MUHASEEN Page 1 Complete by Maryam Star


🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹

(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

     𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔

𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

🤝𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈✊

   𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆

       𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀

بسم الله الرحمن الرحيم.

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 1.

ABUJA NIJERIA

     KUBWA.

07:00am.

Tafiya ya ke akan diga-digan ƙafafuwansa da sukai futu-futu, yayinda yai nidan kiwo a cikin tunanin yanda rayuwa ta ke sauya ma shi a kullum, sababbin ƙofofin wahala da ƙalubale na sake buɗewa a gareshi, ƙunci na cike sauran guraban da suka rage a zuciyarshi, bai ankare ba sai jin ƙugin mota ya yi a bayansa, sautin tsayuwar motar da ƙarfi ta hanyar danne burki da aka yi a gaggauce ya dawo da shi hankalinsa, a hankali ya juyar da jikinshi baya, sai yaga taƙi baifi biyu ba kawai ya rage motar tayi gaba da shi, a maimakon yaji daɗin tsira da lafiyarsa da yai sai zuciyarshi ta raya ma shi.

    'Inama ace motar bata tsaya ba, inama ace tabi takanka wataƙila daka huta da wannan rayuwar me cike da tarin ƙalubale.'

   Bai kula da tambayarshi da me motar ya fito yana yi ba, ya kauce a hanyar tare cigaba da tafiya, ba sauri ya ke ba haka kuma ba a slow ya ke tafiyar ba, sai da yayi tafiyar mintuna talatin a ƙafa, sannan ya tare abin hawa tare da sanar da shi inda zai kai shi.

A daidai Dutse Market abin hawa ya aje shi, nan ya ɗauko raina ɗari biyar ya biya, sannan ya soma shiga cikin kasuwar yana gaisawa da mutane jifa-jifa, da haka harya ƙarasa wajen wa ta runfa, mukulai ya ɗauko daga cikin aljihunsa ya shiga buɗe shagon, bayan ya buɗe ya shiga ciki, nan ya dinga jido buhunnan kayan miya yana firfito da su, sai da  ya gama tas sannan ta naɗe hannun rigarshi ya tsaida me ruwa ya siya, sai ya shiga zazzage kayan miyar a ƙasa yana zubawa cikin bokiti yana wankewa, tas ya tsaftace su tare da jere komi gwanin kyau, har a lokacin kamulalliyar fuskarshi babu annuri amma bakinshi na motsa a ƙalla sau goma a minti ɗaya, ƙasa-ƙasa ya ke furta.

   "Subhanallah, walhamdulillha, Allahu akbar.

    Bayan ya gama ya koma wajen zamanshi ya zauna, kafin masu siya suka koma zuwa su na siye.

    "Assalamu alaikum."

 Tattausar muryar wa ta matashiya ta dira a  cikin kunnuwansa, ɗago da kanshi yayi bayan ya miƙawa bayerabiyar data siyi tomatir leda gami da canji, sai ya amsata cikin muryarshi me zurfi.

   "Amin wa'alaiki salam."

 Bata jinkirta ba wajen faɗin.

   "Yaya Suhail barka da safiya harka fito kenan, yau ka zo da wuri."

   A takaice ya amsa ta, daga nan kuma bai sake cewa komi ba, illa sauraren cikinshi da ke ƙugin yunwa daya soma yi, kamar ba zai ce komi ba, sai kuma ya nisa da muryarsa a dake ya ce.

   "Ki samin na 1k."

Ko da yayi maganar sai ya ciro dubu ɗaya daga cikin kuɗin kasuwancinsa ya miƙa ma ta, da hanzari budurwar ta karma har tana haɗawa da ƴan yatsunsa, sai yai saurin janyewa yana sake ɗaure fuska.


Lafiyayyar masar shinkaface da ruwan tea ta kawo ma shi, koda ya amsa bata juyaba haka ta zauna a wajen tanata kallonsa kamar ta samu TV idan aka zo siyayya kuma sai tai hanzarin karɓa ta bayar, uffan bai sake cewa da ita ba.

    Ba shi ya tashi ba sai gabatowar sallar azahar, sannan ya siyar da komi sai abin da ba'arasa ba, haka ya tattare komi ya kulle shagon, sannan ya kalli budurwar a ɗan fizge ya yi ma ta sallama tare da wucewa.


Raka bayanshi ta yi da murmushi tana jin ranta fes, itadai in dai za ta ganshi tofa kakar farin cikinta ta yanke saƙa.


