*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
Arewapen@nanahaleema11.
*Book 1*
*Page 007.*
A hankali yake cin abincin kamar ba ya so, abincin ma cikin steeze ake cinsa, yana yi yana kaɗa ƙafa.
Rabin abincin ya ci ya tashi daga kan dining ɗin ya dawo cikin falo ya zauna yana shan ruwa.
Tunda ya zauna ake kiransa a waya, wata wayar ya ɗauka wata kuma ya share.
A lokacin Jaafar ya sakko daga sama, ya kalle sa ya ce, "baza ka je aiki bane?."
Ya ɗaga ido ya kalle sa ya ce, "zan je, sai dare."
Jafar ya ce, "to ka san kana da meeting ko? Kuma ka ba da time."
Ya ɗan furzar da iska daga bakinsa ya ce, "na sani Jazy, zan san abinda zan yi."
Jafar zai yi magana aka kira wayar Rehaan, ya duba ya ga video call ne kuma mahaifinsa ne.
Sai da ya yi connenting da laptop ɗin gabansa sannan ya gyara zama, dan Abba ya fi so ya dinga yi masa magana da fulfulde, a ganin Abba in ba ya yi zai manta da yaren ne.
Rehaan ya ɗauki wayar ya ce, "jam bandu na Abba." (Barka da safiya).
Abba ya ce, "Jam Noi a woni? Noi kuuɗe?" (Ya ka ke, ya aiki?).
Rehaan ya ce, "Jam Alhamdu lillah."
Abba ya yi gyaran murya ya ce, "sai na ga ka rame, ina fatan kana lafiya?.."
ya kalli Jafar ya ce, "Jafar ya yi rashin lafiya ne?."
Jafar ya cire glasses ɗin idonsa ya ce, "bai yi ba, kawai kwana biyu baya son cin abinci, sai ya ce komai ba ya yi masa daɗi."
Abba ya ce, "Rehaan yaushe zaka zo Nigeria?."
Sai da gaban Rehaan ya faɗi, ya daure sannan ya ce, "Abba!."
Abba ya katse sa ya ce, "kar ka yi musu Rehaan, wannan lokacin zuwan ka ya zama dole, bazan karɓi uzuri ba."
Rehaan ya ce, "Abba akwai aikin da zan je in yi a Jedda, a bari in na kammala sai in dawo nan."
Abba ya bisa da kallo ya ce, "yaushe zaka je aikin?."
"Nan da four weeks."
"Ka dawo gida ka yi four weeks ɗin, in ya so daga Nigeria sai ka wuce."
Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "to Abba, zan shigo in sha Allah."
Abba ya ce, "yaushe?."
"next week."
"A'a Rehaan, this week nake so ka shigo."
RehAn sauke ido ƙasa bai kalli mahaifinsa ba ya ce, "To Abba, zamu dawo."
Abba ya ce, "Allah ya kaimu."
Rehaan ya amsa da amin, Abba ya ce, "Kar ka damu, haka rayuwa ta ke, yau da gobe sai Allah."
Ya gyaɗa kai ya ce, "in sha Allah." Basu jima suna magana ba suka yi sallama Abba ya kashe wayar.
Rehaan ya daki kansa yana yamusha gashin kansa ya ce, "bana son zuwa, bana son zuwa gida, bana son Jazy!."
Jazy ya zauna a kusa dashi ya ce, "Baka so ka ga Mamy, Banisha da Riyya?."
Ya kalli Jazy da idanunsa da suka fara canja launi ya ce, "ina so, amma bana so in je can. In ina son ganin su zan iya aikawa a ɗauko min su, amma bana son zuwa nigeria."
Jay ya ce, "ka yi haƙuri mu je."
"Ina ji a jikina kamar akwai abinda zai faru in na je Jazy, Ina ji kamar in na je bazan dawo da rai ba."
"Ka cigaba da addu'a, babu abinda zai same ka in sha Allah."
Ya sauke numfashi yana gyaɗa kai cikin gamsuwa da maganar Jazy. Ya san addu'a ce kawai maganin damuwarsa. Jafaar ya miƙe ya ce, "zan fita, Chef zai zo, sai ya yi maka abinda ka ke so." Ya sake gyaɗa kai bai ce komai ba Jazy ya fita.
