Karshen Kaddara Page 17&18 Complete by Ammey Laylerh - Abokiyar Hira Novels


༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*


𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢  𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ


 _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_


Unexpected and Surprising 🔥💥 


𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. 


ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏....


Page 17&18


♡ ♡ ♡ ♡     

ꨄ Ai tin kafin ta ƙarasa yay wani hanzarin amsar peper da byro'n, idanunsa na zubar da wasu ruwan hawaye masu ɗaci da ƙona zuciya yayi rubuta mata sakin ya bata, tana amsa taga ɗaya tak ya mata tace se ya jere mata ukun nan cif cif..... Duk yadda yaso data taimaka ta bar shi hakan, amma haka taƙi sema bakin data sake buɗewar da niyar sake tsine masan, ya sake rubuta mata saki ukun, kana ta fice da takardar sakin a hannunta tana huci......... Kai tsaye gidansu Meenal ɗin ta wuce wacce dawowarsu kenan daga Asibitin wannan fitila'in sakin ya sake riskarsu, komai bata ji ba game da sakin domin dama tasan zamansu dole ya ƙare Ya Ahmad ɗin,duk kuwa da iriyar ƙaunar junan da suke ma juna, amma tasan mahaifiyarsa ba zata taɓa barin hakan faruwa, se da ta tayi cin mutuncin da tijararta kana ta fice ga bar  musu gidan ranta fesss yau dai ALLAH ya kawo mata hanya cikin sauƙi ta raba auren Ahmed ɗin da Meenerl, duk da kasancewar gwaggo Sadiya ba uwarta bace amma seda taji babu daɗi da ababuwan da suka faru da Meenal ɗin,amma kuma ko a fuska bata nuna mata ba, amma dake jajen ciki na munafunci ne shi ta mata, har da cewa ai ƙara da ALLAH ya ɓarar da cikin suma shi ne kwanciyar hankalinsu. Baffa kuwa da Ya Sadeeq ɗin idan hankalinsu yayi dubu to a tashe yake sakamakon sakin nan na Ahmad, wanda bayan sallarn isha'a ya ƙira Baffa ya ringa kuka yana cewa ya yafe masa haka ALLAH ya gama tsara iyaka rayuwar auren da za suyi kenan dama cikin 1 year's kawai, wacce ma saura 1 months su cika shekara ɗin cif da cif, kwantar masa da hankali sosai Baffan yayi yace ba komai Ubangiji yasa hakan shi ne mafi alhairinsu gaba ɗaya, Ya Sadeeq ma sosai yaji maganar sakin har cikin zuciyarsa amma kuma se ya fawwalama ALLAH shi ma,  abu kamar wasa se gashi da dare Meenal ta gaza runtsawa, magabar sakin duk bata dameta se da tazo kwanciyar. Nan idanunta suka sake ƙaiƙashewa suka soye sabo da tsabar azabar da take amsa daga gare su,  Idanunta ta rumtse ko zata ji sun rage daga zogin da suke mata, amma kuma ina babu damar hakan, sema jin da tayi kamar ba zasu iya buɗe mata ba, Wayar tane ta kawo haske alamar shigowar text message kasancewar a silent take, kamar ba zata ɗauka ba amma kuma ta miƙa hannunta da kyar tana janyo wayar, tana kallar test messages ne ta sake kife wayar ba tare data duba taga ko miye ba, don kai tsaye ta san MTN ne don su ne masu mata haka. Alwala ta miƙe ta dauro ta fito ta fuskanci alƙibla, bayan ta idar da sallolin data ringa yi ta ɗauka Alqur'ani ta hau karatu har zuwa sallan asuba, bayan ta idar da sallan asuba ɗin tayi adda'o'i masu kyau da girma kana anan wurin wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, wanda baya farka ba se wajajen sha ɗaya da rabi,  wanka ta fito nan tsakar gidan tayi kana gwaggo Sadiya ta miƙa mata abin kari, kanta kawai ta jijjiga don ba zata iya cin komai ba adai halin da take ciki. Wayar tane ta shiga ruri tana ɗauka taga Maman Yasmin ce makwabciyarta, jiki a matukar sanyaye ta ɗauka wayar ta amsata.... "Meenerl abinda ya faru kenan?" Ta faɗi a raunace domin sosai suke mutumci babu laifi a zaman nasu, dake duk komai da komai be fita ba se a jiyan, zancen sakin kuwa tuni uban kowa har ya sani a cikin anguwar tasu, don yau wajajen karfe goman safe Maman Ahmad ta sake komawa gidan, taje da garada ta saka suka ringa fito da kayan Meenal ɗin har ƙofar gida, inda nan fa yan anguwar suka yi dafifi wasu cike da tausayin Meenal ɗin, wasu kuwa haka kawai suna mata ala ƙara ba tare data tare musu komai ba. A lokacin da dake wannan aika aikar kuwa a lokacin Ahmad ɗin na ciki yana jinyar zuciyarsa don ko gangar jikinsa da kyar take ɗaukarsa. Yana a wannan halin ya fito don jin kwarabniyar tayi yawa, a lokacin da yake kallar Mamyn nasa tana wannan aika aikar ƙiris ne ya sa zuciyarsa bata ƙarasa ficewa a gangar jikinsa ba, da kuma ya mata magana tace kul be rufe mata baki ba yanzu taci mutumcinsa. Shi ne ya koma gefe yay ƙiran Ya Sadeeq ya faɗa masa muryansa ko fita ba yayi sosai. Dan da nan kuwa sega Ya Sadeeq ɗin har ya ƙaraso da wata motar ɗibar kaya, har kuma lokacin Mamyn nasa nan kaf komai daya danganci Meenal seda ta fito da shi, haƙuri ya ta be Ya Sadeeq ɗin yace masa babu komai haka dama rayuwa ta gada. Daga haka suka hau kashe kayan Meenal ɗin suna zubasu cikin motar da yazo da ita ta wurin da yake aiki,  koda yaje shagon waje Baffansu ya buɗe musu suka jibge kayan. Aka ware mata iyaka na sawarta kawai a gefe guda da nufin nan da kamar 1 week se a bata kar abun ya mata kusa da yawa. 


