RAGAYAR DUTSE Page 3 Complete by Nana Haleema

 


RAGAYAR DUTSE.

        ©️ Nana Haleema.

https://whatsapp.com/channel/0029VbC1pVN42DcoY0dAzq46

Book 1

Page 003.

Ƴan mata guda goma ne a tsaye, kyawawa masu ji da haske. Kallo ɗaya zaka yi musu ka san jinin fulani ne, duba da yadda suke da kyau mai sanyi. Dukkansu basu wuce shekaru ashirin ba, babu wacce zata ɗara daga ashirin, sai dai ƙasa da haka.


Suna zaune a babban falo, sai wata babbar mace a zaune tana kallonsu tana murmushi. 


Ta ajjiye wayar hannunta ta ce, "bakwa burin zama a irin wannan gidan don Allah?." 


Suka yi shiru basu ce komai ba, ta sake yin dariya ta ce, "ku saki jikinku, babu abinda zai faru a nan. Na san kun ji daɗin kuɗaɗen da ake baku ko?."


A tare suka ɗaga kai alamun eh, ta ce, "To kun gani. Da kuna gidan marayu kuna rayuwa kamar ta bayi, abinci ma ba wani mai kyau ake samu ba. Ku kalli yadda ku ka canja, ku ka yi kyau kamar ba ku ba. Ni kaina yanzu na tabbatar muna da ƴan mata kyawawa, da an dakusar daku a waje ɗaya."


Gyaran murya suka ji, ta yi musu alamu duk su miƙe suka miƙe tsaye. 


Babban mutum ne ya shigo sanye da shadda fara harda babbar riga. Kana ganinsa ka ga alhaji, wanda kuɗi ya zauna yake shigowa. 


Ganin ƴan matan sai ya yi murmushi yana binsu da kallo, ya kaɗa kai ya ce, Kai! Kai! Kai!!. Daman haka mu ke da kyawawa ƴan mata a garin Yola kamar haka?. Jamila aikin ki yana yin kyau." 


Ta yi dariyar farin ciki ta ce, "Godiya nake yallaɓai." 


Ya murmusa ya ce, "ku zauna ƴan mata adon gari." 


Suka zauna gabaɗayansu, ya bi su da kallo yana murmushi. 


Kafin ya kalli Jamila ya ce, "waɗanan sun yi." 


Ta ɗan rusuna ta ce, "Godiya nake yallaɓai."


"Ina fatan komai daidai."


"Komai daidai yallaɓai, komai zai tafi yadda ake so. Dukkansu babu matsala, na yarda dasu ɗari bisa ɗari."


Ya kalle su ya ce, "ai daga ganinsu, wayayyu ne basu da duhun kai. Kuna ji ƴan mata?." 


Duk suka kalle sa, ya gyara zama ya ce, "Za a kai ku inda zaku samu cigaban rayuwa. Yin karatu a babbar makaranta, hawa mota, riƙe waya mai tsada, kwana a waje mai kyau, da komai za ku zamu. Abinda mu ke so da ku, bama son yawan surutu, ku yi shiru da bakunan ku. Ba ku da iyayen da zasu takura mu ku, abinda ku ke so shi za ku yi."


Jamila ta ce, "in ku ka yi haka, za ku samu abinda baku taɓa tunani ba. Fita ƙasar waje, da komai ma za ku samu. Kun amince?."


Dukkansu suka ɗaga kai alamun sun amince. Ya yi murmushi ya ce, "ku shiga ciki, akwai mai dafa abinci, ku faɗa mata duk abinda ku ke so za a yi mu ku. Akwai driver a waje, in kuna ƙwaɗayin kayan ciye-ciye duk za a baku."  Suka miƙe suka shiga inda ya nuna musu, ya bisu da kallo yana murmusui har suka ɓace.


Ya kalle ta ya ce, "ba a taɓa samu team mai kyau kamar wannan ba, kin yi haɗi yadda ya kamata. Kuma da alama dukkansu lafiyayyu ne, za a samu abinda ake so."


Daɗi ya kamata, ta ce, "sai da na zauna sannan na zaɓa, na fiddo su."


Ya ce, "na san za ki iya. Amma ina yarinyar nan da na gani?." 


Ta ɗan sauke numfashi sannan ta ce, "Hafsa ko?." 


Ya ɗaga kai ya ce, "ita. Ai na faɗa miki ina so a haɗo da ita, wannan da kaina zan ajjiyeta ba wani wajen zan kai ta ba."


"Hafsa da Zainab bana son taɓa su ko kaɗan, saboda yaran nan sune na hannun daman Islaha."


Ya bita da kallon mamaki ya ce, "Islaha kuma, ba mun gama da case ɗinta ba?." 


