SARA DA SASSAƘA...
AYSHERCOOL
YOTA/002
BRIGHT PENS
P4
Bai kula su ba kawai ya wuce, Alina ta tashi ta ce "Sai anjima na gode"
Cikin fargaba ta shiga gida, ta tarar da Yaya Ismail a tsaye yana jiran isowarta.
Aikuwa ya tare ta da "Meye haɗinki da mutumin nan? kin kawo mini ƙara na je na tsawatar masa, yanzu kuma na ganki a gurinsa me ya kai ki gurinsa kuma?"
Alina ta nuna masa takalman hannunta A ɗan tsorace ta ce "Gyaran takalmi na kai masa, ni fa dama babu abin da yake yi mini Yaya, tsoronsa kawai nake ji da, kuma daga baya na gane mutum ne, shi ne na kai masa gyaran takalmanmu, nawa da na Anty"
Ya ce "To dai ki din ga kula da kyau, kuma ki din ga addu'a"
Alina ta jinjina kai, ta ajiye takalman.
*****
Yau Juma'a, da yamma liƙis Ramata ce sanye da ɗinkin riga da skirt na yadi, ta yi wa fuskarta ado da jam baki da kwalli, ta yi kyau. Ta tsaya dai-dai jikin wata bishiyar tsamiya, tana ɗan leƙe-leƙe.
Wanda ta gani yana tahowa ne, ya sanya ta tsuke fuska, gabanta ya tsananta faɗuwa, idanunta suka fara kaɗawa, ta ji tamkar ta juya ta zura da gudu. Tun daga nesa yake wage baki yana dariya cike da ƙeta, ya ƙaraso inda take tsaye, jikinsa sanye da kayan farauta, da karnuka su na bin sa, sai abokansa su biyu.
Ya ƙare mata kallo ya ce "Jikar makiyaya wannan kwalliyar fa?" Ta ƙara tsuke fuska tana jin yadda zuciyarta ta fara tafasa, ta haɗiye wani abu mai ɗaci a maƙogwaronta, tana kallonsa.
Hannu ya miƙo zai kai jikinta, cikin zafin nama, ta buge hannun ta ja da baya tana huci.
Ya sake kwashewa da dariya sannan ya ce "Kafiya da taurin kai tamkar mahaifinki Ramata. Daga nan shiyyarku na so shiga domin na ganki a bar ƙaunata, sai dai na taki sa'a na yi gamo da ke a nan. Ko akwai wanda ki ke jira ne?" Ta tsare shi da idanunta da suka kaɗa suka yi jawur.
"Idan shiyyarmu ki ke son shiga, ki shiga babu wanda zai yi miki komai saboda ki na da ni. Gaya mini wa ki ke jira? Hanne ko kuma Bukar?" Ras gabanta ya yi mummunan faɗuwa. Ta ɗaga ta sake kallonsa.
Ya kwashe da dariya, ya ce "Kin ɗauka babu wanda ya sani ko? Yaro man kaza"
Ya sassauta murya ya matso daf da ita ya ce "Idan ki ka bari abin ɓoye ya fito fili, kin san ke da zuriyarku ne za ku karɓi hukuncin, babu wanda zai hukunta Bukar. Kamar yadda Iro ya karɓi hukuncinsa da shi da Hanne" Sake ware ido ta yi, ta ja da baya, tana ƙoƙarin magana amma maganar ta gagara fitowa.
"Ya ki ke ja da baya, kullum ƙoƙarin nuna ke ta Allah ce ki ke yi, bayan kowa ya san yadda son abin Duniya ya sanya Babanki kai ki birni nema masa kuɗi, ta hanyar karuwanci.. cikin ƙwarin gwiwar da ba ta san tana da shi ba, ta ɗauke shi da wawan mari, sakamakon yinƙurin taɓa ƙirjinta da ya yi lokacin da yake maganar.
A zafafe ta fara magana, duk da siririyar murya ce da ita ta ce "Kai kuma za ka karɓi hukuncin kaf laifukan zuriyarku muddin ina raye, shashasha kawai" karnukansa ne suka fara yi wa Ramata haushi, abokansa kuma suka yinƙuro, amma ya dakatar da su.
