RAGAYAR DUTSE.
©️ Nana Haleema.
https://chat.whatsapp.com/IkYPgd4DkXD8mUAAeCIZax?mode=gi_t
Book 1
Page 002.
Mama tana shiga ɗakin ta kalli Labiba ta ce, "ke bana ciki da iskanci, ki bani abinda ki ka samo ko na saɓa miki."
Labiba a gajiye da maganar ta ce, "Mama na faɗa miki waya zan canja, don Allah ki bar maganar nan. In na samu ai ina kawowa, dan yau kaɗai ban kawo ba bazai zama matsala ba."
Mama ta harare ta ce, "wallahi sai kin kawo su, ko kina so, ko bakya so sai kin kawo kuɗin nan."
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "shikenan zan kawo."
Ta yi tsaki ta ce, "ya fi miki."
Mama ta fita ta shiga ɗakin da aka mallakawa Islaha. Ta same ta a tsaye tana ninke kayan da ta cire, ta bita da harara ta ce, "saura ke, kar ki ga na yi miki shiru ki ɗauka na yafe miki. Dole ki kawo na yau."
Islaha bata son magana, hakan ya saka ta ce,"to Mama" ta fada tana ajjiye abinda yake hannunta ta shiga banɗaki.
Hanan da Labiba da suka biyo bayan Mama, suna daga tsaye Hanan ta ce, "wai Mama kanmu ɗaya da yarinyar nan a cikin gidan nan?."
Mama ta ce, "ta ya zata zama kai ɗaya da ku? Itafa ƴar riƙo ce."
Labiba ta ce, "Amma itace wacce Hammanmu zai aura ko?."
Mama ta Harare ta ce, "da zata auri Saheer sai ta zama ƴar gidan nan?. Ke kin ga an yi aurensa da ita din ne, kin ga ya aure ta ɗin ne, gwana ta gwanaye?" Ta faɗa tana harararta ta fita.
A lokacin Islaha ta fito daga banɗaki ta saka hijjab ta kalli gabas ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta ɗauki wayar ta ta fita daga falon zuwa kitchen.
Aiki take yi tana tunani, dole ce ta saka take zaune a gidansu Hamma, in ba dole ba da yanzu ta tattara kayanta ta gudu. Amma baza ta iya hakan ba, saboda Hamma. In ta yi masa haka bata kyauta ba, kuma ta yi butulci. Bata so ta cigaba da zaman gidan, dan wata ran baza ta iya barwa Mama ba. In tana faɗa tana shiru, wata ran bazata iya yin shirun ba.
Hankalinta yana kan aikin da yake gabanta, ga tunanin da yake zuciyarta, tana ta gyara kayan miya tana wankewa.
Ƙhamshin turaren da ta ji a bayanta ya saka ta murmushin farin ciki, lokaci ɗaya zuciyarta ta mamaye da farin ciki, ta ji daɗi kamar ta buga tsalle.
Ta ɗan sauke numfashi, cikin muryarta mai daɗin saurare ta ce, "Hamma!."
A lokacin kyakykyawan sarauyi fari tass ya shigo kitchen ɗin yana murmushin. Bazai wuce shekaru talatin da uku ba, yana da tsayi sosai, dan da ya tsaya a kusa da ita sai ta zama ƴar ƙarama.
Fari ne sosai, kyakykawa mai kyaun fulani. Yana da hanci dogo, da kyakykyawan gashi a fuskarsa, duk da babu yawa kaɗan ne.
SAHEER kenan, Hamman Islaha, abokinta, masoyinta, abokin shawararta.
Ya jingina da cabinet, ya harɗe hannu a ƙirji yana kallonta ya ce, "ya aka yi ki ka san nazo?."
Ta juyo tana kallonsa ta ce, "tun kafin ka zo turarenka ya ri ga ka zuwa."
Murmushi ya sake yi yana kallon fuskar ta da take fitar da murmushi, ya ce, "Ba wani nan, kin ji shigowata ne kawai."
Ta ɗago kyakyawan idaunta ta kallesa ta ce, "A jikina na ji zuwan ka Hamma. Sannu da zuwa, daman yau zaka dawo baka faɗa min ba?."
"Na kira matar Hamma bata ɗauka ba, sai na ƙyaleta na ce kar na je na yi laifi."
Ta jingina da cabinet itama ta ce, "Hammana ba ya laifi a wajena."
Murmushi ya sake yi, cikin ƙauna da soyayyarta ya ce, "me ake dafa mana matar Hamma?" Ya faɗa yana karasowa kusa ita ya buɗe tuukunyar da ta ɗora.