"Mun gama Yallaɓai, amma ita bata gama damu ba. Daga ranar da ta buɗe ido babu ɗaya daga cikinsu, zata fara yi mana shige da fice a kan lamarinmu. A haka ma dan muna da maganinta a hannu ne, da ba mu san irin ɓarnar da zata yi mana ba."


"Wai wacece Islahan nan da mu ka kasa ganin bayanta?."


"Mun yi nasara yallaɓai, tunda ta bar gidan nan da jimawa. Barinta gidan shine ya dakusar da ita, har yanzu bata da hujja akan abinda mu ke aikatawa. Iya wannan ma nasara ce."


Ya ɗan gyaɗa kai ya ce, "A kashe ta mana, meye amfaninta?." 


Ta yi murmushi ta ce, "ka bar komai a hannuna, indai ina da rai bata isa ta yi wani motsi ban saka ƙafa na fyaɗe ta ba. Ai bata isa ta yi wani abu na zuba mata ido ba."


"Na yarda dake Jamila, tunda muka fara harkar nan bamu samu matsala ba. Amma ina so ko ta wacce hanya Hafsa ta zo gidan nan, na yi miki alƙawarin mota, da kuɗi naira miliyan biyar, da kujerar hajj. bana. Amma in kin kawo min Hafsa kenan."


Ta yi dariya ta ce, "Wallahil azim, ka ji rantsuwar musulmai ko? Islaha ko ita ta haifi Hafsa sai na kawo maka ita, sai ka yi shagalinka da ita yadda ka ke so. Bata isa ta yi komai ba, babu abinda ta isa ta saka ko ta hana."


Ya yi dariya ya ce, "Idon naira, wato tunda na yi alƙawari za ki iya." 


Ta yi dariya ta ce, "Yallaɓai babu abinda kuɗi ba sa sakawa."


Ya ɗaga kai ya ce, "wannan karo, baza mu fitar da yaran nan ba, a nan ƙasar zamu rabasu. An ɗan samu tangarɗa akan fitarsu ƙasar waje, tunda akwai mutanenmu a nan da suke da kuɗi a hannu zamu fanshe komai."


"Babu komai yallaɓai, amma kar a barsu a Adamawa ko kusa da Adamawa."


"Haba Jamila, na san abinda nake yi fa." 


Ta yi masa jinjina ta ce, "tuba nake yi, matsala ce bana so." 


Ya ɗaga kai ya ce, "na fi ki gudunta."


"Yallaɓai kowa da ɓangarensa, in ka duba yaran nan a hannun mu suke, binciken farko ta kaimu za a fara."


"Na ji. Ki je kawai, ki shirya min haɗuwa da Hafsa. Su kuma waɗanan, in anjima ko wacce zata san makomarta" ya faɗa yana miƙewa.


itama ta miƙe ta ce, "an gama ranka ya daɗe. Amma ina so a bani aron yaran nan mu tattauna." Ya nuna mata hanya alamun ta je, ta ce, "godiya nake." 


Tana shiga ta kalle su ta ce, "Kyawawana, ku riƙe amana a duk inda aka kai ku, ban da sata, gulma, ko yiwa babban mutum video da waya. In aka kama ɗaya daga cikin ku da irin wannan laifin, za a ɗaure sa ne. In ku ka kwantar da kai, ƙasar waje sai ta zamar mu ku wajen zuwa ko yaushe."


Ɗaya daga ciki ta ce, "Baza ki taɓa samun mu, da irin wannan abubuwan ba." 


Ta yi dariya ta yi musu jinjina ta ce, "sai mun yi waya" ta faɗa tana fita..


      *****


Tunda ta koma ɓangarenta take kuka, ta dafe kai tana zubar da hawaye zuciyarta duk babu daɗi.


Bata san me ta yiwa dangin mijinta da basa sonta ba, kawai dan ta kasance ba yarensu ba, dan ta kasance ba ƴar ƙasarsu ba, shikenan kowa ba ya sonta?. 


Ba ita ta bawa Rehaan ɗaukaka ba, ba itace take sakawa ya zauna a ƙasar waje ba, ta fi kowa son ganinsa a kusa da ita. Amma da an tashi magana, duk laifinsa sai a juye ya dawo kanta gabaɗaya.


Babu mai kaunarta a cikin gidan sai Janan, wacce ta kasance age mate ɗin Riyya. Bayan ita babu wani, sai a fi sati ɗaya wani yaron gidan bai shigo inda take ba. Sun tsame ta daga gidan, sun mayar da ita kamar annoba.


A lokacin Riyya ta shigo, ganin tana kuka sai ta ƙaraso da sauri ta ce, "Mamy me ya faru, meyasa ki ke kuka?" Ta faɗa tana zama a kusa da ita hankali a tashe. 


Ta sake cewa, "Mamy lafiya?." 


Bata ce komai ba, ta goge idanunta ta kalli Riyya ta ce, "Riyya kira min Rehaan a waya." 


