https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
*MAI BUƘATA DAGA FARKO, YA BI LINK YA DUBA CHANNEL ƊIN NAN. AND MORE PAGES ARE AVAILABLE AT AREWAPEN*
SARA DA SASSAƘA...
YOTA 002
Page 6
Nadiya na jin su ba ta yi magana ba, ta basar Alina ta ajiye ledar raken, tana ta addu'a a zuciyarta dan ta san halin Isma'il sarai, tsaf zai saka ta a gaba da faɗa.
Ga shi ita ba wani abu ne tsakaninsu ba, tana ƙoƙarin kula shi ne, dan wanke abin da yayan ya yi masa har ya tara masa jama'a ya yi masa tijara a cikin jama'a.
Kiri-ƙiri 'yan makarantar su maza, ba sa shiga harkarta, tun da wani yaro ya ce yana sonta tun a Jss 2, yaron yana Ss2, daga ta ba wa Nadiya labari, ta gaya masa yaje har makarantar, ya zane yaron, case har da iyaye da zuwa gurin 'yan sanda. Samari na cikin unguwa kuwa, babu wanda yake shiga harkarta, ko kula ta, da ka nuna alamar sonta ka ke yi ko da gaisuwa ce ta fiye haɗa ku, sai Ismail ya yi wa mutum tijara ya ce za a lalata masa ƙanwa, ba zai lamunci hakan ba. Ita kuma Allah ya hore mata farin jinin mutane, saboda yawan fara'arta da kuma surutunta, da wuya ka yi zaman minti goma da ita ba ku saba ba.
Ko da Isma'il ya je masallaci, sahu ɗaya Ismail ya yi salla da mai gyaran takalmin nan, kallo ɗaya ya yi wa Isma'il, ya sunkuyar da kansa, ya ƙarasa azkar ɗin sa ya tashi sumi-sumi ya fitaya bar masallacin. Yana cikin tafiya ya ji an dafa kafaɗarsa. Babu shiri ya waiwayo a tsorace.
Ismail ya tsare shi da ido ya ce "A tunaninka haɗa sahu da kai da na yi kawai faruwa ya yi ne haka kurum? Gurinka na zo ne ai. Ba kuma tsawaita magana zan yi ba. Hawainiyarka ta kiyayi ramata. Shi ne kawai abin da zan iya gaya maka" Ya sakar masa kafaɗa ya kewaye shi ya wuce.
Yaje gida ya tarar da Nadiya da Alina sun kewaye rake, su na sha su na hira. Sai da Alina ta gan shi, sannan ta tuna ma a yadda ya fita. Sai dai bai kula su ba, ya shiga ɗaki.
*****
"Barwa" Ya kira sunansa.
"Na'am sir"
"Ka ce yaronsa ya aiko maka ba shi ne ya zo da kansa ba?"
Barwa "Eh ranka ya daɗe"
"Dole mu yi taka tsantsan da mutanen nan, amma abin da muke so ba zai yiwu ba, sai da su dole. Ka gaya musu mun amince da dukkanin buƙatunsu, za kuma mu yi, su fara aiki kawai"
"Amma ranka ya daɗe, yarjejeniyar ta yi tsauri da yawa fa, kuma za a kashe kuɗaɗe ne ba kaɗan ba"
Dattijon ya yi murmushi ya ce "Ai yaro bai san wuta ba sai ya taka, bamu za mu biya kuɗin aikin ba, gwamnatin da kanta za ta biya kuɗin aikin da za a yaƙe ta, ka zuba idanu ka gani, sannan kuma na nemi haɗin kan ƙusoshin tsaro, komai zai tafi dai-dai babu gargada. A hanzarta shirya yarjejeniyar kamar yadda suka buƙata"
Barwa ya ce "Shikenan ranka ya daɗe, an gama da yardar Allah"
"A hanzarta domin Allah, dan bamu da lokacin ɓatawa, a gaggauce yakamata mu yi komai. Ba na son ya rufa shekara guda, lissafi bai ƙwace masa ba. Anjima zamu zauna da su Ade, da zarar yaran nan sun fara aikinsu, akwai buƙatar dala ta yi ƙaranci a kasuwa"
Barwa ya kwashe da dariya ya ce "In dai lissafi ne a bar maka Yallaɓai"
"Kash, kai dai ka zuba ido, ka ga yadda za mu mayar da komai baibai ai Jagora ya tsaya mana, sai mu ga da mu da shi, wa zai haƙura ya bi wani. Taƙamarsa ko da mu ko babu mu, yana da soyayyar jama'a yana da yaƙinin zai sake komawa gadon mulki, tun da mun tura motar zai bule mu da hayaƙi, amma mu zuba mu gani...
