*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
Wattapad@NanaHaleema
ArewaPen@nanahaleema11
Tiktok@Nanahaleemawriter
Ig@nana_haleema_writer.
_Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, godiya ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai, da ya ba mu aron rai da lafiyar da mu ka kawo wannan lokacin da rai da lafiya. Ina roƙon Allah, yadda ya bani ikon fara rubutu littafin nan cikin lafiya da aminci, Allah ya sa na gama lafiya. Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani al'umma baki ɗaya, Allah kar ya bani ikon rubutu ɓarna, ko abinda ya saɓa addininmu amin._
_Jinjina da godiya ga mutane masu kirki da karamci, waɗanda suka taimaka suka bani goyan baya har muka kawo wannan lokaci. Na gode da goyan bayanku, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumuncin mu har aljanna, amin._
_Wannan labari mai suna RAGAYAR DUTSE ƙirƙirarre ne, bai faru a gaske ba. Ban rubuta littafin dan cin zarafin wani ko wata, hukuma ko gwamnati, ma'aikata ko mutanen gari ba. Na rubuta shi saboda jan hankali da faɗakarwa, kamar yadda aka saba a littattafan hausa ko finafinai. In ya yi kama da labarin ki, ko labarin ka, a yi haƙuri rashin sani ne ya kawo hakan._
*Note: Akwai wani ɓangare da ake ɗan taɓa zagi a labarin, a yi haƙuri labarin ne ya zo da haka.*
_Ban yarda a canja min labari zuwa wata siga daban ba, ban amince a juya min labari zuwa wata fuska ba ba tare da izini ba!._
https://chat.whatsapp.com/IkYPgd4DkXD8mUAAeCIZax?mode=gi_t
*Book 1*
*Page 001.*
*MAFARI.*
"Bawan Allah ba mu san ka ba, ba mu taɓa ganinka ba, amma mun ji a ran mu zan iya damƙa a amanar yarinyar baiwar Allah nan a hannunka. Barinta a wajen babarta barazana ne ga rayuwarta, barinta a gare ta tamkar an ɗauketa an cilla ta a wuta ne."
"Bawan Allah, ga amanar ƴarta nan, ka riƙe ta hannu biyu, ka bata tarbiyya irin wacce ka ke da ita, ka bata ilimi daidai ƙarfinka."
"Da amincewar babarta muka baka ita, in muka barta a hannunta rayuwarta zata iya lalacewa. Ka riƙe ta hannu biyu, ko da zata waiwayo neman amanarta, ka tabbatar ka san inda zaka ɗauko ta ka bata. Tana matuƙar son ƴarta, dole ce ta saka zamu rabata da ita."
Ta ɗan kalli matar da take zaune bata ce komai ba, sai hawaye da yake sakkowa daga idanunta. Sun san ba a son ranta za a rabata da ƴar ta ba, amma dole ce ta kawo hakan.
Matar ta juyo ta kalli wanda yake tsaye ta ce, "Ƴarta ƴar halak ce ba shegiya ba, ko da wata ran za a yi mata gori ka share mata hawaye, ka tabbatarwa da duniya tana da uba. Ka je da ita, Allah ya baka ikon riƙe amanar da aka baka."
Ya bi matar da kallo kamar yadda take kallonsa tana hawaye, ya juya zai fita jiki a sanyaye.
Kafin ya ƙarasa fita ya ji dashashshiyar muryarta, cikin harshen fulani ta ce,
"Ka kula min da ita, zan zo na karɓe ta duk daren daɗewa!."
Duk suka juyo suna kallon ta cikin mamaki maganar da aka ji ta yi, a daidai lokacin idanunta ya rufe ruf ta zube a wajen babu numfashi.
•••••••
*SHAGARI PHASE 2,*
*YOLA, ADAMAWA STATE NIGERIA.*
"To ke yanzu har sai an ce miki ki kashe aurenki sannan zaki kashe? Har sai an faɗa miki ki kashe aurenki ki zo a buga miki visa ki ɗaga ƙasashen duniya sannan za ki kashe?."
"Hmmm! Ban san me yake damun matan arewa ba wallahi, kuna da dama da lokacin da za ku mori ƙuruciyarku, amma sai ku bari ɗa namiji yana walagigi da rayuwarku. Akwai namijin da ya isa ya yi min haka ne, ko akwai wanda ya isa ya yi min iyaka da burina?. Wallahi babu shi."