Jazy bai jima da fita ba ya ji ana danna doorbell, kamar bazai miƙe ba sai kuma ya tashi ya buɗe ƙofar suka haɗa ido da Alma a tsaye tana murmushi.
Kafin ya bata hanya ta shigo ta mayar da ƙofar ta rufe tana kallonsa tana murmushi. Fuskarsa babu murmushi, ya bita da kallo ganinta da jaket abinda bai cika gani ba. Alma ta yi pecking ɗinsa a kumatu tana shafa fuskarsa, wacce take da kwantaccen gashi mai kyau da ɗaukar hankali.
"Where is Jazy?" Ta faɗa tana kallon sa.
Girgiza mata kai kawai alamun ba ya nan. Sai ta ji daɗi a ranta, ta riƙe hamnunsa suka zauna ta fuskance sa sosai ta ce, "me yake damun ka?."
Ya ɗan kalle ta kafin ya janye ido ya yana girgiza kai alamun babu.
Alma ta miƙewa tsaye ta cire jaket ɗin jikinta ta juyo da fuskarsa dan ya kalle ta.
Ya kalle ta ɗin ya ganta sanye da riga ƴar ƙarama wacce bata wuce yace mata bra ba, sai ƙarmin wando wanda ko cinyarta bai gama rufewa ba. Ta zubo da gashinta tana sake juya gashin a gabansa.
Ya ɗauke kai daga kallon ta, ya rasa meyasa ƙirar turawa bata burge sa, gasu dai farare tas, ko ina yana ɗaukar ido, amma sam baya so, bai sani ba ko dan a cikinsu ya tashi ne oho. Shi ko ƴan nigeria farar fata bata cika ɗaukar hankalinsa, farar fata in dai ba Mamy ba, bata wani burgesa.
Rehaan yi tsamani ba ya ji t ta zauna a kan cinyarsa, ya ɗan yi ƙaramin tsaki jin tana kai hannunt fuskarsa tana shafa gashin fuskarsa.
A hankali ya ce, "Alma please."
Ta matso da bakin ta kusa da fuskarsa ta ce, "Please Ray, i want to you" ta faɗa tana niyar saka bakinta a cikin nasa.
Da hanzari ya janye ta daga jikinsa ya miƙe ya ce, "bana son haka, please ki je."
Ta bi sa da kallo tana sake matsowa kusa dashi, ya bita da kallo yana ji kamar kansa yana sarawa ya ce, "Alma ki ƙyale ni."
Ta marairaice ta ce, "Why?."
Ya rufe ido ya buɗe ya ce, "just go" ya faɗa yana hawa sama da sauri ya barta a tsaye a wajan.
Alma ta bi shi kallo cike da takaici da baƙin ciki, ta kalli camera da ta saka a jikin laptop ɗinsa da take kan table, ta cire tana tsaki dan ba haka ta so ba, koda an ɗauki video yadda ya kamata yanayinsa bai yi daidai da yadda take so ba. So take ta yi masa video a yanayin da kowa ya gani ya san baya cikin hankalinsa, kowa ya san ya shiga wani ɓangare da ya zama private a rayuwarsa.
A lokacin aka yi mata waya, tana ɗauka ta ce, "We fail, next time" ta faɗa tana saka rigar da ta zo da ita, ta ɗauki abinda ta zo dashi ta fita.
Rehaan yana hawa sama ya faɗa kan gado yana sauke numfashi cikin wani irin yanayi.
Wani irin abu yake ji yana tafiya jikinsa, ya dafe kai cikin wani yanayin da bai san meye ba.
Ya miƙe ya tsaya a gaban madubi yana kallon kansa, ya saka hannu ya hargitsa gashin kansa yana girgiza kai.
A hankali ya dinga sauke numfashi, yana jan ajiyar zuciyar, ya diga maimaita Subahanallahi a zuciyarsa, a hankali ya fara jin nutsuwa tana shiga jikinsa.
Ya buɗe ido a hankali yana kallon kansa, ya zubawa kansa ido yana ƙarewa fuskarsa ido, yana kallon yadda Allah ya yi halita mai kyau a fuskarsa.
Tabbas shi kansa ya san yana da kyau, indai kyau ake zance ya san yana sahun gaba a layin masu kyau. Shi ɗin mai kyau ne, kyau wanda ake kira kyau, kyau na shiga gasar masu kyau.
