RAGAYAR DUTSE page 4 By Nana Haleema


 RAGAYAR DUTSE.

           ©️ Nana Haleema.

https://whatsapp.com/channel/0029VbC1pVN42DcoY0dAzq46

Book 1

Page 004.

Da mamaki Baba yake kallon ta jin abinda take faɗa, ya yi shiru ya zuba mata ido har ta gama bayaninta yana girgiza kai.

Ya bita da kallo ya ce, "Maimuna kin san abinda ki ke faɗa kuwa?." 


Umma ta kalle sa ta ce, "na sani mana." 


Baba ya ce, "kuma kina cikin hankalinki?." 


Itama da mamaki ta ce, "in bana ciki ai bazan faɗa ba. "


Baba ya ce, "na fi tunanin bakya hankalin naki, dan mai hankali bazai faɗi abinda ki ka faɗa ba. Cewa ki ke yi za ki tura Safeera ƙasar waje aiki, a gidajen fararen fata fa." 


Umma ta ce, "eh haka na ce. Kuɗi ake samu, kai ka san ba halin aurar da ita muke dashi ba. In ta je ta yi aikin koda na shekara ɗaya ne, abinda ta samu ba sai a aurar da ita dashi ba?." 


Baba ya girgiza kai cikin mamaki, dan shi gani yake kamar bata cikin nutsuwarta, ya ce, "Safeera za a tura aikatau wata ƙasar? Ni tantama nake yi; anya kina cikin hankalinki?."


"Haba don Allah, ina hankalina mana, mahaukaciya ce ni?. Duk wata akwai gidan da ake biyan miliyan ɗaya a kuɗin nigeria, ko da dubu ɗari biyar za a dinga bata, a wata sha biyu nawa mu ke dashi?. In ta je ta yi na shekara ɗaya ba sai ta dawo ba?. Wannan banzar tashar da suke aiki ita da Islaha uwar me suke samu? Tashar tasu har yanzu bata wani ɗaukaka ba, albashin bai wuce dubu hamsin ba. Kai kana gida ba aikin kirki ka ke yi ba, nima ɗan buge-bugen da nake yi ba samu ake yi ba. Ga yara, ga Safeera budurwa wacce aka yiwa baiko, shi kansa wanda zata aura ɗin ba wani abin hannu ne dashi ba. Ya ka ke so na yi?."


Baba ya girgiza kai ya ce, "kuma kawai sai na sallama ƴata ta tafi wata ƙasar aiki, saboda a kaina aka ƙare talauci ko?." 


Ta yi shiru bata ce komai ba, Baba ya gyara zama ya ce, "Ai wallahi ko bara nake yi akan titi, bazan amince Safeera ta yi aikatau a garin nan ba, balle har sai an bar ƙasar nan. Ita woman leader ɗin da ta zugo ki, ki faɗa mata ita ta tura ƴaƴanta mana, sai ke za ki tura naki dan baki da hankali?."


Umma ta ɗaure fuska ta ce, "ina fa da hankali Malam, ka daina cemi bani da hankali. Kuma in Safeera ta je aikin nan ai cigaban mu ne."


"Cigabanki dai, amma ni ban dani. Kuma baza ta je ba, wallahi Allah Safeera baza ta je aiki wata ƙasar ba, matuƙar ina da rai ina numfashi. Ke ko na mutu ban yafe ba in ki ka turata. Tunda na lura abin naki ya tashi daga na masu hankali, ya tsallaka ya koma na mahaukata."


"Ka ji ai, matsalar talaka kenan wallahi. Baka dashi ka ce baza ka bi hanyar samu ba." 


Baba ya girgiz kai bai ce komai ba, dan ba ya so ya biye mata saboda yara, ba ya son yin abinda zai bar musu suna tunawa dashi.


A lokacin Safeera ta shiga da sallama cikin hijjab. Baba ya amsa yana kallonta, ta durƙusa ta ce, "Baba zan miƙawa Islaha wainar fulawa na dawo."


