💋💋💋💋
*JIN DADIN RAYUWA*
(Romantic story)
Mom Islam
👉Idan baki da aure karki karantamin littafi na matan aure ne🔞
*LAST FREE PAGES*👌Wannan shine ƙarshen free pages
*_ayi haƙuri dan Allah asalin kuɗin littafin gashi nan babu promo na daina idan kinaso ga tsayayyen farashin nan👉 Normal group ₦500 Vip 1k account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank shaidar biya ta wannan number 08141799224_*
Page 15-16
Bayan Umma ta fita, Zuhrah ta fito dan tabi bayanta,
Tana fitowa sukayi ido biyu da Shahida hannunta riƙe da bokitin ɗibar ruwa,
"Ah Zuhrah ina zuwa da yammar nan?"
Kafin Zuhrah tayi magana Mama tace "Hamm idan tayi wari maji dan wlhi ba banza ba wannan shige da ficen da sukeyi ita da uwarta,
Zuhrah tayi musu Murmishi ba tare da ta kulasu ba tabar musu gidan,
Tana fita bata ga Umma ba, dan tayi mata nisa, sai da tayi ƴar tafiya kana ta iso gurin Malam, Umma tana cikin ɗakinsa, itama Zuhrah ta shiga bakinta ɗauke da sallama,
Malam da Umma suka amsa, Umma tayi mata nuni da gurin zama kusa da ita, bayan Zuhrah ta zauna Umma ta dubi malam kafin tace "malam wannan yaron da yake son Zuhrah yanada nera, so nake a mallake mana shi sai inda mukayi dashi, yaso Zuhura sosai, kuma ya sakar mata kuɗi sannan a rufewa Alhaji baki kar ya sa mana idanu akan duk abinda zamuyi, malam ga wannan babu yawa asiyi goro"
Umma ta zaiyyane wa malam muradinta tana murmishi, Zuhura kam sai jinjina kai take saboda itama hakan take so ya kasance, dan gani tayi, ada tasha wahala kafin ta samu mai sonta, yanzu kuma ta samu tana gudun kar dare ɗaya ya kufce mata, kuma tana tunanin idan har ya kufce mata bazata sake samun kamarshi ba, ga kuɗi ga kyau ga class.
Malam ya ɗauko wani zabgegen carbi, kana ya fara ja, cikin wata iriyar murya yace "haƙiƙa akwai babban aiki Hajiya, idan har ba ayi masa tarko ba, zuwa gaba zai iya rabuwa da ɗiyarki, dan haka zan yi masa maganin da daga shi sai ita ya sota fiye da komai ya mallaka mata abubuwan duniya da dama.."
Wani ƙullin magani malam ya bawa Umma yace Zuhura ta dinga sha a shayi mai Madara da wani turare da zata dinga shafawa idan Zayn yazo hira, yace bazai karɓi kudi yanzu ba sai sunga kamun ludayin aikin, ya ƙara da cewa, maganar aikin Alhaji da ƴan sa ido mai sauƙi ne, suje suyi anfani da hayaƙin Zuhura ta lulluɓa sosai hayaƙin ya turara jikinta,
Umma tayi masa godiya tare da miƙewa ta kama hannun Zuhura suka fice, tun a hanya ta ƙulle maganin da turaren a jikin zaninta, kasancewar kwalbar turaren ƙarama ce,
Har suka iso gida, Umma bata ce uffan ba, tanata saƙe-saƙe a cikin zuciyarta,
Zuhura ce tayi sallama cikin gidansu, Mama da Shahida suna zaune a tsakar gida, da kallo suka bi Umma da Zuhura har suka shige ciki,
Umma ta kama hannun Zuhura a karo na biyu, lokacin da suka shiga ɗaki tace "wannan faɗi tashin da mukeyi a tsakanina dake ya zama sirri, dan wlhi idan naji wata magana ta fito makamanciyar wannan Zuhura sai ranki ya ɓaci"
Zuhura tace "Umma ai taimakona kikeyi kuma Ubangiji zai taimakeki kema"
Umma ta dafa kafaɗarta kana tace "wlhi Zuhura tausayinki da nakeji Shiyasa nake faɗi tashi a kanki, badan haka ba ai bazan wani damu kaina ba, dangin mahaifiyarki basa Nigeria suna Cameron, ada ai acan muke, bayan mun dawo shine Allah yayi mata rasuwa, tsabar wulaƙanci ma ɗan uwanta mutum ɗaya ne yazo yayi gaisuwa, kasancewar ita marainiya ce, tun daga nan babu wanda ya sake waiwayata, Shiyasa nake tausayinki Zuhura, yanzu dai ɗibo gaushi ki fara yin hayaƙi sai ki kira shi Zen din"
Zuhura tayi dariya kafin tace "Umma Zayn sunansa ba zen ba"
Umma tace "ai nayi ƙokari a hakan ma"
Koda Zuhura ta fita harabar gidan, ta samu Mama a gaban murhu tana kwashe tuwo,
Zuhura ta tsuguna ta ɗibi gaushi bayan tayiwa mama sannu da aiki, mama ta amsa da cewa "Yauwa, idan kinkai wutar ki zo ki ɗaukar muku abinci"
Zuhura tace "toh"
Bayan shigarta ɗaki ta ajiye wutar zata fita, Umma ta tambayeta ina zataje, Zuhura tace "Umma mama ce tace inje in ɗauki abinci"
"Mtswww tuwon na ƙaddara ba surfe babu tankaɗe suci kayansu nidai bazanci ba"
Daga can waje mama ta gama aiki zata koma ɗaki dan har tayi alwala ta ƙwalawa Zuhura kira, kai tsaye Zuhrah tace "sun ƙoshi"
Mama ta jinjina kai tare da ɗaukar tuwon taje ta ajiye,
Sai da Zuhrah tayi hayaƙin kana sukai alwalah sukai sallah, sannan aka fara ƙokarin kiran Zayn Dan wayar tasa chaji,...!
🔥Wohoho masoya kuzo mu haɗu a paid group, ehe akwai bidiri, and then idan bazaki jure abinda yake cikin labarin ba ki bamu guri, matan aure gareku💃💃 billahi karki bari ayi tafiyar nan babu ke..
*Normal group ₦500 Vip 1k account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank shaidar biya ta wannan number 08141799224*
Mom Islam
