Karshen Kaddara Page 13&14 Complete by Ammey Laylerh - Abokiyar Hira Novels


༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*

𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢  𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

 _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

Unexpected and Surprising 🔥💥 

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. 

Page 13&14

_YA ALLAHU ME IKON ZARTAR DA HUKUNCINKA AKAN KOWANNE RAI ME NUMFASHI, GASHI A YAU WASU SUN TAƁO MAKA NI MARYAM WANNAN BAIWAR TAKA DA BATA DA GATAN KOWA SE NAKA, DON HAKA NAKE KAWO MAKA KUKANA AKAN DUK WANI MUNAFIKIN DAKE SON GANIN BAYANA, DA HAƊA MIN TUGGU DA MUNAFINCI AKAN MAGANGANUN DA NI BAN SAN NA FAƊE SU!, YA ALLAH KA SAKA MIN, KA KUMA BI MIN HAƘƘI NA  AKAN KOMA WAYE... ALLAH KA TSAYA MIN ADUK WANI LAMARIN DA ZAI TASO IRIN HAKA, DOMIN NI KAI NE GATANA KUMA ABIN DOGARO NA, DONNI DA KAI NA DOGARA BAWA KO WANNE KATO KO KATUWARBA,YA WADUD KA SHIGA CIKIN LAMARIN..._


_KU KUMA MUNAFIKAI KUJI TSORON ALLAH WLLH ,IDAN KUMA BURINKU WANI YA TOZARTANI TO KU SANI IN SHA ALLAHU BA ZAKU TAƁA GANIN BAYANA BA DA IKON RABBIL ARSHIM AZEEM... DA WATAN AZUMIN ALLAH KUN TASHI HANKALI NA KUN KUMA SA HANKALI NA YA TASHI BA KAƊAN BA, KUJE KUMA NA BARKU DA ALLAH, SHIRUN KUMA DA NAYI BA INA NUFIN NA TSORATA BANE, KAWAI BANA GAGGAWAR ƊAUKAR MATAKI NE DA KAINA, INA BARMA ALLAH YA ZARTAR DA NASHI IKON NE, DOMIN NASAN IN YA TASHI YAFI NAWA ƘARFIN IKO KO MATAKIN DA ZAN ƊAUKA,DON HAKA KUCI GABA DA GASHI ALLAH YANA KALLON KU BABU RUWAN AMMEY LAYLERH  🤸💃_


♡ ♡ ♡ ♡     


ꨄ A can gidan su ameenatou kuwa da kuma Mijinta Ahmad tabbas sun kwana suna baƙin ciki da alhinin iftila'in daya faɗama Meenal ɗin a daren jiya, tabbas sun sake yarda da ake cewa zaɓi guda ɗaya mara kyau a cikin rayuwarka na iya janwo  maka shekaru na gajiyawa da nadamar rayuwarka na har abada, Shi sa masu iya magana suke cewa ka zama mai taka tsantsan aduk wani al'amarin daya danganci rayuwarka. Domin rayuwar tana jujjuyawane cike da tarin abin mamaki da al'ajabi, ta yanda wani lokacin zaka shiga  kwanakin da suke nauyaya maka rai,har kayi tunanin ba zasu taɓa ƙare maka ba.  Har ka wayi gari wata rana kana son kayi sabuwar rayuwa, sedai  lokaci ba zai taɓa baka wannan damar ba, domin shi da kansa lokacin ba zai taɓa baka damar hakan ba,don lokacin daka gama ɓatawa na baya ba za su taɓa dawo maka ba, ta yanda wani lokacin karshen abu shi ne farkon nutsuwar zuciya. Kamar yadda masu hikima suke yawan cewa, karka jira ƙofa ta buɗe bayan ta rufe maka, sannan ka gane babu rufewar data fito daga ALLAH face tana ɓoye da alkhairinsa akan ta. Abu na farko daya kamaci ace kowanne bawa ya gane anan shi ne ka sani cewar, abu na farko daya kamata ka fara yafewa shi ne ka koya daga kuskurenka don ka sake gyara kuskurenka harma kaci gaba da ƙoƙari. Kada kabar kuskurenka ya zama sarƙar yanke ƙauna,ka  mai dashi gyara zuwa matakin gaba na ingantacciyar nasarar ka, don masu iya magana sunce, Rashin nutsuwa yana farawa ne daga nisantar mutum da ALLAH, tsoron ALLAH kuma shi ne sirrin kowanne farin ciki na gaskiya..... Idan har duniya da abinda ke cikinta suka soka da gyara to maza kayi gaggawar gyarawar kuwa, idan kuma ta ƙiƙa to ko zata sake baka wata damar seka sha baƙar wahala da fafutuka sannan. Daga nan labarin ameenatou ya fara.....