Baba ya kalli agogo ya ce, "ƙarfe tara ta yi Safeera, in kin je ki dawo, ban da zaman hira." 


Ta yi murmushi ta ce, "To Baba" ta faɗa tana miƙe ta fita. 


Umma ta ja tsaki ta ce, "yarinya budurwa kamar wannan ace baza a amfana da ita ba. Woman leader ƴaƴanta ne suke kawo mata kuɗi kullum, kuma ba neman maza suke yi ba, da dabara irin ta mata suke samu su kawo. Amma ni aiki na ce zata yi ka ce baza ta yi ba. Ni sai na wanke ƙafata na tafi, ai baza a hana ni ba!. In ka hana ƴarka, ni ai ba haifata ka yi ba!" Ta faɗa tana miƙewa.


Baba ya ce, "Allah ya kai ki lafiya, ƴaata dai baza ta je ba wallahi." 


Mama ta fita suka haɗu da Safeera tana kwashe kayan wankin da suka zube ƙasa saboda iskar sanyi.


Umma ta kalle ta ta ce, "Ke kina son zuwa ƙasar waje aiki?." 


Da mamaki ta ce, "Umma wanne aiki kenan?."


"Aikin Saudia, na gidan larabawa ko turawa.Kina so?."


Safeera mamaki ya hana ta magana, ta dinga bin Umma da kallo ganin yadda ta canja kamar ba ita ba. 


Umma ganin ta tafi tunani sai ta dafata, ta ce, "a wata ana samun albashi kusan miliyan ɗaya, to in ki ka je ki ka tara kuɗin ba sai a zo a ajiiye, kin ga in bikinki ya zo an huta da babu wannan babu wancan. Kin san ba ƙarfi ne da ni ba, babanki ma haka. In ki ka je ki ka samo kuɗin, sai a rufawa juna asiri. Shi kansa Saleem ɗin naki ba kuɗi ne dashi ba, kin ga sai a taimaka masa da wani abun in an samu, ko ya ki ka gani?."



Safeera a sanyaye ta ce, "Umma wai da gaske ki ke?."


"Da gaske nake mana. Kuɗi ake samu, musamman ke da ki ke jin turanci, za ki iya zama a ko ina. Ga ki fara, kyakykyawa."


"Umma ni bani da ra'ayin zuwa aikatau wata ƙasar gaskiya." 


Umma ta yi murmuahi ta ce, "jeki ki kai mata ki dawo mu tattauna, bazan bar wannan alkhairi ya wuce mu ba. In ki ka yi katari ki ka samu gidan aiki a saudia riba biyu, ga ki a garin ma'aiki, ga kuɗi, sannan ga labarawa da kyauta. Me ki ka manta?." 


Safeera ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba ta fita, dan ta ga yanayin Umma baza ta fahimce ta wuri ba.



      Islaha tana zaune a kan kujerun da aka yi su na gini a compund ɗin gidan sanyi yana ratsata, ta ƙanƙame jikinta tana rawar sanyi cikin rashin mafita. 


Ta kalli ƙofar da zata kai falo, ta ɗauke kai tana lumshe ido tana jin numfashinta yana yin sama. 


Ta san ko me zata cewa Mama baza ta bar ta ta shiga ba sai ta ga dama. Mama indai akan kuɗi ne bata ɗaga ƙafa, bata damu da inda zaki samo ba, ita dai kawaai  ki bata shine kwanciyar hankalinta. 


Sau da dama Islaha tana ji har gwara zaman gidan marayu akan gidan Mama. Can babu mai takura mata ta kawo kuɗi, in ta gama abinda take yi ta dawo ta kwanta shikenan. 


Duk da can ɗin ma akwai ƙananun ƙalubale, ta buɗe ido kawai ta ganta a gidansu Saheer, bata san ya aka yi ta amince ta biyosa ba. Dan ta san a dokar gidan marayu, in dai mutum zai yi adopting ɗinka, kuma ka wuce shekara sha biyu, dole sai da amincewarka kafin hukumar gida ta yarda. Balle ita, da ta kusa gama university a lokacin. 