Bayan sun kammala wayar da Maman Yasmin ɗin har zata ajje wayar wani abu me kama da transper na kuɗi ya ɗauki hankalinta, don haka kai tsaye ta shige cikin sakon, kuɗi ne zunzurutun kudi har naira dubu ɗari biyar, me ɗauke da account na Ya Ahmad ɗin ta, jikinta na rawa ta fito daga cikin amoung balance nata messages ɗin dake ƙasar sakon kuɗin ya sake ɗaukan hankalinta don shima ɗauke yake da sunar Ya Ahmad ɗin, tana buɗe sakon bata san lokacin da kukan da tayi ta roƙon jiya su zubo mata ba se gashi kai tsaye na saƙƙo mata, kanta take dan jujjuya a cikin zuciyarta tana sake maimaita abinda sakon yake ɗauke dashi.....


_Tun daga numfashishinmu na farko bayan wanzuwarmu a doron ƙasa,sakanni suke gangarawa cikin mintoci, hakan ne yake bayuwa zuwa ga kowacce Sa'ar dake shuɗewa. Badan komai ba sai dan ta samar da ranakun da muke kidaya makwannin da suke haifar da kowanne da kowanne watan da ke yiwa rayuwarmu giɓi, kwanci tashi nake lissafin watanni da tunanin rayuwarmu, har zuwa jerantuwar da lissafin shekarun da suka shige mana a baya, Amma idan na tuna cewar ALLAH baya buƙatarr fassara, yana ganin irin  girman damuwarmu,yana kuma sane da irin girman ƙaddarar dake tare damu, kuma shi ne zai shirya bamu mafita kamar yacce yace kayan cewa.  Tabbas In sha ALLAHU ba zaki taɓa tozarta ba meenoh!,  Kiyi hakuri na rabu dake ba wai saboda kin sanja bane, Na rabu dake ba wai saboda  na gaji dake bane, Na rabu dake ba wai dan akwai wata a rai na bane,  shiru na kuma a gareki ba kiyayya bace, nisanta wa ta ba rauni bane,kawai ina yaƙi da zuciyata ne, ki gafartamin  canzawar dana miki Meenoh a duk tsayin watannin da suka shude mana, ki kuma yafewa Hajiyata duk irin abubuwan data ringa miki wanda samm ni a karan kaina ko hakan bana son tunawa, ki ɗauka cewar wannan ɗin Ita ce ƙaddarar mu, zanci gaba da miki adda'ar Ubangiji yaci gaba da baki kariya a koda yaushe!,  Ki ringa yawan tunawa kuma da cewar. Har abada akwai waɗan da zuciyarmu ba zata taɓa dena ƙaunarsu ba, saboda  girman halaccinsu garemu na gode My Ameenatou......._