"Marin soyayya ne, tukuicinsa kuma Bukar ne zai biya" Ya yi maganar yana ci gaba da dariya.
Ramata ta ce "Wannan kuma matsalarku ce, dama idan mutum yana mugunta, idan bai yi wa kansa ba, bai iya ba, kuma da sannu wannan zaluncin da ka ke yi, zai waiwayo ku, matsa ka bani hanya kan na ƙara maka wani marin" Yana murmushi ya yi taku biyu, ya bata hanya ta wuce fuuu tana zubar da hawaye.
"Gaskiya ka bada maza, mari fa, mace ta mare ka kana kallonta?"
"Shhh, kar na sake jin bakin wani daga cikinku" Gaba ɗaya suka yi shiru, ba su sake cewa komai ba, suka bar gurin.
Ramata ta yi tafiya mai nisa, ta ji muryar Bukar na ƙwala mata kira, kamar ta share shi ta wuce, amma ta fasa ta ja ta tsaya, ta share hawayen fuskarta.
Ya ƙaraso yana sauke numfashi ya ce "Ramata, na fi awa biyu a rafi ina jiran zuwanki, ga shi yau juma'a ban ganki ba"
Ta numfasa ta ce "Hanyar tsamiya na je na jira ka yau mu tafi tare, kuma ban ganka ba"
Jiki a sanyaye ya ce "Ramata meyafaru ne, na ga fuskarki wani iri" Ganin ya rikice ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Babu komai fa, ka san duk lokacin da zan koma makaranta sai na ji kewar gida"
Ya yi murmushi ya ce "Yakamata a ce kin saba zuwa yanzu fa. Na so mu haɗu yau mu sha hira sosai da sosai, na san sai kin yi watanni uku zuwa huɗu ban sake ganinki ba, kuma kin hana ni zuwa makarantar taku"
"To ai da nisa sosai ba kaɗan ba, kuma ba na son a gida a gane kana zuwa. Bari na ƙarasa gida"
Bukar ya ɗan tsare ta da ido sannan ya ce "Da alama dai wani na damunki, ban so mu rabu a haka ba, amma shikenan Ubangiji Allah ya tsare ya bada nasara. Ga sayayyarki nan ba yawa ki ƙara, zan yi kewarki abar ƙaunata" Ya yi maganar yana miƙa mata ledar hannunsa. Ta tsaya tana kallon ledar.
Ya sake miƙa mata ya ce "Karɓi mana" Sai da ta risuna sannan ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai. Wai ni kuwa ina Hanne? Tsawon lokacin nan ka ce mini ta yi tafiya, haryanzu ba ta dawo ba?.
Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ba ta da lafiya ne, jinya take yi sosai"
"Allah sarki, idan ka je gida ka gaya mata ina gaishe ta, kwana biyu na daina ganinta, kuma ka gaya mata abin ɓoye na shirin fitowa fili. Na so zuwa da kaina na duba ta, amma ina jin tsoro saboda yadda alaƙa a tsakaninmu ta ƙara yin tsami" Ta ƙarasa maganar tana murmushi mai ciwo.
Ya ce "Kamar yaya kenan?"
"Idan ka gaya mata zata gane" Daga haka ta wuce ta bar shi a tsaye, yana kallonta.
Ramata ta gama haɗa komai na tafiyarta, dan washegari Baffa zai mayar da ita makaranta.
Ta ɗaukko wayarta Tab,, da ta samu kyautarta a lokacin da ta ci gasar lissafi. Da fari Baffa cewa ya yi bai yadda ta yi amfani da ita ba, saboda an ce tana lalata tarbiyya, sai dai ya saya mata irin tasa mai madannai. Sai da malamansu suka gaya masa, za ta taimaka mata a gurin karatu, sai kuma ya amince ta riƙe. Dan wasu lokutan har koya masa yadda ake amfani da ita take yi. Ta daɗe tana ɗan rubuce-rubuce sannan ta ajiye ta yi shiru tana tunanin maganganun da Sale ya gaya mata ɗazu. Kamar yadda Iro ya karɓi hukuncin Hanne?
