RAGAYAR DUTSE.
©️Nana Haleema.
More pages on arewapen@nanahaleema11.
Book 1
Page 006.
Su Islaha suna shiga gidan tv, kai tsaye office ɗin Chairman ta wuce kamar yadda ya ce yana neman ta.
Ta yi knocking ya bata dama, ta shiga da sallama cikin nutsuwa da yanga irin ta ta.
"Barka da safiya Chairman."
Ya kalle ta da murmushi ya ce, "barka Ishala, ina ta jiran zuwanki tun ɗazu" ya faɗa yana nuna mata kujera alamun ta zauna.
Islaha sai da ta zauna sannan ta ce, "na ɗan samu matsalar abin hawa ne shiyasa. A yi min afuwa."
"An yi miki. Karɓi" ya faɗa yana miƙa mata envolope mai kyau, an yi mata ado rubutu mai ɗaukar hankali.
Islaha ta karɓa tana jiran ƙarin bayani. Chairman ya ce, "invitation card ne. Na samu labarin Mr Ray yana gab da shigowa Nigeria, shiyasa na saka aka buga min katin gayyata tun yanzu, da zarar ya shigo ƙasar nan ko ba a nan ya sauka ba, zamu ɗauki nauyin ɗaukarki ki kai masa ko ina. Tunda mun yi mail babu adadi babu respond, gwara a kai iv."
Islaha ta ɗan murmusa cike da jin haushin wannan zaƙewa ta ce, "Amma yaushe ake saka ran zuwansa?."
"PA ɗinsa na Yola, ya ce min babu lokaci, amma tabbas zai zo cikin kwanakin nan. Da zarar ya zo zan nemi alfarmar PA ɗina, na haɗa ki dashi."
Islaha ta yi shiru bata yi magana ba, tana mamakin wannan zumuɗi na Chaiman kamar za a yi interview da shugaban ƙasa. Ko gwamna da suka yi interview dashi bai yi zumuɗi haka ba.
Chairman ya ce, "in muka samu ya amsa gayyatar mu wallahi kakar mu ta yanke saƙa, ba wai dan kuɗi ko wani abun ba, kawai dai bai taɓa hira da tashoshin nigeria ba, ba a taɓa ji yana yaren fulatanci ko Hausa a tv ba, sai dai english. Kuma mu da hausa zamu yi hirar, dan waɗanda ba fulani ba su fahimta. Shiyasa mutane da yawa suke cewa baya jin ko wanne yare sai turanci, ni kuma na san ba haka bane. Da zarar ya amsa gayyatar mu, aka gabatar da yaren da kowa zai ji ai mun gode Allah."
Islaha ta ɗan taɓe baki ta ce, "To Allah ya kaimu."
"Amin Islaha. Shiyasa na zaɓe ki, domin kina da nasara da sa'a a rayuwarki. Ba ki taɓa gayyato guest ya yi denying ba, kina zuwa suke saka mana date."
Buɗe ƙofar office ɗin aka yi aka shigo, Islaha ta kalki wacce ta shigo kamar yadda Chairman ma ya kalle ta.
Ganin Islaha a office ɗin sai ta haɗe rai tana bin Islaha da banzan kallo kafin ta ce, "Chairman ba dai ita ka bawa iv ba?."
Ya kalli Ummi ya ce, "ita na nawa."
Cike da takaici ta ce, "Chairman ka ce ni zaka bawa wannan aikin, ka yi min alƙawarin gayyatar babban baƙo na gaba, ya kuma zaka tsallake ni yanzu?."
"Na baki damar ai, kin manta na baki dama ki gayyato mana C.E.O Footwear by tiger da yake Kano, kin iya?."
Ta yi shiru bata ce komai ba, Chairman ya ce, "Ba ki iya yin komai ba, muna ji muna gani haka damar interview dashi ta kubce mana."
"Islaha kuwa sa'ar daga jininta take, bata taɓa kaiwa wani gayyata bai amsa ba, ko ta waya ko a zahiri, indai itace sai ya mun tattauna dashi ba. Kuma magana ake ta za a gayyaci Rehaan Yola, bazan yi sake na tura ki ba. Islaha zan tura, in ya yi rejecting zamu sake komawa, kuma ita zan sake nema."
