I just published "Chapter 17-18" of my story "JIN DAƊIN RAYUWA"::https://arewapen.com/chapter?id=6a0c796514ca64ab57321bf5
💋💋💋💋💋
*JIN DAƊIN RAYUWA*
(Romantic story 🔞)
Mom Islam
*LAST FREE PAGES*👌
Last zai tsaya a page 19-20
*_ayi haƙuri dan Allah asalin kuɗin littafin gashi nan babu promo na daina idan kinaso ga tsayayyen farashin nan👉 Normal group ₦500 Vip 1k account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank shaidar biya ta wannan number 08141799224_*
Page 17-18
Lokacin da yake ƙokarin kutsa hancin motarsa cikin gidan abokinsa Munir wayarsa ta fara rurin neman agaji,
Miƙa hannu yayi kana ya ɗauko wayar tare da duba mai kiran nasa, yaga sabuwar lamba ce babu suna, dan haka bai ɗaga kiran ba har sai da yai parking motarsa a inda aka tanada, lokacin wayarsa ta sake yin ringing a karo na uku, Zayn ya danna kore tare da kara wayar a kunnensa, mutuwar tsaye yayi saboda jin Muryar Zuhura, sai yake jin kamar wannan Muryar Tata tafi ta ɗazu dadin amo, gashi tana ratsa kowane sassa na jikinsa tare da saukar masa da kasala,
In Cold voice yace "Princess kin koma gida lafiya..?"
Daga can ɓangaren Zuhura tace "lafiya Lau ina fatan kaima haka?"
Zayn yace "ban koma gida ba, naje ziyara ne soon zan koma ki kular min da kanki"
Ya katse kiran saboda an buɗe door na parlon abokinsa Munir,
Matarsa Salma ce ta fito tana sanye da farar abaya wacce tayi mata kyau sosai, Salma fara ce kuma kyakkyawa, sannan tanada tsafta kyau iya kula da miji tare da iya kalami bugu da ƙari wayaiyyar mace ce ta gaban kwatance, shekararsu biyar da aure Ita da doctor Munir, yarinyarsu ɗaya, Mimi, tanada shekaru uku, yanzu haka tana gidan hajiyar Munir, kasancewar idan weekend yazo ranar Friday take tafiya can sai Sunday da yamma ake dawo da ita,
Yanzun ma sunyi shirin fita ne, ta leƙo compound na gidan nasu dan ta duba ko mai bawa Flowers ruwa yayi aikinsa, kasancewar yana yawan fama da zazzaɓi, sai ta hadu da Zayn a bakin ƙofa, kuma yana kawo musu ziyara amma ba koda yaushe ba,
Gidan nasu haɗaɗden gida ne, mai kyau da tsari, tabbas nera tayi kuka gurin ginin wannan gidan nasa, sai dai yana zama anan ne bisa Umarnin mahaifinsa, na wasu dalilai...
Cikin fara'a Salma tayiwa Zayn Barka da zuwa, kana tace masa "Hero yana ciki"
Zayn yayi murmishi kafin yace "Heron ki dai, mukam malalaci ne a gurinmu"
Dariya tayi, ta wuce compound, Zayn kuma ya ƙarisa ciki,
A babban parlonsu ya tarar da Doctor Munir yana zaune saman haɗaɗdiyar Sofa mai ƙyalli brown color sai ƙamshi take fitarwa, bayan yayi sallama ya ƙarasa takowa..
Doctor Munir ya ɗago kansa, kasancewar yana danna waya,
"Ikon Allah ashe dai zan ganka Doctor Zayn..."
Doctor Zayn yayi murmishi kamar dai inda ya saba, kafin yace "gani kuma, sai dai naga kamar anguwa zakuje kai da Madam ko?"
"Eh wlhi wai shan ice cream zamuje madam ta matsa min dole dai na biye mata"
Zayn yace "babu wani ɓoye-ɓoye Allah ya inganta in banda ƙwaɗayi ina Salma ina kayan yara"
Kafin tayi sallama tace "gaskiya Doctor Zayn matarka tanada aiki kenan bazaka dinga kaita guraren shakatawa ba kenan?"
Zayn ya girgiza kai yana duban Salma da take maganar har cikin zuciyarta,
Kiran Zuhura ne ya sake shigowa wayarsa, ya kalli Salma ya kalli Doctor Munir kafin ya ɗan fara motsa lips dinsa, saboda yana cika musu baki da cewa "shifa ba a haifi wata mace da zai so a duniya ba"
yanzu dai ƙaryarsa ta ƙare, suɗuɗu ya miƙe ya fita kamar mai koyon tafiya,
Salma ta matsa kusa da Doctor Munir kafin tace "My hero ka lura da abinda na lura kuwa?"
Munir yayi murmishi tare da jan dogon hancinta yace "keee dai kin cika sa ido budurwa ce ta kirashi, kinga har zufa yake yi yasan ya sharara mana ƙarya"
Zayn na fita ya wuce inda motarsa take, sai da ya shiga ya rufe murfin kafin yabi kiran Zuhura, tana kwance a saman gadon Umma cikin shogoɓa tace "nifa ban gaji da son sake ganin fuskar ka ba, ina so in ƙara ganinka"
Zayn yace "ni fa har gizo kike yimin zanso hakan ta sake kasancewa, sai dai yau babu halin mu sake haɗuwa, saboda zan koma hospital nama fasa zan kira wani abokina ya dubamin, zuwa gobe zan zo insha Allah"
Daga yin maganar ya katse kiran
Zuhura taja dogon tsaki tana kallon Umma dake gefe tana tsara mata abinda zata faɗa,
Turo baki tayi tace "Umma nifa sai naga kamar baya sonsa"
Umma tace "kee Zuhrah har yaushe kuka haɗu da zaki banbance hakan? nidai shawarar da zan baki wlhi karki sake wannan damar ta kufce miki mu samu mu siyi gida mai kyau muma mu futo da capacitynmu kinga dai inda mutane suke ta arziki mu kuma kullum muna cikin talauci"
Zayn yana daga cikin mota ya kira doctor Munir yace masa sai da safe,
Daga nan yayiwa motar key, ada yaso komawa gidan Momy amma ya yanke shawarar ya je hotel ya kwana dan idan ya tuna haɗa aurensa da Jawahir da za'ayi duk sai yaji abin babu daɗi,
Bayan ya gama abubuwan da zeyi ya biya ya karɓi key ya wuce ɗakin da yake so, dan a hotuna aka nuna masa ɗakunan...!
Mom Islam 🍷
