Sara Da Sassaka Page 5 Complete by Ayshacool


SARA DA SASSAƘA 

YOTA 002

P5

A tsorace Ya yi turus yana kallonsa, jikinsa a sanyaye yana jiran cin mutuncin da Isma'il zai yi masa a wannan karon.

Sai dai ga mamakinsa bai yi masa magana ba, ya raɓa shi ya wuce. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, ya juya ya tafi.

"Alina" ya shiga gida yana ƙwala mata kira.

"Na'am" Ta yi maganar tana fitowa daga ɗaki.

"Me ya haɗa ki da mutumin nan?"

A shagwaɓe ta ce "Yaya har ka bani tsoro, na dawo daga gidan su Hafsa, aka ɗauke wuta a hanya, shi ne ya haska mini fitila"

"Gidan su Hafsan ne ki ka je ki ka yi zamanki har isha'i ko Alina? Wallahi da na san ba ki dawo ba, har gidan su Hafsan zan je na same ki, na zane ki tun daga can mara ji kawai"

Ta risunar da kai ta ce "Ka yi haƙuri dan Allah"

"Ni ƙyale ni, sai kin yi laifi ki wani kwantar da kai kina a yi haƙuri kamar kyanwa"

Ta yi shiru tana sunkuyar da kai. A gida ya yi sallar isha'i, sannan Nadiya ta zuba masa Abinci.

Ganin yana jin haushinta, ya sanya Alina ba ta yi masa surutu ba kamar yadda ta saba, ta ja bakinta ta yi shiru. 

Can Alina ta ce "Antynmu ni ko na tambaye ki mana"

"To tambai, me za ki tambaya?"

Alina ta karkace ta ce "Anty wai dan Allah ku na faɗa da ke da Yaya?"

Nadiya ta ce "Ai ga yayan naki a nan tambaye shi mana" Alina ta noƙe kafaɗa.

Nadiya ta yi dariya ta ce "Meyasa ki ka tambaye ni?"

"Hafsa ce take cewa babansu na zagin mamansu. Ya ce aure zai yi wa Hafsa da ta yi candy, shi ne ta ce ba ta son ta yi aure, mijinta ita ma ya din ga zaginta"

Nadiya ta numfasa ta ce "Duk yadda muke sonki ba kya laifi mu yi miki faɗa?" alina ta jinjina kai.

"To babu zamantakewar da babu saɓani, amma fahimtar juna ke kawo zaman lafiya.  Ni da yayanki...

Yaya ya katse su a fusace "Shiyasa ba na son yawace-yawacen nan, a can ake gurɓata miki tunani. Babu wani mijin kirki da yake zagin matarsa. Ni kin taɓa ganin na zagi Masoyiyya?" Alina ta girgiza kai.

"Amma idan ta yi laifi, ina yi mata faɗa, shi ma ba kullum nake yi nata a gabanki ba, haka mijin arziki yake. Dan haka baban ƙawarki mahaukaci ne"

Nadiya ta ce "Subhanallah baban ƙawarta ne fa"

"To babanta ne? Mahaukaci ne mana, banda mahaukaci ya za a yi yaranka su san kana zagin babarsu a gabansu dan hauka. Ke tashi ki tafi ki je ki kwanta. Kema tashi mu tafi" Alina ta tashi sumi-sumi ta tafi ɗakinta.


Ko da suka shiga ɗaki Nadiya ta ce "Yaya 

Masoyi, ka din ga gaya wa Alina gaskiya fa. Idan mu soyayya muka saka a gaba lallai ne ta samu miji irirnka".


Ya haye kan gado yana faɗin "Na raini yarinyar na aura maka, ka zagar mini ita, da kuwa na fasa wa mutum baki wallahi. Balle a ce duka sai na kusa binne mutum da ransa ba"


Ta tuntsire da dariya ta ce "Allah mai 'ya"


Ya ce "Sa wasa, ai yau ko da wani aka kama Alina, gara ya sako mini ita salin alin, a kan ya taɓa lafiyarta ko ya zage ta. A yadda Alina take babu yadda za a yi ta yi wa mutum laifin da zai dake ta ko ya ci mutuncin ta. Babu abin da ya yi mini zafi da laifin da ta yi, na aura wa mutum ita ya wulakanta mini sai ya gwammace mutuwarsa wallahi. Idan ta yi ba daidai ba, gara mutum ya dawo mini da kaya ta ta fasa auren"


Nadiya ta ce "Ohh anya zaka iya aurar da ita kuwa?"