Islaha ta ce, "couscous Mama ta ce a dafa. Kamar ta san zaka dawo."
Ya juyo ya kalle ta ya ce, "baki je aiki ba ne?."
"na je."
"Amma ki ke a tsaye a kitchen kina aiki? Ina Labiba ko Hanan, su baza su yi girkin ba sai ke?."
Ta ɗan sauke numfashi ta kalle sa, sai ta ɗauke kai ta yi murmushi bata ce komai ba.
Ta ce, "Mama ce ta saka ni."
Ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta cikin rashin jin daɗin abinda Mama take yi mata a gidan, ya cize baki yana girgiza kai tare da zuba mata ido.
Calmly ya ce, "ki yi haƙuri Islahaa! In sha Allah komai ya kusa ƙarewa, da mun yi aure na ɗauke ki shikenan babu mai takura miki. Da kaina zan dingayi mana girki, bazan bari ki takura kan ki ba."
Kunya ta kamata, ta saka dogayen hannayenta ta rufe fuska. Sautin murmushinsa ta ji yana kallon hannunta ya ce, "yaushe aka aka miki red henna? Yana yi miki kyau Islaha, Ina so na gansa a hannunki, ke kaɗai" ya faɗa yana riƙon hannunta yana kallon zanen red hennan da yake fatar hannunta.
"Dakyau Saheer! Ashe ka dawo, ni uwarka Ina ɗaki baki a sake Ina jiranka, ashe kai kana nan ka saka ƴar gold a gaba. Wato ta fi ni mahimmaci a wajan ka, wajanta ka fara zuwa kafin ka zo wajena ko!?."
Da sauri ya saki hannun Islaha, ya juyo yana kallon Mama.
A sanyaye ya ce, "Mama na shiga kina sallah." Ta harare sa, ta juya ta bar wajan.
Ajiyar zuciya ya yi ya kalli Islaha ya ce, "Zamu yi waya" ya faɗa murya a can ƙasa yana fita ya bi bayan Mama.
Islaha ta bi sa da kallo kafin ta cigaba da aikinta, rayuwar gidan sam bata yi mata daɗi, tana manage kawai dai bata da inda ya fi gidan. Shiyasa take jin daɗi in ta fita aiki, wani lokacin ko lokacin barinta aikin ne ya yi bata dawowa, zama take yi a can ta huta da bala'in Mama.
Dan gidan indai ba Baffa yana nan ba ya yi mata daɗi. Babu mai sonta a gidan, daga Baffa sai Saheer sai babbar gidan wacce ta yi aure. Baayan su babu wanda yake nuna mata so.
Ta san ita ba kowa ba ce a gidan, bata da kowa sai Hamma Saheer, shine uwa kuma shine uba a gare ta, Yayanta kuma mijin da zata aura.
Kallonsa kaɗai yana ƙara mata farin ciki da jin daɗi a zuciyarta, shi kaɗai ne mai tausayawa rayuwarta da son ganin ta je matakin nasara. Ya jure ƙalubale da yawa akanta, ya jure ɓatawa da kowa kawai dan ya riƙe ta a gidansu ba tare da sun haɗa jini ba.
Bata san shi ba, shima bai santa ba. Sanadin zuwa gidan marayu ziyara ya haɗa su, daga nan ta tsinci kanta a cikin gidansu da amincewarta.
Saboda shi take ɗagawa Mama ƙafa, tana sharewa in aka yi mata ba daidai ba. Amma ba dan shi ba, wata ran sai dai azo aga tana dambe da Hanan ko Labiba. Bata son raini da wulaƙanci ko kusa.
Saheer kuwa ɗaki ya shiga wajan Mama, ya same ta zata fito daga ɗakin, bata kula sa ba ta dawo falo ta zauna, shima ya zauna.
Ya ce, "Mama barka da dare." Bata kula sa ba ta yi masa banza.
Saheer ya ce, "ki yi haƙuri, na shiga kina sallah."
"Sai da ka gama gaisawa da ƴar gold sannan zaka zo inda nake ko Saheer?."
Ya sauke numfashi ya ce, "ba haka bane Mama, wallahi na shiga kina sallah."
"Ƙarya ka ke yi Saheer, ka nuna min son da ka ke yi mata ya fi wanda ka ke yi min. Ka ga in ka aure ta, wata ran ma daina kula ni zata ce ka yi."
