Jin Daɗin Rayuwa Page 13-14 by Mom Islam


💋💋💋💋

JIN DADIN RAYUWA*

    (Romantic story)

    Mom Islam 


👉Idan baki da aure karki karantamin littafi na matan aure ne.🔞


Page 13-14


Kai tsaye wani babban shopping mall ya wuce da ita, bayan yayi parking suka fito a tare, Allah ya taimakesa kayan jikinsa bai nuna a yanayin da yake ciki ba, siyayya yayiwa Zuhrah sosai, su kayan makeup su chocolate da su biscuit su milo da madarar gwangwani da kayan ciye-ciye su abaya da atamfofi dan ɓangare ɓangare ne a gurin na kayayyaki,


Bayan ya gama ɗauka, aka tura masa kayan gurin biyan kudi, ya miƙa Atm dinsa, bayan an cire kudin aka kai masa kayan gurin mota, ya danna madanni dake a jikin key din motar, Boot ya buɗe aka saka kayan, ya shiga mota suka wuce,


Kafin sukai ga anguwarsu Zuhrah dake RUGAN JULI, ya tsaya a inda ake siyar da waya, ya siya mata I phone mai kyau,


Dalilinsa na biyowa ta hanyar, akwai gidan abokinsa doctor Munir sun shaƙu sosai, yana son yakai masa ziyara bayan sun rabu da Zuhrah dan yana cikin fushi ada, haduwarsa da Zuhrah yasa yaji zuciyarsa ta wanke,


Zuhrah ta fashe masa da kuka a cikin mota tare da yi masa godiya, dan ita kam yau zuciyarta na cike da farin ciki, ko bai bata komai ba zuciyarta tayi fess, 


Sannu a hankali suka ƙarisa ƙofar gidansu, tunda yaga yanayinta dama yasan ba wani kuɗi ne dasu ba, hakan yasa ya girgiza kai tare da shafar gashin gemunsa, ta buɗe murfin motar tare da cewa "fatan alkairi"


Zayn yayi mata murmishi mai kyau, wanda ya sake baiyyanar da pink lips dinsa da ya lasa a hankali, ya buɗe Boot ya fara fito mata da kayan, ledoji biyu kayan suka cinye,


"Babu simcard a cikin wayar, zan baki kuɗi ki siya i think bazan dawo gobe ba"


Zayn yai maganar yana bude murfin motar mazaunin Driver, ya Ciro bandir na ƴan dubu ɗaya ya miƙa mata sabbi fil, 


Godiya tayi masa, 


Zayn ya miƙa mata wani card wanda numbersa da sunansa yake jiki, yace ta kira shi,


Daga nan sukayi sallama ya wuce.


Hannu bibbiyu ta shiga da kaya cikin gidansu bakinta ɗauke da sallama, Umma ta taso da gudu tana dubanta, fuskarta ɗauke da fara'a take cewa "kawo in taimaka miki ƴar albarka shiga ciki da sauran"


Umma na magana tana harar Mama dake zaune a tsakar gida, ta zuba wa ledar dake hannun Zuhrah idanu,


Bayan sun shige ɗaki itama ta miƙe ta wuce nata ɗakin tana girgiza kai, 


Shahida kam tana can islamiya shi yasa bata nan,


Acan ɗakin Umma ta zauna ta mimmiƙe ƙafafu bakinta har kunne tsabar farinciki, tace "ƴar albarka kice magani yayi aiki, dan da ganin wannan siyayyar bata Alhji bace? dan rabonsa dayin irinta tun muna zaman lafiya muna amare nida mahaifiyarki"


Zuhrah tayi murmishi bata cewa Umma komai ba, ta Ciro waya a cikin kwali ta ɗora a saman cinyar Umma, 


Umma ta kwashe da dariya tana jujjuya wayar, tare da sake gyara zama tace ”ƴar albarka bani labarin abinda ya faru bayan fitar ki?"


Zuhrah ta kwashe labarin inda suka haɗu da Zayn da irin mukaminsa da maƙudan kuɗaɗen da ya bata, sannan suka ci gaba da firfito da kayan da ya siya mata"


Umma tace "Masha Allah Zuhrah, tabbas kinyi goshi wannan irin kashe kudi haka? Kuma abin farin cikin Allah ya haɗaki da matashin saurayi mai nera, ashe dai muna da rabon hutawa a duniya, da lahira.."

Duk abinda Umma taga naci ne sai ta gutsura taci taji irinsa, sai santi take tana dariya, daɗi ya kama Umma Zuhrah tayi saurayi, 

Bayan sun gama ciye-ciyensu, Umma ta ɓoye musu wanda bazai ciwu duka ba, tace sai su dinga haɗa shayi kullum da safe, 

Umma ta ɗauki Mayafi zata fice, Zuhrah dake ƙoƙarin mayar da waya cikin kwalinta tace "Umma ina zuwa kuma yammafa ta fara yi?"

"Ai tare dake zamu fita, Zuhrah dole muje mu yiwa Malam godiya, sannan a bada sunan shi saurayin naki, saboda kar hankalinsa ya karkata ga wata"

Zuhrah tace "ai kuwa Umma wlhi sai ma kin ganshi kyakkyawa, gobe sai mu wuce gurin masu siyar da layin waya ko?"

Umma tace "ke sokuwa ce, da wuri ake kama fara, duba ƙasan katifa zakiga wata farar takarda, akwai layukan wayata a jiki ko ɗauki guda ɗaya, kisa a wayar anjima idan mun dawo sai ki kira shi"

Umma tayi maganar tana ƙarisa sa hijabi, tace "ki biyoni ina gurin Malam sannan zamu bashi koda dubu goma ne..."



*masoyana mun kusa kammala Free pages sannan ba zanyi promo ba ayi haƙuri dan Allah asalin kuɗin littafin gashi nan babu promo na daina idan kinaso ga tsayayyen farashin nan👉 Normal group ₦500 Vip 1k account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank shaidar biya ta wannan number 08141799224*




Mom Islam 🍷

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post