"Eh mana, shiyasa ke ma nake ƙara lallaɓa ki masoyiyya, saboda kar na zaluce ki, wani ya auri ƙanwata ya cutar da ita

Allah ya ba wa Alinana wanda so ta ya kula mini da ita kamar yadda nake sonta. Shiyasa sai na dirje na tantance yadda yakamata zan ba wa mutum" Ya yi maganar yana kwanciya a jikinta. Ta so ta furta abin da ke ranta, amma ta san tana maganar za su yi faɗa, a dole ta haɗiye ta yi shiru ta rungume shi.


****


Yana daga kwance ya dafe kansa, da sallama ta shigo bakinta ɗauke da sallama, ya amsa ba tare da ya ɗago ba.


"Ashe kana nan, ina ƙasa ina ta bulayin neman ka ai"

Ya sauke hannun a hankali ya gyara kwanciyarsa ya ce "Ina nan"


Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ni wai dan Allah ya maganarmu ne?"


"Wacce kenan?"


"A'ah maganar motocina mana, waɗanan fa tsofaffi ne wanda waccan first ladyn ta yi amfani da su ne, a cikin allowances ɗina ka bayar da umarnin a sayo mini sababbi, wannan na rarrabawa mutanen da suka yi mana wahala"


"Dan Allah ni dai a yanzu ki ƙyale ni, mene ne aibun motocin nan, daga zuwanmu sai mu saka wa dukiyar al'umma wawa"


"Haba dan Allah, ba batun saka wawa bane ba, abu ne da yake a rubuce fa, ni dai gaskiya ka yi wani abu a kai, ni wannan motocin sun yi mini tsufa gaskiya"


"Shikenan na ji, zan yi magana da Halilu su duba"


Ta sauke numfashi tana murmushi ta ce "Ko kai fa" Ta tashi ta fice, ya bi ta da kallo, sam ba ta damu da jin damuwarsa ko ƙoƙarin taimaka masa ya sauke hakkin al'umma ba, kawai hanyoyin azurta kanta take nema.


Ya janyo wardrobe ɗin gefen gado, ya ɗaukko waya ɗaya ya gyara kwanciyarsa ya hau internet.


Twitter ya fara shiga ya dudduba gidajen jaridu, da al'amurn siyasar duniya. 

Ya gama da twitter ya shiga wani shafin.


Shafinta suka fara hasko masa, fuskarta ɗauke da murmushin da baya gushewa daga fuskarta, a duk lokacin da zai ganta a kan screen ɗin wayarsa.


"Amincin Allah da yardarsa su tabatta a gare ku, ma'abota shafina. Kamar kullum ina miƙa saƙon gaisuwa ta musamman ga Babana na kaina, kuma his excellency mr. President. Eh mana so so ne amma son kai ya fi. Babana ne, ɗan yankina kuma ɗan garinmu. Yau ba labari zan ba ku ba. Har kullum nice taku Baby Laila Umar Faruk. Ku zo mu yi wa mr. President ɗan waken gujjiya. Ya yi abincin dare da shi"

Sai ya shagala a shafin nata, yana kallon yadda take gudanar da aikin ɗan waken komai daidai na talaka, sai dai tana yi tana bayyana ayyukan gwamnatinsa, tare da koɗa shi a cikin videon. Bai san lokacin da ya shagala da kallon matashiyar yarinyar ba, har ya manta da wasu daga cikin damuwoyinsa ba.

A hankali ya furta "Lallai har abada ba a iya biyan masoyi. Wasu ayyukan nasa yadda take zayyano su, ka san ba ƙaramin bincike ta yi ba, kafin ta gano su. Dan wasu ma tun kan ya ci zaɓe. Ya tsinci kansa da shiga shafinta, ya din ga duba videos ɗin ta na baya. Ya kan ganta lokaci zuwa lokaci, amma yau ne ya tsaya sosai yake kallon abubuwan da take yi.