Ba musu ta ɗauki waya ta kira number sa ta ƙasar uk amma bata shiga. 


Ta kalli Mamy ta ce, "wayarsa bata shiga."


Mamy zata yi magana aka shigo ɗakin da sallama. 


A tare suka amsa, suna kallon wanda ya shigo ɗakin. Riyya ganin Abba ne sai ta miƙe tana kallonsa, ba kasafai aka cika ganinsa a ɓangaren matansa ba, sai abu mai mahimmaci musamman rashin lafiya. 


Riyya tunda ta gansa, ta san an ɓatawa Mamy rai a wajen meeting, shine ya biyo ta ya rarrashe ta.


Riyya ta ce, "Abba sannu da zuwa." 


Ya kalle ta ya ce, "ina Banisha?."



"Ta yi  bacci." Kai ya ɗaga Riyya kawai,  ta fita daga ɗakin ta basu waje. 


Abba ya sauke numfashi yana kallom matarsa da take zubar da hawaye har lokacin, kanta yana ƙasa bata ɗago ba. 


Ya ɗan gyara tsayuwa ya ce, "NADIRA!." 


Bata ɗago ta kalle sa ba sai goge idanunta da take yi, ya san an ɓata mata rai ne, hakan ya saka ya tako yazo inda take ya zauna. 


Ya riƙe hannunta  ya ce, "wannan kukan bashi da amfani, kin san bazan ja da hukuncin Daada a gidan nan ba. Kuma ba laifi bane da an ce Rehaan ya dawo gida."


Cikin harshen hindi, da take yi masa magana dashi ta ce, "Amma ka san duk lokacin da Rehaan ya dawo nigeria sai wani abun ya same sa ko? Ka san ba ya taɓa zama lafiya indai ya saka ƙafarsa a cikin ƙasar nan. Meyasa ake so ya dawo gabaɗaya, a manta a can yake aiki da kasuwancinsa?. In ya bar komai na sa ya dawo nan kenan ya haƙura da komai?. Ka san bana son wani abu ya samu Rehaan, bana so ko kaɗan."


Ya sauke numfashi bayan ya gama jin abinda ta ce. Duk da ba da yarensa ta yi magana ba, amma a zaman da suka yi ya iya yarenta sosai. Kamar yadda ta iya fulfulde da hausa. Yana fahimtar duk abinda ta ce, yadda ta yi maganar ya san abin yana taɓa mata zuciya. 


Ya san macece da take da son ƴaƴanta, bata so ta ga wani abu ya same su. Hakan yana daga cikin dalilin ƙinta da Daada take yi, takance bata da fulako da yakana, su fulani ba haka suke nuna tsantsar son yara ba, suna ɓoyewa. Mamy kuwa bata san ɓoye son ɗanta ba, a gaban kowa take nuna masa soyayyar da iyaye suke nunawa yaransu.  


 "Nadira kin san dole gidan nan, shiyasa nake fɗa miki zamansa a England bazai yu ba. Dole ya dawo nan ya cigaba da zama kamar sauran ƴan uwansa."


"Kasuwancinsa fa? Ka san acan yake yin komai. In ban da yanzu, da ya kawo shopping mall da hospital nan ba, da bashi da komai a nan."


"Zai iya yi daga nan, ba sai a can ba. Muna zamanin da kana zaune daga gida zaka yi meeting, karatu, aika saƙo da komai da komai. Kasuwancinsa bazai dakushe dan ya dawo ba. Aiki da ki ke zance ke kan ki kin san ba yi yake yi ba, sai dai in ya samu contract da wata ƙasa ya je ya gama ya dawo. Bai ɗauki karatunsa na likitanci da mahimmaci ba, ya fi mayar da hankali akan kasuwanci."


Ya yi murmushi ya fuskance ta sosai, tare da riƙe ɗaya hannunta ya ce, "Nadira!."


Ya ɗago da fusksrta yana kallon kyakykyawar fuskarta ya ce, "na yi miki alƙawari, a wannan karo babu abinda zai samu Rehaan, ko da ya yi ciwon da ya saba baza a ɗauki lokaci ba zai samu lafiya. Aiki kuma zai cigaba da aikinsa a nan, tunda kin san ya fi mayar da hankali akan aikin in ya zo nan. Harkokin kasuwancina da nasa da suke a ƙasar da zai bari, za a cigaba da kula da komai daga nan. Don Allah kar ki samu damuwa, kin ji?."


Ta ɗaga kai alamun to, ta ce, "Ni daman ba damuwa nake yi akan zuwansa ba, gidansu ne, komai daɗewa dole ya dawo. Kawai rashin sakewar da ba ya yi ne bana so, ga kuma yawan ciwon cikin nan na sa."


"Babu abinda zai faru in sha Allah."