*****
Baffa na zaune bayan sallar asuba yana lazumi, ya kashingiɗa da jikin gado, yana jan carbi. Yana jin Juma ta shigo, ta kawo masa madara ta ajiye ta fita, amma bai motsa ba. Ya rasa wace irin fargaba ce take ratsa shi har haka, komai baya yi masa daɗi. Tun da ya mayar da Rahama makaranta, ya rasa mene ne yake ba shi tsoron ko saka shi fargabar ji yake yi tamkar ya koma ya ɗaukko ta kawai.
Rahama kuwa na zaune a ɗakin karatunsu na makaranta, tana duba wani littafi, ta ci karo da taƙaitaccen tarihin sir isaac newton, da ake yi wa laƙabi da father of modern physics. Masanin kimiyya ne sosai da sosai. Yana cikin wanda suka bayar da gudummawa a harkar lissafi. Duk da bincike ya nuna kai tsaye ba za a ce shi ne kaɗai father of physics ba, tun da ga Albert Einstein, ga Galileo Galilei.
Shi ya samar da law of motion, bincike ya nuna Isaac newton introvert ne, ana kyautata zaton yawan ta'amalli da chemical ne ya yi sanadiyar mutuwarsa. Babban abin da ya fi ɗaukar hankalin Rahama shi ne, da aka ce bai taɓa aure ba, babu kuma ƙwaƙaƙwarar hujjar da take nuna, ya yi soyayya a rayuwarsa.
Kawai ta yi murmushi tana tunanin, ƙila da ya yi soyayya, ko da yana da aure, da wannan nasarorin bai cin musu ba, dan Sai ya fi mayar da hankali a kan gina iyalinsa, haka zalika da yana da yawan surutu babu lallai ya cimma abubuwan da ya cimma.
Saboda mata na son attention, da kulawa, babu lallai ya din ga samun isasshen lokacin tunani, da bawa ƙwaƙwalwarsa damar samar da abubuwa.
Ta yi ajiyar zuciya tana tuna Bukar, tabbas mata na son kulawa da attention, sai dai ta su soyayyar na fuskantar barazana, du da ƙoƙarin da Bukar yake yi a kan hakan. Sai dai gudun faruwar matsala ya sanya a ɓoye suke haɗuwa. Sai dai sam ba ta jin irin wannan zunzurutun soyayyar tasa a cikin ranta. Babban abin da ya sanya take tare da Bukar tausayinsa ne da take ji.
Sai kuma ta mayar da tunaninta kan Hanne, tare da son tabattar da abin da Saleh ya faɗa gaske ne?
"Kenan idan ina buƙatar yin nasara a rayuwata, dole na fara ajiye batun wannan gurguwar soyayyar tawa da ban ga ta inda zata haifar da ɗa mai ido ba." Ta yi maganar a zuciyarta.
"To wani hali Bukar zai shiga? Idan na jingine batun soyayyarmu" Wata zuciyar ta tambaye ta. Gaba ɗaya sai ta ji ta gaji, ta daina fahimtar abin da take karantawa, kawai ta rufe littafin ta kwanta.
"Bacci a Library Rahama" Ta buɗe idonta, sannan ta tashi zaune a hankali ta kalle shi ta ce "Ba bacci nake yi ba sir"
"Ƙarya na yi kenan?"
Ta girgiza masa kai, tana sunkuyar da kai.
Ya ce "Me ku ka shirya presenting ne, next week in Allah ya kaimu?" Ta ɗaga kai tana kallonsa.
"Press club i mean"
"Introvert" Ta faɗa a taƙaice.