Sai dai tana fuskantar ƙalubalen cin mutunci daga masu bibiyar shafin nata, mussaman waɗanda suke adawa da gwamnatinsa. Sai dai kaf babu wanda take yi wa martani da cin mutunci.


Alarm ɗin wayarsa ya fara ƙara, ƙarfe ɗaya da rabi na dare, ya tashi tsam ya ajiye wayar, ya tafi banɗaki ya yi wanka ya fito ya fice daga ɗakin.


****

Awanni biyu kenan Baffa su na tafiya a mota, a hanyarsa ta dawowa gida daga kai Rahama makaranta. Tun daga ranar farko da ya kai ta makarantar kwana da ƙanan shekaru, duk lokacin da ya kai ta, yana jin babu daɗi a ransa. Amma a wannan karon ba iya kewa ce ke damunsa ba, fargaba ce da ya rasa ta mece ce. Kawai ya din ga maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un.


Ɓangaren Rahama ma, haka ta din ga jin wannan fargabar da ta kasa tantance dalilin jin hakan, duk da tana cikin farincikin cin jarrabawa da ta yi.


*****


Gaba ɗaya hankalinsa ya tattara a kan matashin, da fuskarsa ke ɗauke da matsananciyar damuwa.


"Majeed, ka nutsu ka yi mini bayani, are you serious wai?"


"Ta yaya zan yi jokes da serious issue like this. Wallahi Alpha da idanuna da kumma kunnuwana. Su Okoro ba su san me aka yi ba. Oga  shi ya ce na ba su hanya su wuce, ka ji zuciyata ka ji zafin da zuciyata take yi...


"Shhh ka san me zai faru? Wannan maganar daga ni sai kai, kar ka kuskura ta fita, idan ka bari aka ji maganar nan wallahi kashinka ya bushe"


Majid ya shafi fuskarsa ya ce "Anyway ban gaya wa kowa ba, kai kawai na gayawa in sha Allah ba wanda zan sake gaya wa" Alpha ya daki kafaɗarsa ya ce "Good boy, ka koma office"


Majid ya jinjina kai, ya juya ya fita.


Bayan fitarsa Alpha ya ɗaukko wayarsa, ya daddana, ya kara a kunnensa. Sai dai har wayar ta gama ringing bai ɗaga ba. Ya sake buga wayar ta sake ringing ta gama ba a ɗaga ba. Ya ja guntun tsaki tare da faɗin "Ɗan rainin hankali, babu wanda nake yi wa kira sama da ɗaya idan ba kai ba" Ya yi maganar yana ajiye wayar.


****

Tun da ta fito daga gida yake kallonta, tana tafe tana ta karkaɗe uniform ɗin ta, duk da gugar da su ka sha, da hankicinta a hannu, ta durƙusa ta goge takalmi ta karkaɗe uniform, ta karkaɗe jakarta. Har ta zo tsakiyar layin abin da take ta yi kenan. Sai da ta ɗago suka haɗa ido, sai ta yi murmushi, shi kuma ya sunkuyar da kai, ya ci gaba da kallon Alqur'anin hannunsa. Sai da ta zo inda yake sannan ta risuna ta ce "Ina kwana"


"Lafiya kalau" Ya amsa yana ɗan ɗagowa cikin tsoro, saboda fargabar kar yayanta ya gansu.


Ta sake cewa "An tashi lafiya?"


Sai ya jinjina kai kawai.


"To na gode da haska fitilar jiya da daddare" Sai ya ɗan yi murmushi kawai.


Ita ma murmushin ta yi, ta ce "Da aka ɗauke wutar nan fa tsoro ne ya kama ni, ba na son duhu, ina tsoron duhu kwanan ne na daina kwana da fitila ma"


Ya ɗan kalle ta ya yi murmushi, ƙamshin turaren da take yi, duk ya cika gurin da ƙamshi.


"Na tafi makaranta, idan ka idar ka saka ni a addu'a"


"In sha Allah" Ya furta a hankali yana jinjina kai.


Ta ce "To na gode"


Har za ta tafi ya sake cewa "Ba ki kawo takalmi an wanke ba" Ta kalli ƙafarta ta kalle shi ta ce "Goge shi kawai na yi da duster, ai bai yi datti ba ko?"