 Tana karantawa wani kalan kuka ya taho mata a guje amma tayi hanzarin sanya hannunta ta toshe bakin. Wani kalan rumtse idonta tayi tana ƙanƙame wayar nata cikin jikinta, tana a wannan yanayin se ga shigowar Shareefah a guje  da kuka ta faɗa jikinta, wani kalan kuka Shareefah'n ta saki tana rungume yayar tata cike da ƙauna da tausayi me tsanani, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³" Meenal ɗin tayi ƙarfin halin kamawa tana maimaitawa don ƙanwar nata ta ɗauka. Aikuwa ta kama suka ringa maimaita har zuwa lokacin da zuciyoyinsu suka ji sun yi sanyi, "Mummunar ƙaddarar data sake samun mu Kenan Yaya?,  haka ALLAH ya sake wanzar da ikonsa akan ki kenan?, ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALINNNN koda yaushe, zamu ci gaba da ambatar kalmar cikin kowanne irin yanayi In sha ALLAHU...., Kiyi hakuri In sha ALLAHU wannan ma zai wuce yaya.." wani murmushi me ciwo tayi a matsayinta na wacce take amsar roldin uwa ta shiga kwantarma da Shareefah'n hankali, cikin muryan da yayi laushi sosai take shafa gadon bayan Shareefah ɗin ta ce. "ALLAH ma ya tsare My freind,komai yazo mana cikin sauƙi da amincinsa, ciki kuwa ya fita duk da kuwa cewar naso kayana,amma bana da ja ko hukunci akan duk abinda Ubangiji na ya zartar a kaina. ALLAH Ubangiji ya sake zama gatan mara gata yaci gaba da shiga cikin al' amurranmu yana zame mana jagora a koda yaushe..." Haka taci gaba da kwantar ma da ƙanwar nata hankali har seda taji Shareefah ɗin na  maida numfashi a hankali alamun barcin ya ɗauketa, har tana sauƙe ajiyar zuciya kana yaji hankalin ta ya kwanta sosai, Itama se tayi ƙoƙarin zame  kan Shareefah ɗin ta mayar mata kan pillow da gefen kafadarta tayi, sedai  cikin barcin Shareefah'n ta ƙara janyo yayar nata  jikinta tana gyara kwanciyarta a jikinta  amman idonta dai a rufe, shiru kawai tayi tana bin ƙanwar nata da tayi lif a jikinta tana sauƙe ajiyar zuciya, gashi bata  son ta farka haka kawai take jin bata son ƙanwar nata da kowacce kalan damuwar da zata sake zuwar mata, koda da misƙala zarratin ne, barin ma kalan wannan ɗin da yazo musu hagunce, ba tare da sunyi zata ko tsammanin hakan ba.Tunani barkatai taci gaba dayi akan rayuwarsu har ƙarfe kusan biyar da rabi, kana ta shiga motsawa ahankali, shiru kawai tayi har ta gama tashi bata motsa ba, adda'ar tashi daga bacci tayi a hankali tana zare janye jikinta a na ta, ƙura mata Ido tayi ta cikin ɗan duhun magrib ɗin daya kawo kai. Duk da irin tsananin damuwar da yayar nata take ciki amma hakan bai hana Kyan nan nata fitowa ba, fuskan nan sai glowing na kyau takeyi ko ina kuma  a jikinta fresh, kana ta miƙe ta shige toilet bayan tabi yayar nata da adda'ar gamawa da duniya lafiya. Duk abinda Shareefah'n keyi kuwa a ɓangaren Meenal ɗin tana jinta, shiru kawai itama tayi ƙaunar ƴar gudaliyar ƙanwar nata na sake kamata, tana kwancen idanunta a rufe har Shareefah ta fito daga wankan, itama se taji bata son tashin yayar nata ƙara ta barta ta ɗan huta ko taji rangwame da sassaucin abinda ke sukar zuciyarta.  Ita kuwa Meenal dake daga kwancen idanunta lumshe har bama tasan taja lokaci har haka ba, se da taji anata ƙiraye ƙirayen sallar magrib, da sauri ta mike tana fita itama,  alwala tayo tazo ta tada sallah bayan ta idar ta ɗan kishin gida saman dardumar. Lumshe idonta tayi ababuwan da suka faru na sake nemar dawo mata daki daki, saurin kawar da tunanin hakan tayi tana lalubar kalmar YA WADUD tayi ta maimaita da kuma HASBIYALLAHU LA'ILAHA ILLA HUWA, ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHEEM AZEEM.... Tana nan zaune har aka yi isha'a kana suka fita tsakar gida da Baffa ya leka da kansa har ɗakin yace su fito suci abinci, duk jikinsu babu me kwarin gwiwar cin abincin amma haka suka fito, ALLAH yaso ma bame nauyi bane, yau matar gidan bata ga damar yin tuwo ba, jallop ɗin taliya da maccaroni tayi, se ruwan shayin data haɗa musu dashi,  plat guda aka zuba musu me ɗan girma Meenerl tayi hanzarin cewa a rage amma Baffa yace suci iyaka cinsu in sun yi sauran a bama ko almajiri ɗaya ne. Rabi kuwa basu ciba duk da cewar yadda taliyan tayi daɗi, shayin dai sun sha da ɗan yawa kana aka ɗan taɓa fira wacce mafi yawanci nasihohi suka fi yawa, sai wajajen tara da rabi kana suka yi sallama kowa ya nufi makwancinsa, nan fa yauma baccin nan yaso yama Meenal gaddama, don kuwa yace baisan zance ba, amma albarkacin Shareefah da Adda'ar data fara tofa mata sama sama har bata san lokacin da baccin yayi awon gaba da ita ba, ba tare data san sanda ya ɗauke tan ba. 