Ya yi dariya ya ce "Rahama B Yelwa, Introvert kawai? Meye alaƙar introvert da presentation na press club? Ko da yake akwai alaƙa ai. Amma you went deep, ko personality ɗinki ki ke son yi wa mutane bayani a kai?"
Ta girgiza kai ta ce "No sir, ai am not introvert, za mu rubuta mu kawo maka ka duba" Ta yi maganar tana murmushi.
"To shikenan ina jiranki"
Ta tashi ta tattare litattafanta, ta fice daga Libraryn.
*****
Yau a makarantar dare, Alina bacci ne ya dame ta, dan haka ana tashi babu wanda ta tsaya jira, ta rungumo jakarta ta fito hanya. Tana ta uwar hamma, katse hammarta ta yi ganinsa a tsaye a ƙofar makarantar, ya saka ƙofar makarantar a gaba.
A hankali ta ƙarasa inda yake tsaye, tana ɗan layi saboda baccin da yake kanta. "Wani ka ke jira ne?" Ta yi maganar tana kallon ɗalibai da suke fitowa daga cikin makarantarsu.
Ya kunna fitilar hannunsa ya ce "Wucewa zan yi, sai na ga an ɗauke wuta"
Dariya ta yi ta ce "Saboda ina tsoron duhu ko? To na gode sosai da ka tuna da ni, ka taimake ni mu tafi" Ya jinjina kai su ka jera yana haska musu hanya.
Alina ta ɗan dube shi ta ce "Ka ce mini ka je garinku, ina ne garin naku? Kullum na tambaye ka baka gaya mini"
"Can wani guri"
"Ina?"
Ya ce "Wani waje ne, can ƙauye"
"To meyasa ka baro garinku ka dawo nan?"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Almajiri ne ni"
Alina ta ce "Almajiri kuma? Babba da kai haka, ba 'yan yara ne suke almajiranci ba? To ina ce makarantar ku?"
Ya ɗan yi jimm, jin yadda take ta jero masa tambayoyi kashi-kashi kamar shari'a. Ya numfasa yana tunanin amsar da zai bata daidai da hankalinta. Ya ce "Eh, na yi sauka ne, tuntuni, neman kuɗi nake yi, shi ya zaunar da ni, amma ina zuwa makarantar haryanzu ai ba a girma da neman ilimi ko?."
"Laa nima na kusa sauka fa, mu na kammala haddar izifi ashirin za a haɗa mu yi bikin sauka, Yaya ya ce zai saya mini ƙaton rago idan na yi sauka" Ta faɗa cikin farincikinki.
Ya ɗan yi dariya da gefen bakinsa ya ce "Hakan na da kyau, Allah ya sanya albarka"
"Amin. To yaya sunanka?" Ta yi tambayar daidai lokacin da suka ƙaraso layin.
"Bawan Allah"
Ta ɗan ɓata fuska ta ce "To ai kowa bawan Allah ne, sunanka fa da ake kiran ka da shi, sunanka na gaskiya"
"Mamman" Ya faɗa a taƙaice.
Ta yi murmushi ta ce Muhammad dai ko? Tun da a birni ka ke. Ni kuma sunana...
"Alina" ya ƙarasa mata.
Ta yi turus ta ce "A ina ka san sunana?"
Bai bata amsar ba ya ce "Sai da safe" Ta yi murmushi ta ce "To ai ba shi ne sunana na gaskiya ba, sunana na gaskiya Fatima".
Ya ɗan yi turus yana kallonta, fuskarsa ɗauke da murmushi.
"Ya na ga kana murmushi?"
"Sunan Innata ne da nake matuƙar so, duk da ba ita ta haife ni ba"
Alina ta yi dariya ta ce "Ashe kai ɗana ne, to ɗan albarka zan din ga ce maka"
Jinjina kai kawai ya yi, yana murmushi, ita kuma ta shiga gida. Murmushi ta ɗan din ga yi, da ta tuna saboda ita ya je makarantar su, saboda ya haska mata hanya. Da ta tuna abin da Yayanta ya yi masa sai ta ji babu daɗi, kasancewar yanzu ta fahimci yana da kirki, kawai dai ɗabi'unsa ne wasu lokutan kamar mara gaskiya.