Wacce take zaune a gefenta, ta ɗan taɓe baki cike da damuwa ta ce, "Woman leader baza ki fahimta ba ne babu wanda ya kai ni son zuwa Saudia aikatau, ina so na je, amma bazai bari ba."
Wacce aka kira da Woman leader ta kalle ta sheƙeƙe ta ce, "shiyasa na ce har yanzu ana wannan ƙarnin, har yanzu ana cikin ƙarnin da sai da izinin namiji zaka yi abinda zai amfane ka?."
Sai kuma ta taɓe baki ta ce, "ki ta zama a gida, kar ki fito ki nemi kuɗi. Aikin saudia duk wata naira dubu ɗari biyar ne, ban da kyautttuka irin na larabawa da ake samu. Sannan ga ki a gari mai tsarki, ko yaushe ki ke son shiga harami faɗawa za ki yi baki da wata damuwa. Allah na tuba ko barbaɗe ne ba sai na yiwa mijina na tafi ba, me ye ƙarshen abun ne, saki ne fa. To a sake ni ɗin, sai me?."
Maimuna da zaune ta ce, "wayyo Allah! Garin daɗi ba kusa ba, in ji ungulu da ta leƙa masai. Woman leader da gaske naira dubu ɗari biyar duk wata?."
Woman leader ta ɗan harareta ta ce, "in ba haka bane kin san bazan faɗa miki ba, tunda ke kin zauna sai yadda namiji ya yi dake sai ki yi ai. Ga wata da na santa a bayan bayan ki, wani satin zata hau jirgi. Amma ku waɗanda na sani, duk matsorata ne, rakiyar mata ku ka yo duniya."
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "wannan ya zama dole ayi dani wallahi, duk hanyar da zan bi wajan ganin na tafi aikin nan wallahi sai na yi."
Woman leader ta bata hannu suka tafa ta ce, "daga lokacin za ki nunawa duniya mata suna da ƴanci, kuma dan ka ajjiye ƴan mata da sunan ƴaƴa ba hakan yana nufin ka dakusar da rayuwar ka bane."
"Dakyau Maimuna, ki san yadda za ki yi ki zo a tafi dake, in ba haka ba kina ji kina gani zaki cigaba da tsufa a gida. Kina aurar da Safeera kin tashi aiki, dan jikoki za ki fara raino."
Maimuna ta ce, "Ko kuɗin auren Safeera na je na haɗo ban rage ba.?"
"Muguwar ragewa ma, ke aikin nan fa alkhairi ne. Ke kin taɓa ganin wacce ta je saudia ta baro aikin ta dawo?."
"Ban taɓa ba."
"Tabbacin akwai alkhairi ɗin kenan. Ki zo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe, ki ɗaga kawai. Sai me dan ya sake ki, a kan ki aka fara?."
"In sha Allah, dani za a tafi."
"Assalamu alaikum!."
Wata kyakykawar yarinya ta yi sallama cikin siririyar murya tana shigowa falon, wacce bazata wuce shekaru ashirin da biyar ba.
Kyakykyawa ce sosai, doguwa mara jiki, baza ka saka ta a layin masu ƙiba ba ko kaɗan, kuma bata shiga layin siraran matan nan ba. Tana da brown skin mai kyau da ɗaukar hankali, fatar har ƙyalle take yi kamar wacce take shafa cakuleti.
Tana da manyan idanu zagayayyu masu haske, wanda suke haska brown skin ɗinta. Tana da dogon hanci mai tsaho, ga ɗan ƙaramin bakinta mai saurin ɗaukar hankalin mutane.
Tana da cikakkiyar gashin gira, kallo ɗaya zaka yiwa girarta kasan Allah ya yi ajiyar gashi. Kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana da kyau, in ka kalle ta sai ka kuma kallo, saboda baiwar da Allah ya yi mata.
ISLAHA kenan, matashiya ƴar jarida mai aiki a gidan tv da radio, mai ji da ɗaukaka da farin jini. Fuskarta ta samu karɓuwa a wajen jama'a, saboda kyau da murmushi, ga kirki da iya magana a gaban camera. Ga rashin tsoro da sa a, ga iya magana da wayo.
Islaha bata jin magana, bata da kunya, tana da tsiwa sosai. Tana da ɗaukar dala ba gammo, abinda ya fi ƙarfinta zata ce zata iya dashi.
Tana da gaggawa, bata tsayawa ta nutsu a kan abu, sau tari tana yanke hukunci da zarar abu ya burge ta, bata tsayawa ta yi nazari mai kyau kafin hukunci. Islaha bata da tsoro, kuma bata ɗaukar rainin wayo. Sai dai tana da kirki, fara'a da girmama na gaba da ita, in ya girmama kansa.