"Kai ba zai yiwu ba" ta furta a fili tana kashe Tab ɗin gaba ɗaya. Ta tattare komai ta gyare ɗakin nata, ta nemi guri ta kwanta tana ta tufka da warwara ba dan makaranta da za a mayar da ita ba, tabbas tana buƙatar ƙarin bayani a kan wasu abubuwa da suka saka ta a duhu.
Duk da zuciyarta a cunkushe ta kwanta, hakan bai hana ta ganinsa a mafarkinta ba yau.
Tana tsugune tana wanki a rafi, ta ɗaga kai ta gan shi a tsaye a cikin rafin. Yana sanye da tufafi na birni kamar yadda ta taɓa ganinsa. Fuskarsa babu yabo babu fallasa. Babu shiri ta miƙe tsaye tana faɗaɗa murmushinta, cike da farin ciki. Sai dai bai ce mata komai ya juya ya tafi ya ɓacewa ganinta.
Ta buɗe idonta a hankali, duhu ya mamaye ko ina na cikin ɗakin nata. A zahiri tana son Bukar. Amma wannan kyakykywan matashin ya addaba wa rayuwarta. Har wani farin ciki take shiga, a duk lokacin da ta kwanta bacci ta yi mafarkinsa. Sai dai ta san har gaban abada ya fi ƙarfinta, ba za ta taɓa samunsa a matsayin miji ba.
Tun a ganin farko da ta yi masa, yake yawan zuwa mafarkinta a kai a kai.
Washegari.
Ramata na cikin motar haya, Baffanta na daga gefenta, hannunsa riƙe da carbi yana ta tasbihi. Ya nisa ya ce "Ramatu bacci ki ke yi ne?"
"A'a Baffa idona biyu, kewar gida nake yi ne, duk lokacin da zan koma makaranta sai na ji na damu"
Ya yi murmushi ya ce "Ranar da aure kuma ya zo ya za a yi Ramatun Baffa? Ƙila ma Allah ya kawo wanda zai fito da ke daga Yelwa zuwa birni. Abin da nake so da ke dai, abu ne da nake nanata miki kullum. Ke ba 'yar kowa ba ce face makiyayin daji, ki riƙe mutuncinki, sannan ki ji tsoron Allah. Ba wai ina zarginki ba ne a'a ita dai tunatarwa tana da kyau ga mumini. Ramata ko bangon duniya za ki je ke kaɗai, ba dan hadisin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, da ya ce bai halatta ga wata musulma ta yi tafiyar sama da kwana uku ba tare da muharraminta ba, da Ramata zan bar ki saboda yardar da na yi da ke. Amma a matsayina na uba, ina sake nanata miki ki ji tsoron Allah, kuma ki yi addu'a."
Baffa kenan bai samu wani ilimin addini ko na zamani mai zurfi ba, tsabar alaƙa da radio ce, ta sanya shi sanin rayuwa, har yake iya wa'azi. Sai dai duk da rashin ilimin nasa nutsatsen dattijo ne mai dattakun gaske. Haka suka ci gaba da tafiya yana ta yi wa Ramata nasiha.
Ƙarfe ɗaya na rana suka isa makarantar 'yan mata ta kimiyya da fasaha, da Ramata take yi, ana ta mayar da ɗalibai ranar.
Baffa suka gaisa da malaman su Ramata, cikin girmamawa Ramata ma ta gaida su.
Vice ya dubi Ramata ya ce "B Yalwa, kin duba jarrabwarki kuwa?" Cikin tsoro Rahama ta girgiza kai.
Ya yi murmushi ya ce "Kin ci jarrabawa, kuma mun yi ƙoƙari, an bar mana ke a nan reshenmu, dan ba zamu gama rainonku ba, a yi posting ɗinku wasu makarantun ba, su fi mu amfanarku ba, muna alfahari da ke Rahama Bashir Yelwa"
Cikin matsanancin farin ciki ta ce "Alhamdillah, Allah na gode maka"
Baffa ma cikin farin ciki ya wahse baki ya ce "Ma sha Allah, malam ta yi nasara kenan, za ta ci gaba da bokonta babu wata matsala?"