Bai san meyasa ba, yana jinsa kamar fanko, kamar akwai abinda ya rasa. Ya rasa me ya rasa haka? Meyasa yake jin kanasa a yanayin da yake ciki meyasa?.
*******
Tunda suka gama haɗa record ɗin ranar suka rabu da Salim sai nufi hanyar gidan marayu da ta tashi a can. Sai sauri take yi sboda kar ta je an kulle gate, dan yamma ta kusa ta san ƙarfe shida ake rufe shiga.
Tun daga gate ta ka gaisawa da mutane cikin raha da wasa da dariya, kowa ya santa, tunda gidan gidansu ne, a nan ta tashi, ta rayu, ta yi makaranta, da komai da komai.
Kai tsaye office ɗin wacce suke kira da Mama ta nufa, ta ɗan yi knocking kaɗan aka bata damar shiga ta tura ta shiga da sallama.
Mama ta amsa kafin ta ce, "A'a Islaha, kece tafe?."
Ta ɗan yi murmushi ta ce, "ni ce. Ina yini?."
"Lafiya lau, ya aiki?."
"Alhamdu lillah."
"Yau ke ce kika shigo?."
"Eh ni ce, na kawo ziyara ne."
Mama ta ce, "kin kyauta kam. Gashi ƴan uwan naki basa nan, sun ɗan fita."
Da mamaki ta ce, "sun fita kuma Mama, yanzu shida ta kuaa, daman ana kaiwa after six a waje?."
Mama ta ce, "tunda na ce basa nan sai ki yarda ba nan, kin san suna sana'a. Ɗaya tana ƙunshi, ɗaya tana zuwa koyan ɗinki. Na san yanzu za ki gansu."
Islaha ta ɗan girgiza kai ta ce, "shikenan, in sun dawo ina gaishe su" ta faɗa tana ɗaukar handbag ɗinta ta fita.
Mam ta bita da harara ta ce, "sai da na faɗa mata yarinyar nan tana da matsala amma ta ce ita ba haka ba. Mtsw! Ni na san matakin da zan ɗauka a kanta, in ba haka ba akwai damuwa babba. Yarinyar nan ƴar jarida ce, zata iya aikata komai, dan ba mutunci ta cika ba."
Islaha lokacin da ta fita cikin gidan ta shiga, ma'aikata gidan suna ta gaisawa kafin ta shiga asalin ɗakin da take kwana.
A guje ƴan mata biyu suka taho wajanta suna faɗin, "Adda Islaha."
Suka rungumeta itama ta rungume su tana murmushi ta ce, "Ƙanena ya ku ke?."
Ɗaya daga ciki ta ce, "Lafiya lau muke Adda, jiya na kira ki a waya baki ɗauka ba."
"Ayya ban gani ba ma, da na gani a guje zan kira ki Hafsy."
Ta ce, "ku zo mu je daga waje."
Suka fita suna hira, cikin nishaɗi Hafsy ta ce, "Adda tunda ki ka bar gidan nan ba ya yi mana daɗi wallahi."
Ta yi dariya ta ce, "ni kaina da tunanin ku nake kwana nake tashi. Yanzu meye labari? Ina su Humaira da Sauda? Ban gansu ba."
Hafsy ta ce, "Hmm!" Ta faɗa tana kallon bayanta alamun bata so ta yi maganar a ji.
Zainab ta ce, "Adda lamarin Sauda da Humaira sai addu'a kawai, yanzu sai su kwana biyu basa cikin gidan nan."
Islaha ta gyara tsayuwa ta ce, "ina suke zuwa?."
"Waye ya san inda suke zuwa Adda?."
"Kuma Mama ta san suna fitar?."
Zainab ta ce, "wani lokacin ma tare da ita suke fita da ita."
Ishala zata yi magana suna ji an ce, "Ke Zainab, Hafsa! Ku koma ciki!. Bakwa ganin yamma ta yi ne?."
Islaha ta kalli Mama sannan ta kalli su Zainab, ta ce, "Ku koma, zamu yi waya."
Suka gyaɗa kai suka koma. Mama ta ce, "lokacin ziyara ya ƙare, sai wani lokaci." Islaha bata ce komai ba, ta wuce ta fita daga wajen.
Tana fita Mama ta koma office, ta ɗauki waya tana zagaye tana jira a ɗauka. Ana ɗauka ta ce, "Ni fa yarinyar nan Islaha tana bani tsoro, kun san yarinyar nan ƴar jarida ce, abu kaɗan zata yi ta saka a shiga tashin hankali."
