Karshen Kaddara Page 15&16 Complete by Ammey Laylerh - Abokiyar Hira Novels


༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*


𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢  𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ


 _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_


Unexpected and Surprising 🔥💥 


𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. 


ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏....


Page 15&16



♡ ♡ ♡ ♡     


ꨄ Daga cikin motar da take zaune take  ƙarewa harabar kotun kallo, wacce take cike da mutane kowa na harkan gabansa, wanda da dukkan alamu wata Shari'a ce aka gudanar me zafi, wanda ganan jama'a se famar mayar da yadda al' amarin ya kaya suke. Gaba ɗaya a yau ɗin data tsinta kanta a cikin kotun se take jin kamar zata sare ne, domin taki bama lawyer ɗin da aka kawo mata dama, wanda ita a karan kanta take son zamewa kanta da kanta lawyer kamar yacce Yami Ghautam tayi a cikin Film ɗin ta na HAQ wato ƙare Haƙƙi, za tayi iyaka yinta In sha ALLAHU itama har taga tayi nasarar da ikon ALLAH. Buɗe Motar da wata police tayi ne ya katse mata tunaninta, tana sanye cikin ɗamararta ta cikakkar ƴar sanda, hannunta da ɗan kulkensu  wanda tin a daren jiya suka je har gida suka tafi da ita,sedai hakan bata faru se sune suka kwana a ƙofar gidan suma suka zama kamar body gurds nata ne, ita kuma ta a daga cikin gidan soye da zuciyar da tayi kwanan wasi wasi da fargaban ko me ze faru a cikin shari'an nasu. "Mrs Meenal zaka iya fitowa?" Christian police ɗin ta fadi, wanda ya sakata yunƙurowa tana zube kyawawan ƙafafunta da suke fess tayi, akan ta tsaya akan diga diganta tana fesar da wani gauron numfashi, Idanunta ta lumshe a can cikin zuciyarta ta furta....


_ALLAH kai ne ALLAH!, kai ne kuma buwayi gagara misali, UBANGIJIN da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Ya ALLAH na san mutanen nan sun fi ƙarfina ta ko wace siga, amma ni ban damu ba sabo ni kaine GATANA kuma  abun DOGARO NA!, na san ba za ka taɓa bani kunya har na tozarta a idon duniya ba.Ya ALLAH gasu nan sun fi ƙarfina ka fi mini ƙarfinsu kai ma. Ya ALLAH ka nuna  musu irin naka ikon na KUN FAYAKUN akan wannan shari'an!, Ta inda HASKEN dake cikin shari'an ya bama GASKIYA kariya ya shafe Ƙarya da sharrin dake cikin ta, Ya ALLAH ka zamana a bayana duk da ina da wanda suke tsaye a bayan nawa kuwa, amma ALLAH goyon bayanka nake buƙata, Ya Wadud!,UBANGIJINA ka iya mini badon iyawata kota wani na ba......._ tana kai nan ta soma tafiya cikin nutsuwa, Nan ƴan jaridu su kayo Caaaa a kansu wasu jami'ai biyun dake bayanta da aka rasa daga inda suka fito na bata kyakkyawar garkuwar da babu Yar jaridar data ko sake yunƙurin tun kararta,  a nata ɓangaren kuwa tana tafiyar kawai amma Zuciyarta bugawa take duk lokacin da take sake tunkarar ƙofar shiga kotun, zuciyarta naci gaba da  tsananta bugawa,tana fata da roƙon  ALLAH ya shiga lamarin ta. Bayyanuwarta tsaye a gaban kotun ne ya saka wata hayaniya ɓarkewar da seda tayi yunƙurin kai hannunta da nufin toshe kunnuwanta ta tuna da Onka ɗin dake ɗaure da hannuwar nata, Wata tsawa ɗaya daga cikin lauyoyin dake zazzaune wani ya doka musu wanda ya saka kotun wani irin tsit, ta yanda har ba ka jin sauti da motsin komai face na  ƙarar gudun A/Cn , gaba ɗaya mutanen sun kame sun zama kamar wasu gumaka tamkar kuma masu jiran wani sakamako. Kana sannan kotun ta sama nutsuwa har aka wuce da ita wurin da ake tare wanda ake tuhuma, gaba ɗaya kowa ya gama hallara a babbar kotun se dai anki fara gudanar da shari'an ne akan One Man ɗin da suke jira, wanda kowa be san ko wanene ba, kana babu mutumin daya san shi ko meye huriminsa akan Shari'a ɗin....