Cike da baƙin ciki da hassada ta ce, "Amma Chairman a bayana Islaha ta fara aiki a gidan nan, sai da na shekara biyu ina aiki sannan aka ɗauke ta. Kuma kafin zuwanta ni ce a sama, dani ake ji ba ita ba. Yadda ka ke yabonta kana cewa indai ta yi sai an karɓa nima haka, ni ce top presenter a gidan nan kafin ta zo. Amma yadda ka ke fifitata kamar ta riga mu fara aiki a nan..."
Ya ɗaga mata hannu ya ce, "Ummi fita ki bani waje, in kin ga dama ki canja wajan aikin, ki ji inda za ki zama sama da Islaha. Babu dole."
Ummi ta bi Islaha da kallon kishi da hassada, ta yi ƙwafa, ta ja ƙofar ta fita cikin tsananin baƙin cikin da ya bayyana har akan face ɗinta.
Chairman ya kalli Islaha ya ce, "ki riƙe a hannunki, komai dare in damar zuwa a kai masa ta zo, zan kira ki."
Islaha ta ɗaga kai jin wai komai dare, ta ce, "To Chairman."
"Don Allah kar ki bani kunya Islaha, bana jin ki, na san kina da ƙoƙari, amma a kan wannan ki ninka. Babban baƙo ne na musamman, ki tabbatar da kin yi masa kalaman da zai saka ya bamu date da time. Don Allah."
"In sha Allah zan yi."
"Kina gani ana nuna miki baƙin ciki ƙarara, ki bawa maƙiya kunya, kar su yi mana dariya."
"In sha Allah zan yi."
Ya yi murmushi ya ce, "yauwa na gode. Mun samu labarin an samu gobara a cikin Jimeta, an mutu sosai ta silar hakab, zaku je ɗauka. Ki nemi Salim zai faɗa miki."
Islaha ta gyaɗa kai ta ce, "Na gode" ta faɗa tana miƙewa ta fita.
A waje ta tarar da Safeera tana jiranta, zata yi magana Ummi ta tsaya a gabanta tana aika mata da hararar baƙin ciki.
Islaha ta haɗe rai tana bint da kallon up and down ta ce, "lafiya?."
Ummi ta girgiza kai ta ce, "shi ya kawo hakan. Islaha ki tsaya a iya matsayin ki, ki tsaya a inda na ajjiye ki, kar ki yi gangancin shiga gonata. Domin duk wanda ya shiga gonata ya yi irin da na shuka, dashi zan haɗa girbe amfaninta."
Islaha ta yi murmushi ta ce, "Ai na fi ƙarfin na shiga gonar ki Ummi, sai dai ke ki shigo tawa. Kuma duk abinda ki ke ji dashi ina ji dashi, banbancin kawai, ni bana nuna baƙin ciki akan abinda Allah ya yiwa mutum."
"rufewa mutane baki, waye bai san asalinki ba? Tsintacciyar gidan marayu, tabbaɗaɗiyar ƙaramar karuwa, wacce masu gadi da ma'aiakta suka gama lalatawa. Har kina da bakin magana?."
Islaha ta yi murmushi ta ce, "Na gode, kin faɗi wace ni. Sau ke, wacece ke?."
Ummi ta sake fusata zata yi magana, Islaha ta ce, "a haka tsintacciyar gidan marayu, kuma ƙaramar karuwa ta je matakin da ke ba ki je ba. Nazo gidan nan a bayanki, kuma a yanzu dani ake damawa ba ke ba. Duk inda ki ka shiga a gidan nan, sunan Islaha ake kira, saboda ƙarfin da nake dashi wanda ke ba ji da. Kin ga ko a nan an nuna miki banbanci tsakanin tsintaacciyar gidan marayu dake!."
Ummi cikin ɓacin rai ta ce, "Islaha sai na yi maganin ki, wallahi sai na ga bayan ki! Sai na ɓatar dake daga duniyar nan, sai na tarwatsa ki, sai kin bar aikin nan gabaɗayaa. Sai na yi miki abinda baza ki sake marmarin zuwa wajn nan ba."