Yanda taga daren wannan rana haka taga wayewarsa masu cike da almara da  irin ƙarfin iko na Ubangiji,  lallai idan har bawa beji tsoron mahaliccin saba to kuwa yaji tsoron hukuncinsa, don idan yaso ka da ramane fa kuskuren saɓa masan da kai ke farawa tin daga nan gidan duniya, idan har shi wannan bawan me zuciyar nagartane seya gyara, nadamar rayuwa da dana sanin biyema son zuciya da kuma rudin zamani shi ne abu na farkon daya farawa dirar mata, A cikin zuciyarta take zubar da hawaye bawai don yana fitowa daga cikin idanun taba, A ahhh yana daga can cikin zuciyarta yana mata illar da tafi zubar shi azaba, cinnaku da kukan sauro sune abu na daya fara addabar rayuwarta, wanda take jin kamar ta sare da rayuwar ta huta haka nan, Sedai kuma kamar yacce  hausawa ke cewa wahala bata kisa sedai asha baƙar hawala a hannunta,  tuna wannan kawai da tayi ne yasa har taji a ranta cewar sauyin rayuwa da munin ƙaddara ba zata taɓa barin su kaita ƙasa ba, bare sauyin rayuwar data samu kanta kwatsam a ciki besa taji zata sarema rayuwar ba, sai ma wani 

 ƙarfin imani dana zuciyar karɓan kowacce iriyar ƙaddarar da tazo mata da hannu bibbiyu, wannan kwana ɗayan da tayi a cikin cell a kulle da har a da take jin  kamar ba zata iyaba, saboda  rayuwa ce da ko a idon zuci bata taɓa ko tunanin hasasoma kanta ba ko da a mafarkin tane da. Rayuwar data tsinta kanta a ciki se taji tama tata rayuwar nauyin da kamar ba zata kai labari ba. Amma ƙarfin imanin daya shigeta na danne hakan take.  Hasken daya haske mata idanune ya sakata motsawa tare da kare fuskanta da duka hannuwanta biyu, Wata police macece tace ta fito se famar wani kukkumbura take tana cika tana batsewa, domin ku su duka jami'an ba hakan suka so ba daga yarinyar, don da  a son samu ne se ta samu kamar kyakkyawar sati guda cif a kulle ba tare da ko sauron waje yasan inda take ba, sedai wanda ta tarar a cikinsa amma kash wani ya musu kutse a cikin tarkon nasu, wanin da suke da tabbacin tsaf ze iya saka a dakatar dasu a aikin nasu, dakatarwar kuma ta har gaban abada, domin shi kansa yaron nada wani irin karfin iko a cikin garin bare kuma azo kan mahaifinsa da yake kamar father's ne na manyan mutanen da duk suke jin sunkai a garin Kanon. Fatar bakinta tayi wani kalan bushewan da har tsagawan hawala tayi, idonta yayi zurfin da ya sake fitar da iyaka zallar jigatuwar da tayi, domin tin da suka wullota ko ruwa babu wanda ya bata bare abinci, domin sen Garba Aliyu na Yaya da Matarsa Haj Madina kamar kwangila kisan tane suka bayar suma. Shi ya saka ko a jiyan ziryan Yayanta biyu amma suka ce su bama su san wata me wannan sunar ko me kama da ita. Ana haka sega wannan Gabjejen bakin police ɗin ya fito, wanda sarai Ya Sadeeq ɗin ya gane sa don haka ya nufi wurinsa yana cewa don ALLAH ya taimaka ya faɗa masa inda Meenal ɗin take. Amma haka wannan police ɗin yay mirsisi yace shi baima taɓa ganin kome kama dashi ko wata can ba se yanzun daya fara ganinsa, Wannan abu shi ya sake rikita  Ya Sadeeq ɗin, barin ma da sauran ƴan uwansa ma suka goya masa baya wai shi bama ya gari ai yanzu ya dawo, Nan fa suke neman haukata kan Ya Sadeeq ɗin... 