"Allah ya sa."


"Amin. Rehaan yana da wacce yake so ya aura ne?." 


Ta ɗago ta kalle sa tare da girgiza kai, sannan ta ce, "bai taɓa bani labari akan hakan ba, sai dai ko yanzu."


Abba ya yi shiru yana kallon ta, sai ta ce, "Daada ta ce ya yi aure ne?." 


Ya ɗaga mata kai ya ce, "ta ce a haɗa da aurensu Riyya." 


Ta ɗan buɗe ido ta ce, "Riyya! Bikin Riyya ai ya kusa, har yaushe ya dawo da aka haɗa aurensu lokaci ɗaya?."


Ya ɗaga kai ya ce, "hakan za a yi Nadira. Za a san abinda ya kamata ayi."


"Ka zaɓar masa matar ne?."


"A'a, ke kina da zaɓi ne?."


"ko na faɗa ma baza a amince ba, baza a so na sake ɗauko hindi na kawo cikin fulani ba. Bani da zaɓi" ta faɗa a sanyaye.


Abba ya girgiza kai ya ce, "is okay, mu jira ya dawo, wataƙila yana da wacce yake so." 


Mamy ta ce, "ina so in je gida, na jima ban je canja." 


Ya miƙe tsaye yana cewa, "zaki je, amma ba yanzu ba Nadira. Ina jiran zuwa ki, ki kawo min tea" ya faɗa yana fita daga ɗakin. Mamy ta dafe kai tana tunani.


Tunaninta ɗaya wacce mata kuma za a zaɓa masa a cikin gaggawa haka? Ita fa bata son a aura masa wacce ba ya so, kuma bata so a aura masa wacce zata so shi dan kuɗi ko dan kyau. Shiyasa ta fi so ta zaɓa masa mata da kanta, amma ta san baza a taɓa bata dama ba. 


Ko wacece wacce za a zaɓa masa, matuƙar baya sonta itama baza ta taɓa sonta ba har abada. Abinda Rehaan yake so shi take so, zaɓinsa shine zaɓinta. Ta sauke numfashi, ta miƙe ta shiga banɗaki cikin tunani.


Ɓangaren Daada Mama Saddiƙa ta nufa da sassarfa, ta shiga da sallama ta same a yadda suka bar ta. 


Ta zauna a ƙasa ce, "Barka da hutawa." 


Daada ta ce, "Yauwa Saddiƙa. Ya ki ke ganin abubuwa za su tafi? Ina so a haɗa auren Juwairiyya da Muhammad a lokaci ɗaya, kuma bana son wani hayaniya, da kaina nake so na zaɓa masa matar aure."


Gaban Mama ya faɗi, jin kalmar Rehaan zai yi aure, gumi ya keto mata a goshi, ta share gumin ta ce, "Duk yadda ki ka yi daidai ne."



"Kina da matar da ki ke ganin ta cancanci ya aure ta?."


Da sauri ta ɗago ta kalle ta, ta ɗan yi dariya ta ce, "Hajiya Daada ni kuma, ni zan zaɓawa Rehaan mata?. In Nadira tana da rai ai bani da wannan ikon."


"Ni ke na zaɓa, kuma ke nake so ki zaɓar masa matar aure, amma in kina da ita." 


Mama ta yi murmushi ta ce, "abinda ki ka ce daidai ne Daada. Ƴan mata masu tarbiyya ai baza mu rasa ba, zan bincika in sha Allah." 


Daada ta ce, "kar ki samo wata a cikin jikokin abokan zamana. Kar ku ga na amince da auren Juwairiyya da Jaafar, a ɗauka za a amince da ɗan wanda bani na haifa ba. Ki yi yi tunani mai kyau, ko a danginki ne ki samo masa. Jinin fulani, mai tarbiyya, mai kyau, wacce zata zauna dashi tsakani da Allah."


Ta yi murmushi ta ce, "in sha Allah Daada, za a yi."


"Tashi ki je. Saboda yanayin lokaci, ki yi gaggawar nemowa."


"Ki huta lafiya" ta fada tana fita zuwa ɓangaren ta da sauri.


Tana shiga ta cire hijjab ɗin jikinta ta cillar, yaranta da suke zaune, suka kalle ta. Kafin su yi magana ta ce, "Rehaan! Wannna yaro ya tsaya min a zuciyata." 


Babban ɗanta mai suna Zayyad, wanda suke kira da Hamma Zayyad ya miƙe tsaye  ya ce, "Mama wani abun ne ya faru?." 


Ta juyo ta ce, "Aure! aure Daada take so ya yi. Ta ya zamu bari Rehaan ya yi aure? Da zarar ya yi aure ya haihu shikenan mun shiga uku, komai ya sake lalacewa."