★..


Tin bayar fitowarsa daga gida daya hau titi yake fuskantar kamar ana bin bayansa, gashi shi dama ba gwanin yawo da security ba don yace yawo da security ai na matsoratane masu raunin zuciya lolz 🤩 ba inji LAYLERH ba, Inji Majeed tin dai masu ɗan security ɗin nan daɗi ne dashi, ko kuwa yanzun mace Yaya Kuwait ɗin mu ÈÃGLÊ yana da tsoro🤸, kai tsaye ya ƙira security line na gidansu ya basu umarnin su biyo bayan shi akwai  wata Black Bentley car ɗin dake bin bayansa da be gama yarda da ita iba kawai suyi kidnapping nata.

Tun daga nesa yake hango irin uban tarin car's ɗin dake cike da harabarn kotun, wani murmushin gefen baki yayi tightly yana parking nashi ka ɗin a wurin da aka tanaja don ajje motoci.

Bayyanuwarsa a wurin ne kuma yayi sanadiyar da iskan wurin ya sanja da ƙamshin daddaɗan out irin me sanyin daɗin nan, be san me yake ji game da case ɗin ba, abinda kawai ya sani tausayinta yake ji, yana tuna ameenatou ɗin sa ne, don haka duk wani taku ɗaya da zai yi sai ya ji  ƙirjinsa yana amsawa, tun kafin ya iso wajen wani kalan kamshin da yake fitarwa me azabar daɗi da saka mutum yaji ya fara jin bacci take....   Alƙalin da ze gudanar da shari'an ne ya miƙe tsaye, tare da gyara farin yankakken gilashin dake idanunsa na ƙara ƙarfin gani, kafin yayi ɗan gyaran murya ya fara da cewa.


   "A yau data kasance ranar Juma'a  wacce tayi daidai da _27/2/2026_ Zamu gudanar da Shari'armu akan laifin kisan kai, wacce ake zargin AMEENEERH SHEHU USMAN da laifin a cikin wannan KOOOTU!, tamu me albarka"  Alƙalin  yayi maganar yana  buga ƴar hidimarsa,  tsittttt kuwa kotun ya ɗauka shiru....

  Nan ya umarci da lawyer ɗin dake kare ɓangaren iyayen yaron da aka kashe da su fara fitowa su gabatar da shari'ansu...  Mutum ɗaya ne daga cikin lauyoyi biyun da suka diba ya miƙe tare da furta....  "Ya me girma me shariya  sunana lawyer Ibrahimul-khaleel datti!, nine kuma lawyer ɗin da yake kare  ɓangaren shari'an iyayen Sameer,akan Rashin tallafin da ɗaya daga cikin Dactor's na asibitin 4&4 suka kashe mana shi!!!!..." Ɗaya lawyer ɗin ne ya miƙe tare da ci gaba da faɗin.. "Kwarai kuwa yame girma me shari'a!, kamar yadda ɗan uwana Lawyer  Ibrahimul-

khaleel datti  ya faɗi haka ne, domin a lokacin da iyayen Sameer suka kai shi cikin asibitin 4&4 lokacin daya sama accident aka kai shi can, amma se Dr Meenerl Shehu Usmanu taki amsar shi tin uwar yaron nayi da ranta har ya koma ga ALLAH, Na gode yame Shari'a...." Lawyer ɗin ya faɗi yana ɗan dukar da kansa ƙasa ya koma mazauninsa ya zauna.... Ɗan gyaran murya Alƙalin yayi tare da faɗin "Ina son ganin lawyer me kare haƙƙin  DR AMEENEERH SHEHU USMAN" Tsit da shiru kotun ta ɗauka, kowa na son ganin ta inda lawyer ɗin da zai kare Meenal ze fito, ciki kuwa harda su Dr pooja dasu Dr Bilal, sedai shiru har na wosu ƴan mintuna babu alamar zai fito ɗin kuwa. Don haka Lawyer Ibrahimul-khaleel datti ya sake miƙewa yana me furta...."Tun daga nan ma sun bayar da shedar cewa lallai Dr AMEENEERH SHEHU USMAN ita ce sanadiyyar mutuwar Sameer  Garba Aliyu na Ya......