"Yanzu nan na tarar da ita ta tsare yara tana yi musu tambayoyi, kun san tana da yawo, kuma jarida aikinta ne, dole mu samu mafita kafin wani abun ya zo ya faru."
Ta yi shiru alamun ana bata amsa sannan ta ce, "ya dai kamata, ya kamata a san abinda za a yi, in ba so ake lamari ya lalace ba."
Ta sake gyaɗa kai ta ce, "shikenan" ta faɗa tana kashe wayar tare da buɗe window tana kallon islaha a harabar gidan.
Ta girgiza kai ta ce, "tauraruwa mai wutsiya, ganin ki ba alkhairi bane. Kin bar gidan ma baza ki bari mu yi rawar gaban hantsi ba. Ina godewa Saheer da ya zama silar barin ta gidan nan, da nan ta cigaba da rayuwa ban san ya zamu yi ba" ta faɗa tana sakin labulen ta koma ta zauna tare da dafe kanta.
Ko kaɗan bata yarda da Islaha ba, ta san halin yarinyar, dan ba sanin yanzu ta yi mata ba. Tun tana depty head of orphanage ta san illar ta, yanzu gashi Head ɗin ta bata waje har yanzu ba a huta ba. Ta santa tun bata kai haka ba, zata iya aikata komai dan ganin ta binciko abinda yake faruwa, in kuma hakan ya faru za a tafka babban tashin hankli a faɗin garin Yola.
Islaha bayan ta gama gaisawa da mutanen gidan ƙofar gate ɗin ta tsaya tana jiran abin hawa dan lokacin magriba ta yi.
Sai kuma ta tsaya tana tunanin ina zata je, dan gaskiya bata son komawa gidansu Saheer, gwara ta ta san inda zata nufa.
Horn ta ji ana yi mata daga bayanta, ta juya ta ga bata san motar ba ta ɗauke kai ta cigaba da kallon titi.
Na cikin motar ya fito ya ƙaraso wajan, yana hararata ya ce, "ke ƴar wulaƙanci ce, kina ji ina yi miki horn baza ki zo ba.?"
Ta kalle sa, ta saki fuska ta ce, "Hamma Suraj ai ban gane ka ba wallahi, na ga ƙatuwar mota ana yi min horn, ta ya zan fahimta?."
Murmushi ya yi ya ce, "bakya nemana ta ya za ki san na canja mota Islaha? Tunda ki ka bar gidan nan shikenan ki ka canja, ko ɗan zuwan ma bakya yi."
Ta ɗan yi murmushi ta ce, "ina zuwa mana, aiki ne yake ɗan riƙe ni, shiyasa abubuwan sai a hankali wallahi."
"Ina Saheer?."
Ta ɗan yi murmushi ta ce, "yana nan, yana
gidansu."
Shima ya yi murmushi ya ce, "ki zo mu je na sauke ki, kina ta tsayuwa tun ɗazu."
Ta yi ajitar zuciy ta ce, "daman akwai maganar da nake so mu yi da kai." Ya gyaɗa kai ya ce, "to mu je." Ta ƙarasa suka shiga motar suka fara tafiya.
Ta kalle sa ta ce, "Hamma Suraj baka taɓa fahimtar wani abu a gidan nan ba? Ni wallahi tun ina ciki nake zargin wani abu."
Suraj ya ce, "kamar me ki ke zargi?."
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce, "ina da baban zargi akan Mama da manyan gidan wallahi, kuma sai na binciko ko meye, sai dai ayi duk abinda za a yi. Amma ban yarda da zama a gidan nan ba, ban amince da yadda take mu'alama da kowa ba."
Suraj ya ce, "shine na ce miki kamar me kenan? Me ki ke zargi har haka?."
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "zamu tattuana maganar nan gaba, amma tabbas na saka question mark akan Mama da gidan gabaɗaya."
"Sai magana ki ke a juye, ki faɗa min kasa faɗar abinda yake faruwa. Ki faɗi akan me ki ke zargin?."
Ta yi shiru ta ce, "sauke ni a gidansu Safeera kawai."
Ya kalle ta ya ce, "baki bani amsa ba."
"Zamu yi maganar."
"Meyasa baza ki faɗa min yanzu ba?."