Washe gari suna tashi bayan sunyi sallar asuba suka sake komawa se wajajen bakwai suka tashi, tare suka fita zuwa tsakar gidan duk kuwa da yanda Shareefah taso Yayar nata ta sake hutawa amma tace ta barta, idan ta barta a ɗakin ita ɗaya bata jin daɗi ne, haka suka kama aikin gidan a tare, se Shareefah'n ta kama shara wanke wanke tace Meenal ɗin tayi musu abin kari, kitchen nasu ta shige ta ɗora musu farar taliya ƴar Hausa da manja, ganin yajin gidan se a slow ne ya sa tayi saurin daka me daɗi kana ta sake ɗora musu ruwan tea yaji kayan ƙamshi. Tana gama dafa musu  tea ɗin ta juye a flask, kana ta gyara komai data bata ta ɗebi ruwan zafin data ɗora musu ya yawa ta shiga wanka, tana  fitowa Shareefah ta shiga itama, bayan ta gama  shafa mai wata  doguwar riga ta zira ta yadi kana ta  fito  daidai shigowar Shareef. A zaune taga Baffansu saman tafarma, tsakar gidan nan yayi ƙal ƙal gwanin birgewar sharar da yasha,  gefensa gwaggo Sadiya se famar hamma take tana wani murza idon daya bada  alamun yanzu nema take tashi a baccin, ɗan murmushi kawai Meenal tayi tana ƙarasa  fitowa  cikin kaunar ta take ma Baffanta da  baya taɓa ɓoyuwa a fuskata tace "Barka da safiya Baffa!". Murmushi yai me kyau  yana me furta.  "Barkanmu dai Ameenatou!, fatar kina lafiya?" "Lafiya ALHAMDULILLAH" ta bashi amsa tana tashi cilak ta ɗebo musu kayan karin, gwaggo Sadiyan ce ta zuzzubama kowa kana ta ɗauka nasu da niyar shigewa ɗaki, amma Baffa yace ta dawo ta zauna yana kwalama Shareefah ƙira kan tayi tayi ta fito, don ya santa da nauyi akan komai. Bayan sun karya kana suka miƙe suka nufi ɗakinsu. Kallon Shareefah dake shirin kwanciya Meenerl tayi data riƙe bakin ganin wai kwanciya ne ma za tayi, "Ke Shareefah baki san zaki iya makara ba?" Kallonta Shareefah'n tayi tare da cewa "Wai me kike nufi da nine Yaya Meenal?, nufinki daga zuwa yau ɗin shikenan se in ɗebi jiki in koma yau kuma?, cab wllh da sake, ai sena cinye satin nan tsaf tare dake..." Murmushi Meenal ɗin tayi me cike da dattako tace "Yanzu ke Shareefah ko wani yace ki zauna ki cinye satin seki yarda ki zauna karatun duk da aka muku ya tafi a banza?" Turo madaidaicin bakinta gaba tayi kana tace. "A tinaninki kenan ai, ga yawa ne nan ta waya zanka amsar duk lesson ɗin da ake mana...."  "To ai shikenan, ke kuma  ALLAH ya taro min ke..."


★..


Zaune suke a lafiyayyan palourn gidan nasu kusan dukansu , tin daga kan Ikleemerh Ummiensa,Daddy se Dr Bilal shima, kusan tin da suka zaune kowa shi kaɗai ake jira ya fito su fara dinner, amma haka suka share fiye da fin 30 minutes a zaunen da suke zamar jiransa, ita kanta Ayla ta gama matsuwar Papa'n nata ya fito, sedai hakan be sa ya fito ɗin ba, wanda har ƙiransa a waya se da Bilal yayi amma wayan a kashe, don haka Daddy kawai ya basu umarnin su fara cin abincin nasu kawai, Ɗan saurin kallon Daddy'n Ummiensu tayi jin yace su fara cin abincin wai, wacce take sanye cikin wani mayen lace ruwan ƙasa, an masa zane zane da sky sak mai matuƙar tsadar gaske wacce ta haska farar fatar ta, wanda kallo ɗaya zaka mata kasan cewar ita ɗin ba baya bace wajen tattali da kuma tsaftar jikinta, wacce zata kai shekaru 45/47 haka,  Amma jikin ta bai nuna ba saboda  tana da jiki nai kyau ga kuma uwa uba kulawar da yake samu, wanda kai tsaye ma ba ka isa cewar ita ne ta haifa wannan zabgegen matashin magidancin kamar Majeed ba. Shima kallonta Daddy'n yayi yana sakar mata murmushi mai cike da SO ɗin nan, "Afwan ummien Majeed, wato nace kar mu jira shalalenki shi ne kike wani tsare ni da ido" yayi maganar yana kallonta da itama take sake mayar  masa da martanin murmushin tai tana masa wani kallo na ƙasan ido. Wayarsa ya ɗauka kai tsaye yana dokama Majeed ɗin ƙira, kai tsaye ya bashi umarnin ya fito ƙasa shi kaɗai suke jira, wani yamutse fuskarsa yayi shi fa badon Daddy bane da kansa ya ƙira shi wllh da babu inda yay niyar zuwa, bare wani cin abincin da sun san ba woni ci sosai yake ba, don ze iya fita yaje ya dawo ma ba tare dako ruwa yasha ba kaɗan kenan daga cikin aikinsa. Tamkar wanda yake gabansa haka Daddy'n ya gyaɗa kai kawai yana maida kallonsa ga ummien yace "Se a dai na min wani gani gani kuma ko Hajiya na ƙira Shalelen naki" ba'a ɗau wani lokaci mai tsayi ba kuwa suka fara jiyo takunsa daya ratso  palourn, don haka tamkar wani bako ko wanda basu taɓa gani ba gaba ɗayansu suka zubama ƙofar shigowa palourn ido duk da kuwa sun san ko waye zai shigo ɗin kuwa. 

