"Na amince da saka Ayshatul-Iftihal, Ifti a cikin cacar, ina da yaƙinin ni zanci" wani irin shu'umin murmushi Garbati ya yi ya juya ya kalli Alhaji Baita kafin ya ce "Sai a yi komai a rubuce ai"
Suka ɗakko takadda kowa ya yi rubutu.
"Ni Alhaji Baita na saka Naira miliyan ashirin a wannan cacar, idan Daada ya ci, zan bashi kuɗin, kamar yadda sharuɗan cacar yake"
Shima Daada ya rubuta. "Ni Daada, na amince da saka ƴata Ayshatul-Iftihal Ifti, a cikin wannan cacar, idan Alhaji Baita ya ci, zan mallaka masa ƴata Iftihal da hannuna"
Aka saka kwanan wata, da saka hannun kowa dana shaidu suka tsayar da ranar da za'ayi wasan kamar yadda aka tsara.
**
"Baba Bala ina yini"
"Kinga yini akan ki Ana, ni za ki kalla ki kira da Bala, ina mace ƴar'uwarki ta ina na yi miki suffa da namiji, shi yasa bana son shigowa cikin gidan nan wallahi aikin kawai"
Ana ta tura baki gaba ta ce
"Ai shi ya sa naga nono a ƙirjinka, wallahi mugun duka ne baka ci ba, da sauri zaka dawo asalin namiji ina faɗa maka"
Iftihal ta buɗe baki da mamakin Ana. Innti ta ce "Ana, wacce magana ce haka?"
"Innti ki bari na faɗa masa gaskiya, sai ya dinga yawo yana zubar mana da rigar mutumci, waye zai aure mu idan yaga ƙanin babanmu ɗan daudu ne, ni da nake burin auren kyakkywan miji, kuma kin san kyakkywan maza yawanci masu kuɗi ne"
Innti ta kasa magana.
Ana ta murguɗa baki ta ce
"Wallahi walakiri ba zai maka da kyau ba idan ka mutu a haka, jibgarka za'ayi kamar jaki, ai sai ka auri namiji ƙarshen daudu kenan"
Bala Sukunbiya ya ce "Ni kike faɗawa haka? Kamar a bakin Daada wallahi, sai na ja miki masifa za ki san kin yi da watsastse"
Caraf Ana ta ce "Kaga watsewa a kan ka, da kai da Daada duk ku kaga duhu, wlh sai na yi addu'a in sha Allah nono ya fito maka har ciki, wai Sukunbiya?" Sai ta sheƙe da dariya
"Mahaɗita yau miyarmu da Sukunbiya za'ayi" takaici ya kama Sukunbiya.
Sai ya yi ƙwafa kawai.
"Daɗin ciwo nishi, inda me maka sannu"
Inji Ƴar Beauty.
Caraf Abar ƙauna ya amshe da faɗin.
"Ni dai ki yi sauri yaya, ina da aikin suyar waina zani yinin suna kuma, kar a yi mini asarar haɗuwa da ƙawayena masu capacity"
"Heeee riii" suka sake saka shewa da haɗe kwankwaso waje guda abinsu.
Sukunbiya ya ce "Daman kuɗin adashi na kawo gashi, ina neman alfarma a bani zubi na gaba, saboda bikin ƴar aminiyata za'a yi"
Ya ranƙwafar da hannu wajan miƙa mata kuɗin, ganin Innti bata amsa ya dire kuɗin ya ce "Na rasa ta cewa, wai uwar gulma ta yi cikin shege, sai aron rigar mamakin za ki bani zani suna yau, naga size ɗinmu ɗaya dake matar Daada, kema dai tubarakallah"
Abar ƙauna ya riƙe zancen da faɗin.
"Kallabi tubani, wai anwa uwar kwarto fyaɗe ya ce mama riƙe mini wando ina zuwa"
"Riiiii!" Suka sake yin shewa.
**
Wani irin ɗaci take ji a maƙoshinta, ta tsani a ƙaryatata, ta sani a nemi cin zarafinta, gata da wata baƙar zuciya da riƙe abu a rai
"Kake cewa na maka sharri?"
Ta runtse idanunta, ta sake ware idanun wannan hasken me kama da magic ya sake sauka akan yaron "Zaka gani"
Ganin abin na neman zama rigima aka ce yaron ya tafi zuwa wani kantin, ita kuma ta cije a wajan jikinta sai kakkarwa yake yi.
Yaron na ƙoƙarin juyawa kawai ya faɗi a wajan yana murɗewa idanunsa suka kakkafe, cikin sauri ta kalli yaron domin itama ta tsorata sosai sai ta juya caraf wani ya riƙe hannunta ya ce "Mayya ina za ki bayan ki kama yaron mutane shine za ki gudu?" Da rashin fahimta Ana take kallon cikin idanun mutumin ranta ya sake ɓaci ta rasa abin cewa, da alama yau bata da sa'a. Wani ya ce "Daman ta ce zai gani"
"Kuma zai ga abin da zai same shi" in ji wani.
Mutumin ya ce "Bidiri kashin rana da kiɗa, gashin nan tun ba'a yi nisa ba ta kame shi"
Nan da nan wajan ya cika ana faɗin.
"Mayya ce Mayya ce"
Mene kuma mayya? Wani abu ne hakan da bata san dashi ba har ake jifanta dashi?
Gabaɗaya sai ta rasa fahimta ta zama confused lokaci guda, ta haɗiye wani abu mai ciwo a ƙirji taƙi barin ruwan daya taru a cikin idanunta zuba, wanda ya sake sawa idanun nata suka sake zama manya.
"Ni ba mayya bace, me na yi masa?"
"Ai wallahi babu inda za ki sai kin tsallaka shi" cewar yayan yaron daya ƙarasu.
Jaheed bai san meke faruwa ba, domin ko da wasa bai taɓa tunanin Ana zata fito ba, balle har ta ƙarasu kantin nasu.
"Kul, kurwata kur ina faɗa miki" mutumin ya sake furtawa yana jefa wa Ana harara
"Idan kun su ko kashe ni, babu wanda ya isa na tsallaka yaron nan, ku kuka san wata mayya kamar wani man shafawa aikin banza" sannu a hankali Yaa Sam ya ƙarasu wajan saboda hayaniyar da ta yi yawa, kuma ya hango Ana a tsakiyar mutanen, ya dubi mutanen kaf ya kalli Ana sai ya ce "Menene?" Cikin rawar murya ta ce
"Wai ni ce Mayya zai na tsallaka yaron nan"
Read the complete chapter 3 on ArewaPen.
Bright pens
08164069385