Da kanta ta amince masa ta biyosa, ba ta san meyasa ya yi adopting ɗinta a lokacin ba, ta san shaƙuwar da suka yi ne sila, amma wani lokacin tana danasani.


In Mama ta yi wani abun, sai ta ji kamar ta haɗa kayanta ta koma, duk da ta san baza a karɓe ta ba, kamar an yaye ta ne. Amma tana da yayyun da ƙawayen da suka tashi tare, suka yi aure a manyan gidajen da zata iya zuwa can ta zauna. Kawai bata son zubawa Hamma ƙasa a ido ne, da wata ran sai dai ya buɗe ido ya ga bata nan.


Ɗankwalinta ta jawo ta rufe kunnenta ta jin sanyi yana shigar mata kunne ta ko wanne ɓangare. 


Buɗe gate ɗin aka yi aka shigo, sai ta ɗaga kai ta kalli wanda ya shigo. 


Safeera ta gani, ganinta a zaune a wajan sai ta ƙaraso da roba a hannunta ta ce, "Islaha lafiya ki ke zaune a nan? Kin san dai wajan nan ba wajan zamanki bane, tunda ba cikakkiyar lafiya ce dake ba ko?." 


Islaha ta kalle ta tana ƙanƙame jikinta ta ce "Safeera Mama ce ta ce in fito na zauna."


"Akan me?."


"Akan ban kawo kuɗin ba, kuma bani da kuɗin ne shiyasa. Da meye dubu goma ko ashirin da na bata?."


Safeera ta zauna kusa da ita, cikin fusata ta ce, "Amma Maman nan ƴar...." 


Islaha ta dakatar da ita ta ce, "kar ki zage ta Safeera, ta yi min abinda babu wanda ya yi min irinsa a duniya. Duk da ba zaman daɗi nake yi ba, amma babu laifi ina kwana na tashi har na ci na sha. Ɗanta kamar shine bangona, shi nake kallo a matsayin Yayana, aboki, kuma mijin da zan aura. Ta cancanci girmamawa ko ya ya ne."


Safeera a ƙufule ta ce, "to neman maza take so ki fara ko me? Haka kawai namiji zai ɗauki kuɗi ya ba ki ba tare da kin bashi wani abun ba?."


Islaha ta ce, "duk yadda ki ke tunanin Mama akan son kuɗi ta wuce haka. Ita gani take yi haka yaranta suke yi, tunda suna fita su samo mata."


Safeera ta yi tsaki ta ce, "to ki zo mu tafi gidan mu kawai, in ba haka ba kin san sanyin nan zai cutar dake."


Ta girgiza kai ta ce, "a'a, ƙyale ni kawai Safeera. Me ya fito dake a daren nan."


Ta miƙa mata pack ɗin ta ce, "Wainar fulawa ce, na soya shine na kawo miki."


Islaha ta karɓa ta ce, "kamar kin san tun jiya nake muradin cinta wallahi, sai dai sanyin nan bazai bar ni ci ba." 


Safeera ta ce, "ki zo mu tafi gidanmu, yanzu numfashinki zai riƙe, kin san yanayinki kamar na masu asthama."


Islaha ta ce, "ki bari kawai Safeera, na tabbata yanzu zata ce na zo na koma. Ki je gida, dare ya yi kar Baba ya yi miki faɗa."


"Ya san na fito ai, kuma in dai tare dake ne ba ya  yi min faɗa." 


Islaha ta bita da kallo ganin fuskarta babu walwala ta ce, "wai me ya faru?." 


Safeera ta ce, "Umma ce Islaha, wai zata tura ni aikatau ƙasar waje." 


Islaha ta zaro ido ta ce, "kamar ya?."


"Kamar yadda ki ka ji, kuma na san Mama ce ta zugata."


"Tabbas kuwa, dan ɗazu tare na dawo na tarar dasu a falo, kuma na san itace zata yi mata maganar."


"Lamarin Umma ai sai a hankali, ita bata ga bata tura nata yaran ba sai ita zata zugata tura ni?."