Sai da ya tsaya a masallaci ya gabatar da sallah haɗe da addu'a me tsayi sannan ya tari abin hawa ya hau, yana jin yanda tsoro, zullumi gami da fargaba ke lulluɓe zuciyarshi, bai tsaya ako ina ba sai a ƙofar wani gida marar fasali a ido, bakinshi ɗauke da sallama ya shiga gidan bugun zuciyarshi na ƙaruwa sosai, ilaikuwa abin da yai gudu ne ya faru, daga shigowarshi wa ta mata marar fasali tai wuf tare da fitowa daga ɗaki tana ɗaura zaninta da ke kuncewa, kayan jikinta duƙun-duƙun kamar me suyar ƙuli, haƙiranta yalo shar a waje yayinda kanta kamar sheƙar tsuntsu, cikin ɗaga sauti kamar me magana da maƙota ta ce.

   "Kai Suhailu shine ɗan tsabar barbaɗa da iskanci sai yanzu zaka dawo gidan?."

   Hakan da tace bai wadaceta ba sai da ta haɗa da warce kuɗinda ya fiddo daga aljihunsa har lokacin tana zaginsa, lumshe ido yayi kawai yana jin zafi a zuciyarsa.

   Lissafa kuɗaɗen ta yi, sannan ta ware wasu ta maƙale a hamata, tana ci gaba da lissafa sauran wani matashin saurayi ya shigo gidan ya yi shiga irinta wiziy kannan yasha aski irinna banza.

   "Oh Mommcynah ki ce na shigo da sa'a to abani nawa kason."

   Ya faɗi daidai lokacinda ya ƙaraso tare da wartar wasu daga cikin kuɗin ya hau lissafi.

    Buɗe ido Suhai ya yi, yana jin wani abu me kama da takaici na danneshi a game da guy ɗin, ko kaffara ba zaiyi ba idan ya rantse akan sanda ya fita daga gidan shi yana can yaba shan barcinsa.

    "Kai gaskiya Suhail kana ƙoƙarifa, wallahi Allah sai da kai, ai ina faɗa ma ki Mommcy idan ba me girma Suhail babu mu dan tuni zamu mutu murus."

    Bai aje zancen ba ta hayayyaƙo ma shi tana faɗin.

    "Ubanka ne zai kashe mu ko, to ƙarya ne wallahi, ko da shi ko babu shi tsaf zamu rayu, yo Allah na tuba wannan har wa ta moriya ya ke mana, har yanzu bai biyamu koda kwatan abin da mu mukai ma shi ba."

   Sai kuma ta maida kallonta ga Suhail bayan ta gama ƙidayar kuɗaɗen ta miƙa ma shi wasu ƴan kaɗan tana faɗin.

   "Yakamata kasani har yanzu baka biyamu koda kwatankwacin rabin wahalar da mukasha ta rainonka ba, dan haka Suhail dole kana da biƙatar kayi kuɗi, kayi kuɗi badon kanka ba sai dan ka inganta rayuwarmu, ba kai ke da kanka ba mu keda kai, saboda mune muka tsinceka muka kuma raineka."


Wani abu ne me kama da dutse ya taushe zuciyar Suhai, nan take idanuwansa  suka sauya launi zuwa jajaye, wani abu me kama da ruwan hawaye na taruwa a cikinsu, cukin nauyin zuciya ya buɗe baki ayanayi marar daɗi ya ce.

    "Umma, dan Allah!, dan Allah koda sau ɗaya ne ki kirani da ɗanki, zan ji daɗi, zan samu ƙwarin gwuiwa, sannan nayi miki alƙawarin zanzama abin da kike so a rayuwa, lokaci ne bai yi ba har yanzu, amma da zarar lokacin yayi zan wadata ki, zan inganta rayuwarki ingatattanki."

    Cike da yaƙini da fata ya yi maganar yana kallon fuskarta, sai ji yayi ta matso kusa sosai da shi, tare da ɗaura hannunta akan ƙirjinsa, sannan ta ce.

    "Suhail ɗana, sai de banice wacce ta haifeka ba, kai ɗana ne Suhail amma ɗan tsintuwa karka manta cintatsoyar mage bata mage, kai ɗin kamar bawane a gareni, zaka yi min bauta iya bauta, zaka wuni nema badan kanka ba sai dan ni, kai bawana ne ba ɗana ba."

  Tana gama faɗin hakan taja da baya tare da ɗaura murmushin mugunta akan baƙar fuskarta tanajin ranta ƙal, musamman da yau kasuwar tai kyau.

   "To Mommcy ni zan ware dama kinga na kwan biyu ban kora me sanyi ba, idan Suhai ya dawo da rabaje anjima akirani dan Allah, karkuma kice kin manta dan nasan halinki da mugunta, tsaf zaku tsige ɗan naman ku kasa ke da waɗancan munafukan ƴaƴan naki ki cinye banda ni, ni na ware."

   Yana gama faɗin hakan ya juya yana wani bubbuɗawa irinna gayu, kiran sunanshi wanda ya kira da Mommcy ta yi, amma yai biris.

     "Hamza, baka ji Umma na kiranka ba."