Cikin takun dake nuna ko a jikinsa ya shigo palourn, yana sanye da riga da wando masu taushi brown colour, saidai rigar irin armless ɗin nan ce ga ta kuma ya ɗan buɗe botir na  gaban rigar guda uku, wanda hakan ya bayyana ƙirjinsa a waje, ƙafarsa sanye da versace slipper's masu taushi irin room parlourn nan, cikin takun jarumta ya karaso tsaƙiyar palourn bayan ya cire takalmin sa daga bakin grass carpet ɗin dake tsaƙiyar dining ɗin,  binsa da kallo ummie tayi tana girgiza kanta ganin yanayin da har zuwa yanzun yake a cikin bame kyau bane,  a natse yakai zaune kan farar chiar ɗin data saura yana me furta.  "Evening Daddy" ba tare daya jira amsar saba ya juya ga ummien nasa ita ma yace "Evening Ummiena" kana Ikleemerh da Ayla suka shiga rige rigen fara gai dashi, ɗan hararansa Dr Bilal yayi yana kallon Daddy yace..

  "Wato ni ka gama rainani nine ba zaka gaida ba ko?, Daddy Don ALLAH ban fi wannan yaron ba???." Dr Bilal ɗin ya faɗi yana wani turo bakinsa gaba, wanda yake ɗan gidan yayan Daddy'n ne, sedai iyayensa basa Nigeria suna Istanbul..... Wanda shi kuma kishin Majeed ɗin ne yasa yafi son zaman nan ɗin fiye da can, Wani kallo Majeed ɗin ya wurga masa kafin ya shiga motsa bakinsa kamar wanda ke tsoron yin maganar yace... "Koma dai miye ni ban yarda ba, sabo da karka manta ni har budurwar Ƴa gareni ƴar five year's wacce take ƙoƙarin shiga ta 6, ga kalla kuwa ta ina zan yarda cewan ka fini???.... Kuma ai ko makaho ya laluba yasan daidai, dan ubanka Yayan Fahaad shi ne Sa'a na bama Abdul-maleek..."  Yayi maganar yana wani yamutse fuska kamar yaga kashi, kana ya shiga duba  apple watch ɗin dake ɗaure a tsintaiyar hannun sa na hagu ganin pass 9 na ƙoƙarin shigowa ya kalla Daddy'n nasa da su har sun riga sun fara cin abincinsu yace "Zan iya tafiya?" Bayan yasha apple juice kawai. Shi dai Bilal in banda aikin hararansa babu abinda yake.  Girar sa ta hagu ya ɗan sosa jin Daddy'n yace babu inda zai tafi sau yaci abinci, gwalo Bilal ya masa daya saka Majeed ɗin ɗaukan robar da yasha apple juice ɗin ya jefe shi da ita, kare jifar yayi da hannunsa yana dariya yana cewa ai ba shi yakar zomon ba... Da kyar ya iya cin kaɗan don a cunkushe yake jin jikin nasa kana yasha ruwa ya mike bayan yama Ayla peack a goshi, don yau itama ko ƴan maganar bata samu ba, wanda itama yarinyar ta san duk wani motsi nashi don haka se baya woni takura masa ba.... Kai tsaye ya mike ya nufa samar sa. Binsa da kallo cike da tausayawa ummien tayi, a ranta tana adda'ar ALLAH ya kawo ma ɗan nata mafita da ɗaukinsa.... Ayla da har ta fara bacci Ikleemerh ta ɗauketa suka wuce dakinsu, sallama Dr Bilal ya musu shima yana nufar nasa ɓangaren da yake guda shima.  