Duk suka amsa suna kallon ta, kafin woman leader ta ɗauke kai ta cigaba da abinda yake gabanta bata ce komai ba.
Islaha dawowar daga wajan aiki kenan, ganin Ummansu Safeera a zaune kusa da Mama sai ta yi murmushin da ya bayyanar da kyauwanta, ta ɗan taka kaɗan ta ce, "Umma ashe kina nan, yanzu mu ka rabu da Safeera, bata san bakya gida ba da tabiyo ni" ta faɗa tana kallon ta.
Wacce ta kira da Umma ta ɗan murmushi, ba yabo babu fallasa ta ce, "Ina nan, ya aikin?."
"Alhamudu lillah."
Sanin ba wani shiri suke yi da Umma ba sai bata sake cewa komai ba. Kar ta faɗi abimda zata kasa jurewa ta mayar mata.
Ta kalli Mama ta ce, "barka da hutawa."
Mama ta kalle ta kallon sama da ƙasa har tana taɓe baki, ta ce, "maza ki je ki ɗora min abinci."
Islaha ta sauke numfashin gajiya, a sanyaye ta ce, "To" ta faɗa tana wucewa dan har ga Allah a gajiye take sosai, amma bata isa ta faɗawa Mama haka ba.
Tana barin wajan Maimuna ta kalle ta ta ce, "wani lokacin kamar tana da hankali, amma ni haka kawai bata yi min ba. Amma dai kin yi sa'ar sirika."
Mama ta ce, "bata yi miki ba, ko bata yi min ba? Ina ƙyaleta ne kawai dan wani lokacin ina son aurenta da SAHEER."
"Kin ganni nan, bana son sirika ta shigo ta juya min ɗa, na fi so na juyata kamar yadda zan juya ɗana. Bazan lamunci ina uwarsa da ta haife sa, kuma ace wata mace ce take da iko dashi ba, bazan yarda da sai ya fara kai mata kafin ya kawo min ba."
"Shiyasa na amince ya auri Islaha, dan ita ta sanni na santa, ta san bana son raini, kuma duk abinda na shinfiɗa shi zata hau kai ta zauna. In ba dan haka ba ya za a yi na amince ya aure ta?."
Ta yi dariya ta ce, "Amma ke kanki kin san Islaha bata da kunya, kema ba raga miki take yi ba wani lokacin."
"Tunda tana son ɗana dole ta kwantar da kai. Ba fa son auren nake yi ba, ko yanzu zan iya soke shi wallahi."
"Ke dai Allah ya rabaki da sharrin sirikan zamani, ita Islahan ai ba a goshinta aka rubuta zata yi miki abinda ki ke sba. Kin san halinta sarai, bata jin magana, buɗaɗɗen ido ne da ita. Tunda a gidan marayu ta girma."
"Rashin kunya ai bata isa ta yi min, tunda tana matuƙar son Saheer dole ta bi duk abinda nake so. Ta isa ta ƙi yin abinda nake, a gidan nan ta ke zaune ina so ki tuna, babu dangin uwa ko na uba a tsakaninmu, kawai shegen taurin kan Saheer ne ya saka ya kawo min ita na karɓa. Kuma ko da ya fito da maganar aurenta zai yi saboda haka na bashi dama, bata isa ta aikata abinda bai yi daidai da ra'ayina ƙyale ta ba."
"Ya kamata ki dage, dan irinsu in suka kama yaro basa saki da wuri. Islaha tana da buɗaɗɗen ido, babu inda aikin jaridar nan ba ya kaita, har kwana tana yi a waje. Akwai abinda za a nuna mata wanda bata sani ba?. Ke bakya ganin yadda ta kanainaye Saheer ɗin, yake sonta kamar ransa."
"Kamar ya haɗɗiyeta kuwa, ni wani lokacin son har tsoro yake bani wallahi, yarinya kamar ta lashe masa kurwa? Ko ni ba ya nunawa son da yake nuna mata."
"Ahaf, ba na faɗa miki ba. Sai kin miƙe tsaye, in ba haka ba wallahi kina ji kina gani zata mallake miki ɗanki. Islaha, ke dai ki kalli yarinyar nan kawai, ta wuce tunaninki."
"Duk shegantakar da take ji dashi na fita, duk wani iskanci da yawon duniya da take taƙama dashi wallahi na fi ta."