 Tunanin wannan police ɗin ya dakata ne daga lokacin da wannan macen police ɗin take fitowa da Meenal ɗin, 

 ɗago ƙananun idanuwansa da suke a matse kamar na ƴan Japanese yayi, yana sake tsayar da kallonsa akan  Meenal ɗin da lokaci guda harta sanja saboda mummunar halin da take a ciki, ga yunwa da ƙishin da suka gama wajigata. Wata nannauyar ajiyar zuciya police ɗin yayi ganin kamar Wada damar ce ALLAH ya kawo musu, masu ƙarfin ikon faɗa da nera biyu sun haɗu akan case guda ɗaya, se yake jin a ransa cewar hakan ma kamar dama ce ALLAH ya kawo musu ta yanda zasu jefi  tsuntsu ɗaya da dutse biyu a wannan gaɓar. Da wurin zama ya mata nuni yana sassauta zuciyarsa akan tsananin son abin duniyar da yake da. Zama tayi  a inda ya nuna mata ɗin tana ta baza idon taga ta inda Mijinta ko Yayanta a cikinsu wani zai ɓallo, don tasan kaf duniyar babu masu zuwa wurinta daya zarta su. Se dai zama da kamar 30 minutes ɗin da tayi bata ga kowannensu daga cikin su ne ya sakata ɗaga kanta ta kalla police ɗin dake tsaye, mamakin Mutumin da kuma jin kansa na sake kashe sa, ehhhh mana ai dole yace jin kai mana yace a fito masa da yarinya kuma ta fito sama da 30 minutes be ce mata komai ba. Ta buɗe baki kenan da niyar tambayarsa a ina wanda ke ƙirar nata ya wani ɗago kansa yana wurgama  Police ɗin wani mugun kallon da ko be buɗe baki yayi magana ba, idanunsa kawai sun isa isar da hukuncinsu ga  mai laifi, don haka tin kafin ya furta masa wota magana ya bar wurin. Don kai tsaye ya gane spece or balance yake nema daga gare shi. Gabanta sosai taji yayi mummunar wata bugu da ganinsa kawai, me ya kawoshi wurinta?, miye kuma haɗinta dashi?, ama ina yasan tana nan ɗin, ko kuwa ya sake biyota har nan ɗin ne don ya sake wulaƙantata kamar ranar?. Maganar sa ce da wannan No nonsense muryan nashi ya sakata dakatawa cak daga tunanin nata.   


  "Me ya sa kika biyosu?, bayan mijinki da yayanki sun yi ƙoƙarin baki kariya?"  


Haka maganar nashi ya sake dakar tsakar kanta da yake mata wani kalan mugun ciwon da take jin har kamar  zai tsage gida biyu. Komai bata ce masa ba saima saka hannunta da tayi ta dafe goshinta da nufin ko zata ji sassaicin abinda ya riƙe mata kan, amma kuma sai taji ciwon kamar a tsakiyar kan yake, wanda taji kamar ma ba ciwon yake ba, kamar wuta ce ake hurawa a cikin kan nata da zafin ta yake saka gumi tsiyayowa daga cikin gashin kanta zuwa fuskar da ilahirin jikinka. Ba ciwon kan ne ya fi damunta ba, ciwon da zuciyarta ke mata ne yafi addabarta fiye da komai, se kuwa zafin kalamansa da tambayar daya mata ke sake taso mata, suna son wargaza sauran jarumtar da take jin tana da. Wani irin zafi take ji na taso mata daga cikin ƙarƙashin tsakiyar ƙirjinta irin mai kama da ƙaiƙayin nan, gashi tana lullube a ƙirjinta dan haka babu damar ta  sosa ta bare tayi tsammanin samun sassauci daga suka da ƙaiƙayin da take matan. Don haka ta saka ɗayan hannunta  ta dafe zuciyar tare da yin  ajjiyar zuciya da nufin ko zata sama sassauci ko wani rangwame daga azabar da zuciyar ke mata amma sai taji tamkar kara kaikayin ne ma tayi.... 