Mamman kuwa bayan ya shiga ɗakinsa, ya zare rigar jikinsa, ya gyara shimfiɗarsa, ya fito da indomie a leda, ya zazzage a wani kwano, ya cinye ya sha ruwa. Ya ɗaga ƙasan 'yar katifar da ke ɗakin, ya din ga kallon ƙasan katifar sannan ya mayar da katifar ya gyara ya kwanta yana ɗan yin miƙa.
Ya ciro wayarsa daga gefen katifarsa, ya tura wasu code zuwa ga wata lamba. Ya juya ya kwanta.
*****
YELWA
Baffa ne ya yi zuguum yana sauraren radion da ke gabansa, yanayin fuskarsa ya nuna ruɗewa da tsoro.
Ya numfasa ya ce "Juma"
"Na'am" Ta amsa tana tattara hankalinta a kansa.
"Ki na jin wata masifa ko?"
"A ina?"
"A radion nan da nake ji"
Ta girgiza kai ta ce "Me aka ce?"
"Faɗan manoma da Makiyaya a can wani yanki, an yanka manoma yankan rago su kusan goma sha biyu da sunan ɗaukar fansa"
Juma ta waro ido ta ce "Yankawa kuma?"
"Wallahi yankawa, ga shi ina ji a radio"
"Innalillahi, yanzu Jauro sai a yanka mutum, kuma da wuƙa aka yanka su ko da me?"
Baffa ya ce "Ina zan sani, abin da dai suka ce kenan. Wallahi abin nan yana bani tsoro. Mu ma kusan irin wannan rikicin muke fuskanta tsawon shekaru, ina tsoron ya rikiɗe ya zama wani abu daban."
Juma ta ce "Babu abin da zai faru sai alkhairi da yardar Allah"
Baffa ya jinjina kai ya ce "Haka nake fata, amma haryanzu ina haƙurƙurtar da samarinmu, a kan lallai sai sun ɗauki fansar abin da aka yi mana. Ke dai Allah ya kyauta kawai".
*****
Rahama ce ke zaune a bakin kwanarsu, tana kallon 'yan hostel ɗinsu, sun sha kwalliya su na ta raye-raye kasancewar weekends ce. Sun saka bokitai da jarakuna su na ta kaɗe-kaɗe. Littafi ne a hannunta amma tana kallon littafin tana kallonsu, saboda abin da suke yi ɗin yana saka ta nishaɗi.
"Yelwa, kin noƙe kina wani murmushi, taso ki taka"
Cewar wata senior ɗin ta.
Rahama ta hau dariya tana girgiza kai.
Ruƙayya ta ce "Idan Rahama ta yi rawa, na yi alƙawarin bayar da kyautar sadine gwangwani goma wallahi" Shewa suka hau yi, Rahama kuwa rufe fuska ta hau yi tana dariya.
"Ai wallahi Ruƙayya kin san sadine ɗin nan ba zai ciwu ba, in dai sai Rahama ta yi rawa za a ci shi. Ita a makiyayan ma ma irin na 1980s ɗin nan ne."
Suka din ga tsokanar Rahama, ƙarshe ta bar musu Hostel ɗin. Naja ce ta biyo bayanta tana faɗin "Yaya Rahama" Rahama ta tsaya ta waiwayo ta ce "Na'am Nana".
"Dan Assignment ne da ni, na kasa ko za ki koya mini"
Rahama ta ce "Me zai hana na koya miki, wanne subject ne?"
Naja ta ce "Your favourite Maths"
Rahama ta ce "Mu je Library, sai mu yi a can" Naja ta jinjina kai, ta karɓi litattafan hannun Rahama suka tafi. Boarding kenan, gidan ka zo na zo, amma duk ƙin ka da mutane haka zaka haɗu da wanda za ku rayu tare tamkar yan gida ɗaya.
Duk da akwai ƙalubale, amma ana koyon darussan rayuwa.
*****
"Assalamu alaikum. Salamu alaikum" Cikin bacci yake jin 'yar muryar na yi masa sallama. Da kyar ya iya motsawa, ya tashi ya saka rigarsa, ya buɗe ƙofar. Da idanunsa ta fara tozali, ta ɗan ja da baya a tsorace.