 Se dai kuma ya dakata ne da maganar a lokacin da nutsatsestsiyar muryan wanda zata bata zatansu ya karede ilahirin kotun, "Ina da ja nima  yame Shari'a....."  Cikin nutsatstsen kamala da wani kalan  kwarjinin da yake da miƙe, tare da ɗan rausayar da kansa gefe yana me furta  "SUNANA LAWYER  MAJEED DAWOUD ISHAQ!,  Lawyer me kare mutumcin Dr MAANAL, Me kuma kare Kima da darajar asibitin 4 4...."  Tirƙashi!, wannan fa shi ake ƙira da tashin hankalin da ba'a sa masa rana, haka zuciyoyin mutane da yawa dake zazzaune a wurin suka fara furtawa, na kawai ganin MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin a matsayin wanda zai jagoranci shari'an, su kansu iyayen Sameer ɗin seda ƙirajensu ya buga da ganin bayyanuwar nashi, don kuwa a lokacin da suka ganshi a cikin asibitin se suka shiga taytayi da hankalinsu, wannan dalilin ya sanya suka sanja akalan wasar nasu zuwa kan Meenal ɗin ita kaɗai, wanda suke da tabbacin indai suka ce zasu buga wasar tare da shi ta hanyar tsomo asibitin sa ciki, to kuwa ba za su taɓa nasara akan case ɗin...


Amma duk da hakan se suka fara karfafama kansu gwiwa, tun da suna da tabbacin bawai sanin ainihin takamaimain case ɗin yayi ba, amma kuma se  sukaji woni zance na daban bama wanda sukay hasashen bane....

    "15/9/2025  Itace rana mafi munin da Mr MAANAL SHEHU USMAN ba zata  taɓa mantawa da ita ba, domin kuwa itace rana mafi munin da ta munana rayuwarta tun daga farkon ginata har zuwa wannan lokacin da nake tsaye a gabanka ya me Shari'a!!..... Se kuma ya fesar da iska daga bakinsa yana kuma sassauta teayneck ɗin dake wuyarsa kana yaci gaba da furta...  "A lokacin ta sama ƙirar gaggawa daga cikin asibitin 4 4 akan wata tiyatar taimakon gaggawar da zata shiga!,  wanda da farko ma har taki amsa ƙirar ne, sabo da kusan 4 months kenan data dena fita aikin nata, amma bisa maganar da Mijinta Ahmad Ibrahim Shareef da yayi ya sakata fitowa ba dan taso ba..."  Alƙalin ne ya dakatar dashi yace yana  buƙatan ganin Mijin Dr Meenerl.. wanda ya mike take yana fitowa, bayan ya risinar da kansa yace..." Tabbas anyi haka yame Shari'a!, domin kuwa ni ne da kaina na ɗaukota na kawota har cikin asibitin bayan na bata baki akan ta taimaki rayuwar dake cikin hatsari,  kasanwar abokiyar aikinta Dr pooja ta ƙirata akan ta taimaka ga wata operation ta gaggawar data taso musu..." Shima daga nan Alƙalin ya dakatar dashi yana cewa ya koma inda yake, idan da buƙatar sake ganinsa ze masa magana, kana Dr pooja ta fito daya bukaci ya ganta itama, amma kafin nan se lawyer Ibrahimul-khaleel ya miƙe yana rusuna kansa yace....


"Ya me girma me Shari'a!, ba kwana kwana ce da bada labarai ya tara mu anan wurin ba, domin kuwa a ƙa'idar Shari'a babu kwana kwana ko wani dogon labari, kawai a tafi cikin shari'an daya tara mu kai tsaye..." Daga haka ya risinar da kansa yana komawa zaune, "uyhmmmm zaki iya magana" Alƙalin ya bama Dr pooja damar magana, wacce idonta ya cika taf da ruwan hawaye... 