 A matuƙar jigace ta mike tsaye tana dafe da kan nata ta dube shi tare da cewa.  "Stop it!, da duk wata baƙar maganar data saura wacce baka gama gaɗamin ma, domin a yanzun wannan zuciyar ba zata taɓa iya ɗauka ba ka temaka ka tafi ka barni Please!!!...." 


Shima tsayen ya miƙe ba tare daya kalla inda taken ba ya wani gumtsi iska ya kuma fesar duk a lokaci guda kafin ya wani furta. "Damn it!" ya fada da karfi  

 sannan ya koma ya zauna a inda ya tashi yanzun.  Kafin a natse ya dubeta tare da magana kai tsaye akan case ɗin da take cikinsa. Wani irin hope taji ya sake  ratsa zuciyarta da jikinta don haka kai tsaye tace bata buƙatan taimakonsa yaje ya riƙe abin sa, amma ita a wurin mahaliccinta take nema, Ganin kamar zata bashi wahala ne yasa shi faɗa mata wata baƙar maganar da dolen dole yake da tabbacin seta amayar masa har fiye da abinda yake buƙatar ji daga gare ta, don yaga za tayi mugun taurin kai yarinyar. "Kar kiyi tunanin zan tsaya ɓata lokacina ne akan mace  mara kima da daraja irin ki, me take dokokin ALLAH data aurenta, ki sani na shigo cikin maganar ne domin kawai a cikin asibitina case ɗin kisar ta faru, badon haka ba ke kin ma isa ki tsaya ko inuwar dana tsaya balle har kiyi tunanin raɓarta? IDIOTS....." A lokacin daya gama yaɓo mata maganar kuwa har bata san lokacin da jikinta ya soma rawa ba, duk yanda taso  jurewa kuwa gazawa tayi ga hannunta  ɗaya daya soma rawa. Ta riƙe hannun da ɗaya hannun da niyyar bashi kariya amma sai suke rawar a tare. Wannan ya saka ta haɗesu  duk biyun ta rungume a ƙirjinta tare da jan dogayen numfashi sau uku ta hancinta, tana  sakin ajiyar zuciya da niyyar calming nerves ɗin ta down ko dan ta sama damar  ce masa yaje ta amsa hakan za kuma taci gaba amsar kowanne irin hukunci daga mahaliccin tane. Idanunta ta runtse tare da kokarin goge hawayen da kai tsaye taji sun zobo mata, wanda a daren jiya tayi tayi ya zuba yaƙi, se a cikin zuciyarta ya dinga kwarafniya, fara goge hawayen tayi amma wasu suna sake yin replacing ɗin kan su gare ta.... Abinda kawai take  hangoma kanta a cikin idonta shi ne girman laifinta ga mahaliccinta da kuma Mijinta, fuskar Ya Ahmad da Ya Sadeeq ɗin ta kawai take hangowa a yadda ta baro su a tsakiyar compound na gidanta,  don haka take jin ba zata taɓa barin zuciyarta ta yaudareta akan wani daban ba kuma, shi dama bata gama sanin ko shi waye ba?, daɗi da ƙari Ita Matar Aure ce babu hurimin wani yace zai shige mata gaba akan lamarin da ya faru da ita. Don haka cikin kwarin gwiwa ta soma tafiya ta barshi, Saboda aganinta hakan shi ne dai dai, hakan shi ne zai fi alkhairi gare su, barin ma data  shafa cikin jikinta da 

 shi ne silar komai,wanda zata iya rantsewa kamar motsinsa taji a karon farko ya mata....