MAJEED 


Drectly yana isa ɓangaren nasa yakai zaune kan wata ƙerarriyar silver chiar. Yana kwantar da kansa da jikin kujerar,  lallausar rigar amrless ɗin dake  jikinsa ta wani lafe a dark  shiny skin nashi, wanda kai tsaye ke  bayyanar da asalin hutu da luxurious life ɗin da yake cikinsa. Fuskar nan kai tsaye dake bayyanar da kwantacciyar damuwar da yake a cikinta, tin daga lokacin daya fara ɗora idonsa a kanta. System ce a gabansa ya zuba mata fararen  idanuwansa, wanda a zahirin gaskiya bawai kallon system ɗin yake ba ya tafi ne duniya irin ta tunani.Wani zazzafan numfashi mara sauti ya fesar jin,yanda zuciyarsa ke ci gaba da sake karta masa a karo na ba adadi. Gaba ɗaya kansa nemar juye masa yaje da tunanin  Ameenatou ɗin sa, wacce har gaban abada yake jin bazai taɓa iya haɗa sonta dana ko wacce mace ba, duk wata macen da zai so to ta biyo bayanta.

Duk da cewar  Ƙaddara ta riga da ta buɗe tafin hannun kowannensu ta masa zanen rubutacciyar ƙaddararsa, ta raba su rabuwa kuma irin ta har gaban abada ɗin nan ,  Wani gauron numfashi ya kawo yana sake zubama laptop nashi farare ƙal ɗin idanuwansa. Pisc na ameenatou ne tare dashi da sukayi a Goa bakin wani gaɓar ruwa, ga ɗan ƙaramin matashin cikin tanan daya bayyana tana sanye da wata faffaɗar rigar slik fara me kyau, da wando ash me faɗi shima kanta da farar hura daya zame sosai, ganan kwantaccen baki wulik ɗin gashinta ya bayyana da yake har gaban goshinta. Farar fuskarta me kyau ɗauke da murmushin da baya taɓa mantawa dashi, wanda suna shan ice cream ne ta shanye nata shi kuma yana cikin shan nashi ta warce masa tana masa gwalo fuskanta ɗauke da wadataccen murmushin ta me kyau, da komai da komai kalan nata ne Ayla ta ɗauko,duhun fatarsa ne kawai kega yarinyar farin ne kawai na uwar bata dauko ba, se maganan da suke sakk irin nashi da baki bakinta.... Pisc ɗin yake kalla a cikin laptop nashi  idanuwansa har kalan bala'i bala'in yaji suke mai na tsananin damuwar da yake son cusama kansa, yasha zama irin haka idan abun duniyar suka ishe sa har kusan saɓo yake wani sa'in, amma kuma idan yay duba da yadda Ubangiji ke juya

lamuransa daga kyawawa zuwa munana se ya sake jinjina lamari na ubangijin da babu kamarsa a duniya, dan kuwa shine kaɗai wanda ya isa yayi abinda babu wanda ya isa juya hakan. dan yana da tabbacin idan wani na juya ƙaddarar wani da tuni ya jima da fara  juya nashi  ƙaddarar, yasan kaf cikin duniyar nan ya tabbata babu abinda ya rasa a rayuwarsa se ita, se sauran mataye biyun da suka bayanta ma wato Ramlah da kuma Fareedah. Se dai wannan maganar ta *TUN RAN GINI* da tsarin  ƙaddararsu  ya daɗe da rubuta komai da ze wakana da rayuwar ko wanne bawa nashi, amma duk da haka bazai gajiya ba wajen kaima ALLAH kukansa kan kawo masa mafitarsa cikin wannan hali da yake ciki. Janye  fararen idanuwansa da sukai ja yayi a kan laptop ɗin a  sanyaye kuma ya maida ya rufe  yana sauƙe  numfashi me zafin gaske, kana ya nufa bathroom,wanka yayo yayi nafila kana ya kwanta zuciyarsa cike da sake saken ababuwa.... Har besan lokacin da wani nannuya wahaltaccen bacci yin gaba da shi ba....


Meenerl....