Sameer ya miƙe tsaye ya ce, "Dole mu hana auren nan Mama, in Rehaan ya yi aure a wannna lokacin da yake samun ɗaukaka akwai matsala."


Mama ta dafe kai ta ce, "Nadira kin cuce ni, kin lalata min shirin da na shekara talatin da biyar ina yi. Yanzu meye abin yi?."


Adda Zuhra da take cikinsu ta ce, "Yaushe ne auren?."


"Ni ta bawa zaɓi na nemo matar da zai aura."


"Shikenan faɗuwa tazo daidai da zama. Ina Sajida." 


Mama ta kalle ta ta ce, "Sajida! Wacce sajidar?."


"Sajida ƴar ƙawar ki mana."


"Baki da hankali, a wannan ɗaukakar da Rehaan yake samu zan bari ya auri Sajida? In ta aure shi ta kere ki fa kenan. Domin Rehaan ya ninka mijinki kuɗi, sau babu adadi. Babu yadda za a yi na ɗauko ƴar ƙawata da kaina, na bata wanda ya fi mijin ƴata ɗaukaka. Ko labari na ji za a yi, zan shiga na fita na dakusar da auren, balle ni da kaina."


"Inaaa! Har abada wallahi. Ke ko ƙanwata da muke ciki ɗaya, da tana da ƴa mace, bazan ɗauki ƴarta na bawa Rehaan ba. Ke ko ita kanta ƙanwar tawa, wallahi bazan iya bari ta auri Rehaan ba. Komai a ɗakina nake so ya tare, bana so ɗaukaka ta tsallake ni ta je wani waje."


Zuhra zata yi magana ta dakatar da ita, cikin fusata ta ce, "ya isa malama, ki bar batun nan bazan amince ba. Babu ta yadda za a yi in bari ta auri mijin da yafi na ki kuɗi. Rehaan ga kyau, ga kuɗi, ga iko, ga farin jini, ga ɗaukaka. Ba iya nigeria ba, a kaf ƙasashen ƙetare babu inda Rehaan bashi da alfarma. A hakan zan bari wata wacce ta raɓe ni ta same sa?. Da dai ace akwai aure a tskaninku ne, ko ba ya so sai ya auri Janan wallahi."


Zuhra ta ce, "Kamata ya yi mu zauna ayi magana sosai akan hakan, yanzu dare yana yi." 


Sameer ya ce, "Mama ya kamata a san abinda za ayi in, in ba haka ba wallahi muna gani komai zai fi ƙarfin mu."


Zayyad ya girgiza kai ya ce, "To ku ƙyale Rehaan ɗin mana, shekara nawa ana wahala a kansa an kasa samun nasara?." 


Mama ta kalle sa cike da harara, ta ce, "babban banza, a haka zaka ƙare ai. Ina kishinku amma kai kana zuba min ƙasa a ido, dama Sameer ko Zubair ne babba ba kai ba." 


Ya yi murmushi, bai ce komai ba ya fita.


Mama ta dafe kai ta ce, "innalilahi! Na auri mutum tun yana saurayi, amma saboda tsafi irin na ƴan india tana shigowa rayuwarmu ta tarwatsa komai. Ni da nake da ku mu ne manya a gidan nan, amma itace take riƙe da gidan." 


Zuhra ta ce, "gabaɗaya sunan Abba ya ɓata, sunansa ake ambato. Ko ni, in aka ganni sai ace ga ƙanwar Rehaan Yola."


Mama ta dafe kai, ta girgiza kai ta ce, "mu zuba mu gani. Sai na dakusar da wannan ɗaukakar wallahi. Ina zuwa" ta faɗa tana shiga ɗaki da gaggawa.


*****


         "Rehaan yana gab da shigowa nigeria, kana da labari?." 


Wanda yake zaune a gefensa, ya girgiza kai ya ce, "bani da labari, sai yanzu." 


Shima ya zauna yana girgiza kai sannan ya ce, "na sanar da kai yanzu, duk yadda  za a yi a wannan lokacin ayi. Kar a saɓa saiti, a tabbatar da Rehaan ya daina numfashi. Barinsa duniya kaɗai, shine zai zama silar ɗagawarmu. Matuƙar yana da rai, babu inda zamu iya zuwa."


Ya girgiza kai ya ce, "za a san abinda za a yi ranka ya daɗe, a ko yaushe umarninka kawai nake jira. Zan san duk abinda za a yi da zarar ya shigo nigeria." 


Ya ɗora ƙafa kan ɗaya sannan ya ce, "a wannan karon bana son matsala, wannan karon bana son kuskure. Ina so na ji labarin Rehaan ya mutu, ina so na ji labarin babu shi a duniya. ." 


"An gama ranka ya daɗe."


"Aje a yi abinda ya kamata, duk abinda ake buƙata a yi min magana."


"An gama" ya faɗa tana fita. Ya yi ƙwafa yana girgiza kai zuciyarsa cike da mugun nufi.