"Ƙwarai kuwa, ai ko ba ta yi nasara ba, za ta ci gaba da boko, sai dai nasararta a wannan jarrabawar yana nufin za ta ci gaba da karatu ƙarƙashin makarantu na mussaman na koyar da ilimin kimiyya da fasaha"
Baffa ya ce "To ma sha Allah, Ubangiji Allah ya sanya albarka"
Ƙawayen Ramata suka zo gaida Baffa, babban dalilin da ya sanya suke son zuwa gaida Baffa, duk yanayinsa na ƙauyanci wasu lokutan, ya din ga kwarara musu addu'a kenan. Addu'ar uba da 'ya'ya, addu'a da nasiha mai shiga jiki.
Farkon zuwan Rahama makaranta ta fuskanci ƙalubale, saboda ƙauyancinta, hakazalika babanta ya zama abin bayar da labari, kasancewarsa makiyayin ƙauye typical, dan takalmin nan nasu na roba da makiyaya da ake cewa fillo tomes shi yake sakawa. Abin yana sosa mata zuciya sai dai ba ta bari hakan ya zama rauninta ba. Da alfahari take nuna mahaifinta ga kowa bata ɓoye asalinta. Tamkar kar su rabu, haka ta ɗan raka Baffa zuciyarta cike da karaya ta juyo.
Ta ɗauki kayanta, tare da ƙawayenta, suka nufi hostel cikin farinciki, kasancewar galibi sun ci jarrabawarsu, kuma ba a yi musu transfer zuwa wasu makarantun ba.
*****
Sannu a hankali ya sanya ƙafarsa a cikin katafaren falon, ya tsaya cak yana ƙarewa falon kallo. Set ɗin kujeru kawai uku ne a ciki, ga wani irin sanyi da yake ratsa ko ina.
Ya saki wani irin murmushi, ya sake gyara zaman takunkuminsa ƙafarsa sanye da takalminsa ya shiga falon.
Wanda yake yi masa jagorancin, ya yi gaba suka wuce wannan falon, suka ɗan yi tafiya sannan suka shiga wani.
Shi ma wani falon ne a can ƙuriyar gidan, an yi masa da ado da dukiya mai yawan gaske. Ya sauke idanunsa a kan agogon ɗakin, ƙarfe biyu saura mintuna goma na daren juma'a.
Babban mutum ne dattijo a zaune, ya miƙe tsaye yana murmushi ya ce "Barka da zuwa kacalla Sumale"
Ya tsaya ya ɗan ƙarewa mutumin kallo da falon, sannan ya yi taku biyar ya tsaya, ya ce "Ba mai gida bane, yaron mai gida ne, Sadauki nake, amanar kacalla Sumale mai Allah" Ya yi maganar yana sauke rawanin fuskarsa.
Mutumin ya yi turus. "Amma meyasa Sumale zai yi mana haka? Ya zan yi magana da shi, kuma ya turo mini wani daban?"
"Ka shirya harƙallar, ko na juya na tafi?" Ya yi maganar yana tsuke fuska.
Ya jinjina kai ya ce "Bismillah zauna"
Ya samu guri ya zauna a ƙasan carfet ya miƙa ƙafafuwansa. Ya ɗago idanunsa da suka sha uban farin kwalli ya dubi mutumin ya ce "Shi madugu, hawainiya ne, idan ya juyo nan a wannan kalar, idan ya juya can a wata kalar za a gan shi. Haka zalika kullum a tafe muke mu, bama zama guri ɗaya. Yau zaka iya ganina gobe ka ga wani daban. Amma ka kwantar da hankalinka, ni karɓar aikin ne nawa, aiwatarwa kuma tasa ce. Ina jinka.
Mutumin ya ce "Ko kana buƙatar wani abu na ci?"
Sadauki ya ce "A'a faɗi harƙallar kawai" Ya yi maganar yana kunna karan taba sigarinsa.
Dattijon ya gyara zamansa cikin nazarin matashin ya ce "Amma na san ka san waye ni a ƙasar nan ko?"
"A'a" ya ba shi amsa kai tsaye yana jingina da kujerar da take bayansa.