Saheer cikin damuwa ya ce, "ki yi haƙuri Mama."
Ta ja tsaki cikin faɗa ta ce, "ni fa tun yarinyar nan bata kai haka ba ba sonta nake yi ba, saboda kai na amince take zaune a gidan nan tun ba a kai haka ba. Haka kawai babu dangi uba da uwa, ka kwaso mana yarinya ka kawo mana?."
"Mahaifinka da yake bakin ku ɗaya, ya goya maka baya harda shige maka gaba a aurenta. Wataƙila yarinyar nan mayya ce, wataƙila ba ta hanyar aure aka same ta ba. Tun farko laifina ne da na amince wallahi, gashi yarinyar tana neman ƙwace min kai, tun kafin ka aure ta!."
A sanyaye ya ce, "har abada babu wanda zai ƙwace miki ni, ke ki ka haife ni fa Mama, bani da wata sama dake."
"Ƙarya ka ke yi, ka fi sonta dani."
"Ina son Islaha Mama, amma bata kama ƙafar son da nake yi miki ba. Ki yi haƙuri" ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ɗauko rafar ɗari biyar ya ajjiye mata.
Sannan ya ce, "a yi haƙuri Mama." Dan ya san indai da kuɗi yanzu zata sauka.
Ganin ya ajjiye mata kuɗi masoyanta, sai ta basar ta girgiza kai, ta ja kuɗin kusa da ita ta ce, "shikenan ai. Ka je ka huta."
Ya miƙe ya fita, yana so ya ga yanayin da Islaha take ciki, dan yana da tabbacin ta ji kalaman Mama.
Islaha ba jimawa ta gama girkin, ta fito ta wuce ɗaki ta ɗauki wayarta a lokacin ta ga kiran chairman.
Kiransa ta yi, yana ɗauka ya ce, "Islaha gobe ki zo office da wuri, akwai aikin da nake so mu yi." Ta amsa da to ta kashe wayar ta ajjiye tana sauke numfashi.
Falon ta dawo ta tarar kowa ya zuba abinci yana ci, bata ce komai ba ta zuba nata ta zauna a gefe tana ci a nutse. Tana ganin irin kallon da Saheer yake yi mata, amma ta basar ta cigaba da cin abincin ta bata sake kallonsa ba. Bata so ya jawo mata hayaniya, dan Mama bata raina ƙaramin abu.
Wayar Mama aka kira, ta ɗauka tana cewa, "Kin faɗa mata gobe ne tafiyar?."
Daga can ɓangaren aka ce, "eh ta sani."
"Yauwa, ta san tsarin dai?."
"Ta sani."
"Yauwa, sannan ki faɗa mata, ni ban damu da alkhairin da fararen fata suke yi ba, kawai a haɗa min kuɗina. Dan wallahi bazan ɗaga ƙafa ba." Mama ta yanke wayar.
Hanan ta ce, "Mama nima a tura ni aikin nan mana, ana samun kuɗi muna zaune a gida?."
Mama ta kalle ta ta ce, "ke da ki ke neman mijin aure ina ke ina tafiya wata ƙasar?."
Ta juya ta kalli Islaha ta ce, "Dama dai Islaha ce sai ta tafi, ko babu komai ta tattara kuɗin aurenta."
Saheer ya tarin numfashin Mama ya ce, "Allah ya kiyaye, me Islahaa zata je yi aiki wata ƙasar Mama? Babu inda zata je, komai da ake yi na aure zan yi mata."
"Indai babar Islaha ba mayya ba ce, to tabbas jikar ƴan bori ce. Ko sun lashe maka kurwa, ko sun tsafe ka" Mama ta faɗa tana kallonsa.
Shiru ya yi bai amsa ba, dan baya so maganar ta yi ta tsayi, a Islaha a wajan.
Mama bata dakata ba, ta ce, "tun kafin ayi auren har an asirce min kai? Wato ga mai kuɗin banza, kai zaka yi komai ko?." Shiru ya yi bai ce komai ba, kafin ta sake magana ya miƙe ya fita daga falon.
Labiba ta ce, "Mama kin haɗu da sirika tun yanzu. Wannan in ta auri Hamm wallahi sai ta hanasa gaishe ki" ta faɗa tana nuna Islaha sa yatsanta.
Mama ta ce, "ita ɗin banza, yaushe aka ƙyanƙyashe ta da zata hana Saheer gaishe ni?."
"Ga zahiri nan Mama. Kina gani yana katse ki kina magana, yana cewa shi zai yi mata komai?. Wallahi nan gaba zata iya saka ki kuka."