Islaha ta ce, "me ki ka ce to ke?." 


Ta kalle ta ta ce, "kema kin san ai bazan amince ba. Ni anya topic ɗin mu na ranar monday baza mu sake maimaitawa akan hakan ba?. Abin ya yi yawa Bestie, iyaye basu san inda yaransu suke zuwa ba, kawai kina nan kin tura ƴarki budurwa tana wata ƙasar aiki. Babu abinda ya dame ki da a hannun wa ta sauka, aikin me take yi, waye yake bata kuɗin, duk babu ruwansu. Kawai ta turo musu kuɗi. Wannan abun yana taɓa zuciyata Islaha, kuma wallahi iyaye mata sun fi wannan katoɓarar


Islaha ta ce, "hmmm! Kamar na fi ki tsanar wannan abun nan Safeera. In kin ga ƴan matan da Mama take turawa ƙasar waje sai abin ya ba ki mamaki. Kuma laifin iyayensu ne, sune suke bada damar wannan ɓarakar wallahi. Kuma da wahala ki ga uba mahaifi ya aikata irin haka, kamar yadda ki ka ce matan ne dai. Dan su za ki dinga gani a wajan Mama, ana washe mata baki zata kai ƴarsu Saudia. Zan yi magana da Chairman, zamu sake saka wannan a cikin topics ɗin mu in sha Allah."


Safeera ta ce, "gwara mu sake tattaunawa, dan da yawan yaran ba so suke yi ba, iyaye mata ne suke takura musu."


Islaha ta girgiza kai ta ce, "da na je aikatau wata ƙasar ba gwara na yi bara ba, Allah ya kiyaye." 


Safeera ta ce, "Amin Islaha. bara na wuce, sai mun haɗu gobe."


"Kamar kin san Chairman ya kira ni, wai yana so gobe na je da wuri zamu tattauna akan wata magana." 


Ta yi ƴar dariya ta ce, "Chairman dai yana ciki, amma na san bashi da space, wajan Hamma Saheer ne." 


Ta yi murmuahi ta ce, "gaskiya ne, bana iya kallon ko wanne namiji da fuskar soyayya sai Hammana, ina sonsa sosai Safeera." 


Ta yi dariya ta ce, "ya cancanta ki so shi ai Bestie, ya yi miki komai a rayuwar nan." 


Safeera ta miƙe ta ce, "sai mun haɗu, don Allah ki samu ki shiga ciki." 


Islaha ta ce, "To bestie, ki kwana lafiya." Daga haka suka yi sallama ta fita.


Wainar fulawar take son ci amma baza ta iya ba, sanyin ratsa ta yake yi, ga sauro da ya fara kawo mata hari. Duk da wajan akwai haske amma sauro ya dame ta sosai. 


Ta miƙe ta ƙarasa ƙofar sai ta tarar an kulle ƙofar,  ta ɗan yi knocking aka yi mata banza, kuma tana jin motsinsu. Ajiyar zuciya ta yi ta zauna a wajan tana tunani kala-kala.



     "Islaha!" 


Ya faɗa yana ƙarasowa wajan da sauri. Ta kalle sa, bata yi magana ba har ya ƙaraso. Ya bita da kallo ya ce, "me ki ke yi a wajan nan a zaune ga sanyi? In ki ka samu attack fa?."


Islaha ta karyar da kai, cikin shagwaɓa ta ce, "Mama ce ta ce in fito." 


Da mamaki ya ce, "ki fito kuma, to akan me?." 

Ta girgiza masa kai alamun bata sani ba. 


Ya ɗan yi tsaki ya ƙarasa yana buga ƙofar falon Mama amma aka ƙi buɗewa. Ya kira Maman a waya bata ɗauka ba, ya kira ƙannensa duk suka ƙi ɗauka. Ya dawo kusa da ita ya ce. "Taso."


Ta miƙewa tsaye, ya riƙe mata pack ɗin ya ce, "mu je ɗakina ki zauna, in wannan sanyin ya yi miki illa fa, mai lafiya ma ya cika balle ke?." 