Dattijon ya yi saroro yana kallonsa, yana ganin amsar tasa kamar rainin wayo.
Mutumin ya dake ya ce "Amm to ni ne...
Sadauki ya tari numfashinsa ya ce "Ba gabatar da junanmu ne ya kawo ni ba, yarjejeniyar aiki ce ta kawo ni, Kacalla ya san yadda zai ji da komai"
Dattijon ya yi murmushin ƙarfin hali sannan ya ce "Gaskiya ne. Haƙiƙa muke riƙe da sitiyarin ƙasar nan, mune muke juya lamura yadda muke so. A duk lokacin da aka kawo abin da yake saɓanin tsarinmu, muna iya karkata motar mu kifar da kowa. Nan da na gayyace ka, ina magana ne da yawun wasu mutane da ba lallai sai ka san suwaye ba. Mu na son a ɓata ruwa ne ba dan a sha ba. A mayar da tsaro tsoro, a gwamutsa gari da ƙasa."
Ya yi murmushi ya dubi dattijon ya ce "Aikinmu ne wannan, gwari-gwari ku na so a yi kururuwa a gabas sai kuma a koma yamma a tayar da ƙura a gabas?"
Dattijon ya yi murmushi ganin ya ɗau haske ya ce "Gaskiya ne"
"Mene ne sadakin aikin?"
Za a yi raba dai-dai a ganimar, mu ne sitiyari ku ne injin mota, sai an bi mu sannan komai zai tafi yadda ake so.
Sadauki ya miƙe ya ce "Za ku yi magana da Madugu, yallaɓai ku na sararawa fa, irin wannan duniya haka, mu muna dawa muna riƙe muku ƙasa" Ya yi maganar yana ƙyaƙyata dariya.
Dattijon ya miƙe ya ce "Za a baka saƙonka a hanyar komawarka gida"
"Yayi" Ya furta yana nufar hanyar fita.
Ya bi bayan Sadauki da kallo, muddin wannan ba shi ne Kacalla Sumale ba, to shi ma ba ƙaramin tsagera ba ne ba....
*****
Yau kasancewar Asabar ce, kuma an yi hutun islamiyya, Alina ta nemi izinin Yaya, ta tafi gidansu Hafsa.
Wuni suka yi wasanninsu, da shiriritarsu ta yara. Yayar Hafsa da suke satarwa littafi su karanta, ta saka Alina a gaba, sai da ta yi mata kitso, saboda kullum kanta a tsfefe yake babu kitso.
Bayan sun keɓe a ɗaki su na hirarrakinsu, Hafsa ta ce "Alina kin san wani abu?"
"A'a"
"Babanmu ne ya ce mu na gama makaranta aure zai yi mini, wannan ɗan abokin nasa ne wai sona yake yi, ni tsoro nake ji"
Alina ta ce "Meyasa ki ke jin tsoro, ba kya son sa ne?"
Hafsa ta ce "Nima ban sani ba, ba na son na yi aure ya din ga zagina kamar yadda babanmu... Da sauri Alina ta rufe wa Hafsa baki tana girgiza mata kai. Tuni hawaye ya cika wa Hafsa ido, ya fara gangarowa. Jiki a sanyaye ta sauke hannun Alina, ta ce "Dan Allah Alina Yaya yana zagin Antynku? Ai kamar ma su ba sa faɗa ko?"
Alina ta ce "Wallahi ban sani ba ko su na yi, amma bai taɓa zaginta ba, dan Allah kar ki gaya wa kowa Baba na zagin Ummanku"
"Wallahi Alina ji nake ba na son shi, idan na ga ya zage ta tana kuka, jiya har miyar kuka mai zafi ya watsa mata. Idan kuma abin ya wuce, sai na ji na fara son sa, idan ya kuma yi mata sai raina ya ɓaci.