"Ke ba dan kura ta yi lafiya ba, da na aikata abinda har ta koma ga Allah bata isa ta yi sa ba. Dalilina ɗaya, saboda na mallake Saheer ya saka na ƙyale mata shi, na san halinta, babu wani motsi da zata yi ban fahimta ba. Kin ga bata isa ta kawo min kissa akan mallake min ɗa ba, na dame halayenta na shanye."
"Tana ji tana gani zan juya ɗaya, sai dai ta zama ƴar kallo. Kuma daman ya fi ƙarfinta, yaro fari kar dashi jiki duk madara, ita kuwa fa?. Waye ya san me iyayenta suka aikata aka haifo ta, aka kasa rainonta aka cillata gidan marayu? Ke daga ganinta kin san ba dukkanta ce fulani ba, akwai sirki."
"Ai haske kawai Saheer zai nuna mata, amma wallahi ta fi sa kyau. Ki duba zagayyun idanun da Allah ya yi mata mana, wallahi kaf gidan nan babu mai kyaun Islaha. Shiyasa nake faɗa miki ta waye, ta san komai, manyan mutane sun daina yayin mata masu haske, irinsu ake kai musu. Sun ce sun fi laushin jiki."
Mama ta taɓe baki ta ce, "shegiya, sai taurin kai da rashin kunyar tsiya. Amma zan yi maganinta wallahi."
Dariya Umma ta yi suka cigaba da tattaunawa akan fita ƙasar waje aikatau.
Sallama aka sake yi aka shigo, Mama ta amsa tana kallon kyawawan ƴan matan ƴaƴanta guda biyu, ko wacce ta ci kwalliya ta yi adon gashi, sai tashin ƙhamshi suke yi.
Mama ta bisu da kallo har suka zauna sannan ta ce, "haka mu ka yi da ku, tun safe baza ku dawo ba, sai yanzu magrib ta kusa?."
Ɗaya daga ciki, fara mara jiki, mai kyaun fulani, wacce take amsa sunan Hanan ta ce, "Mama aiki ne ya tare ni, sai da na ciko jakata sannan na dawo" ta faɗa tana buɗe jakarta, ta ɗauko rafar ɗari biyar guda uku ta ajjiyewa Mama.
Mama ta harari kuɗin ta ce, "duk wannan jimawar a naira dubu ɗari da hamsin kawai?."
Hanan ta ce, "Sai a gode Allah."
Mama ta kalli ɗayar, wacce take baƙa mai kyau ta ce, "sai wani cika ki ke kina batsewa, ke kuma nawa ki ka ƙwamuso?."
Labiba ta ɗan kawar da kai ta ce, "dubu ɗari biyu ce, kuma na bayar zan canja waya. Ni na gaji Mama, bacci nake ji" ta faɗa tana niyar miƙewa.
"Zauna dan ubanki, ki kashe kuɗin kuma ki ce min kin gaji, aikin uban me ki ka yi da ki ka gaji?. Me saurayin na ki ya yi miki?. Ban ja mu ku kunne akan ban da iskanci ba, me ya aikata miki ki ka gaji?."
Labiba ta ce, "Mama ni babu abinda na yi, kawai na gaji ne" ta faɗa tana tashi ta bar wajan Hanan ta bi bayanta.
Umma da take kallon Mama da mamaki, tana girgiza kai ta ce, "kina tura su wajan samarinsu samo kuɗi, amma sai ki ce kar su yi iskanci. To in ba iskanci suke yi ba me zasu yi maza su basu kuɗi irin wannan?."
Ta kalli Umma, sai ta haɗe rai ta ce, "Uhum Maimuna, bana so a saka min ido a lamarin gidana dana ƴaƴana, dan na tura su samo kuɗi ai ba ta hanyar iskanci da maza ake samun kuɗi ba, akwai hanyoyi da yawa da zasu ciko jaka ba sai sun bada kansu ba."
"Kina da abin mamaki, to me suke yi suke samun kuɗin, wa'azi suke yiwa mazan?."
"Maimuna ya isa haka, in ma karatu suke koya musu babu ruwanki. Na tabbatar ƴaƴana basa neman maza, suna samun kuɗi da dabara irin ta mata. Sai anjima."
Maimuna ta miƙe ta ce, "Allah ya kyauta, ke kika haife su ai" ta faɗa tana fita daga falon.