"Kwarai Sir haka ne, kasancewar ranar babu da yawan Dactor's, Dr Bilal baya ƙasar, shima Dr Majeed daya kasance me asibitin baya ƙasar, ni kuma dake banyi ƙarfi sosai a fannin tiyatar ba ya saka sau da dama bana kasadar yinta, indai bata ɓangaren haihuwa bace!!!. Dake inda na karanta ɓangaren Radiology ne, shi yasa ban cika ganganci akan kowacce tiyatane, don haka na ƙira ta, kasancewarta kwararra a fannin ita, amma se tace min nayi hakuri ta ajje aikin ne kawai, wannan ya saka ni ƙiran Dr BILAL da baya ƙasar na sanar masa, wanda shi kuma ya ƙira mijinta kai tsaye daje aminin sane, shi ne dalilin daya kayo ta, wanda ni AYSHA wacce a da nake amsa sunan Dr Pooja Raju na musulunta, saboda wasu kalmomi na Yayanta Sadeeq da suka ratsani lokacin da yake mata nasiha...."


 Daga nan ta koma mazauninta ana sake buƙatan ganin lawyer Majeed.  Se da ya sake risinar da kansa kafin yaci gaba da faɗin. "A lokacin data shiga tiyata room ɗin da niyar fara tiyatar wanda idanuwanta suka gane mata ne ya sakata sakin kayan aikinta, ta fito ranta ɓace ko ganin gabanta bata yi saboda ainihin abinda idanun nata suka ganar mata, ba kowa bane ba kuwa face Sameer Garba Aliyu na Yaya, Mutumin daya keta mata haddinta da daraja da martabar aurenta ta hanyar mata fyaiɗe...." Daga haka ya dakata yana kawar da kansa gefe, don bazai iya ci gababa kuma daga nan, ga wata irin hayaniyar da cikin kotun ya ɗauka. Wanda ya saka lawyer Ibrahimul-khaleel datti miƙewa a matuƙar fusace yace. 


"Tayaya akasan cewar Sameer yama Dr Meenerl Shehu Usman fyaiɗe?, ko dan kawai anga baya raye?, shi ne ake son renama alkalai da masu Shari'a hankali ta hanyar kirkiro ƙagaggen labari?, da wannan hujjar nake son wannan kutu me adalci tayi duba domin kawar da zargin da ake ma wannan yaro" yay maganar yana ɗan dukan table ɗin da yake kai.... "Saboda ina da shaidar hakan...." Lawyer Majeed ya sake faɗi shima daidai da lokacin da wannan shegen tight security ɗin nashi ke shigowa da zaratan samari har su uku..., wanda ya saka iyayen yaran da suka zo domin marama abokinsu Sen Garba Aliyu na Yaya baya suka miƙe ciki da kiɗimar uban me zai kawo yaransu kuma cikin shari'an... Alƙali ne ya bada umarnin ya tare su wurin da ake tsare masu laifin... Gaba ɗaya sun yi wujiga wujiga sedai babu alamar duka wa ko wannensu. "Waɗan nan sune shaidar yame Shari'a" Majeed ya faɗi yana isa har inda yaran suke, kana yaci gaba da cewa, "Nasan duk wanda yama Sameer Garba Aliyu na Yaya farin sani, to kuwa tare da waɗan nan yaran ne ya san shi, sabo da sune yaran dake mara masa baya wajen aikata kowanne kalar ɓarna..., Wannan sunan sa MUJAHEED, wannan kuma TAREEQ,shi kuma wannan CLEVER BOY..." Yakai ƙarshen maganar da rusunar da kansa bayan yace su ne zasu bada cikakkiyar shaidar komai daya faru a lokacin.... Nan suka shiga zayyano komai tin daga lokacin da suka taho bayan sun bugu a motarsu daga club ɗin da suka kwana,  kawai sun zo gitta hanyar suka ganta tsaye alamar wani taimako take nema, har sanda suka isa gare ta da lokacin da shi Sameer ɗin ya musu inkiyar su zubar masa da ita, har zuwa kan magiyar data ringa musu tana kuka da kuma sumewar da tayi, wanda ada duk su huɗu suka so afka mata amma ganin bata numfashi ne ya saka suka gudu, gashi kuma gefen titi suke wani ka iya kamasu.... 