Sai a lokacin ya juyo fuskarshi na canzawa da ɓacin rai, aɗan hasale ya ce.


   "Haba dan Allah Suhail taya zaka dinga kirana da wannan suna irinna ƙauyawa ka kira ni da  Handsone, ko kuma ka samu wani sunan me daɗi ka dinga kirana da shi, banason wannan baƙauyen sunan marar daɗi bana so Suhail."

Sai da ya tattare naman goshinsa waje guda sannan ya ce.

   "Idan kuma Hamzan bakina ya iya faɗa ba, sai ince da kai ya?."

   Ya yi tambayar da yanayin raini wayo tare da tsare Hamza da birkitattun idanuwasa masu cike da kwarjini.

    Tsaki Hamza ya saki baice komi ba ya juya ya fice, yana jin zafin kwarjinin da Suhail ke yi masa.


"Oh ni Binta naga takaina, ka haifi ɗa baka haifi halinsa ba, Allah dai ya shirya min kai ɗan asali."

   Sai kuma ta juya sashen Suhail tare da faɗin.

  ."To kai Suhailu sai ka tafi nema ko, Allah ya bada sa'a, yau de banwani ɗaura tukunyaba, dan Auduwa bayanan bai dawo ba, waɗannan kuɗin kuma zangi zubin dashe da su, idan ka nemo wasu ka kawo sai anjima nayi mana sanwar yanzu dai kayi haƙuri."

   Baice komi ba illa kallon wajenda aka keɓe dan yin girki da yayi, daga inda ya ke yana iya hango suracin da ke fitowa daga yar hudar saman murfin tukunyar, kallon wajen ta yi itama sannan ta ce, tana wayancewa.


"Ka tafi mana ka tsayamin a kai ƙerere, sai ka dawo, amma kasa a ranka ni zaka fita nemowa ba kanka ba, ba zaka mallaki komi ba a rayuwa sai bayan ka wadatani ka biyani ladar rainon da nai ma ka."

Zuciyarshi a cunkushe ya soma takawa yanajin wani abu na dunƙulewa a ƙirjinsa, bai tsaya ba sai da ya fita daga gidan, a ƙofar gida ya tsaya tare da dunƙule hannayensa da ƙarfi ya soma shaƙar iska yana fesarwa daga bakinsa haɗi da fitar da huci, tazbihi ya soma yi har ya samu nauyin ƙirjinshi ya ragu sannan ya soma taka dogayen ƙafafuwansa yana yin nesa da unguwar, bai tsaya ako ina ba sai a bakin shiga wani haɗaɗɗen ƙaramin restaurant, yakai mintuna biyu a bakin shiga wajen yana kallo kayan jikinshi, shi kanshi sai da ya ji ƙyanƙyamin kanshi ya kama shi, ga zafin cefane da yatsun hannayensa ke yi, hakanan ya daure bayan ya saddar da kanshi a ƙasa ya shiga wajen, daidai wajen da aka tanada dan ma'aikata ya nufa, yana hango tarin kwanikan da aka aje dan wankewa, numfashi ya sake ja da ɗan ƙarfi ya kuma fesarwa bayan ya cika bakinshi da iska sannan ya ƙarasa wajen yana ƙaƙƙalo ɗan guntun murmushi a saman pink lips ɗinshi da suka bushe, a saidai lokacin da wani me sanye da riga fara irinta kuka ya tarbeshi da faɗin.


   "Ah Suhail sai yanzu ka samu ƙarasowa, sannunka da zuwa yaukan akwai tarin aiki wallah, dan yau kasuwa tayi riba yanzu haka wajennan cike ya ke da mutane, ga aikinka can ya taru."

   Ya yi ma shi maganar lokacinda ya ke yi mashi nuni da tulin wanke-wanke kuma yana bashi hannu alamar suyi musabiha, sai Suhai ya girgiza kai tare da faɗi a taƙaice.

   "Assalamu alaika, kayi haƙuri hannuna babu kyau, wallahi sai yanzu na samu kaina, amma yanzu zangama aikin da yardar Allah."

Daga haka bai sake cewa komi ba ya nufi wajen haɗi da soma aikinsa bakinsa bai huta ba da ambaton Allah, sannan nauyin ƙirjinsa da maganganun Binta suka asassa ya soma kwararewa.....✍🏻


Alhamdulillah, Ayau Allah ya nufe ni da fara sabon littafi, Allah yasa yanda na fara a sa'a ingama lafiya...

Ina taya ɗaukacin al'umar musulmai barka da sallah Allah ya maimaita manah ya gwada mana wa ta shekarar.


DOKA❌❌❌

Ban amince a sauya min koda kalma ɗaya ba tare da izini na ba, wannan littafin mallakina ne, ban yarda a sarrafashi ta ko wane sigaba ba tare da amincewata ba.


NICE TAKU

MARYAM STAR⭐⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post