Islaha ta bi bayansa, a hankali dan gaskiya bata son sanyi, tana da wani irin ciwo kamar asthma, duk da Hamma ya ce asthma ce, dan alamominta gabaɗaya ya bayyana a kanta, amma an je ayi test an ce babu. Hamma dai ya ce ƙarya suke yi, asthma ce da ita.


Ɗaki ne babba mai ɗauke da gado da komai na kayan gado, gashi a gyare babu tarkace sai takalmansa da laptop ɗin da yake aiki da ita. 


Ya nuna mata gefen gadon ya ce, "ki zauna." 


Ba musu ta zauna ya ce, "me zaki ci?." 


Ta fara sosa kunnenta da sanyim ya shiga ta ce, "Zan ci wainar fulawa, Bestie ce ta kawo....." ta kasa faɗa saboda atishawar da ta zo mata.


Saheer ya fusata, cikin faɗa ya ce, "meyasa ba ki zo nan kin zauna ba za ki bari sanyi ya yi mili illa? Gashi nan har kin fara atishawa, kin manta kina da asthma ne?. Haba Islaha, meyasa baza ki faɗa min ba?." 


Cikin sanyin murya ta ce, "ka yi haƙuri. Kuma har yanzu ba a tabbatar asthma ba ce."


"Ni na tabbatar. Ƙarya likitocin suke yi, duk wanda ya ga yadda ki ke yi ya san itace."


Ya sake yin tsaki ya ce, "ki ci wainar, zan fita na samo miki magani. Akwai ruwa a fridge ki ɗauka ki sha. Akwai abinda ki ke so in kawo miki?." Ta girgiza kai alamun babu sannan ya fita.


Tashi ta yi ta buɗe fridge ta ɗauki ruwan da babu sanyi sosai. Ta dawo a hankali ta zauna ta fara cin wainar ta hankali a kwance. 


Bayan ta gama ta wanke hannunta ta goge da tissue ta sha ruwa. 


Tana zaune ta yi shiru sai ta ji wayarsa da ya bari tana ƙara, ta duba gefenta ta ganta ajjiye, sunan boss yana yawo a kai. Bata ɗauka ba ta ɗauke kai, ta saka hannu ta jawo bedside drawer ba tare da zata yi wani abun ba. 


Har zata rufe sai ta sake buɗewa ganin abinda yake ciki, ta saka hannu ta takadar tana kallo. Copy visa ne na mata da yawa, ta dinga bi tana karantawa wasu an tura su ƙasar larabawa, wasu ta turawa. Amma ƴan Saudia duk sun fi yawa. 


Ta girgiza kai ta ce, "Hajiya Mama, ashe abin ya bunƙasa haka."


A lokacin ya buɗe ƙofar ya shigo, ta kalli ƙofar shima ya kalle ta, ya ƙaraso ya ce, "har kin gama ci?." 


Ba tare sa ta mayar da abinda ta ɗauko ta ce, "na gama." 


Ya bata magani ya ce, "ki sha." Ba musu ta sha maganin, takardun suna cinyarta. 


Ya kalli abinda ta ajjiye a jikinga ya ce, "kina kallon copy visa ne?." 


Islaha ta ce, "uhum, kawai na gansu ne. Na ce ashe Mama har kai take bawa ajiya." 


Ya yi murmushi ya ce, "Hajiya Mama kenan." 


Ta yi murmushi ta ce, "Chairman ne ya kira ni dazu, wai gobe yana son ya yi magana dani."


Ya kalle ta ya ce, "wacce magana kenan?."


"Ban sani ba, amma na san baza ta wuce akan Rehaan Yola ba."


"Rehaan Yola da na sani, nake jin sunansa a gari?."


Ta ɗaga kai ta ce, "Shi fa, ya matsa yana so mu yi hira dashi a channel ɗinmu. Ya dame ni akan ni zan kai invitation card ɗinsa, ko ta ya zai amsa gayyararmu ma oho."


"Daman ba mail ku ke turawa guest ɗin ba?."