"In tana da iyaye a duniya, ko su ƙarya suke yi. In kuma yar titi ce, na fi iyayen nata tantiranci.."
Mama ta kalli Islaha da take aikawa da Labiba harara ta ce, "Ke Labiban ki ke harara?."
Islaha ta haɗe rai, cikin ɓacin rai ta ce, "bana so su dinga shiga harkata, in kina yi min faɗa su daina saka min baki, ai basu ne gaba da Hamma ba, shine gaba dasu."
Labiba ta buɗe baki, bata yi mamaki ba, dan ta san Islaha zata aikata fiye da haka. Ta ce, "Tabɗi, to ke a su wa?."
Islaha ta buɗe idanunta ta ce, "ni a matar Hamma."
Hananan ta ce, "to daman waye zai kwashe ki, Ai sai dai Hamman, in ba shi ba sai wa?. Waye zai ɗauki ragowar titi?. Ki bari a ɗaura ɗin, kafin ki fara kiransa da mijinki."
"Wanda ya ɗauki ragowar titi, shima ragowar titin ne Hanan. Kuma tunda har ake tsayar dake aka ta ya, Islaha ta wuce ace waye zai kwashe ta."
"Kutmar uba! Me ki ke nufi? Hamma ne ɗan iska?."
Zata yi magana suka haɗa ido da Mama, sai ta fasa ta ɗauke kai daga kallon Mama.
Mama ta ce, "mara kunya, kina gidan ubansu kina cin arzuƙi kina yi musu rashin mutunci. Zo nan."
Islaha a hankali ta ƙarasa ta zauna, Mama ta bita da harara ta ce,"ban ga kin bani komai ba yau, ko dan kin ga ɗazu ban yi miki magana ba, shiyasa ki ka ɗauka yau kin ci banza?."
Islaha ta rufe ido ta buɗe, ta ce, "Mama aiki na ke zuwa."
"Dan aiki ki ka je ina ruwana? Aiki ke ya dama ba ni ba, abinda na sani ki bani kuɗin yau kawai."
Islaha ta ce, "Mama ni bana zuwa wajan ko wanne namiji balle ya bani kuɗi."
Mama ta wara hannayenta ta ce, "ni na hana ki? Ai ban hana ki samo min kuɗi ne. Dan haka ki fito da dubu hamsin yanzun nan."
Islaha ta wara ido ta ce, "Wallahi Mama bani da dubu hamsin, sai dai in an yi salary....."
kafin ta karasa Mama ta katse ta, ta ce, "Keda salary na ci ubanku, sa'ar wasanki ce ni Islaha!?."
Ta girgiza kai ta ce, "ki yi haƙuri, kuma kin san ina kawowa duk sati, yau ɗin na aiki ne ya yi min yawa, shiyasa ban fita."
Mama cikin tsawa ta ce, "Wannan ke ya dama, ki bani kuɗi kawai. Ƴaƴan gida suna fita su kawo, ke da ake ciyar sake a sadaka ki ce baki dasu ba. Baki isa ba Islaha."
Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Allah ya sani da tana da dubu hamsin da ta bawa Mama ta huta, amma bata da komai sai dubu biyar, ɗazu Safeera ta karɓi rancen dubu talatin ɗin da ta rage mata, da in ta bawa Maman ta san zata dan sauka kaɗan.
Bata son wannan ɗabi'ar, ace burin Mama kawai ka kawo mata kuɗi, bata damu da inda zaka samu ba. In ba dan dole ba ya za a yi ta zauna a gidan nan? Shi kansa Hamman in zaka biye ta Mama, ai ba mijin aure bane.
Mama ta katse ta ta ce, "bani."
Islaha ta ce, "wallahi Mama...." Mama ta kai mata mari, Islaha ta kauce.
Mama ta ce, "kin isa..? Wacece ke da zaki kwana a gidana ya baki kawo komai ba?."
Ta nuna su Labiba ta ce, "ƴaƴana ne na cikina, sun fita sun nemo kuma sun bani, balle ke bari karan kaɗa miya, kwashe, shara, ragowar gidan marayu?. Ki shiga hankalin ki Islaha, ki daina ganin ina wasa dake ki samu damar raina ni."
Islaha ta haɗe rai, duk da ta saba da kalaman Mama amma ko yaushe in ta faɗa bata jin daɗi.
Ta ce, "ki yi haƙuri."
"Tashi ki bar min falo, ki fita harabar gidan nan ki zauna sai na neme ki."