"Zan faɗa maka, zamu yi magana. Amma kar ka faɗawa kowa don Allah."
Ya yi murmushi ya ce, "ni fa lauya ne Islaha, dan mun yi magana dake sai na faɗawa wasu?."
Ta gyaɗa kai a lokacin wayarta ta fara ƙara, tana dubawa ta ga Saheer ne, ta ɗauka daga can ɓangaren ya ce, "Ina ki ka je?."
Islaha ta ce, "Na je gidanmu."
"islaha sai da na ce miki kar ki je ko? Yanzu nufinki zasu bar ki ki kwana ne? Kin san dokar gidan, ke ba ƴar gidan bace yanzu."
"Gidansu Safeera, kafin gobe na haɗo kayana na san inda zan je."
"Ki dawo gida Islaha, ga Baffa ya dawo yana neman ki."
Zata musa ya katse ta ya ce, "ki dawo don Allah, ke nake jira yanzu. Ko in zo na ɗauke ki?."
Ta girgiza kai ta ce, "ina kan hanya."
"Sai kin ƙaraso" yana faɗa ta kashe wayar ta ajjiye ta a jikimta tana sauke numfashi.
Suraj ya kalle ta suka haɗa ido, ya yi dariya ya ce, "Islaha ta Saheer, Allah ya bar wannan soyayyar ta ku har aljanna. Yana sonki kina sonsa, ya taka rawar gani sosai a rayuwarki, shine masoyina gaskiya, wanda ya ke sonki tsakani da allah ba dan wani abu naki ba."
Ta ɗan yi murmushi ta ce, "to ni dan me ma za a so ni?."
"Kyau mana."
Ta wani kalle sa, ta yi dariya ta ce, "sai ka ce wata kai, ko shi Hamman?."
Ya yi dariya ya ce, "baki yarda kina da kyau ba?."
Ta girgiza kai ta ce, "ko da wasa."
Ya yi dariya shima ya ce, "to na faɗa miki." Bata ce komai ba suka cigaba da tafiya har ƙofar gate ɗin gidansu Saheer.
Suraj yana tsayawa da mota Saheer yana fitowa daga cikin gida.
Suran ya kalle ta ya kalli Saheer ya ce, "Amarya kin san angonki baya so ya gan mu tare, kishi yake yi dani, sai ka ce ni ba yayanki bane."
Ta yi dariya ta ce, "so ne yake kawo kishi."
"Kina bayansa kenan ko? Shikenan ai, bazan fita mu gaisa ba, ƙarshe raina ne zai ɓaci. Sai mun yi magana."
Ta gyaɗa kai ta ce, "Na gode Hamma Suraj." Ya yi mata murmushi ta buɗe ta fita shi kuma ya ja motar.
Tana nufar ƙofar gidan ta ga Saheer ya haɗe rai matuƙa, ta ɗaure fuska itama, dan bata son rainin wayo, ko hamman ne ya yi mata ba kasafai take jura ba. Ta ƙarasa ta ce, "ina yini."
Ya bita da kallo ya ce, "waye wannan ya sauke ki?."
Ta ce, "Hamma Suraj ne."
Ya dafe kai ya ce, "Islaha so nawa zan yi miki magana akan mutumin nan? Ban isa na hana ki ba kenan?."
Ta sauke numfashi ta ce, "na je gidan mu ne fa, shine muka haɗu ya dawo dani."
Ya girgiza kai yana sake tamke fuska ya ce, "amma na ce miki bana so ki dinga sauraren sa ko? Na faɗa miki ni ban yarda dashi ba."
"Hamma, Suraj fa yayana ne, tare muka tashi dashi, da makarnata duk tare mu ka yi. Akwai laifi dan na sauraresa?."
"To ni bana so, bana son mu'amalarki dashi."
Ta ɗan girgiza kai ta ce, "ni na gaji, ban yi sallah ba."
Ya sauke numfashi ya ce, "ki shiga gida." Ta ɗan yi turus tana kallonsa, ya sake kallon ta ya ce, "ki shiga Baffa yana nan, babu wanda zai yi miki wani abun kema kin sani ko?."
Ta turo baki ta ce, "ni da ka bari na je gidansu Safeera."
"Baza ki ba, ki shiga kawai." Babu yadda ta iya haka ta shiga cikin gidan ba dan tana so ba.