Mama ta bita da harara ta ce, "munafukan banza, ko yaushe aka ce musu sai ta hanyar ba da kai mace zata samo kuɗi a wajan maza oho" ta faɗa tana kwashe kuɗin da Hanan ta ajjiye ta shiga ɗakinsu. Dan tana ta je ta samu Islaha, bata isa ta ce bata samo kuɗi ba. Ko a ina ne sai ta nemo ta bata, ba a banza take ciyar da ita ba.
•••••••••
*MAFI’AS QUATERS,*
*YOLA, ADAMAWA STATE.*
Alhaji AbdulAziz Zubair Yola, babban mai kuɗi ne a faɗin garin Adamawa, kuma mahaifin matashin mai kuɗin da ake ji dashi a kaf faɗin africa. Mutum ne mai kirki, girmama mutane, biyayya da sanin ya kamata. Yana ƙaunar iyalansa, abinda suke so shima shi yake so.
Alhaji AbdulAziz yana mata guda huɗu, Hajiya Saddiƙa itace uwa gida sarautar mata, AbdulAziz number two kenan, domin kuwa in AbdulAziz ba ya gari itace take zama tamkar itace shi. Tana da iko a gidan, kowa a ƙasanta yake, hatta mai gidan a hannunta yake. Yadda ta dama haka ake sha, babu mai ja da ikonta, dan ko ka ja kaine zaka sha wahala.
Duk manyan ƴaƴan gidan yaranta ne, mazan huɗu mata biyu. Duk wani abu na harkar gida ƴaƴanta ne a kan gaba, dan su ne manya dasu ake damawa.
Matarsa ta biyu Hajiya Salamatu, ɗanta guda ɗaya namiji, kuma ya kasance mara lafiya kamar mai taɓin ƙwaƙwalwa, duk ragowar da suka biyo baya mata ne, su ne manyan ƴaƴanta.
Hajiya Nadira itace matarsa ta uku, haifaffiyar ƙasar india, cikakkiyar likita a ɓangaren mata, karatu ya kai sa ƙasar india, suka haɗu ya aure ta.
Mace ce mai sanyin hali da son jawo mutane a jiki. Sai dai ta zama kamar bare a cikinsu, babu wanda yake shiga sabgarta balle a je inda take, sun ajiiyeta a gefe basa mu'amala da ita, saboda ta kasance ƴar wata ƙasar ba jinin fulani ba. Ƴaƴan Nadira uku, namiji ɗaya mata biyu.
Hajiya Amina itace amarya, mai ƙarancin shekaru da yarinta, dukkansu sun haifeta. Ƴaƴanta biyu duka mata.
"Mama!."
Ta ɗago ta kalli wanda ya kira ta da ta ce, "meye?."
Ya zauna a kusa da ita ya ce, "Mama abin nan yana ɗaure min kai, kin san me ya faru?."
Ta ajjiye wayar hannunta ta ce, "me ya faru?."
Ya sauke numfashi ya ce, "REHAAN!."
Ta bisa da harara tana jan tsaki, in akwai sunan wanda ta tsana a duniya to Rehaan ne, bata son jin sunansa a kusa da kunnenta, ba ta so ambace sa in tana waje. In an ambacin sunansa ta ji daɗi, to tabbas an faɗi faɗuwarsa, ko an faɗi wani mai muni. Amma indai aka faɗi alkhairinsa, yanzu zata ji ranta ya ɓaci.
Ta ce, "me ya samu Rehaan ɗin?."
"Mama yaron nan yana neman wuce tunanin mu, yana so ya zarce inda mu ke tunanin yake."
Cikin fusata ta ce, "dallah ka faɗa min, meye ya faru?."
Ya sauke numfashi ya ce, "Sunansa ya dawo na biyu a jerin sunayen masu kuɗin africa masu ƙarancin shekaru."
Idanu ta buɗe tana kallonsa ta ce, "Sameer kar ka yi min ƙarya."
"Ba ƙarya nake yi miki ba, kalli ki gani" ya faɗa yana nuna mata wayarsa.
Bata musa ba ta karɓa, ta ga yadda aka yi analysis ga sunansa nan a layi na biyu, saura kaɗan ya tarar da na farko.
Baƙin ciki ya mamaye mata zuciya, ta miƙa masa wayar, ta miƙe tana zaga falon cike da tunanin mafita.
Ta rasa yadda zata yi da Rehaan, kuɗin da ya kamata ace ƴaƴanta ne suka yi shine yake mallakarsu. Hakan yana taɓa zuciyarta, yana sakawa mata baƙin ciki da hassada.