Tun daga lokacin da suka fara bada labarin suke kuka suna cewa wllh shi kaɗai yayi banda su ana tambayeta, don ALLAH a musu sassauci a sake su su tafi, har lokacin daya sama accident ɗin suka kaishi cikin asibitin da nan ne mafi kusa,  abin mamakin kuma da ya sake bama kowa mamaki be wuce cewar da suka yi, daidai wurin da abin ya faru dai dai wurin sukayi accident ɗin, kuma shi kadai ya raunata, amma su duk basu yi komai ba...  Haba sega ido yana fara rena fata, basu sake tsinkewa ba har se lokacin da Majeed ya bada umarnin sake shigo masa da wasu daga cikin jami'an da suka ringa barazana ga rayuwar Meenal ɗin, wanda wannan kuma duk aikin Haj Madina ne bama tare da sanin Mijin nata, har mutane ukun dake cikin wannan Black Bentley car ɗin data biyo bayansa suma.... Nan fa kowa yayi ɗifff an rasa me bakin magana, Se Haj Madina data mike tana rusa uban kuka tana cewa wannan duk cikin shirin Majeed ɗin ne, nan kuwa yace yana da wata hujjar ma, ya bama Alƙali CCTV footage ɗin dake yankin room's ɗin da komai ya faru, don dama ko ina da akwai, nan kuwa plash ta fara haska musu tin daga farkon kawo shin da su Muhajeed ɗin da suka yi, da shigar Meenal ɗin da fitowar, da zuwan Haj Madina ɗin, da irin maganganun da suka gayama juna, ciki kuwa har sanda Haj Madina ɗin ta fara bama Meenal ɗin bakin cewar ta taimaka ta fara duba mata yaronta in yaso koma miye ɗin ya biyo baya da bayyanuwar mijinta bayan da ALLAH yama Sameer ɗin cikawa.... Shike nan ƙurunƙus kan ɗan ɓera, don kuwa dai babu zance na gare kai yanzun...  Alƙalin yayi gyaran murya da nufin yanke hukunci, amma suka sake  tsinkayar muryan Meenal wacce tin da aka fara gudanar da shari'an kanta ke duke, Baffan tama haka tare da Ya Sadeeq.... "Ya me Shari'a ƙarar bata ƙare ba ai....." Tayi maganar tana bayyuwa gaban kotun, wanda ƙirjin Ahmad yayi wani kalan bugawa, don yasan maganar cikin ne za ta yi, shi kuma be shirya rabuwa da ita, be kuma shirya sake shirya amsar tozarci gaban dubban mutane ba, don kuwa zancen cikin nan da zata furta daidai yake da shi kuma fitar numfashinsa..... Kafin kiftar ido ya isa gabanta yana tin kafin ta furta wani abu ya rigata ta hanyar cewa. "A ahhh Meenoh ba muyi haka dake ba, Pls don't forget kamar yacce na faɗa miki...." Raba jikinta da nasa tayi tana me furta. "A yanzu haka Ya me girma mai Shari'a sanadiyyar fyaiɗen da la'antaccen mutumin ya min ina ɗauke da cikin da yake daidai da lokacin da abin ya faru, wato wata huɗu da kwanaki 23 uku yau, wanda a ranar da accident ɗin ya faru dashi a ranar Dr pooja data bani taimakon gaggawa bayan sumewar da nayi bayan farfaɗowa na take cemin ina ɗauke da cikin wata huɗu da kwanaki biyar....."  Wanda wata kalan hayaniya ta karaɗe cikin hol ɗin, ita kuma jikinta na ɗaukan wata wata tsuma, "Wanda Cutarwa da muzancin da wannan mutumi ya mi nake jin ba zan taɓa yafe masa ba!, Na so ace rayuwarsa bata ƙare ta cikin sauƙi da sassauci haka ba, naso ace se duniya ta gama wulaƙanta shi shi da macuta ma'intan iyayensa, ALLAH shi ne zai mini sakayya domin dama ni shi na barwa hakan tin faruwan abun..."  