Islaha ta karyar da kai ta ce, "Mama ana sanyi sosai, don Allah ki bari gobe zan nemo na kawo miki, duk inda zan samu kuɗi zan samu na kawo miki."
Labiba ta ce, "Raini, Mama tana faɗa kina faɗa?. Lallai Mama kina da aiki, duk ranar da Hamma ya auri wannan kin mutu."
A fusace Islaha ta ce, "Labiba bana son shirme."
Labiba ta ce, "ya za ki yi dani?."
Mama ta ce, "Fita ki bani waje."
Islaha zata sake magana Mama ta ce, "Na ce ki fita!."
Abinda Islaha ta tsana a duniya shine tsawa, ta ta fita da ɗan sauri tana sauke numfashi.
Mama ta bita da harara ta ce, "shashasha Mara hankali, ni za ki mayar ƙaramar yarinya? Wanne kalar iskanci ne bakya aikatawa? Dan kin raina ni, naira dubu hamsin ce zata gagare ki?."
Hanan ta ce, "Wallahi Mama kuɗi yarinyar nan take samu, ba ki ga manyan mutanen da take hulɗa dasu ba. Hotels kuwa, babu inda bata zuwa."
Mama ta ce, "na sani Hanan, duk wani iskanci da take aikatawa na sani wallahi."
"A haka kuma zaki bari ta auri Hamma Saheer? Ta gama watsar da kanta a titi, ta gama raba jikinta ki bari ta aure sa?."
Mama ta kalle ta tana wani shegen murmushi, ta ce, "mu zuba" ta faɗa tana tashi ta shiga daki.
*******
Yanayin yadda suke zaune a babban falon zai tabbatar maka da ba ƙaramar tattaunawa ake yi ba, kowa yana zaune a ƙasan carpet, duk sun sunkuyar da kansu suna sauraren umarni daga hajiya Daada.
Ita kaɗai ce a zaune a kan kujera, ƙafarta tana miƙe tana ƙaɗawa, hannunta riƙe da jarbi tana ja cikin isa da ƙasaita. Shiru falon ya yi, babu sautin komai sai sautin karatun alkur'ani da yake tashi daga tv.
Kowa a cikin falon farin ciki yake da taron, saɓanin Mamy da ta san ƙarshen alawa ƙasa, ƙarshen taron akanta da yaranta zai ƙare, tunda ba ƙaunarta suke yi ba. Shiyasa kanta yake sunkuye, bata ɗago ba balle ta ga abinda zai ɓata mata rai.
Daada ta bisu da kallo ta ce, "AbdulAziz kana jin abinda nake faɗa ko?."
Abba ya ce, "ina jinki Daada."
"Ka yi shiru baka ce komai ba."
Ya gyara zama ya ce, "ina jira ki gama ne."
Daada ta ce, "na gama, ina jinka."
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Daada ba ƙin dawowarsa nake yi ba, abinda nake dubawa a can yake aiki, a can kasuwancinsa ya fi ƙarfi, ban da yanzu da ya kawo asibiti, kasuwar zamani, da sauran abubuwa ƙasar nan kin san komai nasa yana can. Komai da komai nasa yana can, hatta takardar haihuwa a can take. Dawowarsa nigeria...."
Ta katse sa ta ce, "AbdulAziz ba wannan maganar na kira ka ka yi min, ina bada umarnin dawowar Muhammad cikin gidan nan!. Umarni ne ba shawara ba, komai yake yi ya tattaro ya dawo cikin gida."
"Ban damu da a can aka haifesa ba, ban damu da rabinsa ba ɗan ƙasar nan bane, abinda na sani ɗan cikin gidan nan ne ya samar da cikinsa. In daga lahira aka auro uwarsa ban damu ba, dawowarsa gidan nan kawai nake da buƙata. Kuma dole ayi ko sa bakwa so."
Abba ya ce, "Allah ya huci zuciyarki, ban faɗa dan ɓata ranki ba."
Daada ta ce, "in ma ka faɗa ɗin ai na soke yanzu. Ba wani ne ya ce ka auro ƴar wata ƙasar ba, kai ka ga zaka iya har ka aikata. Ba tare da shawarata ba ka aure ta, ban san anyi auren ba sai labari na ji, babu albarkata a cikin aurenku."