Mama ta ce, "ya aka yi haka yake faruwa, Ya aka yi abubuwa suke jagule mana ne Sameer?. Rehaan fa, kai kanka ka girmesa da shekara ɗaya. Ya aka yi yake samun ɗaukaka, bayan ku ne manya a cikin gidan nan?."
Sameer ya ce, "wallahi zamansa a england babbar illa ce a gare mu, ni ban yarda ba dukiyar Abba ce a hannunsa ba. Ta ya yaro ƙarami ace ya mallaki abinda mahaifinsa bashi dashi, Hamma Zayyad da yake babba bashi dasu, mu ma da muka biyo baya bamu dashi. Kina jin wannan kin san haɗawa aka yi, gabaɗaya dukiyar Abba tana hannunsa, mu muna nan an haɗa mu da ƙananun abubuwa na banza. Babu damar mu yi magana sai ace ai shi a nan ya girma ba, shi a a can aka haifesa, a can yake kasuwancinsa da sauran shirme. Mama in muka zuba ido, kaf dukiyar Abba da take can zata zama haram a gare mu."
Mama ta girgiza kai ta ce, "ya aka yi hakan yake faruwa, ya aka yi abubuwa suke lalace min ne?. Meyasa na kasa ɗaukar mataki akan Rehaan, meyasa yake shigar min hancina na kasa fato shi?."
Sameer ya ce, "dole a san abinda za a yi, bazai yu kina babba a gidan nan, muna manya a gidan nan, ace komai yana hannun Rehaan ba, dole ki san yadda zaki yi ya dawo nigeria, in ba haka ba wallahi muna ji muna gani komai zai fi ƙarfin mu."
"Ƙarya ne wallahi, yadda ku ka kasance manya a gidan nan babu wanda zai samu ɗaukaka sama da ta ku, dole a dakusar da ɗaukakar Rehaan, dole Rehaan ya dawo ƙasar nan.."
"Ɗaukaka ta nawa kuma Mama? Sunan Rehaan da labarin Ray ina ne bai shiga ba a faɗin ƙasar nan?. Sai dai a kiyaye gaba, amma wannan ya riga ya faru. Kai tsaye ki samu Daada da wannan maganr, ki same ta ita kaɗai ce zata zama silar dawowarsa ƙasar nan har abada."
Ta girgiza kai cike da gamsuwa ta ce, "yanzu nan zan je na same ta, indai a kan ganin bayan ɗaukakar Rehaan ne babu abinda bazan yi ba Sameer, zan iya sadaukar da duk abinda na mallaka dan ganin Rehaan ya dawo ƙasa, ku kun hau sama."
Sameer ta miƙe ya fita cikin gamsuwa sa kalamanta. A ganinsa ta ya ya suna manya a gidan, ƙaninsu wanda ya zama shine namiji ƙarami a kaf gidan, ya zo ya fi su ɗaukaka.
Mama kuma ta dafe kai cikin rashin mafita, a bayyane ta ce, "Rehaan! Rehaan! Rehaan! Ka shiga rayuwata, ka hanani sakewa Rehaan, ka hanani cika burina....."
Ta girgiza kai ta ce, "Baka isa ba wallahi, baka isa ɗaukakarka ta disashe ta ƴaƴana ba, yadda na kasance gaba da kowa a matan gidan nan, dole ƴaƴana su kasance gaba da kowa a yaran gidan nan. Babu wanda ya isa ya sha gabansu, su ɗin su za a kalla aje ace su bayar, ba kai ba. Tun kana yaro ka ke bani wahala, amma a yanzu bazan barka ba Rehaan, bazan taɓa barin ka ba."
A fusace ta ja hiijabi ta fito daga part ɗinta zuwa part ɗin Daada.
Daada mahaifiyar Abba ce, tsohuwa mai rigima, duk abinda ta ce a gidan babu wanda yake tsallakewa, duk dokar da ta shinfiɗa sai an hau kai ba a karkacewa. Daada mace ce mai fitar da ƙoƙon usuli, nata nata ne, wanda ba nata ba, ba nata bane. Daada bata son Nadira ko kaɗan, duk abinda zata yi zata ce daman ba jinin fulani ba ce ba.
Mama ta shiga da sallama, Daada da take zaune ta amsa mata zauna a akan carpet.
Mama ta ce, "Daada barka da yamma."
Ta yi murmushi ta ce, "Yauwa Saddiƙa."
"Na same ki lafiya?."
"Lafiya lau."
Mama ta gyara zama ta ce, "Daada wata magana ce take tafe dani."