Gaba ɗaya jikin Baffan ta se ya sake yin sanyin jin wai har da ciki ke gare ta kuma bana mijin taba na wanda ya fyaiɗen!, Ahmad ɗin kuwa jikinsa ne ya shiga wata kalan rawa idanunsa suka yi jajir ɗin tashin hankali, Ya Sadeeq kuwa sumar zaune yayi ba tare da kowa ya ankare ba. Kafin kuma kowa ya ankare ɗin ne Alƙalin yay gyaran murya a natse cike da tausaywa ga Meenal ɗin ya shiga furta. "A ta dalilin manyan hujjojin da mukaji da kunnuwanmu?, muka kuma gani da idanuwanmu zamu zartar da hukunci daidai da lefin kowa dake da hannu cikin rep na Dr AMEENEERH SHEHU USMAN, ciki kuwa har kalan barazana da tare tan da jami'an da suka yi ba bisa ka'ida da dokar aiki ba, za kuma mu hukunta harsu kansu jami'an da kuma hukuncin shi kansa yaron, ta yanda Yan baya za su ringa jin tsoron rep ga matan aure, dama yara ƙananan da muke samu case na rep akan su, ta yanda matasanmu masu tasowa zasu nutsu su ringa jin tsoron aikata lefin, domin dama ganin ba'a yanke hukuncin daya kamata ne yake basu kwarin gwiwar ci gaba da aikata miyagun ayyukansu babu Ƙaƙƙautawa... Ku sani daga rana me kama ta yau idan mun yanke hukunci ya zartu kenan, babu zancen beli, ko ƙaiyadewar kuɗi ku rubuta a dokance domin wannan ɗin kai tsaye umarnine daga *NI ALƘALI YAHAYA SHEHU ƊAN BATTA*, Na kuma yankema Iyayen Sameer Garba Aliyu na Yaya hukuncin ɗaurin shekara Goma Goma bisa  laifin ɗan su da suke ƙoƙarin ɓoyewa,  shakara ɗaya ɗaya kuma bisa bazaranar da suka sanya aka ringa ma Dr Meenerl tare da taran Million biyu, bisa ɗawainiyar renon ciki da kuma haifewar da Dr Meenerl za tayi, su kuma ɓata garin Yan sandar da wasu daga cikin ƴan siyasa ke yi na yanke musu hukunci ɗauri na shekara uku, gaba da ƙara in sun fito, Kana wannan kotu me adalci ta wanke AMEENERH SHEHU USMAN,bisa ga zargin kisan kan da ake tunanin tayi wa Sameer Garba Aliyu Na Yaya.... Haka yaci gaba da zartar da hukuncinsa har zuwa waɗan nan mutane ukun da suna yarin za suyi na 1 year's kawai. Yana gana yanke hukuncin nasa ya doka hidimarsa da kyau sosai domin ba kaɗan ba tausayin Meenal ɗin ya dirar masa take. Kafin kowa ya ankare sega Haj Madina isa ga Meenal, ta zube gabanta tana kuka sosai tana cewa don ALLAH ta yafe masa, ta kuma kula mata da cikin jikinta tana son ganin jinin Sameer a duniya, tana kukan tana komai tana furta wllh da an kashe Meenal ɗin da bata san da cikin Sameer a jikinta da bata yafewa kanta ba wllh haka tayi ta koke koken ta.  Wani kalan kabbara mutane suka  ɗauka domin ba ƙaramin mahaukacin cika kotun tai ba, kasancewarta babbar kotu ce kuma dama an gabatar da wata Shari'ar ne kafin wannan ɗin,  Baffa ne ya miƙe wani jiri na ɗibarsa da nufin isa ga Ya Sadeeq da se lokacin ya lura da somewar da Ya Sadeeq yayi, se dai shi ɗin ma takunsa ɗaya ana biyun jirin dake ɗibarsa ya ɗibesa ya kayar. Jin faɗuwar abu a ƙasa, ya saka kowa kallar wurin ciki kuwa harda Meenerl, da ganin Baffanta zube a ƙasa ya saka zuciyarta wani irin buga mata, ta nufo wurin da niyar isa ga mahaifin nata, se dai itama taku biyun tayi jiri da harɗewan da ƙafafunta suka yi, suka ɗebeta suka kayar akan wani ƙarfe ta zube babu alamar numfashi tattare da ita, domin kuwa tashin hankula ba hankalin da take ciki ba, don dama sune suka fara bugar mata da zuciya.... Ahmad ne yayi kanta a gigice yana ɗagota yaga bata numfashi, ya kai hannunsa kan hancinta yaji bata numfashi, ya kama babbar yatsarta ta ƙafa yaji itama bata harbawa, don haka ya rungumota gaba ɗaya zuwa jikinsa,sedai abun da yaji hannunsa ya taɓa me ɗumi da ɗan ƙauri ne ya saka shi saurin kallar wurin, Gaba ɗaya jinine kwance ke malalowa daga ƙasanta me uban yawa,  Ganin yadda al' amura suke nemar rikicewane ya saka  hankali jama'a saje tashi, kotun kuma ta hargitse aka gaza countrol nata alƙali yayi iyaka ƙoƙarinsa amma kotun taƙi dawo wa daidai, Ga Haj Madina data fasa wani uban kukan daya sake jan hankalin kowa tana birgima tana cewa ta shiga uku ta lalace in cikin nan ya zube..   ita kuwa ya zata yi?, me kuma zata ce da rayuwar, tun da tana gani a gabanta taga ci  ta ga rashi from grace to grass..... Ga nadamar daya sauƙar mata lokaci guda, wanda masu iya magana dama sukan ce Mai ido ɗaya baya taɓa godema ALLAH har sai yaga makaho.... Da tin farko bata ji nadamar ba har seda lokaci ya gama kure mata, wanda kuma a zahirin gaskiya hakan shi ake ƙira da a ɗauri kashi ko a ɓata igiya..... 


