi ba. Bayan ƙaran bude gate dinta da yaji ne ya saka shi mikewa a gaggauce ya fincike igiyar wutan Tv da na DVD ya gyara ya kwanta, tunda ya san zata iya riskan shi idan yace zai kawar da plate din da yaci abinci sai kawai ya bar su a wurin.
Cikin sa’a a kowani lokacin da zai sha sigari a gida yana gamawa yake ɗaga labule hayaƙin ya fita sannan yabi gidan da airfreshner baki daya, bakin shi kuma ya jefa masa alawar tom-tom.
“Nne, ilotala (mama kin dawo?) ya tambaya cikin harshen Igbo yana hamma.
“Abdulhameed mai kake yi a gida lokacin makaranta” ta mayar mishi tambayar da turanci.
Dafe goshi yayi yana yamutsa fuska “headache Nnem.” ya bata uzurin da yake da yakinin shine kawai zai sanya yau ya sha a wurinta. Ya dora da “ina aji kan nata sara mun shine naje clinic aka mun allura aka ce na dawo gida na huta” bai ce magani bane saboda kada ta tambaye shi sauran wanda aka bashi.
Hannu ta kai kan goshin nashi, babu wani zafin da ya wuce mizani amma dake zuciya irin ta uwa mai cike da ƙaunar danta ne ke bugawa a kirjin ta, take tausayin shi ya lullube ta.
Ta sassauta murya tana mishi sannu da igbo shima sai ya dada narkewa har tana tambayan shi ko su je asibiti ne.
“Naga likita ai a clinic Nnem. ta ce idan na samu isasshen hutu zan samu sauƙi”
Sai ta jinjina masa kai fuskar ta lullube da damuwa. “Ina ba damuwar abinda nace jiya bane ya saka maka rashin lafiya?”
Bai amsa ba sai mayar da kan shi da yayi yana kallon gefe. Don damuwa abinda ya dame shi kenan, shiyasa bai samu nutsuwa da safiyar yau ba saida ya bunka ma kan shi hayaki, kuma yaga babu amfanin zaman ajin da yake yi domin ya cika ma mahaifiyar shi burin ta, ya zama irin abinda take so, idan ita ba zata iya cika mishi nashi burin ba.
Ɗofanuwa tayi a kujeran ta gefen kafar shi tare da shafo gefen fuskar shi cike da kulawa tana leka idanun shi, cikin murya mai taushi tace “Nwam. baban ka baya son waƙa, ka zabi wani abun daban ko menene shi ni zan tsaya maka amma banda waƙa tunda baya so. Nayi mishi alkawarin ba zaka yi waƙa ba.”
Da ƙwallar da zancen ta na yanzu ya tara a idanun shi ya juyo ya dube ta. “Daman yana sona ne balle ya so abinda nake so?”
Lumshe idanu tayi tana sauƙe numfashi cikin rashin jin dadin abinda ya fada. “Kada ka damu, ni na ishe ka rayuwa.” tace tana shafa gashin dake cike a kan shi wanda babu yanda ba’a yi da shi ya rage tsayin shi ba a makarantar su, amma askin punk yake so yayi na gayu da manyan mawaka wanda za,a aske gefe da gefe a bar mishi tsakiya shiyasa yake tarawa.
Nokia mai murfin ta da ya shiga ringing ya sanyata mikewa tana cire makulli daya daga jikin mariƙin su ta mika mishi. “Gashi ka bude bedroom dina ka dauki wayan ka a bedside drawer duk abinda kake ciki ka kira ni. Idan kuma ka dan samu sauƙi kafin na dawo sai ka dauki kudi ka fita ka sayi abinda kake so.”
“Okay Nnem. thank you” ya fada a cikin ranshi yana fama da matsanancin farin ciki. Daman siezing din wayar tashi da tayi ya zaunar da shi a gida amma yanzu tana fita shima ficewa zai yi.
Ta sumbaci goshin sa hannunta a kan kumatun shi sannan ta fice daga gidan kafin wani kiran ya sake shigowa.
Minti sha biyar a tsakani haka, bayan yana da tabbacin tayi nisa ya miƙe ya bude bedroom din. Wayar shi ƙirar blackberry ya fara dauka sannan ya bude ma’ajiyar kudinta ya zari dari biyar-biyar guda shida. Har ya fita ya janyo kofar dakin ko mai ya tuna? Sai ya koma ya kara guda biyu. Key din ɗakin ya ajiye mata a kan TV stand, bai ko sauya uniform din jikin shi ba ya fice daga gidan baki daya ya rufe da key din shi.
Shagon unguwan su ya tsaya ya sayi katin dari biyu ya loda sannan ya kira numbern da yayi saving da “Fire”.
“wassup Nigga” shine abinda ya shiga kunnen shi bayan an ɗaga kiran.
Hannu ya saka ma mashin ɗin da yazo wucewa ta gaban shi Sannan ya amsa da “ka Same ni a studio yanzu. Kuɗin sun cika”
“Weeehuu. Bari na kira ɗan Malam ya karɓo mana wancan saƙon toh”
Bai amsa ba ya katse kiran sannan ya hau bayan mashin ɗin suka ɗau hanya yana mishi kwatancen wurin da ze kai shi.
•~•~•~•~•~•~•
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