      *LONDON, UNITED KINGDOM.*


      A hankali yake kaɗa ƙafarsa idonsa a rufe, sanye yake da ƙaramar riga mai gajeren hannu, hannunsa riƙe da glass cup yana juya ragowar drink ɗin da yake ciki. 


Fari ne tass, kallon farko zaka yi masa ka san haskensa ba na ƴan Nigeria ba ne, kana kallonsa ka san haske ne ba gama gari irin wanda mu ka saba gani ba. 


Yana da dogon baƙin gashi, wanda ya sakko har shoulders ɗinsa, gashin ɓaki ne sosai, mai tsaho da cika. Yadda ya rufe ido, eyelashes ɗinsa sun kwanta akan fuskarsa, ga dogon hanci mai tsaho da kyau. Yana da cikakken sajen da ya zagaye fuskarsa, bai yi yawa ba, kuma ba a cire sa ba, ya sha gyara, kai daga gani ba sai ance yana shan kuɗi ba.  


Yana da smallest lips, masu kyau da ɗaukar hankali. Ta ko ina ya haɗu, kana ganinsa ka san kyau ne ya haɗu da kyau. Fulani ne ya haɗu da india, shiyasa aka samar result mai ɗaukar hankali. In ka kalle sa sai ka kuma kallo, domin kyaunsa ba na kallo ɗaya ka haƙura bane.


REHAAN ABDULAZIZ YOLA kenan, wanda ake yiwa laƙabi da RAY, saurayi matashi ɗan shekara talatin da uku zuwa da huɗu. Cikkaken likita a ɓangaren tiyata, kuma shararraen ɗan kasuwa, wanda sunansa ya ratsa duniya gabaɗaya. 


Ray ya ɗaukaka, Allah ya saka masa albarka a cikin kasuwancinsa, sunansa shine taƙamar ƴan garin Yola. Yadda ƴan Kano suke alfahari da sunan ɗangote, haka ƴan Adamawa suke alfahari da sunan Rehaan. Yana daga cikin matasa mafiya shahara a Nigeria. 



   "Ray kana ji na?."


Kyakykyawan saurayi mai irin shekarunsa ya faɗa yana zama a kusa dashi. 


Jafaar Ahmad Zubair Yola kenan, wanda Rehaan yake yiwa laƙabi da Jazy ko ya ce Jay. Cousin ɗinsa, kuma amininsa. Tare suka tashi, tare suke yin komai. Tsiran shekara ɗaya ne a tsakaninsu, Rehaan ya girme sa da shekara ɗaya.


Kowa akwai abinda ya saka a gaba, Jazy ba a ƙarƙashin Ray yake aiki ba, shima da kansa ya dogara, aiki ne yake kawo shi uk kamar Rehaan ɗin. Mamy ta ɗauki amanar Ray kacokan ta tamƙawa Jazy, dan ko yaushe suna tare. 


Sai a lokacin ya buɗe kyawawan idanunsa masu kama da madara, ga girma ga haske, gasu zagayayyu, sun fito waje kamar ka saka hannu ka cire. 


Ray ya sauke ƙafa ƙasa, ya kalli Jafar ya ɗan girgiza kai.  


Jazy ya ce, "mun yi waya da Mamy ɗazu da baka nan, ta ce min akwai batun zuwan ka Nigeria a kwanakin nan."


Rehaan ya ɗan yi tsaki, cikin harshen fulfulde, wanda suka fi amfani dashi in suna tare ya ce, "Makircin tsohuwar nan ne ko?."


"Kaima ka san itace zata ce ka dawo, in ba ita ba babu mai takura maka."


"Ni ban san me na tare mata ba. Ko in na koma can ɗin me zan yi mata oho" ya faɗa yana ɗaukar band a gefensa ya ɗaure gashin kansa a tsakiya. 


Hakan da ya yi ya sake ƙara masa kyau, ya fito da asalin zatin da Allah ya yiwa fuskarsa.


Jazy ya kalle sa ya ce, "kamar kuwa kasan Mamy ta ce min na saka ka ɗan rage gashin nan, bata son abinda zai jawo mata magana." 


Ya yi masa kallon ƙasan ido, sannan ya ce, "Bazan cire ba wallahi, sai dai duk abinda Daadan zaata yi ta yi. Na gaji da wannan abubuwan na su, komai sai abinda suke so za a yi, dan sun ga ina ƙyalewa sai a dinga zaƙewa? Ya isa."


Jazy ya yi dariya ya ce, "To Rehaan ba ni na ce ka koma ba fa, wannan faɗan na me ye?." 


Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "bana son zaman Nigeria Jazy. Bana son zama a gidanmu, bana son abinda zai haɗa ni da gidan nan. Ba dan Mamy da Abba dasu Riyya ba, babu abinda zai mayar dani Nigeria. Gabaɗaya gidan nan ba ƙaunata suke yi ba, Janan ce kaɗai take kula da ni a gidan, sai kuma Hamma, amma kowa burinsa...." Sai ya dafe kai ya yi shiru bai ce komai ba.


Jazy ya ce, "sorry Ray, ko wacce nasara haka take zuwa da ƙalubale." 


Ya kalle sa ya ce, "Ni meyasa jarabawar ta zo a kan gidanmu? Jazy babu wanda bana so a gidan nan, ina ƙaunar ƴan uwana ka fi kowa sani, amma su ba haka ne a wajansu ba. Riyya da Kiddo sune ƙannena, sai Janan. Bana jin daɗin hakan da suke yi min."


Jazy ya ce, "na sani Ray, kai mutum ne mai son ƴan uwa da son kyautata musu, jarabawarka ce a haka shiyasa hakan ya faru." 


Ya sauke numfashi tare da ɗora hannayensa duka biyun a gashin kansa, ya cire band ɗin da ya saka, ya yamutsa gashin yana barbaza s ko ina. 


Ya ɗan cize baki ya ce, "Zan shiga Jedda Jazy."


Jazy ya ce, "yaushe kenan?."


"Soon."


"Amma akwai batun zuwa Nigeria fa."


"Aiki ne dani a can Jazy, zan tsalleke aikin na tafi nigeria ne?."


"Amma tunda har aka fara batun nan gwara mu je ɗin, in ya so daga can sai ka wuce." Ya ɗan girgiza kai bai ce komai ba. 


Jazy ya yi murmushi ya ce, "Mamy ta ce min baka da budurwa har yanzu?." 


Kyakykyawan murmushi ya yi, wanda ya bayyanar da fararen haƙoransa farare masu kyaun kallo. 


Ya shafa fuskarsa ya ce, "Mamina kenan. Me ka ce mata?."


"Na ce mata babu kowa har yanzu."


"Ka yi mata ƙarya kenan, bayan ka san akwai Alma ko?." 


Jazy ya haɗe rai ya ce, "Ray meyasa lokaci ɗaya ka ke son sako Alma a cikin rayuwarka? Ka san aurenka da ita ba abu ne wanda zai yu ba." 


Ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana ɗan taɓe baki ya ce, "akwai haramci a aurena da ita ne? Infact Alma musulma ce ba arniya ba, ko arniya ce addini ya bani damar auren ta balle musulma ce. So Alma she's my girlfriend, zan faɗawa Mami, next month zamu yi court marrige a nan."


Jazy ya ce, "Rehaan! Me ka ke faɗa haka? Kana so ka jawowa Mamy wani abun ne?." 


Ya miƙe tsaye yana ɗan stretching kaɗan ya ce, "Mamy babu ruwanta dan na auri Alma, haka Abba ma babu ruwansa, dan shima ya auri Mamy, bazai damu dan zan auri ƴar Uk ba. Sauran mutanen gida duk abinda zasu ce su ce, i'm ready to face any challange for that."


Jazy zai yi magana aka danna door bell, Ray ya ƙarasa ya buɗe yana kallon wacce ta shigo. 


Siririyar baturiya ce, mai farin gashi mai tsaho. Sanye take cikin dogon jeans da riga wacce ta rufe iya ƙirjinta kawai, gabaɗaya cikinta a waje yake. Gabaɗaya flat tummy ɗinta a bayyane yake, ga navel ɗinta a bayyane, an yi mata ado da stone mai kyau a cikinta.


Rehaan ya ɗan kalle ta, kafin ya yi magana ta yi hugging ɗinsa harda ɗafewa jikinsa. Bai yi denying ba, ya yi hugging ɗinta back hannunsa zagaye da cikinta wanda ya kasance a bayyane. 


Ɗagowa ta yi daga jikinsa, ta yi pecking goshinsa tare da shafa gashinsa ta ce, "I missed you Ray."


"I'm just talking about you sai ga ki kin zo. Ina ki ka je."


"I'm here to invite you to go on vacation with me. Can you come?."


Ya kalli Jazy da yake kallonsa, sannan ya kalle ta ya ce, "Alma ina da aiki yanzu, amma na yi alƙawari next time." 


Ta yi murmushi tana shafa gajensa ta ce, "take your time Rehaan, i'm leaving."


"Okay, byee." 


Ta sake hugging ɗinsa ta ce, "byee" ta faɗa tana fita, ya raka ta har bakin ƙofa ta tafi, sannan ya juyo yana kallon Jazy da yake aiko masa da harara. 


"Amma ka san hakan ba yi daidai da addininka da al'adarka ba ko? Kai bafulani ne, wannan kuma ba al'adarmu ba ce." 