"Kawo a saka masa mai" Ya yi maganar yana kallonta. Duk da kwarjinin da yake yi mata sai da ta yi murmushi ta ce "Ai ba ni da kuɗi yau".


"Eh kawo" Ya yi maganar yana fito da kayan gyaran takalminsa.


Ta zauna a dakalin gefensa, ta ciro masa takalman. Ya zauna ya ɗauki takalmin nata tomes, ya fara gogewa.

A zuciyarta take faɗin dama ya cire wannan gashin na fuskarsa sai ya fi kyau.

Ya shammace ta ya ɗago idanunsa, ta yi saurin sunkuyar da kanta, tana goge jakarta. Ya kammala goge mata ya ajiye mata a gabanta. Cikin murmushi ta saka hannu ɗago takalman ta ce "Wow wannan ai sai na gano fuskata a jikin takalmin nan,  ya yi kyau sosai ya gogu,  na gode sosai Allah ya saka da alkhairi. Ka na bi na bashin wankin takalmin nan" Ta ƙarasa maganar tana ajiye takalmin a ƙasa. Tana kallon yadda yake  ta ƙyalli.


Ya jinjina mata kai, ta saka takalman ta tashi ta tafi.


****


Hanne ce take kallon Bukar, ya gyara zamansa ya ce "Hanne, Ramata ce ta ce mini na gaya miki, saƙon nan, cewar abin ɓoye ya kusa fitowa fili, me hakan yake nufi?"


Hanne ta sunkuyar da kanta, hawaye ya fara gangarowa daga idanunta.

"Ki yi mini bayani, me Ramata take nufi da abin da ta faɗa?"

Hanne ta girgiza kai tana sunkuyar da kai.

"Hanne ki yi mini bayani kin san me take nufi"


Ta ɗago fararen idanunta. Hanne baƙa ce mai fashin goshi irin nasa. Ta ce "Yaya mene ne alaƙarka da Rahama ne, har ta yi wannan sakewar da kai, ta baka saƙo ka gaya mini?"


Ya tsuke fuska ya ce "Ina tambayarki kina tambayata?"


Ta ja numfashi ta ce "Ina kyautata zaton alaƙar da ke tsakaninka da Ramata, ita ce ta shiga tsakanina da yayanta. Kaf Yalwa Rahama ba ta da ƙawar da wuce ni, na san halinta ciki da bai, bana raba ɗaya biyu soyayya ku ke yi"


Ba shiri ya gyara zamansa yana waiwaye da fatan babu wanda ya ji abin da ta faɗa, ya yi ƙasa da muryarsa ya dube ta da kyau ya ce "Hanne, kar dai abin da nake tunani ne, dama saboda ke ne aka kashe Iro?" Ta fashe da wani irin matsanancin kuka tana kallonsa.

"Hanne dama saboda haka ne, aka saka miki takunkumi aka hana ki shiga, aka hana ki fita? Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace irin masifa ce wannan?"


Hanne ta haɗa kai da gwiwa tana wani irin kuka, mai tsuma zuciya. Saleh da ke laɓe a jikin taga ya ja da baya yana ƙwafa, ya fice daga gidan.


*****


Dandazon 'yan mata ne, suke ta ɓarkowa daga area classes zuwa hostel ɗinsu, kasancewar an tashi daga ɗaukar darasi.

Sannu a hankali cike da nustuwa take takawa, fuskarta ɗauke da yanayi na gajiya, ko da ta shiga Hostel ɗin su, kai tsaye kwanarsu ta wuce.

Cak ta tsaya tana murmushi, wadda take yi wa murmushin, ita ma ta hau murmushi ta ce "B Yalwa, ina ta addu'a Allah ya sanya kar a yi miki transfer" Ramata ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita tana faɗin "Anty Ruƙayyata, dama za ki dawo, na ga sati guda kenan da dawowa amma shiru ba ki dawo ba, har na fid da ran za ki dawo"


Anty Ruƙayya ta ce "Ina can ina ganin Likita ne, ba ni da cikakkiyar lafiya, sai da na gama sannan aka dawo da ni. Wai ƙodata ce ke cikin hatsarin kamuwa da ciwo"


Cikin tausayawa Rahama"Allah sarki, ya jikin naki?"