Motar taimakon gaggawa ce ta iso cikin kotun, zuwa lokacin har an cafke masu laifin, mutane kuma duk sun fice se tsiraru, Dr pooja kuma na tare da Meenal wacce  take ma ALLAH roƙon cikin ya zube kai tsaye, don haka take wasu ƴan dabarun su na likitoci wanda take da tabbacin ko da akwai sauran cikin ze ƙarasa zubewa... Shi kuma Dr Bilal yana tare da Baffa da Ya Sadeeq, shi kuwa dama Majeed tuni ya jima da barin kotun baki ɗaya, tin kamin ta gama rikicewa. Kai tsaye aka yi hospital dasu don basu taimakon gaggawa.  


Ahmad da mahaifinsa kuwa bayan barinsu daga asibiti bayan sun bi bayan su Meenal ɗin suka wuce gida cike da jimama da alhinin hakan, Baban nashi ya wuce gida shima ya wuce nashi gidan don kansa wani bala'in sara masa yake, don abubuwan duk sun zo masa ne But I was shocked, really shocked dan da ƙyar ya kai kansa parlourn gidan, yana isa ya zube ya riƙe kansa dake barazanar fashe masa, Sedai zaman nasa babu jimawa se ga shigowar Mahaifiyarsa nan, wacce tin kan ta iso masifarta ta ƙaraso. Wani rumtse rinannun jajayen idonsa yayi yana jin yadda ƙirjinsa ke bugawa. "Kana ina baƙin maye, wanda mace ta gama jikawa ta wanke ta baka ka shanye,to wllh ka sani zaman ka ya zo ƙarshe kai da wannan tambaɗaɗɗiyar yarinyar..." 


Sake rumtse rinannun jajayen idanuwansan ya sake yana riƙe kansa daidai da isowar ta parlourn babu wata wata tana zuwa ta zabgesa da mari ta ƙara masa wani . "Mara zuciyar da babu ƙirji a jikinsa, har macen take ɗauke da cikin shege amma kaci gaba da zaman aure da ita, dake kai ɗan Akuya?, to wllh yanzu yanzu ba sai an jima ba seka saki wannan mayyar yarinyar, in kuma ba haka ba in tsine maka kabi duniya dan ubanka Ahmad..."  Tayi maganar tana huci. Kansa ya ɗago yana kallon mahaifiyar nasa yace "Yanzu saboda da wata ƙaddara kawai ta gitta tsakani shi ne kike cewa in saki Meenal Mamy?, wllh ina son ta ba zan iya rayuwa ba tare da ita, don ALLAH ki sassauta  min Mamy ki janye kalamanki, ki tuna cewar ƙaddara tana kan kowa, kuma kowa be isa shallakemata ba. Don ALLAH Kiyi haƙuri mubi komai a sannu..." 



Jefa masa takarda da byro'n dake hannunta tayi tana me furta. "Wllh idan har baka rubuta mata kalmar sakinta anan ba, to ka sani daga yau na yafe ka daga cikin yarana kai ba ɗan dana haifa bane, kuma in yi maka bakin da se ɗeɗeta goben rayuwarka Ahmad, za ka sa ko kuwa?..." 


Rarrafawa gareta yayi yana riƙo ƙafafun mahaifiyar nasa yana mata magiyar ta taimaka ta rabu dashi dashi ta janye kalamanta akansa amma ba zai taɓa iya sakin Meenerl ba, idan ya saketa wllh mutawa ze yi....



"ALLAH ya tsin.......



"BY AMMEY LAYLERH ✍️....



08104493215





Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post