Kuɗi sosai ya bama tarin police ɗin a matsayin na belinta da yayi har zuwa lokacin da za'a yi shari'an ba tare da sanin taba, kana yace idan har wani abu ya sameta koda kwarzanene se yayi sanadiyar rasa aikinsa, rasawa kuma ta har gaban abada kamar dai yacce Dpo ya tsammata ɗin kuwa. Daga nan ya wuce babu jimawa se ga Ya Sadeeq da Dr BILAL ya sanar dashi inda take ya kuma je anyi belinta. Lokacin tsaƙiyar ranace don irin sha biyu da rabi ɗin nan ce, gashi kuma ba laifi an tashi da ranar. A karo na biyun da akace ta fito cewa tai ta yafe ko waye. Har seda wannan mummunar baƙin police ɗin ya bayyana a gabanta kana ta nutsu ta kuma fito, ganin yayan tane ya sakata shigewa jikinsa kawai tana sakin kuka. Lallashinta ya shiga yi kafin ya jata ya zaunar kan wani plat chiar dake wurin, ruwa ya ɓalle ya bata  da kuwa ta kafa kai bata janye gorar ba har se da ruwan ya ƙare, kana ya bari ta nutsu sosai kafin ya sama napep su wuce gida kai tsaye, ganinta ya kwantar da hankalin Baffa ba kaɗan ba nan Baffan yasa Bilkisu ta dafa mata ruwan wanka me ɗumi, har ban ɗakin dake tsakar gidan ta kai mata ruwan bayan ta dafa mata, wanko tayo sosai da gasa jikinta da kyau, kayan Shareefah ta saka jallabiya se kuwa gashi tudun cikin ya ɗan bayyana ta cikin rigar. Haɗe kanta da jikin gadon kawai tayi tana jin yadda zuciyarta ke tsanar cikin dake jikin nata kai tsaye da kuma ƙaunarsa na kasancewar a jikinta yake, haka duka abu biyun suka haɗe mata tsana da ƙaunar cikin jikinta,wanda ita dai ko a tarihin rayuwa bata taɓa jin SO da TSANA sun dirarma mutam lokaci guda ba se a kanta, shigowar mahaifinta dakin ne ya sakata sese ta natsuwarta tana zama daga ƙasan wurin. Cikin taushi da kuma lausasa murya ya dubeta cike da wani kalan matsanancin tausayinta me girma a gareshi, domin kusan ze iya cewa ita ce zuciyarsa kai tsaye. Don haka komai da zai shafi rayuwarta yake jinsa me girma na kuma daban a cikin rayuwarsa. Ahankalin cikin taushin murya yace.....


"Kiyi hakuri ameenatou ki amsa wannan ƙaddarar, domin rayuwa ba zata taɓa ginamu kamar yacce muke so ba, harma abinda muke ganin yafi ƙarfinmu na iya zama abu mafi sauƙi da zarar munfi karɓi zaɓin da ALLAH ya mana, se kiga zuciyoyinmu sun sama nutsuwa ata sanadiyyar hakan... Ameenatou ina son ki saka a ranki cewar har yanzun rayuwarki na nan matuƙar kina numfashi!, duk wani zaɓi yana hannunki idan kika so ki sanja dole ne ki fuskanta matsalolinki da kanki, muddin zuciyarki naci gaba da aikinta na bugawa. Kin ga kenan har yanzun zaki  iya sake *RUBUTA LABARINKI...*, Amma se kin fara fahimta da sanin cewar yin haƙuri yana kawo nutsuwa, yin godiya ga ALLAH yana ƙara ni'ima,yin adalci kuma yana samar da aminci da nutsuwar zuciya......" Se kuma ya ɗan fesar da wani huci me zafin da yaji yana nemar kuncushe ƙirjinsa. Kafin yaci gaba da fadin..... "Duk wanda yayi Adda'a sannan ya kyautatama ALLAH zato, to kuwa ya jira zuwan mafita daga gareshi zai sama ladan wannan jiran da kuma kyautata zaton da yayi, domin kyautata ma ALLAH zato da kuma  tsammanin mafita daga gare shi suma ayyukan ibada ne, don haka kada jinkirin amsawa ya sanya ka sare!!!, ko kuma munana zato ga ALLAH, domin ALLAH yayi alƙawarin amsawa amma a lokacin da yace, don haka gaggawarka ba zata sanya ALLAH gaggawa ba... Ki wanke hawayenki da ruwan alwala,kiyi sallah, ki ɗaga hannayenki sama ki zayyanawa ALLAH damuwarki da buƙatarki. Idan zuciyarki tayi nauyi da damuwa ki sani Rahamar ALLAH tafi damuwarki yawa!, idan  duniya ta matseki ki buɗe zuciyarki da tuba da istighfari.... Babu hanya mafi sauƙi na cire damuwa fiye da sujjuda a cikin dare, damuwa ba zata taɓa dawwamaba!, domin ALLAH yana tare da masu hakuri, ki riƙe alƙawarinsa domin shi ne da kansa yace... *INNA MA AL' USRI YUSRA*  ki ɗaga hannunki ki kuma fuskanci sama ki ce.... *HASBINALLU LA'ILA HA ILLA HUWA,ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHIM AZEEM....* Zuciyarki zata huta!, za kuma ki sama nutsuwa, kwanciyar hankali kuma zata sama gurbin zama a cikin zuciyarki.... Ki sani tsoro ba zai taɓa gina mutum ba, sedai ya ruguza, domin ita kanta rayuwar ƙalubece. Amma ita nasara tana zuwar mana ne tamkar kiftawar ido,kamar yadda ajali ke zuwar mana kamar kiftawar idon shima. Anan ina son ki sani cewar damuwar da za'a barta a cikin kwakwalwa tafi kowacce kalar damuwa cutarwa, ki amayar duk abinda ke cikin zuciyarki ki kuma tsarkake ta tsarki irin na gaskiya da gaskiyar da ALLAH ke so, za kiyi albarka In sha ALLAHU....."   Kuka sosai take yi wanda sautinsa ke fita da amo da kuma irin raunin dake bayyana  me yin sa, Tsaye mahaifin nata ya miƙe hannuwansa a gadon bayan sa yace. 