"Alhamdillah. Na samu sauƙi sosai da sosai"


"Allah ya ƙara afuwa"


Ruƙayya ta ce "Amin, su Rahama an shiga Ss1 ina fatan komai normal?"


Rahama ta jinjina kai tana murmushi. "To Alhamdillah, duk da ba na jinki, ƙwaruwa ce ke, amma duk abin da ba ki gane ba, ki yi mini magana Rahama, iya wuya sonake muƙamin headgirl ko health prefect kar ya bar kwanar nan tamu mai albarka, dan haka za mu ƙara zage damtse a kan karatu"


"To iyayen son zuciya, wallahi kuwa sai ya bari, ko ba kwa so" Cewar ta gefen gadon Ruƙayya, da take class mate ɗin Ruƙayya.


Ruƙayya ta ce "Ƙwalli ki kiyaye ni, so so ne amma son Kai ya fi ehe, an san yan kwanarmu dai akwai kai"


Rahama dai murmushi kawai take yi, ba za ta taɓa mantawa da Ruƙayya ba, lokacin da aka kawo ta, ga ƙuruciya, ga ƙauyanci, kusan ma ƙyamarta ake yi. Ruƙayya ce take yi mata komai, dan haka akwai shaƙuwa sosai a tsakanin su, yanzu Ruƙayya na ss3 Rahama kuma ss1 wanda suka yi candy head girl da health prefect 'yan kwanarsu ne, Ruƙayya aka bawa riƙon ƙwaryar head girl. Ta kuma bawa Rahama gudunmawa sosai a wajen karatu.


Kamar kullum bayan dawowa daga pref, sai da Ruƙayya ta tara 'yan kwanarta su Rahama, suka yi karatu, sannan suka hau gado domin su kwanta


A kan gadon ma, Rahama addu'oin kwanciya bacci ta yi, ta ɗan sake buɗe litattafanta tana karantawa, bacci ya yi awon gaba da ita.

Misalin ƙarfe uku saura, Ruƙayya na gadon ƙasa tana karatu ita ma, kawai ta ga Rahama ta diro daga saman gado, a gigice za ta yi waje. Da sauri ta fito daga net, ta riƙo Rahama.

"Rahama lafiya kuwa?" Gaba ɗaya bata cikin nutsuwarta, kamar wadda hankalinta zai gushe. Ruƙayya ta sake cewa "Rahama lafiya kuwa?...


"Hayaniya na ji ne"


"Wace irin hayaniya kuma? Mafarki ki ke yi, amma ba wata hayaniya" Da kyar ta lallaɓa Rahama ta koma kan gadonta ta kwanta, amma zuciyarta na ci gaba da bugawa, saboda ita dai kamar a zahiri ta ji hayaniyar mutane.


Sai dai kwanciyar tata babu wuya, ta tafi mafarkin abin ƙaunarta da bai san tana yi ba. Mutumin da ba ya shafe sati bai zo a mafarkinta ba. Wasu lokutan yanayin mafarkin har kunya yake saka ta.

*****


Tun da Alina taje makaranta, take kaffa-kaffa da takalmin nan, take goge shi, gani take idan ta bari ya yi ƙura bata kyauta ba, saboda yadda ya dage ya goge mata shi ya saka mata mai, ba tare da ta bayar da ko sisi ba


*****

Cikin girmamawa yake kallon ubangidansa, ya risunar da kansa yana ɗaga masa babban yatsansa alamar jinjina ya ce "Kacalla mai Allah, ka tsare gida ka tsare daji, uban gidana na kaina, gugan ƙarfe sha kwaramniya"


"Sadauki"


"Na'am Kacalla"


"Ka san mutanen nan, miyagu ne, ba kuma abin yarda ba ne, dan haka za mu yi musu aiki, bisa ga tsatstsauran sharaɗi, da ko an shiga hanyar da ba za ta ɓulle ba, mutuwar kasko za mu yi da su. Sannan dole Jagora ya san da sun bayar da wannan aikin"