"Ahh, ka yi haƙuri, ban san bacci ka ke yi ba, da dam..dama takalimina na kawo, yi haƙuri." Ya miƙa mata hannunsa yana tsare ta da ido. Jikinta na ɗan rawa ta miƙa masa takalaman nata.
Ya fito tare da kayan aikinsa, sai dai yau ta ga fuskarsa a tsuke sosai da sosai. Ta lura da yadda yake aikin yau a hankali sosai da sosai.
So take ta tambaye shi ko lafiya, amma ta kasa sai satar kallonsa da take yi. Gani ta yi ya tsaya cak da wanke takalmin, yana ɗan rintse idanunsa.
"Meyafaru?" Ta faɗa a ɗan rikice tana kallonsa.
Da hannunsa ya nuna mata cikinsa, ya tashi, ya ajiye komai a gurin, ya koma ɗakinsa. Jikinta na rawa ta tashi ta tafi gida. A kitchen ta samu Nadiya tana aikin girki. Cikin damuwa ta ce "Antynmu idan ki na da maganin ciwon ciki ki bani zan ba wa Mamman cikinsa ne yake ciwo"
Nadiya ta tsaya ta ce "Waye hakan?"
"Mai gyaran takalmi"
"To ba shi da lafiya, to Allah ya ba shi lafiya, duba jakar magungunan ki gani idan akwai" jikin Alina na rawa ta shiga ɗakin Anty, tana duba jakar da suke ajiye magunguna, ta dubo maganin ciwon ciki. Ta fito tana faɗin "Anty na samu, amma akwai sauran kunu? Kin ga ba zai sha magani bai ci komai ba"
Nadiya ta ce "Eh gaskiya ne, amma dai da yayanki na ajiyewa kunun, kin san zai iya nema da rana ya ce zai sha"
Cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Antynmu ki kawo a ba shi, sai ki cewa Yayan kununan ya ƙare.
Nadiya ta ce "To Alina, a ba shi Allah ya sauwwaƙe, ya sanya kaffara"
Ta tsiyaye kunun gyaɗar a kofi mai murfi, ta yi waje da sauri. Nadiya ba ta kawo komai a ranta ba, saboda sanin halin Alina. Wasu lokutan a hanya za ta tsinto almajiri, ta kawo shi gida ta ce sai a ba shi Abinci ko ta ce sai Isma'il ya ba shi kuɗi. Duk da rashin mu'amala da ita da samarin unguwar ba sa yi, amma tana shiri da alamajirai sosai da sosai. Saboda tana son bayar da abu.
Cike da wauta da ƙuruciya, Alina ta faɗa ɗakin Mamma, ba tare da sallama ko neman izini ba. Da wani irin mugun zafin nama, ya saka filo akan wani abu ya rufe. Idanunta ba su kai ga tantance mata abin da ta gani ba, ya rufe da fulon.
Ta ɗan sororo amma ta basar ta miƙa masa kofin kunun ta ce "Ga kunu sai ka sha, sai ka sha maganin. Tsigar jikinsa duk ta tashi, saboda azabar ciwo har wani gumi ne yake tsatsafo masa ta kan karan hancinsa. Ya saka hannu ya karɓi kofin. Kunun da zafinsa ya kafa kai ya din ga zuƙarsa. Bai shanye ba, ya miƙa mata hannunsa, ta saka masa maganin ya ɓalle ya haɗiye ba tare da ko ya haɗa da ruwa ba.
Ta tsaya cike da rashin sanin abin yi tana jera masa sannu. Bai amsa mata ba, sai yatsun ƙafarsa da ta ga yana ta lanƙwasawa, alamar yana cikin matsanancin ciwo.
Ya juyo da fuskarsa a hankali, duk gumi ya tsatstsafo masa, wasu irin jijiyoyi sun shata a goshinsa raɗa-raɗa, sai idanunsa da suka yi jawur.
"Je ki" Ya furta da kyar. Maimakon ta fita sai ta tsaya tana kallonsa, ganin kamar zai fita hayyacinsa.
"Ki fita!" Ya yi magana cikin tsawa, yana nuna mata hanyar fita. saboda rikicewa ba ta san yadda aka yi ta ganta a waje ba. Ta kwashe takalmanta ta nufi gida a tsorace.