"Ameenatou a yanzun kuka ba shi ne mafita ba.... Kiyi Adda'a ki kuma yi injoining na ƙaddararki In sha ALLAHU duk bayan wani tsanani sauƙi na bayansa.... Daga haka ya fita. Bakinta yake son buɗewa tama Baffan nata magana, ta masa godiyar Adda'a da nasihohinsa gare ta amma kukan daya sarƙe maƙoshinsa na hana mata hakan,  take kuwa ta fara rera kukan mai taɓa zuciyar duk wani mai sauraro, ta jima tana yi kafin ta share wata irin nutsuwa da sanyin kalaman mahaifin nata gare ta na ratsa ilahirin jikinta, kukan da ya zama mafarin buɗewan yin sa kenan a cikin rayuwarta, domin kuwa daga wannan tangarɗar daya faru da ita daga nan ƙaddarar ta fara. Tin da ta shige ɗakin sallace kawai ke fito da har aka yi isha'a, tin kuma data shigo gidan gwaggo Sadiya bata ko leƙo taba, Bilkisu kuma tana maƙarfi taje wurin dangin Ummanta wani biki da suke Malam ya hanata zuwa shi ne ta tura Bilkisun. Bayan sallar isha'a ɗin Ya Sadeeq ya shigo tare da Ya Ahmad har tsakar gidan, dake gwaggo ƴar duniyace harda su ahimfiɗa tabarma, a mutumce ya gaidata sega shigowan Baffan shima, ɗakin da Meenal ɗin ke ciki duk suka shige, wanda hakan bema gwaggo Sadiyan daɗi ba, don haka ta wani ja tsuka tana furta.


 "Munafincin banza..." 