Ba na son na yi aure mijina ya din ga zagina ko dukana, wallahi zan iya mutuwa, Alina ba na son na yi aure tsoro nake ji"
Cikin kulawa Alina ta saka hannu tana share mata hawaye ta ce "Ba zai din ga dukan ki ba ko zaginki in sha Allah, ki yi addu'a. In sha Allah rayuwa za mu yi irin ta littafin da muke karantawa"
Hafsa ta waro ido ta ce "Novel fa ba gaske bane"
Alina ta ɗan yi shiru ta ce "Haka ne, amma dai ai idan muka roƙi Allah zai bamu" da haka suka koma hirar littafi, suka bar waccan maganar.
Sai bayan magariba Alinan ta taho gida, sai dai ta san sai Yaya ya yi mata faɗa, ƙila ma ya haɗa mata da ranƙwashi ko murɗe kunne. Tana ta sauri, ta zo daf da inda za ta karya ta shiga layinsu, aka ɗauke wuta. Ta ja ta tsaya, tana ɗan waige-waige. Kamar mai tsoron shiga duhun, ta ɗan yi jimm sannan ta shiga. Daga bayan ta ta ga an kunna fitilar waya ana haska hanyar.
Ta yi ajiyar zuciya, tana bin gefen hanya tana tafiya a hankali, da son bawa mai fitilar damar wucewa, amma ta ga idan ta rage sauri sai ya rage, idan ta ƙara sai ya ƙara kamar dai ita ake haskawa fitilar.
Ta nemi guri ɗaya ta tsaya, tare da waiwayawa, dan ta fara tsorata da tunanin ko bin ta ake yi. A hankali ya ƙaraso yana haske mata fuska. Ta saka hannu ta kare tana ɗan motsa baki za ta yi tsiwa.
"Wai waye?" Ta yi maganar tana tura baki. Bai amsa ba, sai da aka yi wasu sakanni, sannan ya haska mata fuskar sa da fitilar wayar.
Ajiyar zuciya ta yi tare da faɗin "Wai dama kai ne, ka bani tsoro fa"
Bai ce komai ba, ya ci gaba da haska mata hanya. "To na gode" Ta faɗa tana bin bayansa ganin zai wuce ta.
"Amm ƙafarka ta gama warkewa?"
"Eh" ya furta a taƙaice.
Ta ce "To ina ka tafi kwana biyu na daina ganinka?"
Ya amsa da "Gida"
"Ina ne gidan naku?"
"Wani guri"
Ta sake cewa "Ina ne gurin, nan unguwar ne, ko wani gurin?"
"A'a"
"To ya ka baro 'yan gidan naku?" Ya yi shiru bai amsa ba, dai-dai lokacin da suka shiga layinsu.
Ta dube shi ta ce "Na gode sosai da sosai"
Ya ce "Mu je na ƙarasa haska miki"
Alina ta ce "Idan ka hasko mini ma daga nan zan hango har cikin soronmu" Gaba ya sake yi ya bar ta, a dole ta sake bin sa tana cewa "Ai da kar na wahalar da kai ne, amma shikenan"
Daga tsallaken ƙofar gidan ya tsaya yana haska mata har cikin soron su.
Ta tsaya ta waiwayo ta ɗaga masa hannu "Na gode sosai da sosai, sai da safe"
Shi ma ya ɗaga mata hannu, ya tsaya har ta shige.
Ya juya zai tafi, ya yi karo da Isma'il a tsaye a bayansa yana kallonsa.
More pages available at Arewapen
1k ne a telegram via 0069675881
Aisha Adam stanbic shaidar biya ta 08081012143.
AMANA KAYAN MATAN
Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.
Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..
Gumbar madara
Gumbar mata
Gumbar aya
Gumbar chaku
Gumbar dake saukar da ni'ima
Gumabar taƙadari
Gumbar riɗi
Gumbar dabino
Gumbar uku alkhairi
Kazar amare
Jijjiɓen saniya
Tabaje
Tsimi
Rikita mai gida
Jigidar tada sha'awa
Ruwan boom ruwan daɗi kenan
Ɗan matse
Karya gado
Maganin sanyi
Zumar ƙarin ni'ima
Zumar rage ƙiba
Zumar ƙarin ƙiba
Zumar riɗi
Mai zamani
Emergency powder
Tarhama
Kafi budurwa
Sabon budurci
Alfijir
Gamzaki
Garin dahuwar nama
Sabaya
Miskin ɗahara
Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.