Sadauki ya ce "Wannan gaskiya ne"


"Ya ce maka su ne sitiyari mu ne inji, su dirje mu yadda suke so kenan yadda suke so ko? Tabbas sai mun je tsakiyar hanyar za mu ɗau zafi mu tsayar da aikin motar. Za mu yi musu aiki, amma mu ma mu na da bamu sharuɗan. Idan suka cika sharaɗinmu. Za mu ba su abin da suke so koma fiye, idan suka saɓa yarjejeniyar injin mota zai buga a tsakiyar hanya"


Sadauki ya yi dariya yana gyaɗa kai, Allah ya taimaki uban gidana"


Ya gyaɗa kai yana murmushi tare da faɗin "Ka huta na wajena"


*****


Hafsa har mamakin Alina take yi, ta saba idan suka taso daga makaranta, har sake tsayawa suke yi a bakin hanya, su sha hira, har lokaci ya nemi ya ƙure musu, sannan su rabu, amma a kwanakin nan, sai ta lura Alinan har Alla-Alla take yi su rabu ta tafi. Ta daina tsayawa su yi wannan hirar da suka saba.


Yau ma ana tashi daga makarantar, Alina ba ta ko tsaya Hafsa ba, ta fice ta nufi hanyar gida. Sai dai duk saurin da take yi, tana shigowa layinsu, ta tarar da inda yake kwana, a rufe da kwaɗo. Take jikinta ya yi sanyi, ta so sake yi masa godiya amma ba ta tarar da shi ba.

Ta shiga gida da sallama, ta tarar da Yaya da Anty, su na ta aikin kayan ciki.


Ya ɗago kai ya kalle ta ya ce "Alinan Yaya, an dawo?" Ta gyaɗa masa kai.


Nadiya ta ce "Yau mai kurmanataka ce kenan?" Ba ta ce komai ba, ta nufi ɗakinta. Yaya nata nuna mata kayan ciki, yana tsammanin ta yi murna, dan masoyiyyar nama ce, amma ya ga ba ta yi murna ba.

Gaba ɗaya ta ji babu daɗi, rashin ganin mai gyaran takalmi da ba ta yi ba, mutumin da ko sunansa ba ta sani ba.


Da azahar ma ta shirya ta fita Islamiyya,  ta dawo, ta tafi makarantar dare ta dawo, amma babu shi babu alamar sa, ɗakin nan a rufe. Haka kurum ta din ga jin babu daɗi, tare da tunanin ina ya tafi haka?.


Da daddare, kamar an mintsini Alina ta ce "Antynmu kin san wani abu?"


"A'a Alinanmu"


"Ɗazu mutumin nan, na ƙofar gidan Malam Sadi, ya ce ban kawo masa wankin takalmi ba, na ce masa ai ba ni da kuɗi ne, ya ce na kawo ya wanke mini, ya wanke mini kyauta. Kuma tas ya fita takalmin. Ni fa ko, ban taɓa ganin an wanke mini takalmi ya fita kamar yadda yake yi ba shi"


Kasa haɗiye abincin ya yi, ya tsura wa Alina ido.


Nadiya ta ce "Aikuwa ya kyauta, kin ga yanzu kun ji kunya da ke da yayanki, kun je kun tara masa jama'a, kun yi masa tijara, kuma ya zo yana miki mutunci. Shiyasa wulaƙanci babu kyau.


Alina ta yi murmushi ta ce "Wallahi da tsoro yake bani ne, mussaman idanunsa ƙwal-ƙwala, ashe yana da kirki, idonsa ne abin tsoro, ƙatun-ƙatun kuma jajaye, idan ya kalle ni sai na ji gabana ya faɗi. Har ruɗewa nake yi wallahi, na ji ni kamar dai ba ni da gaskiya ko dai makamancin haka. To yanzu ba na bari ya kalle ni, na daina haɗa ido da shi kwata-kwata dama bana iya haɗa idon ma da shi. Ga shi ya wanke mini takalmina. Da na dawo daga gidansu Hafsa ma aka ɗauke wuta na yi dare, shi ya haska mini hanya."