Bata sake sarewa da lamarin ba seda ta sake ganin Ya Sadeeq da Ya Ahmad sun sako Meenal ɗin tsaƙiyarsu, ita kuma se famar share hawaye take, domin gani take da ba sai ta koma gidan Ahmad ɗin ba, don tasan koda ace ta koma ɗin taƙi kaɗan ne ƙaddara zata raba zaman nasu. Haɓa Gwaggo Sadiyan ta riƙe a bayyane tace. "Ji wata ƙaddarar liman da sket....."  Wanda ya saka Ya Ahmad waywayenta banda sauran da ko kallo bata ishesu ba su duka, har bakin motarsu suka rakata ta shige gidan baya, duk yacce Ahmad ɗin yayi data shiga gidan gaba kuwa, ita kuma ta zaɓa gidan bayan ne yadda zata fi sakewa ta kwanta sakamakon cikinta dake mata wani kalan ciwo da marar ta. Koda suka kawo gidan yaso taimaka mata amma ta dakatar dashi ta yunƙura da kanta ta nufi cikin gidan, kai tsaye ɓangarenta ta wuce ta rufe babu jimawa kuma se gashi ya biyota har nan ɗin, zama yayi daga ƙasan da itama take daf, hannunta ya kamo cikin tafin hannunsa yana ɗago fuskanta kuma da ɗayan hannun, ga mamakinta ruwan hawaye ta gani kwance sharkaf a saman fuskarsa, hannunta dake cikin nasa ya ɗan damƙe, tare da soma magana.... "Komai kikaga ya faru da bawa dama can tin daga Rabbil Izzati ne hakan, don haka nake son ki fawwalama ALLAH duka lamurran, kana roƙon da nake son na miki da kuma Alfarmar da zaki min shi ne....." Se kuma wani kukan ya sake sarƙe maƙoshinsa ya kife kansa a jikin kafaɗarta yace. "Duk yin Duniyar da za'a yi akan cikin nan karki furta komai indai kinsan ba nawa bane zaki ce, naji na kuma gani har cikin zuciya ta na wuce zan kuma karɓi wannan ƙaddarar da duka hannayena biyun nan..." Yay maganar yana ware mata tafukan hannayen nasa. Kana yaci gaba da furta. "Nie banji ma a jikina cewar cikin nan ba nawa ne Meenorh, kwanaki biyar ɗin da kika ɗora ina kallar kamar hindawar wasu kalmomi ne kikai kika aza bisa watanni huɗun, na ji na gani koda ace ba nawan bane kada abinda yasa kika shigo da maganar wannan cikin kinji *ZUCIYAR AHMAD IBRAHIM SHAREEF.....*, mu roki ALLAH gafararsa!, mu kuma rokeshi da ya yafe mana kusakuranmu na baya, ya bamu juriyar ci gaba da gudanar da rayuwarmu kamar baya koma zarta hakan..." Kuka sosai take rerewa a jikin nasa kafin cikin muryan da kuka ya gama cinyewa tace..... "Ta ya kake tunanin ni zan yarda na yaudareka, bayan na gaza kare maka kaina martaba da kuma darajata data aurenmu?, Ya Ahmad na gode da kalan haliccinka gareni kuma bazan taɓa mantawa da wannan masoyin na gaskiya da gaskiya ba, Sedai banji a jikina cewar zamanmu zeci gaba da gudana a haka ba, koda ace zai ci gaba ɗin dole se kalmar saki ta shiga tsakaninmu naje nayi istibra'i na tsarkaka kaina daga dattin zinar dake tare dani. Sena haife abinda ke cikin kina na ware shi daban, domin kuwa bazan taɓa cakuɗashi da yaran da zamu haifa masu tsarki ba I LOVE U too much love Ya Ahmad......"  Daga haka ta kwace jikinta a nashi ta shige bathroom tana rufewa duk yacce yata mata magiya da roƙon ta buɗe masa amma ta ƙiya, kuma take wanda bata san ya matsaya da iyaka tsayin da yake da ba, kukane irin na kai da kai ɗin nan, kukane da iyaka me yinsa kawai ne yasan illarsa ga lafiya da gangar jikinsa!, kuka ne irin na wanda ya gama sallamawa.....


Sati guda cif  suka shafe  suna fuskantar azabtarwar da suka zaɓa suma junansu, taki aminta dashi, taki amsarsa a matsayin mijinta, domin tace masa ita ɗin a yanzun tamkar wata datti da zunubi ce,  a kuma cikin waɗan nan satikan babu kalar barazanar da bata gani ba daga su sen Garba Aliyu na Yaya, Sedai ALLAH ya kan tseratar da ita daga jami'an ɓoyen da Sir MAJEED DAWOUD ISHAQ ya zuba musu a gaba ɗaya anguwar ba tare da sanin daga ina jami'an suke ba,  ita kanta ba tare da saninta ko mijin taba, don wani lokacin se ya fita zuwa wurin aikinsa kana suke affecting na shiga gidan, ganin babu nasara ne ya saka Hajiya Madinah cewa kawai a shiga kotu, don haka kwana biyu bayan haka se gashi har office an kaima Ahmad takardar fara shari'an, tun da gidan babu dama shiga, wannan abu shi ya sake tada hankalin Ahmad daya dawo gida a birkice, Me makon ace shine zai kwantar mata hankali se ya zaman ita ce ke kwantar masa hankalin,   cikin ƙwarin gwuiwar jin cewa zata fuskanta duk abinda ke tunkaro ta, wannan daren da mutane suka gaza runtsa bacci, yanda Ya Sadeeq yaga Wannan tsayin dare haka shima Ya Ahmad ya gani, ita ɗin ma haka ta gani sedai ita zamu ce ta raya daren da bautama mahaliccin ta kukanta, ta yi masa kirari ta kuma roke sa akan ya kawo mata mafita ya kuma zama gatanta....