Daada ta murmusa ta ce, "Uwar gida kenan, kina gaba da kowa a gidan nan, kuma kin fi kowa hankali. ina jinki."
Mama ta ji daɗi, ta sake samun ƙarfin guiwa sannan ta ce, "Yanzu Daada fisabinillahi haka zamu zuba ido abubuwa suna faruwa a gidan nan mu yi shiru, haka zamu cigaba da rayuwa a gidan nan?. Ka yi magana ace baƙin ciki ne, dan ba kai ka haifa ba?."
Cikin rashin fahimta Daada ta ce, "wani abun ne ya faru?."
"Daada akan Rehaan nake magana. Daada wai yaron nan ƙarfin ikon ki ya fi a gidan nan ne, da ki ka zuba ido yana zaman wata ƙasa, yana watsewa da turawa baki saka ya dawo ba?."
Daada ta ce, "Ko ubansa bai fi ƙarfina ba, balle shi."
Mama ta ce, "Daada a cikin ƴan uwansa ƙanana akwai wanda bai san fuskar ba sai a tv. Yaro ɗan dangi, an tsame sa daga dangi ya koma gefe kamar babu shi a gidan nan?. Rabon Rehaan da zuwa ƙasar nan shekara ɗaya kenan, ƙananun jikokun gidan nan duk basu san shi ba. Hakan zumuncin zai kasance? Shi ba aure ba, yana can cikin turawa yana abinda ya ga dama?. Yana zubar da ƙimar gidan nan, da mutuncin gidan nan?."
Daada ta giegiza kai tana taɓe baki ta ce, "Me ake yi da auren bare? Me ake yi da auren wacce ba jinin fulani ba?. Haka kawai AbdulAziz ya ɗauko mana annoba ya kawo ta cikin ahlinmu, ya ɗauko mana baragurbi ya haɗata damu. Ko da yake ba laifinsa ba ne, asiri ta yi masa. Har a faɗawa ƴan india tsafi?."
Mama jin ta fara samun nasara sai ta ce, "gaskiya lamarin abin dubawa ne Daada, ke kan ki rabon da ki saka Rehaan a idonki na san an kwana biyu."
"An kwan abiyu kam, tun haɗuwar da muka yi dashi lokacin da aka kaini Jedda akan ciwon ƙafa, tun daga nan ban sake ganinsa ba."
"Haka rayuwa zata tafi kenan? Yana can yana rayuwa a turai suna lalata masa tarbiyya da al'adarsa. Ƙanensa mata duk sun yi sun bar shi, Jafar ɗin da yake ji dashi shima gashi auren zai yi ya bar sa. Shi yana can wata ƙasa bai yi auren ba yana mu'amala da turawa. Yanzu sunan gidan nan yana ɓaci kowa sunanki zai fara kira, a dinga cewa ai kina gani komai ya faru baki tsawatar ba. Ƙawata ce ta kira ni, take faɗa min yadda abubuwa suke tafiya a can ƙasar. Shiyasa na taso, na ce zan zo na same ki. Bazan zuba ido ina ganin ɓaraka, na kama bakina ba."
Daada ta girgiza kai ta ce, "Gaskiyarki ne Saddiƙa, kin yi hangen nesa da tunani mai kyau. Bara mijin na ku ya dawo, dole Rehaan ya dawo Nigera ko yana so ko ba ya so wallahi. Dole ya dawo a nema masa mata ya yi aure, ni kaina zan nemo masa mata, dan bazan bari ya ɗauko wata ƙabilar ya sake haɗamu da ita ba. Bafulatana kamar sa zai aura, bazan amince da baturiya ko baindiya ba."
Mama ta taɓe baki ta ce, "Allah dai ya kiyaye. Dan kuwa na samu labarin yana can yana soyayya da baturiya."
Sai kuwa Daada ta fusata ta ce, "ƙaryarsa ta sha ƙarya, bai isa ba wallahi, bai isa ba matuƙar ina raye. Jeki abin ki zan yiwa tukfar hanci."
Mama ta yi murmushi tare da cewa, "Godiya nake, a tashi lafiya" ta faɗa tana fita kai tsaye ɓangaren Salamatu ta biyu ta shiga, kishiyarta kuma abokiyar haɗa gulmarta.
•••••••
Kyakykawar mace ce a zaune a parlour tana amsa waya cikin murmushi, kallo ɗaya zaka yi nata ka san ba kyawun fulani gare ta ba, kyau ne irin na foreign countries, ba irin kyau ne irin na mu na gama gari ba.