Kasancewar inda yake zaune, babu haske zuba wa Alina ido ya yi, amma ba ta san yana yi ba daga ita har Nadiyan, Alina kuwa da farinciki take hirar, tana ba yi mata hirar mai gyaran takalmi. Ismail ya din ga jujjuya cokalin hannunsa yana kallonta tare da sauraren yadda take bayani a kan mutumin.


A wannan karon ma, kwanaki uku a jere, ba ta sake ganinsa ba, ƙofar ɗakinsa a kulle da ƙaton mukulli.

Sosai Alina ta din ga jin babu daɗi, tare da tunanin ina ya tafi.

Babu tsammani, an taso su daga islamiyya, ta hango shi a bakin titi, a gefen mai shayi, yana kankare rake.  Babu tunanin komai ta nufe inda yake da fara'arta. Tsayawa ya yi yana kallonta, har ta ƙaraso.


Tana zuwa inda yake ta hau surutu "Ina ka tafi kwana uku baka nan?"


"Na je gida ne"


Alina ta jinjina kai ta ce "Ina ne gidan naku ne wai?"


"Ƙauye" ya bata amsa.


"Ohh Allah sarki, to sayar da rake ka dawo yi, gyaran takalmin fa?"


Ya ce "Ina yi haryanzu"


"Ma sha Allah, to ba ni na ɗari" Ta yi maganar tana duba jakarta ta ciro ɗarin.


Ya ɗaukko sandar raken ya fara kankarewa. Ta ƙare masa kallo yana kankare raken ta ce "Laa tsawonka ɗaya da raken, kanka ma ya wuce raken tsawo" bai ɗago ba ya yi murmushi, ya ci gaba da kankarewa.

"Dan Allah kar ka bani tsolo, ƙasan nan zaka bani"


Ya jinjina mata kai.


Ta ga yana ta sara sandar raken. Har ta yi shiru, ta ɗan gyara tsayuwarta ta ce "Na ɗari fa zaka bani"


Bai amsa mata ba, sai da ya gyara sandar raken duka, ya saka a cikin leda, ya miƙa mata.

Ta kalli ledar ta ce "To ai na ɗari na ce fa"


Ya ce "Eh na sani"


"To ai kuɗina bai kai ba"


Idanun da suke bata tsoro, ya ƙura mata, da sauri ta saka hannu biyu ta risuna ta karɓa ta ce "To na gode" Ta yi maganar tana miƙa masa ɗarin. Bai ko kalli ɗarin ba, ya koma ya zauna. Haka Alina ta yi dakon rake, ta tafi gida.


Da Yaya ta fara karo, ya yi alwala dan magariba ta kusa.


Ismail ya ce "Wannan raken fa?" Ta yi shiru tana kallonsa.


"Tambayarki fa nake yi"


"Bani aka yi" Ta yi maganar numfashinta na kaiwa da kyar.


"Waye ya baki?"


"Amm.. ban san sunansa ba"


"Waye shi, a ina yake?"


"Mai gyaran takalmi ne ya bani"


Ya tsare Alina da ido, yana nazarinta, tare da tsuke fuskarsa, fuuuu ya raɓe ta ya wuce.


Ta waiwaya tana kallonsa tare da fatan Allah ya sanya ba zuwa zai yi ya yi masa wata maganar ba.


1k ne a telegram via 0069685771

Aisha Adam stanbic 

Shaidar biya ta 08081012143

*MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN*




AMANA KAYAN MATAN

Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.


Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..


Gumbar madara 

Gumbar mata

Gumbar aya 

Gumbar chaku 

Gumbar dake saukar da ni'ima

Gumabar taƙadari

Gumbar riɗi 

Gumbar dabino

Gumbar uku alkhairi 

Kazar amare

Jijjiɓen saniya

Tabaje

Tsimi

Rikita mai gida

Jigidar tada sha'awa 

Ruwan boom ruwan daɗi kenan

Ɗan matse

Karya gado

Maganin sanyi

Zumar ƙarin ni'ima

Zumar rage ƙiba

Zumar ƙarin ƙiba

Zumar riɗi

Mai zamani

Emergency powder 

Tarhama 

Kafi budurwa

Sabon budurci

Alfijir

Gamzaki

Garin dahuwar nama

Sabaya

Miskin ɗahara

Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post