Islaha ta ce, "baki isa ki ga bayana ba wallahi, ba ki isa ki ɓatar dani ba, dan ke ba wata tsiya ba ce a duniyar. Ina jiran ganin abinda zaki aikata Ummi, ina zuba ido in ga ta ina zai ɓullo. In kin cika ƴar halak ki aikata mu gani, in kin cika Ummi daga yau kar na sake zuwa aiki a wajan nan, ki yi min kurciya, na ji na daina sha'awar aikin gabaɗaya."
Ummi ta matso kusa da ita ta ce, "Haka ki ka ce?."
Islaha ta ce, "haka na ce."
Ta girgiza kai tare da yin ƙwafa ta bar wajan.
Ta kalli Safeera da ta ji ji komai, suka juya zuwa office ɗin Salim.
A cikin Office ɗin Safeera ta ce, "Islaha ki tsaya, wannan ba maganar wasa ba ce ba, wannan iƙirarin da Ummi ta yi ba abinda za a ɗauke kai daga kansa bane ba. Ba wasa bane ba, ba abinda za a yi dariya a wuce bane."
Salim ya kalle su ya ce, "me ya faru?."
Safeera ta kalle sa ta ce, "Ummi ce ta tare ta tana cewa sai ta ga bayanta. Sai ta ɓatar da ita daga duniya. Ka ga wannan ai ba maganar wasa ba ce ba."
Salim ya ce, "gaskiya ba ta wasa ba ce, ya kamata a sanar da Chairman. Irin waɗanann kalaman suna iya girma a nan gaba, sai ka ga sun haifar da abinda ake gudu."
Islaha ta ce, "ku share ta, babu abinda zata iya wallahi. Baƙin ciki take yi dani, kuma bata iya ɓoye hassadarta a gare ni, shine kawai."
Ta nuna musu iv ɗin ta ce, "katin gayyatar Rehaan Yola aka bani, shine gabaɗaya ta ɗaga hankalinta ta kasa ɓoye haddasarta."
Saleem ya ce, "duk da haka dai Islaha, zahirinta mu ke gani bamu san me zata aikata a bayan idon mu, yana da kyau a tsawatar mata."
Islaha cikin ko in kula ta ce, "ku share ta don Allah. Chairman ne ya ce in zo na same ka akwai inda zamu je."
Saleem ya ce, "yanzu nake niyar kiranki."
Ta kalli Safeera da ta fita damuwa, ta ce, "Safeera kar ki damu fa, babu abinda zai same ni wallahi. Aikin banza, ta ɗaga hankalinta kawai dan an bani katin gayyatar Mr Rehaan, sai ka ce shi ɗin wata tsiya ce."
Saleem ya yi dariya ya ce, "wata tsiya ce mana Islaha, ke kin san dawa aka haɗa ki kuwa? Kin san wa ake so ki gayyato kuwa?."
"Rehaan Yola, ko na ce Ray, ba haka sunansa yake ba? Bayan haka waye shi?."
Yayi dariya, dan ya san halinta akwai drama, ya ce, "A'a fa Islaha, Rehaan ya wuce ace masa waye shi. Duk inda ki ke tunanin bawan Allah nan ya zarce haka. Ke kanki da aka haɗa ki da kati, iya haɗuwa da PA ɗin nasa ma babban aiki aka baki, balle babbar giwar."
Islaha ta ce, "Kar ka manta Hamma Saleem, ni na yi interview da gwamnan garin nan, na zauna a babban falonsa na gidan gwamnati, aka saka min camera na yi masa interview. Nasan duk capacity da yake ji dashi, bai kai gwamna ba."
Saleem ya kalli Safeera ya ce, "My love da alama Islaha bata san waye Ray ba wallahi, da ta san waye shi da ko kuɗi za a bata ta faɗi abinda ta faɗa bazata iya ba. Amma muna yi miki fatan nasara, in ki ka samu damar ganin Rehaaan, ko ba ki yi hira dashi ba, abin alfahrin mu ne balle kuma a kai ga kin yi hira dashi. Daga ranar zamu sake tsada, ganin mu sai an cike form."
Ta yi tsaki, cike da takaicin yadda ake koɗa sa ta ce, "kamar wani sahabi?."
Safeera ta ce, "ke dai Allah ya bamu sa a kawai, amma ya wuce tunaninki wallahi."