Ko Baffa da Ya Sadeeq ya nasar dashi Adda'a kawai yayi akan batun yace ALLAH ya kai su lokacin,  ɓangaren su Hajiya Madina ma duk sun gama har haɗa shedunsu akan cewar lallai Meenal ita ce sanadiyyar mutuwar yaronsu, wanda ranar juma'a za'a yi zaman, wacce ta kama saura kwanaki uku kenan a shiga Shari'an,  sosai aka sake linka tsaron dake cikin anguwar wanda su kansu masu anguwar har mamakin hakan ya gaza barinsu,gashi kullum suna bakin aiki duk irin daren da zaka tsala zaka taddasu kiƙam ɗin nan.  Sosai kan Ahmad ke ɗaukar hayaƙin shiga kotun da za'ayi, wanda se a daren washe garin ranar da za'a gudanar da zaman yake sanarma mahaifinsa IBRAHIM SHAREEF komai, sedai be musu zancen fyaiɗen ba, don a ganinsa ya wuce fannin tun da har yace Meenal ɗin karta yarda ta faɗa maganar fyaiɗen bare kuma cikin jikinta, sedai ya makaro kusan zamu ce, don kuwa a nata ɓangaren ta gama shirya duk wasu hujjoji nata ba tare da sanin kowa ba ta naɗe kayanta a kanta, ko lawyer ɗin da Ahmad ya ɗauko mata bakinta be jiba, duk kuwa da irin bugun cikinta daya ringa yi, amma haƙarsa bata cimma ruwa ba......


_To fa wannan shi ake ƙira da ana wata ga wata_


_Jama'a ya kuke tunanin wannan zaman ze wakana kuwa?, shin kuna jin wani ƙanshi ƙanshi koni kaɗai ce nake jiyo mana?_


_Wannan tafiyar fa itama da nata kalan salon da tazo mana shi,  don na fahimta yanzun alƙalamin nawa nema yake ya faɗa kan iyaka ƙaddara da kuma ƙalubalen rayuwa Tabbas, to koma dai miye nidai AMMEY LAYLERH burina in nayi rubutun jama'a su amfana dashi_ 


_Nasan zaku ringa tunanin cewar ya alƙalamin yake nemar mana wasa da hankali ne ko?, zuwa yanzun nasan ko kowa be furta ba to kuwa abinda ke ƙumshe cikin rai da ruhinsa kenan..._


_Se dai ku sani cewar indai wasa da hankali ne Hhhhhhhhhhh badai zan ce komai ba amma dai akwai zatan da zakuyi tayi kuma na sanja salon tunanin naku kamar dai yacce aka saba, lolz 🤩 Ni kaina nasan banyi kamar wannan littafi ba, gashi  dai labarin ba tsayi zeyi irin sosai ɗin nan ba, amma kuma nace sena rikita tunaninku, na gama assignment ta yacce zakuyi ta hasashe da tsammatar abinda be shi ke akwai ba, karfa ku manta sunan littafin ƘARSHEN ƘADDARA!!!. Kun ga kenan ai ƙaddarar ba ɗaya bace kenan ƙaddarorine da yawa....._


_Hhhhh to lolz 🤩 🤩 🤩 koma dai miye ku muje zuwa🤸🤸🤸💃💃💃💃💃💃🤸🤸🤸_


*BY AMMEY LAYLERH ✍️ 


08104493215


Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post