Da sallama ta shiga falon duk suka bita da kallo, Baffa ne kawai ya amsa mata, da fara'a ya ce, "Islaha barka da zuwa, tun ɗazu nake tambayarki aka ce kin tafi wajan aiki."
Ta yi murmushi ta ƙarasa ta tsuguna ta ce, "Baffa barka da dawowa."
"Barka dai Ishala, ya aikin?."
"Alhamdu lillah. An dawo lafiya?."
"lafiya lau Islaha, fatan komai lafiya ko?."
Ta ɗaga kai ta ce, "lafiya lau Baffa."
"Ma za ki je ki huta ki zo ki ci abinci." Ta miƙe ta kalli Mama da take aika mata harara, ta ce, "Mama Ina yini."
Ta zabga mata harara ta ce, "baki isa ki kwana a gidan nan ba, sai kin barshi dan ubanki."
Baffa ya kalle ta ya ce, "Haba Zulaiha! Meye haka?."
Ta kalle sa ta ce, "baka san me ya faru ba kar ka saka baki, tunda baka nan ɗazu baka san abinda ta yi min ba."
Baffa ya ce, "Amma sai ki bari ta huta ta ci abinci sai komai ya biyo baya ko?."
Ya kalle ta ya ce, "Islaha tashi ki je." Bata musa ba ta miƙe ta shiga ciki.
Kuɗi ta ɗauko a jakarta ta ajjiye akan madubi sanann ta shiga banɗaki. Sai da ta yi wanka sannan ta fito ta saka kaya ta tayar da sallah. Tana idarwa ta haɗa da i'sha da ake ta kiran salla ta zauna tana azhkar.
A lokacin Mama ta shigo ɗakin, Islaha ta miƙe tana kallon ta, kafin ta yi magana ta ɗauki kuɗin ta miƙa mata ta ce, "gashi Mama, ki yi haƙuri."
Mama ta kalli kuɗin, ta fizga daga hannun Islaha ta irga ta ga dubu hamsin ne cif.
Ta bita da harara ta ce, "da kin san inda za ki dinga samo kuɗin ki ke raina min hankai?. Me ki ka aikata aka baki dubu hamsin?."
Islaha ta ce, "Mama tunda dai na kawo ai shikenan."
"Shikenan kam, ko me ki ka aikata bai dame ni ba, tunda kin kawo min ke ki ka sani. Ina yi miki gargaɗi akan saka min yaro a ɗaki, ɗana ba ɗan iska ba ne, kar ki iskanata min shi."
Islaha ta ɗaga kai ta ce, "To Mama zan kiyaye."
"Ya fi miki" ta faɗa tana fita daga ɗakin.
Islaha ta bita da kallo tana sauke ajiyar zuciya, zama a gidan ma ko tashin hankali, in ba dan ɗan gidan zata aura ba, zaman gidan ma babbar matsala ce a gare ta. Tunda wata ran zata yi aure, kuma za a zo neman auren ta, kaf unguwar sun san abinda Mama take yi, kuma kowa ya san ta fi ƙarfin Baffa, itace take juya gidan.
Kai tsaye ƴan bariki ake kiranta da ita da ƴaƴaanta. A gabanta ƴaƴanta mata zasu yi wanka su fita, ta bisu da albarka babu kwaɓa. Su dawo ta buɗe musu gida, su bata kuɗi baza ta ce ta wacce hanya aka samu ba.
Itama tunda yanzu tana gidan ta zama ƴar barikin, shiyasa bata jin hausin masu cewa ita ƴar iska ce, tana cikin ƴan iskan ne shiyasa ake yi mata kallon haka. Shi kansa Hamman, in Mama zaka duba ai ba mijin aure bane, in ban da lamarin najeriya, lokacin da ya je neman adopting ɗinta baza a bashi ba saboda backround ɗinsa, kuma a ƙa'ida sai an bincika backround ɗin mutum kafin a bashi yaro.
Ta sauke numfashi ta miƙe tsaye ta ninke sallayar, ta fito falo jikinta a sanyaye.
_Book 1 free ne, Book 2&3 paid ne akan naira 1k kacal. Pay into Sadiya Nuhu Mukaddas 5903999117 Moniepoint MFB. A tura shaidar biya a wannan number 09030398006 ko 0701 809 8175._
Nana Haleema✍🏻