Saleem ya yi dariya ya tattara kayansa, dan tunda bata ra'ayi bazata karɓi ra'ayinsu ba, sun san halinta kaf, akwai jan magana. Saleem ya kalle ta ya ce, "ina jiran ki" ya faɗa yana fita daga office.
Safeerata ce, "Islaha in tambaye ki don Allah."
Eslaha ta kalle ta ta ce, "ina jin ki."
"don Allah meyasa ake yawan jifanki da sunan karuwa? Wanne abu ne ya faru da hakan yake kasancewa?."
Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "ni kaina ban sani ba Safeera, abinda na sani yana da alaƙa da zaman gidansu Saheer. Shiyasa maganar bata damuna ko kaɗan, duk yadda ka ke kallona a haka nake, sai me?."
Safeera ta ce, "Haka ne. Amma magana mai kyau daga bakin mutane ma rahama ce Islaha."
Ta taɓe baki ta ce, "ki wuce record office, mu mun wuce" ta faɗa tana fita daga office ɗin.
Safeera ta bita da kallo, a bayyane ta ce, "tabbas zamanta a gidan su Saheer zai saka a dinga yi mata wannan zargin saboda kowa ya san wacece Mama. Amma meyasa ake zargin tun a gidan da ta tashi ta lalace? Meyasa bata damuwa?." Babu mai bata amsa, ta yi ajiyar zuciya ta fita daga office ɗin.
*********
Mama tana zaune a gabansa malamin duba yana duba mata ƙasa, ta yi shiru tana jira ya gama ya zayyano mata abinda ya gano. Yana gamawa ya kalle ta ya ce, "tabbas akwai dawowar Rehaan ƙasar nan, nan ba da jimawa ba."
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "na ji daɗin hakan sosai."
Ya girgiza kai ya ce, "kuma zamu yi nasarar aikin mu a wannan lokacin."
Mama ta yi dariyar jin daɗi ta ce, "yauwa, haka nake so. Amma bazai koma ba dai ko?."
Ya sake dubawa kafin ya ɗago ya ce, "eh to, akwai yuwar komawar sa ƙasar waje gaskiya, amma kafin ya koma za a ɗan sha ƙalubale kaɗan."
Mama ta ce, "ni yanzu abinda nake ka yi masa, ayi masa bazai sake marmarin komawa can ba, sannan yadda yake shiri da Janan, yadda Janan take bashi abu ya ci, a sake haɗa alaƙarsu ta yadda komai ta ce masa zai yi."
Ya girgiza kai ya ce, "wannan abu ne mai yuwa Hajiya" ya faɗa yana juyawa ya ɗauko magani ya bata.
Sannan ya ce, "gashi nan ki riƙe."
Ta karɓa ya ce, "wannan jan maganin, a bashi a abinci ya ci, zai yi rashin lafiya mai yawa wacce zai jima a kwance, harkar kasuwancin nasa ma zai manta da ita. Wannan koran kuma a bashi a abin sha, ruwa ko kunu ko dai wani abun, a tabbatar da ya sha. Za ki ga aikin maganin ko ban faɗa miki ba."
Mama ta saka maganin a jaka, ta kalle sa ta ce, "na gode Malam. A ɗaukaka su Zayyad, ya zama yadda suke manya a gidan, su ne dai manya gaba da baya, ya zama komai dasu za a dinga damawa ba Rehaan ba. Bana son ace Rehaan shine ƙarsmi kuma shine a kan gaba, bana ƙaunar hakan. So nake yadda na kafu a gidan, ƴaƴana ma su kafu, yadda na gagari kowa, suma su gagari kowa malam."
Malam ya yi dariya ya ce, "tunda mu ka iya yaƙi da tsafe-tsafe ƴan india a kan ki, wannan ƙarsmin abu ne a wajan mu."
Mama ta yi dariya ta ce, "Na sha wahalar Nadira, na sha baƙar wahalar matsafiyar nan. "
"Yadda mu ka yi maganinta shima zamu yi maganinsa. Ko a wajan mijinta bata da wata power, komai yana hannunki."
"Shiyasa nake jin daɗin aiki dakai Malam, kana yi min komai yadda nake so."