Gaba ɗaya yinin ranar ta yau ta sake yinsa gata nan gata nan ne, barin ma makwafta da mutanen anguwa da suka ringa shigo mata jaje, wasu kuwa dama da gayya suke zuwa  su yayyaɓa mata magana a matsayin jajantawa suke mata, har da masu ce mata ai tama godema ALLAH da cikin ya fita shikenan babu ita babi idda ko a yau taga damar sake wani auren za tayi,  duk cikin masu zuwan babu wanda ya taɓa tankama, daga ƙarshe ma se ta wuce dakinsu se yamma  kana ta dawo tsakar gidan, zama tayi tace Shareefah ta mata kitso, suna cikin kitson sega shigowar Bilkisu nan daga wurin bikin da taje. Ciki a sanyaye ta ƙaraso don ummar ta harta riga ta sanar mata da komai, wacce matuƙar tausayin yayar nasu ya sake rufeta da ganin nata kawai zai ne a gida. Idonta fall da ruwan hawaye ta zauna tana gaida yayar nasu tare da jajanta mata lamarin, da cewa ALLAH ya rufa asiri ya tsare gaba. Da Amin suka amsa ita da Shareefah sega fitowar gwaggo daga ɗakinta ta fara masifar wato ko wurinta ba zata shigo ba shi ne ta tsaya a wurinsu, da uban wani ne yace karta kama kanta ko ita ta aikata ne bare ace ita ce silar ƙaddarar nata. Babu daɗi samm haka Bilkisun ta miƙe tana sake bama Meenal ɗin hakuri,  ko da aka yi sallar isha'a se aka fito tsakar gidan zaman fira bayan anci abincin dare. Se dai shiru shiru Meenal daga shiga daki ɗaukan abu har yanzun shiru, tun Shareefah da Bilkisu na saka ran fitowa Meenal ɗin har su hakura. Ita kuwa Meenal a nata ɓangaren tana shigewa ciki duk da ba barci take ji ba, se kawai tayi kwanciyarta don tun safiyar ranar take wani  sukuku da ita kamar marar lafiya. Akan sallayan da tayi Sallah ta zauna tayi shiru tana istigifari ga ALLAH da Salati ga fiyayyan halitta Annabin Rahama, duk yanda tunani yaso ya bijiro mata saida ta kawar dashi kawai ta fawwalawa ALLAH lamarinta tasan duk rintsi yana tare da ita, a haka har bacci yaci ƙarfin ta ba tare data shiryama hakan ba. Cikin kwanaki uku amma anguwar ta gama haɗewa da zancen wannan zancen abinda ya sama Meenal ɗin, Nan  kuwa mutanen anguwa harma da tsallakenta aka samu abin yamaɗiɗi a unguwar, 

Gaba ɗaya se  suka sako Meenal a gaba har seda Shareefah ta yankama ɗaya daga cikin munafukan katin rashin mutumci kana sauran suka shiga taitayinsu, wannan abu da Shareefah tayi shi ne ya ɗan kwato Meenal ɗin daga munafukan anguwar.


"Yahanasu...."

 Abban Ahmad ya  wani irin ƙiran sunanta a mugun tsawacen da ya sanya kowa dake wurin  rawan jiki. Don ba abu bane daya taɓa faruwa a zahirance duk kuwa irin tijara da jalalar da Umman Ahmad ɗin keyi akan duk wani abu daya danganci Ahmad ɗin. Bakinta dake rawa ta buɗe da kyar tace "I'm sorry Abban Ahmad, wllh sharrin shaidan ne" Ta furta muryan ta na rawa sosai. 


"I said get out my friend! Nace ko?" Gaba ɗaya se jikin yaran nasu yayi sanyi ganin dai da gasken gaske mahaifin nasu ya rantse se tabar masa gidansa itama, in yaso se taji idan sakin da daɗi itama. Be sama labarin sakin data titseye Ahmad ɗin yama Meenal ba se a wayewar yau daya kasance kwanaki huɗu kenan da faruwar abun. Don haka yace itama wllh se ta bar masa nasa gidan se lokacin daya ne mata, domin dama ya jima da mugun gundura da halin nata, kawai yana dauke kai ne sabo da yaransu, to amma tun da ta nuna masa iyakarsa da cewar shi be isa ba to ya rantse a yau ba sai gobe ba seta bar masa gidansa. Ahmad ɗin idanunsa sunyi jajir ya nufa Abban nasa yana bashi hakuri shima ya buga masa wata tsawa yace ya fice ya bar masa gida. Fatima kuwa wani irin kuka take na nadamar halayen momin nasu marasa kyau.  Ta buɗe baki da niyar sake bashi wani hakurin ya sake buga mata wata uwar tsawar da tafi ta farko ba shiri ta haɗiye maganar da bata ƙarasa taba, tana barin wurin don  A yadda ta ji muryarsa a kausashe kam ta tabbata babu wasa a cikinta ko sauran mafaka, 