Ray ya kalle sa ya ce, "Nan ba a Yola nake ba, a Uk nake. Ina so ka tuna Alma ƙawata ce tun ina school, tare muka fara karatu tun daga farko har ƙarshe. Alma ta taimake ni, musamman akan karatuna. And hug and kiss normal abu ne."


Jazy ya ce, "kana son jawowa Mamy wani abun kenan?." 


Ya ɗan rausayar da kai ya ce, "na faɗa maka auren Alma zan yi."


"yaushe ka yanke wannan hukuncin? Ko dai..." sai ya yi shiru bai ƙarasa ba. 


Rehaan ya ce, "ko dai me?."


"Nothing."


"Jazy ya zama dole na auri Alma, a jikina nake ji aurenta ya zamar min dole." 


Da mamaki ya ce, "meyasa ka ce haka?."


"I dont know, amma a jikina nake ji ya zama dole na aureta Jazy. Ban san me yake damuna ba, ban san me nake ji ba. Bana son Alma a matsayin wacce zan aura, amma ina ji a jikina ya zama dole na aure ta Jazy." 


Jafar ya bi sa da kallon mamaki ya ce, "ni ka ɗaure min kai."


Ray ya ce, "nima kaina a ɗaure yake Jazy, nima ban san me zan yi ba."


Ya faɗa yana zama a akan kujera yana rufe ido, dan shi kansa bazai ce ga abinds yake damunsa ba. 


Jafaar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Rehaan ka cigaba da addu'a kawai." Ya ɗaga masa kai alamun to, ya dafe kai bai ce komai ba.  


Jafar ya buɗe window, sai ya taɓe baki ya ce, "ban san meyasa hausawa mu suka zubar da mutuncinsu ba. Ka ga wannan apartment ɗin? Wani bature ne a ciki, ake kawo masa ƴan nigeria kala-kala, yana biyansu ya yi abinda yake so da ita. Kalli dai wannan yarinyar, kana ganinta ka san yarinya ce, sannan kana ganinta ka san yar ƙasar mu ce."


Ray ya miƙe ya ƙaraso ya kalli Window ɗin ya kalli yarinyar ya kalli Jay ya ce, "hmmm! Shiyasa ma gwara ka auri turawa ka huta, ƴan ƙasar mu sun lalace da zuwa outside countries suna zubar da mutuncinsu." 


Jazy ya kalle sa ya ce, "Amma kai ka ce min baka sha'awar auren farar mace, ka ce black beauty ka ke ra'ayin aure. Me ya kawo Alma?."


Ya sake kallom window ya, ya jingina da bango yana ɗan murmushi kaɗan ya ce, "nima ban sani ba, but brown skin is my favorite!." 


Jazy ya ce, "kamar wacce kenan?." 


Ya sake kallon window yana kallon wacce ya nuna masa, ya kalli Jazy yana taɓe baki bai ce  komai ba ya ɗauki wayarsa ya hau sama.


 Jazy ya bisa da kallo yana sauke ajiyar zuciya, a kaf duniya shi kaɗai ya san waye Rehaan, ko Mamy bata san halayensa kamar yadda ya sani ba.


Shi kaɗai ya san abubuwan da suke baibaiye da Rehaan, ya tabbatar shigowar Alma rayuwarsa kawai nufi mara kyau. Haka kawai yake ji a ransa kamar zuwanta rayuwar Rehaan plan ne, gabaɗaya ba ya so ya dinga ganinta tana zuwa inda yake. Tana son cewa zata taɓa shi, duk da hug and kiss ba komai bane a wajenta, shima tunda a Uk yake rayuwa kusan ya saba da hakan. Amma na Alma ya yi yawa, akwai abinda take nufi da Rehaan.


Waye ya turo ta? Shine abinda bai sani ba.


******


Alma tana fita daga apartment ɗin wata luxury car da take ajjiye shiga. Ta kalli wanda yake ciki a zaune, ta miƙa masa abin hannunta ta ce, "here is his hair." 


Ya karɓa ya ce, "his signing?."


"We are coming there."


"Dont forget, we need everything from Ray."


"I know."


Ya sake kallon ta ya ce, "can you do me a favor? If you do it, i will give you fiffty million naira."


Alma ta yi murmushi ta ce, "i can."


Ya sauke numfashi ya ce, "ki yi ƙoƙarin jan hankalinsa, ku gama sabawa, sannan zan faɗa miki." 


Ta yi murmushi ta ce, "Okay Sir." 


Ya yi murmushi, suka gaisa ta sauka daga motar shi kuma ya ja motar ya tafi.



_Book 1 free ne, Book 2&3 paid ne akan naira 1k kacal. Pay into Sadiya Nuhu Mukaddas 5903999117 Moniepoint MFB. A tura shaidar biya a wannan number 09030398006 ko 0701 809 8175._



Nana Haleema✍🏻

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post