"Sai maganar matar auren da aka ce na samo masa. Tunda an bani komai a hannuna, zan nemo daidai da ra'ayina. Bana so ya samu mace ta gari, tabaɗaɗɗiyar ƴar iska nake so a samar masa, saboda hakan zai yi min amfani nan gaba."
Ya yi murmushi ya ce, "ki ɗauka an gama Hajiya, ki rubuta wannan kamar an yi an gama. Zan yi miki duk abinda ki ke so."
Ta yi dariya ta ce, "indai komai ya tabbata, umarar bana da kai za a yi."
Malam ya sake gyara zama ya ce, "wallahi Hajiya babu abinda bazan yi miki ba, Allah ya ja zamaninki ki, allah ya ja zamanin uwar gidan Alhaji AbdulAziz Yola, Allah ya ja zamanin uwar Zayyad da Sameer."
Ta yi dariyar farin ciki da jin daɗin yadda yake zugata, ta ce, "yadda Daada ta dawo hannuna, haka nake so komai ya dawo hannun Malam, bana so a samu matsala. Ni ce a gaba, ƴaƴana su biye min a baya, sai jikokina, sannan sauran su biyo baya."
Ya girgiza kai ya ce, "an gama Hajajju, duk abinda ki ka ce haka za a yi." Mama ta miƙa masa kuɗi tare da miƙewa.
Shima ya miƙe ya yi mata rakiya har mota, ta shiga ta tafi shi kuma ya koma.
*******
Mamy tana zaune a falo ta yi shiru tana tunani. Riyya ta shigo ta zauna a kusa da ita ta ce, "Mamy!."
A hankali ta kalle ta, ta ce, "Riyya kin dawo?."
Ta ɗaga kai ta ce, "na dawo. Mamy tunanin me ki ke yi haka?."
Mamy ta ce, "Riyya Rehaan nake tunani, bana son dawowarsa ƙasar nan, bana so ya saka ƙafa a gidan nan, domin baya taɓa kwana lafiya."
Riyya ta ce, "Mamy nima bana so, last time da ya zo har ya koma bai samu lafiya. Ni ban san meyasa ake so ya dawo ba, wasu suna son ya dawo, wasu kuma basa so."
Mamy ta ce, "tsanar da suka yi min itace ta shafi Rehaan, sannan ana ganin shine autan maza a gidan nan, kuma shine mafi arzuƙi da ɗaukaka a cikinsu. Wannan shine dalilinsu, basa sonsa basa ƙaunarsa."
Riyya ta dafata ta ce, "Mamy ki daina saka damuwar nan a ranki, babu abinda aka isa a aikata wanda Allah bai rubuta ba. Dan ba sa sonsa ai mu muna sonsa."
Mamy ta ce, "Abba ya fito ne?."
"A'a, yana falonsa a zaune."
Ta girgiza kai ta ce, "ina son magana dashi."
Riyya ta ce, "in yi masa waya?."
Ta girgiza kai ta ce, "zan je in same sa." Ta faɗa tana miƙewa ta saka hijjab zuwa bangaren Abba.
A ciki ta samu Umma, suna haɗa ido ta haɗe rai, Mamy dai bata ce komai ba ta yi mata sannu. Sama-sama suka gaisa.
Mamy ta ce, "Abba yana nan?."
"Eh yana ciki."
"ki yi min magana dashi don Allah."
Umma ta wani kalle ta ta ce, "ki yi masa me?.
Mamy ta kalle ta jin abinda ta ce, sai kuma Umman ta yi tsaki ta shiga ciki. Mamy ta nemi waje ta zauna tana jiran fitowarta.
Ba jimawa sai gashi ya fito, Mamy ta miƙe tsaye tana kallonsa har ya ƙaraso wajan. Mamy ta ce, "Barka da fitowa."
Ya ɗan kalle ta sannan ya ce, "barka."
Ya zauna a kan kujera ya ce, "lafiya ki ke nemana da safiyar nan?."
Mamy ta zauna itama ta ce, "Akan maganar dawowar Rehaan ne, yaushe aka saka ranar da zai dawo?."
"Ban zaɓi lokaci ba, amma zuwan nasa bazai wuce cikin satin nan ba."
"To shikenan."