  Jiki a sanyaye Ahmad ɗin ya fice a parlourn nasu itama Fatima ta wuce nata ɗakin. Ita kuma Umman nasu da  jikinta ke rawa ne ta wuce ɗakinta babu jimawa se gata ta fito da hijjab ɗin bata fiye yawan da shiba. Ganin daga se himar nata ne ya saka shi sake buga mata tsawa yana cewa maza ta haɗo kayanta a akwatu don ba nan kusa zai nemeta ba,  har se lokacin data dawo da Meenal ɗakinta. Sosai ta sake  razana da lamarin wata muguwar nadama na sake kamata, tana jin tsanar mugwayen halayenta da har yay sanadiyyar rabata da bugun numfashinta wato Abban, don ba ƙaramin mahaukacin SO take masa ba. Shi yasa ma take taka tsantsan da duk wani abinda ya shafe sa, amma se gashi yau saboda wata watsatstsiya can daban har yana mata barazana da nata auren, sosai ta sake jin tsanar Meenal ɗin a cikin rai da ruhinta. Babu jimawa se gata ta fito da akwatun ta taf da kaya ta fice tana jan majina, ido yayi fulin fulin tsabar kuka... Kai tsaye daga nan gidan su Meenal ɗin tama tsinke, taje ta sake yayyaɓa maganganunta san ranta, har da cewa yo dama ita yar malamai ba dole ubanta ya shiga tsakanin zaman lafiyarta da mijinta ba, daidai kuma Baffa ya kawo kansa lokacin da take faɗar kalaman nata, don haka ya ƙaraso yace da ita. Ta sani ita data koma gidan ɗan nata har abada, domin ta gama zaman aure dashi, tana nan zaune In sha ALLAHU se taga mijin Meenal ɗin zata aura ko ba jima ko ba daɗe, kuma taje duk abinda tayi kanta, se da Baffa ya mata tasss kana ya komar da Meenal ɗakinta da idanunta suka sake rinewa sosai,  Runtse idanunta a karo na biyu tai  tana ƙoƙarin kwatar numfashin ta dake barazana wa gangar jikinta.  danne dukkan abinda ke yunƙuro mata tayi,  tun da ga aurenta da Ahmad da irin baƙar tsanar da ummansa ke nuna mata haka kawai, har zuwa loƙacin da tafiyar su tasha banban da juna wacce wata shuɗaɗɗiyar Ƙaddara tazo ta ratsa tsakani, amma duk da haka baiwar ALLAH'r nan ba zata barta ta huta haka nan ba, se tayi ƙoƙarin mantawa da abu kana se wasu mutane su sake tado mata da danyen raunin da ya dauka hanyar warkewa.Lallai ta sake yarda  duk inda Kalmar KADDARA take, lallai  kalma ce dake motsa zuciyar ko wanne bawa domin kuwa tabbas wannan kalmar ta KADDARA kalmace me girma da faɗi wacce ta ƙunshi abubuwa masu yawan gaske a cikinta,  domin kuwa Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya  tamkar ƴan uwa juna. haka kuma  kowacce rayuwa tafe take da nata salon ƙaddarar ita ta amshi nata da hannu bibbiyu In sha ALLAHU, kamar yanda Baffan ta yasha ce mata Idan har bawa zeyi haƙuri wajen jure wannan tarin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin rayuwarsa  game da duk abinda ALLAH ya riga tsara masa, to kuwa lallai kayi hakuri da duk  abinda ALLAH ya tsara  maka domin kuwa shi ne mafi alkhayri agareka. Sake  Runtse rinannun idonta tayi sakamon kanta da taji ya wani kalan mugun sara mata da tsanin ciwo. Zaune takai bakin bed haryanzun hannuwanta riƙe da saman kanta dake jujjaya mata. Maganganun Umman Ahmad ɗin na son  haifar mata da wani damuwan. Wani kalan zazzafan numfashi ta fesar tana hana kanta bama damar hakan faruwa. Domin kuwa ita ɗin mutumce me tsananin ƙarfin zuciya. Ba kowanne abu take bama dama yay crossed nata mind ba, duk yadda maganganun suka so haukata kanta amma ƙin bama  hakan dama tayi. Lumshe idonta tayi ta taji hawayen da suka tara nemar zubo mata, amma ta sake shanye hakan har  tana jin yadda jinin jikinta ke wani irin harmutsawa tamkar ana aza wuta a jinin jikintan haka take ji, shigowar Shareefah ne ya sakata ɗago rinannun idanunta ta zuba mata, zuwa loƙacin kuma  jikinta har rawa yake a mugun wahalce ta nufi jikin Shareefah'n , dama tasan ita ɗince ta biyo ta lallashi bayanta. Rungumeta kawai Shareefah ɗin tayi  tana bata baki da haƙuri. Ganin duk yacce Shareefah'n tabi ta ruɗe ne ya sanya Meenal ɗin ɗan janye jikinta ana Shareefah 'n  tare da ƙaƙaro murmushin dole wai duk don ta kwantar mata da hankali. Saidai zubowar ruwan wahayen dake yankar zuciyarta da bala'i bala'in zafi da ƙunar da suka kusa  haifar mata attack take ne ya saka Shareefah fashewa da nata kukan itama, jin yadda jikin yayar nata ke jijjiga......

     

_The comments are dropping. 😔 ko dai baya muku daɗi ne? Naga ba comments ba reactions naku._


_Please don't be a silent reader. Comment, vote and share. Thank you 👏👏👏_


_Love you all my mutanena Amanana😘🫂_ 


_Put a smile on my face please. Vote, comment, and share My lovely friend's ana tare_


# Voice of the innocence

# Team AMEENEERH SHEHU USMAN where Are You???


 _Team Meenal wai kuna ina ne haka? meke  meke shirin faruwa daku haka?_


*BY AMMEY LAYLERH ✍️*


08104493215 



Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post