Kai da ka ganta ka san ba bahaushiya bace, kallo ɗaya zaka yi mata a fassarata a ƴar india, saboda kamanninta, maganarta, da komai ya gwada hakan.
Waya take amsawa cikin murmushi, kafin murmushin ya gushe daga fuskarta, tana kallon fuskar wayarta alamun video call ta ce, "Jaafar kana saka ido akan Rehaan kuwa? Ka tabbata babu wani abun da yake aikatawa?."
Fuskar wanda take kallo a wayar ya ɗan yi murmushi ya ce, "Mamy wallahi babu abinda Rehaan yake yi na ba daidai ba. Ke kin san halinsa, bazai aikata wani abu mai muni ba."
Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ka tabbata babu budurwa a tare dashi, ba ya zuwa club, Bar, chill spots, ko wani romantic vibe?."
"Wallahi ba ya zuwa ko ina Mamy. Ki yarda dani, amma Rehaan ko taba ba ya sha balle ya je Bar. Bashi da budurwa, sai abokan kasuwanci da aiki."
"Jafar ka san ya nake zaune a cikim gidan nan, ka san ƙiris ake jira Rehaan ya aikata wani abun a kambbabasa zuwa wani abun daban. Bana so ya aikata abinda zai jawo cecekuce akansa. Shiyasa nake so ka dinga saka masa ido, da ka ga wani abu mara kyau just call me and let me know. I will handle it."
Jaafar ya ce, "Ki yarda dani Mamy, Rehaan ba ya daga cikin abubuwan da ki ke tunani, bussinees da aikinsa kawai ya saka a gaba Mamy."
Mamy ta ce, "Alhamdu lillah. Yaushe za ku dawo ne?."
"Ni dai na kusa dawowa, shi ɗin ne ban sani ba. Kin san halinsa, kamar an saka masa tsanar zuwa gida."
"In za ku dawo ka tabbatar ka saka ya cire gashin nan na kansa, kasan jama'ar gidan nan ba ƙaunar sumar nan suke yi ba, yanzu zaka ji ana magana ana cewa dan babarsa ba bafulatana ba ce shiyasa yake aikata haka. Ka saka ya rage tsahonsa ko ya ya, ka ji?."
Jaafar ya murmusa ya ce, "To Mamy, kin san halinsa akan gashin nan, babu lallai ya amince."
"Zan yi masa magana, bara dai ku tashi dawowar."
"To Mamy."
"Duk da bana son dawowarsa ƙasar nan, amma babu yadda zan yi."
Cikin sigar rarrashi ya ce, "Mamy don Allah ki kwantar da hankalin ki, babu abinda zai samu Rehaan in sha Allah."
Ta sauke numfashi ta ce, "Allah ya sa hakan Jaafar, ka gaishe sa in ya dawo daga aiki."
"Okay Mamy."
Ta kalle sa ta ɗan yi murmushi, cikin tsokanarsa ta ce, "na hana hira da Riyya ko? sorry ka kira ta, ko na kira maka ita ku cigaba da magana."
Dariya ya yi kaɗan ya ce, "take your time Mamy, ba ita nake nema ba."
Ta kalli gefenta, inda wata budurwa ta fito mai kama da ƙabilar babarta, tana gyara dogon baƙin gashinta.
Mamy ta ce, "tana jinka, babu ruwana" ta faɗa tana murmushi, shima murmushin ya yi yana sake ƙaunar Mamy, dan ko kaɗan shi mantawa yake yi da ƴar cikinta zai aura.
Mamy ta datse kiran ta kalli Juwariyya cikim harshen hindi ta ce, "in an yi sallah zamu shiga mu gaishe da Daada."
Riyya ta gama naɗe gashinta, ta saka hula tana turo baki gaba ta ce, "Mamy ni bana son zuwa."
"Sai kin je, ki faɗawa Banisha" ta faɗa tana tashi ta ɗaki.
Riyya ta bi Mamy da kallo, ta sauke numfashi. Bata san me Mamy ta yiwa mutanen gidan basa sonta ba, shiyasa itama bata son shiga cikinsu, ta fi son rayuwa ita ɗaya, dan bazata jure ƙiyayyar da ake nunawa babarta a fili ba.....
Na fara rubuta littafin 3/12/2025.
_Book 1 free ne, Book 2&3 paid ne akan naira 1k kacal. Pay into Sadiya Nuhu Mukaddas 5903999117 Moniepoint MFB. A tura shaidar biya a wannan number 09030398006 ko 0701 809 8175._
Nana Haleema✍🏻❤️🔥