Nadiya ta ce "Alina yanzu nake shirin fita na ga ko lafiya, ki ka daɗe, kin san fa fita zan yi, zan je Asibiti"
Alina ta ce "Lafiya ƙalau, sai kin dawo" Ta shige ɗaki. Nadiya ta bi Alina da kallo tana mamakin meya tsorata ta haka, ba ta sake magana ba ta fita. Cike da tausayawa Alina take tuno yanayin da ta bar shi a ciki, amma da tuna tsawar da ya yi mata, sai ranta ya ɓaci gaba ɗaya, ta ji haushi ba kaɗan ba"
Sai dai ba ta daina tantama da zuciyarta ba a kan abin da ta gani a ɗakin nasa ba. Idan ba gizo idonta ya yi mata a kamar dai bindiga ta gani a ɗakin ya saka pillow ya rufe. Sai dai ta ƙi yarda da hakan ta gani, ta basar ta ci gaba da kokwanton ba bindiga ta gani ba.
Sai dai hakan bai hana ta lokaci-lokaci ta din ga leƙa ƙofar gida ba, ta ga ko za ta hango ya fito ba.
*****
Kacalla ne tsaye a cikin dokar daji, tare da Sadauki, gabansu wani buhu ne a ajiye.
Ya dafa kafaɗar Sadauki yana kallon idonsa.
"Sadauki amanar kacalla"
ya yi murmushi ya ce "Allah ya taimaki Uban ɗakina"
"Ka ga dai yadda lamari ya kaya, na yarda da kai na san ba za a samu kowace irin matsala ba da yardar Allah. Ka je ka ƙarasa shirya komai da mutanenka, duk abin da ake ciki, mu yi waya."
Sadauki ya ce "An gama shugabana, ka yi layar zana, ka bi ta gabasa zan Kudu da kayan, ka saka a gyara mana hanya"
"Shikenan babu damuwa, Allah ya tsare"
"Amin" ya saɓa buhun nan a kafaɗarsa ya yi gaba.
*****
ALINA
wunin ranar ba ta sake ganin gilmawarsa ba, abin ya din ga damunta, ta din ga tunanin ko yaya yake.
Monday da ta fito makaranta, ta tarar da ɗakinsa a rufe, amma bai saka mukulli ba.
Har guri ta samu ta ɗan tsaya, ta gani ko zai fito, amma shiru ta gaji ta tafi, dan sai da ta makara ma.
*****
YELWA
Baffa ne yake tafe sannu a hankali, yaje ya bawa wani yaro maganin maciji, saboda maciji ya sare shi a ƙafa, ya duba ya ga wani mara lafiya da ya yi wa ɗorin karaya, daga nan ya biya kasuwa, ya ɗan yi sayayya ya nufo gida.
Yana ta sauri, ya ji ana yi masa sannu da zuwa, ya tsaya ya waiwaya ya ga wane ne, kawai ya ga Saleh. Baffa ya yi shiru bai ce komai ba, ya sa kai zai ci gaba da tafiya.
"Ba za ka amsa sannu da zuwan nawa ba? Babu faɗa mai ya kawo gaba?"
Baffa ya tsaya, ya kalle shi ya ce "Ɗan samari, ina gama ka da Allah, idan ka san shi. Kana kuma tsoron sa, ka fita daga harkata" Ya yi maganar idanunsa suna yi ja, muryarsa na rawa.
"Baba tun da Allah ya haɗa mu zaman guri ɗaya, ai haraka ta zame mana dole. Abin da zai iya cutar da kai na gano, na ce bari na sauke hakkin maƙwabtaka"
Baffa ya tsaya cikin rashin fahimta yana kallon Saleh. "Duk da lokaci ya so ya ƙure, amma ina tausayawa yadda ƙaddara ke bin ahalinku, mussaman ma kai.
Duk da Ramata ba ta gari, amma kana iya ɗaukar mataki."
Baffa ya ce "Ramatan kuma me ta yi muku, yarinyar da tana makaranta ma?"