"Mail ne mana. Shi sau nawa ana yi masa mail? An yi ya fi a irga, bayan shi har wani Jafar ake yiwa duk a banza. Shine za a je a kai masa Iv."


Ya bita da kallo ya ce, "To Ray ɗin ya dawo Nigeria ne? Ba fa a nan yake rayuwa ba, ance a Uk ne ko Us ban sani ba." 


Ta taɓe baki ta ce, "waye ya sani? Tunda ka ji yace nazo maybe ya ji magana akan zuwan nasa. Yana son yin hira dashi, ni kuma nasan bazai amince ba."


Saheer ya yi murmushi ya ce, "ke kin san waye Ray kuwa? Daga ranar da ya je tv ku, ko ya gayyace ku ai kun gama ɗaukaka Islaha. Har yanzu bai taɓa hira da wata channel a Nigeria ba, shiyasa ko wacce channel take marmarin ta fara hira dashi."


Cikin ko in kula ta ce, "Ni fa wallahi ban taɓa ganin hotonsa ba, ko maganarsa na ji ana yi zan wuce bazan kalla ba. Ba wai dan baƙin ciki ko hassada ba, ni bai yi ba Hamma. Bana son mutumin da ya cika ɗaukaka da yawa, kuma yana banzatar da mutane. Kuma ance yana da abubuwan cigaban da in ya kawo Yola, zamu zama na farko a Nigeria da aka fara samu. Amma ya tare a ƙasar turai." 


Ya yi dariya ya ce, "ke waye ya faɗa miki?." 


Ta turo baki ta ce, "haka na ji an ce."


"Haka ki ka ji, dan haka baza ki ɗorar ba. Ban taɓa ganinsa, ba amma ana faɗa halayyarsa masu kyau. Kuma ya kawo babban asibitin da babu kamarsa a nigeria, kuma ga kasuwar zamanin da in ki ka shiga zaki ce a dubai ki ke. Ai mun je dake kin ga yadda take, zan ɗauke ki mu je asibitin ki yi kallo."


"Ni fa ba wani burge ni yake yi ba, in na je ma bazan gani ba."


"A'a matar Hamma. Ki faɗi gaskiya."


Ta yi dariya ta ce, "shiyasa ake so na kai masa  invintation da kaina. Tunda sun ce ina da sa a, ban taɓa gayyatar wani ya yi denying ba. To ni kasan bana son raini ka sani, in ya yi min wulaƙanci wallahi ba ƙyalesa zan yi ba. Ka san halina, bana ɗaukar raini. Tsaf zan yi tsalle na gaggaura masa mari."


"In ya saka aka zane masa ke babu ruwana."


"Ina da kai, zaka rama min."


"Gaskiya ne, babu mai taɓa ki ya kwana lafiya."


Ta yi dariya. Saheer ya ce, "Ba dan kar na rantse ba, da na rantse da Allah sai ya yi accepting ɗinki, kin san meyasa?." 


Ta girgiza kai tana murmushi, ya kalli idanunta ya ce, "saboda daga jininki abin ya ke, Allah ne ya baki ba wani ba, matar Hamma." 


Murmushi ta yi tana rufe fuskarta cikin jin daɗin abinda ya ce. Shima murmushi ya yi yana kallon ta cikin soyayya, kafin ya miƙe ya ce, "zan fita, zan koma wajan Sadik mu kwana tare." 


Ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce, "fita zaka yi?." Ya ɗaga mata kai yana kallon idonta. 


Ta shagwaɓe fuska ta ce, "ni kaɗai zan kwana? Allah tsoro nake ji." 


Ya ɗan matso kusa da ita ya ce, "to ya ki ke so ayi, Debbo am?."


"Ka zo mu kwana, sai in kwanta a kan floor."


"Sai ni na kwanta akan gadon ke kina ƙasa?" Ya faɗa yana bin fuskarta da kallo. Ta ɗaga masa kai kamar ƙaramar yarinya.


Ya yi murmushi, tare da jan hancinta ya ce, "A'a Debbo am, zan je mu kwana da Sadik, ke ki kwana a nan." 