"lafiya?:"
"tsakani da Allah zuciyata bata kwanta da zuwan Rehaan ba wallahi, haka kawai nake ji bana so yazo ƙasar nan."
Abba ya dafe kansa ya ce, "Nadira ba mun gama maganar nan dake ba?."
Zata yi magana ya katse ta ya ce, "meyasa ki ke yin abu kamar ke kaɗai ki ka haifi Rehaan ne? Meyasa ki ke yin abu kamar ke kaɗai ki ke sonsa ne?."
Mamy ta girgiza kai ta ce, "Ba haka bane, kawai dai...."
Ya dakatar da ita ya ce, "yadda ki ke sonsa haka nake sonsa nima, yadda bakya so ya cutu nima bana so ya cutu. Meyasa ki ke haka ne?. Ko kina ganin zan cutar dashi ne?."
Mamy jin ya fara faɗa sai ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ba haka nake nufi ba, i'm sorry."
Abba ya ce, "to ki dakatar da maganar nan don Allah, ki bari na yi abinda nake ganin ya dace, kin ji ko?. Zan ƙi yin abinda mahaifiyata ta ce in yi ne, ko zan zaɓi abinda ki ke so na bar nata?."
Ta yi shiru bata ce komai ba, ganin haka sai ya sassauta murya ya ce, "Nadira don Allah ki nutsu, nima bazan so abinda zai cutar dashi ba. Tun ranar muka gama magana dake, ban yi tunanin za ki sake dawo min da batun ba."
Mamy ta ce, "to babu komai. Allah ya dawo dashi lafiya."
Abba ya ce, "Amin ya Allah. Abinda za ki ce kenan. Ki je zan shigo."
Ta ɗaga kai alamun to. Ta faɗa tana miƙewa ta fita zuciyar ta gabaɗaya babu daɗi.
Umma da ta ji komai, Mamy tana fita itama ta daga ɓangaren ta shiga wajen Mama.
Mama ta cire hajjibi ta ajjiye, Umma ta shigo ta zauna ta ce, "Mama."
Ta kalle ta ta ce, "ya aka yi?."
"Wallahi in ba mu sake shiri ba, Nadira zata hana Rehaan dawowa ƙasar nan."
Mama ta ce, "me ya faru?."
"yanzu ta samu Abba akan maganar, kamar zata yi kuka saboda damuwa. Ita bata so ya dawo, waye waye."
"Me ya ce?."
"faɗa ya yi mata, ni ban taɓa ji ya yi mata tsawa kamar yanzu ba."
Mama ta ce, "dakyau, ai duk bala'inta sai ya dawo ƙasar nan wallahi, yadda ƴaƴanmu suke ƙasar nan, ake ci ake sha dasu, shima sai ya dawo. Ai ba fin kowa ya yi ba."
Umma ta ce, "an tattara masa dukiya a ƙasar waje, sai an yi magana ace dukiyarsa ce. Har nawa yake da zai tara wannan uban kuɗin shi kaɗai?. Ai in Abba ya mutu a yanzu akwai tashin hankali wallahi."
Mama ta ce, "ki bar ni dashi, ba dai zai dawo ba? Hmmm! zai ga abinda zanyi wallshi, a wannan karon bazan ƙyale sa ba wallahi."
Umma ta ce, "gwara a san abinda za a yi kam, dan lamarin yana neman lalace mana. Bara in koma, kar ya neme ni" ta faɗa tana tashi ta koma.
Mama ta bita da harara ta ce, "Shashasha, wai in Abba ya mutu akwai rigima."
"Mtsw! To kema ba sai abinda na ɗauko na bawa ƴaƴanki ba? In aka ce yau babu Abba ai kakata ta yanke saƙa wallahi. Shiyasa kafin hakan nake so yarana su zama sune akan dukiyar ba Rehaan ba, yadda ko mutuwa ta zo sai abinda na ga dama zan bayar. Mu zuba mu gani" ta faɗa tana yin ƙwafa zuciyar cike da mugun nufi....
_Book 1 free ne, Book 2&3 paid ne akan naira 1k kacal. Pay into Sadiya Nuhu Mukaddas 5903999117 Moniepoint MFB. A tura shaidar biya a wannan number 09030398006 ko 0701 809 8175._
Nana Haleema✍🏻