"Tana soyayya da ɗan uwana Bukar, wanda ka sani na sani, babu ga maciji a tsakaninmu da ku, duk abin da ya faru ka kuka da 'yarka, na gaya maka ne ka yi wa tufkar hanci, kar ita ma ka rasa ta"
Cikin mamaki Baffa yake kallon Saleh, sai dai ya gaza cewa komai, sai bin sa da yake yi da ido baki buɗe cikin mamaki. Sam bai ji maganganun Saleh sun shige shi ba. Yarinyar da ba ta garin ma, ga ta da gudun magana yaushe za ta je ta yi wannan katoɓarar. Kawai ya sanya wa zuciyarsa ƙarya Saleh yake yi.
*****
Bayan kwana biyu.
An taso 'yan makarantar su Alina, Hafsa ta ce "Ke na sato mana littafi, yau zan karance shi cikin dare in sha Allah"
Alina ta ce "Haba dai ya sunansa?"
Hafsa ta ɗan yi shiru ta ce "Na manta, amma dai zan karanta mana"
"To shikenan, sauran gobe in Allah ya kaimu, ki ƙi ba ni labarin. Allah dai ya sa an zuba soyayya a ciki"
Hafsa ta yi dariya ta ce "Ai da ganin bangon littafin ma, ke dai ki jira, zan karance mana shi, shi kuma mu ji me aka yi a cikin sa"
Alina ta ce "Kin san littafi idan da soyayya a ciki, subhanallah har wani nishaɗi yake sakawa."
Hafsa ta gyaɗa kai ta ce "Ina ta ƙoƙarin ganin na sake da yaya Hafiz ɗin nan, nima mu din ga soyayyar nan na kasa, kunya ma nake ji wallahi"
Alina ta kwaɓe baki ta ce "Ke kenan, da aka bawa damar ki yi soyayyar ma, ni duk wanda ya ce yana sona zagi yake sha a gurin Yaya ya kore shi, wai ni yarinya ce. Idan aka ganni zata ake babba ce ni"
Hafsa ta ce "Kuma ga maza na sonki, amma wataƙila sai kin yi candy zai bari"
"Mhmm ai ni na zubawa sarautar Allah ido ne ma, na bar Yaya da halinsa"
Tun da Alina suka fito daga makaranta, take ankare da yana bin su a baya, amma ta basar, suke ta hira da Hafsa. Amma a ƙasan zuciyarta, ta ji daɗin ganinsa da alamar ya warke. Suka yi sallama da Hafsa ta bi hanyar gidansu, Alina ma ta bi tata hanyar.
"'yar ƙwalisa" Ya yi maganar yana ɗan ƙara sauri.
Sauri ta ƙara ita ma, ta ƙi ko waiwayowa, ta basar da shi.
"Alina" ya kira sunanta. Ta tsaya tana zumɓura baki, ta waiwaya kai tana kallonsa.
"An taso?" Ya yi maganar yana kallonta. Ta yi shiru tana kawar da kanta gefe.
Ya sake cewa "Amm dama zan ce miki na gode ne"
"Da aka yi me?" Ta yi maganar tana tattaro jarumtar kallon idonsa amma abu ya gagara.
Ya ɗan ja numfashi ya ce "Maganin ciwon ciki, da kuma Abinci da ki ka bani"
Ɗan murguɗa baki ta yi ta ce "Daka yi mini tsawar" Ta yi maganar tana tura baki.
Ya ɗan rungume hannayensa ya ce "Ohh zafin ciwo ne fa, kuma ina jin tsoron kar a zargi wani abu, mussaman yayanki, na san ya ganki a ɗakina zai iya yi mini duka ma"
Idanunta ta ɗaga tana ƙare masa kallo, sai dai ba ta kalli idonsa ba, ta tura baki ta ce "Tun da abin alkhairi na yi maka, sai ka gaya mini a hankali ai. Amma ka yi mini tsawa. Kuma ni ba na son a yi mini tsawa, sai da na tsorata"
Ya yi shiru yana kallonta.
Ba tare da ta kalle shi ba a shagwaɓe ta ce "ka bani haƙuri to"
Ya yi turus yana kallon 'yar abar da da kaɗan ta fi ƙugunsa, tana iƙirarin ya bata haƙuri, kuma yanayin fuskarta ya nuna da gaske take abin da take faɗa har zuciyarta...
Ayshercool
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
Sai shaidar biya ta 08081012143