Cikin shagwaɓar da ta saba yi masa ta ce, "ni dai A'a, Allah bazan iya bacci ba." 


Ya sake yin murmushi ya ce, "tsoro ki ke ji?." 


Ta ɗaga kai alamun eh. Ya ce, "babu abinda zai same ki, ki kwanta kin ji."


"Ni dai a'a, don Allah ka kwanta kawai."


"islaha bazan kwana a nan ba."


"Meyasa?."


"Akwai shaiɗan Matar Hamma, gwara na baki space, zan dawo da asuba in sha Allah."


"Ni ba ƙanwarka ba ce? Ai babu komai." 


Ya yi dariya ya ce, "ƙanwar Hamma. Na san ke ƙanwata ce, kar ki damu babu abinda zai same ki." 


Ta yi shiru bata ce komai ba, ya san bata yarda ba kenan. Ya sake yin dariya ya ce, "za mu kwana tare wata rana, ranar ba sai kin ce min in zo mu kwanta ba, da kaina zan riƙo hannunki mu kwana tare. Na yi miki wannan alƙawarin, indai ranar nan ta zo zan tuna miki. Kin san me zan yi?.


Ta girgiz kai tana ɗan murmushi, kanta yana ƙasa saboda kunya. 


Saheer ya ce, "bazan bari ki kwanta akan komai ba, ni zan zamar gadonki kuma pillow ki. Alƙawari na ɗaukar miki, kuma zan tabbatar miki dashi, Debbo am!." 


Islaha ta ji kunya mai tsanani, ta juya masa baya harda rufe fuska da hannunta. 


Ya yi dariya ya ce, "kina da aiki gobe matar Hamma, ki kwanta sai da safe. Ki kulle ƙofar kin ji? Sannan kar ki yi alwala da ruwan sanyi." Ta ɗaga masa kai ba tare da ta juyo ba.


Ya ce, "to ki juyo na ga fuskarki sai in tafi." 


Ta noƙe kafaɗa ta ƙi, ya ce, "ki juyo na ganki." 


A hankali ta juyo kanta yana ƙasa, ya yi dariya kaɗan ya ce, "ki kwana lafiya." 


Ta ɗaga ido tana kallon kyakyawar fuskarsa, mai cike da kwarjini ta ce, "Allah ya tashe mu lafiya."


"Amin matar hamma" ya faɗa yana niyar fita. 


Sai ta ce, "Hamma!." Ya tsaya cak yana kallon ta, ta juya ta ɗauki wayarsa ta ƙarasa kusa dashi ta miƙa masa, ta ce, "ka manta wayarka." 


Kafin ya karɓa sai da ya bi hannunta da kallo sannan ya sake kallon fuskarta, ya murmusa ya ce, "Thank you matar Hamma." Murmushi ta yi ya ja ƙofar ya fita.


Islaha da murmushi ta zauna a akan gadon tana kallon ɗakin. Tana jin daɗin yadda ba ya zaƙewa akanta, soyayya yake yi mata mai tsafta ba ya zaƙewa irinta zamani. 


Yadda ya ce saboda shaiɗan ɗin nan ba ƙaramin daɗi ta ji a ranta ba, dan sai mai hankali ne zai tuna da hakan har ya faɗa. 


Shiyasa a kullum take ƙara ƙaunarsa har zuciyarta, domin bata da kowa sai shi, kuma yana yi mata so na tsakani da Allah, ba ya tunawa da ita ɗin a gidan marayu ta tashi. Yana yi mata so mai tsafta, wanda zata bugi ƙirji ta ce ita matar so ce a ko ina. Da wannan tunanin ta ɗan kwanta, tana sake kallon ɗakin dan bata taɓa jimawa haka a ciki ba.


_Book 1 free ne, Book 2&3 paid ne akan naira 1k kacal. Pay into Sadiya Nuhu Mukaddas 5903999117 Moniepoint MFB. A tura shaidar biya a wannan number 09030398006 ko 0701 809 8175._



Nana Haleema✍🏻

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post