"Sannan da yake ita ta fi kowa, baza ta zauna a cikin mu ba, sai aka sauke ta a england, saboda baza ta iya zama a nigeria ba. Yanzu kuma ɗan na mu ma baza a bamu shi ba? Shima a can burtaniyan zai cigaba da rayuwarsa?. Har yanzu a cikin dangi akwai wanda bai san Rehaan ba, ko ni bazan iya banbance kamaninsa ba, tunda rabona dashi yau shekara huɗu kenan."
"Dadda ya zo lokacin ƙaramar sallah." Mamy ta faɗa jin ana neman ɗora masa shekara huɗu..
Da sauri Abba ya kalle ta, amma kafin su haɗa ido Daada ta ce, "ina magana kina katse ni? Wacece ke ina magana kina kawo min ta ki?."
Ta kalli Abba ta ce, "ka ga rashin tarbiyyar irin na yaran ƙasashen waje ko? Baka koya mata a yadda ake magana da manya ba ne? Baka ko ya mata cewa ko kai in ina magana baka isa ka dakatar dani ba?."
A sanyaye ta ce, "Allah ya wuci zuciyarki."
Daada ta ce, "da yazo lokacin bikin sallah kwana biyu ya yi kacal ya koma, Tunda ya gaishe ni sau ɗaya bai sake waiwaiyona ba, saboda an riga an jefa masa ƙin dangin babaansa a zuciyarsa. Ke ga mai ɗa, ina magana kina katse ni saboda ke ki ka haifesa."
"Wallahi baza ta saɓu ba, dole ya dawo gida, kuma in ya dawo, ba a isa nan da wasu kwanaki ace zai koma aiki ba. Ya dawo aiki a Nigeria, kar na sake ji ance zai koma burtaniya da zama."
Abba ya ce, "in sha Allah, zai dawo Daada."
Daada ta ce, "ya yi kyau. Kowa ya watse, AbdulAziz ka zauna."
Cikin lokaci kaɗan kowa ya tashi daga falon cikin farin ciki, kaf gidan babu mai ƙaunar zaman Rehaan a wata ƙasa, dan babu mai ƙaunar cigaban rayuwarsa kowa so yake ya ga ya ɗurkushe. A ganinsu dawowarsa Nigeria babbar naƙasu ce a gare sa.
Aka bar Abba kaɗai a zaune kusa da ita. Daada ta ce, "AbdulAziz, bana so na sake ji ance zai koma wata ƙasar, ya zauna ya cigaba da rayuwa kamar yadda muke yi."
Ya ɗaga kai cikin gamsuwa ya ce, "in sha Allah za a yi."
Ta ɗaga kai ta ce, "Ya batun auren Juwairiyya da Jaafar?."
Abba ya ɗan yi jimm dan ya san bata son batun auren Jaafar, amma sai ya ce, "yana nan yana tafiya yadda ta kamata."
"Da zarar Rehaan ya dawo, a haɗa auren harda shi."
Da sauri ya kalle ta ya ce, "Daada ba ja da maganarki nake yi ba, amma ta ya za a haɗa da Rehaan bayan, ko budurwa ma bashi da ita?."
Daada cikin baƙar magana ta ce, "Ai na ɗauka shi ɗin ma baturiya zai ɗauko ko balarabiya."
Ya yi shiru bai ce komai ba, dan ya san shi take faɗawa magana. Tunda ya auri Mamy kullum sai an yi haka, an kwashe shekaru da auren amma Daada taƙi saduda.
Daada ta ce, "ina so ka sani, babu yaren da Rehaan zai aura in ba bafulatana ba, wallahi ko ya ɗauko wani yaren ba fulani ba sai an soke auren!. Yadda ka auri baindiya ta lalata mana zuri'a, bazan bari a sake maimaitawa ba."
Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "in Allah ya amince."
"Zaka iya tafiya."
"Sai anjima" ya faɗa yana miƙewa ya fita.
Daada ta yi tsaki ta ce, "kawai ka ɗauko mana dangin masu tsafi cikin gida, ƴan india me suka iya in ba tsafi ba? Gabaɗaya ka gurɓata mana ahlinmu" ta faɗa tana kallon gefenta.
Daada ta ce, "ke Indo?."
Wacce aka kira da Indo ta zo ta ce, "gani Daada."
"Ki je ki kira min Saddiƙa."
"To" ta faɗa tana tashi ta fita daga falon.
_Book 1 free ne, Book 2&3 paid ne akan naira 1k kacal. Pay into Sadiya Nuhu Mukaddas 5903999117 Moniepoint MFB. A tura shaidar biya a wannan number 09030398006 ko 0701 809 8175._
Nana Haleema✍🏻❤️🔥
