Karshen Kaddara Page 11&12 Complete by Ammey Laylerh - Abokiyar Hira Novels


༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*

𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢  𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

 _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

Unexpected and Surprising 🔥💥 

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. 

Page 11&12

♡ ♡ ♡ ♡     

ꨄ A ƙasa ya tarar da Ummiensa da ƙanwarsa Ikleemerh, dama AYLA wacce ke lafe jikin Ummiensa. Idanunsa ya lumshe da sake buɗe su akan Ayla ɗin dake jingine da jikin Ummien tana mata rigima, domin bata jin daɗi lumonia ɗin tane ke nemar tashi. Sakamakon hunturun da aka tashi dashi, gashi jiya da dare ba tare da sanin Ummien ba taje ta sheƙama jikinta ruwan sanyi, Shi yasa yau bata wani tashi da kuzarinta da ƙarsashin taba kamar kullum, Shi ne ma yasa ko school bata je ba duk da kasancewar Monday ce yau ɗin. Suna haɗa ido yaji wani irin raunin da ganinta ya sake haifar  masa na ƙoƙarin taso mar, Ayla kuwa  da ganin Papa ɗin nata ne ya sanya ta a farin ciki ne ta taso da gudu zuwa wurin sa, hannayen sa kawai ya buɗe mata domin ya san mine take shirin yi, tsamm ya rungume Babyn nasa  zuciyarsa na masa wani mahaukacin bugu, Jin yadda jikin yarinyar ya saki, ga wani ɗan banzan sanyin da gaba ɗaya jikinta ya ɗauka. "Paapa" haka ta ƙirayi sunan shi cikin maraitacciyar murya.wanda hakan ya sanya Majeed ɗago haɓarta ya zuba idanunsa cikin muryan shirin yin kuka tace. "Paapa na dena wasar ruwan, kuma ma I hate him!, tin da yake sani jinya."   Yanda tai maganar a hankali cikin rauni ne yasa kaɗan ya rage zuciyarsa bata fito waje ba, amma ya daure  cike da son nuna jarumta yana ƙara  ƙanƙameta  sosai a cikin jikin sa. Kafin ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya, yana jin gaba ɗaya komai na nemar cinkushe masa. dole ne yana buƙatar ƙara ƙadaice kansa, domin gudun kada iyayen sa su fahimci rauni da kuma halin da yake ciki, zare ta yayi daga jikinsa  samm baka isa kai tsaye ka fahimci halin da yake a ciki ba, amma a baɗini da zaka ga irin tarin raunikan dake chunkushe a cikin zuciyarsa, da kuwa tabbas saika tausaya masa. 


Da wani kallon zallar tausayin ɗan nata Ummeh ta shiga binsa  dashi, A cikin zuciyarta tana jin inama ace wani na iya  ɗauke damuwar wani, da kuma ciwon wani,da ita kuwa tabbas ita ce uwa ta farkon ta zata fara ɗauke duk tarin abubuwan yaron nata, ba  tare da ko shi kansa ya san da hakan ba. Idanunta ne ya ciko da hawayen tausayin ɗan nata. Maganar Ayla ne ya sake katse duk tunaninsu da tace. "Papa shike nan nima zan mutu ne irin na Maama narhhh ko???" Da sauri Majeed ɗin ya rufe mata bakinta shima yana danne nashi bakin da ɗaya hannun sa da yaji kukan shima na dab da subce masa. da sauri Ummiensa ta miƙe daga wurin da take tana faɗawa kitchen itama, Ikleemerh ce tayi ƙarfin halin isa gare ta tana shirin ɗaukarta daga wurin mahaifin nata, dakatar da ita yayi ta hanyar girgiza mata kansa, rungume kanta yayi sosai yana tunawa da Ameenatou mahaifiyar ta,  Wanda yake mata wani irin mahaukacin SO da ƘAUNAR da be taɓa tsammanin zema wata halitta bayan taba. Ɗaukarta tsam yayi yana yin woje da ita bayan ya furta mata. "Ba zaki mutu ba In sha ALLAHU Ummiena...." Dake sunan ummin ameenatou ɗin tace yasa mata, wanda shi kuma da ita ya niyar yima takwarar, amma tace ita dai ya saka sunan ummien, idan ta sake haifa musu wata Babyn ya saka nata sunan amma ummien first kafin ita. Kai tsaye wajen parking manyan motocin gidan ya nufa, wata Black Bentley ya faɗa tana jikinsa yake driving zuwa hospital. Yana zuwa shi da kansa ya wuce da Ayla wani special room ya ɗaura mata ruwa, bayan wani lokaci ya cire mata ya ƙira wani Dr Saif ya kwanta yace ya zuƙi jininsa ya ƙarama Ayla da nata yayi ƙasa sosai, ana dibar jinin nasa ya miƙe zaune tare da  ziro ƙafafunsa ƙasa ze sauƙa, saurin dakatar dashi Dr Saif ɗin yayi yana me furta. "Zaka ɗan huta ne Sir. Domin akwai buƙatan ka huta ɗin, zan maka allura ne.... Da hannunsa yayi amfani wajen dakatar da Dr ɗin daga dogon sharhin da yake koro masa, kafin cikin zurfin murya yace. "Bana buƙata...." Daga haka ya fice bayan ya ƙira pooja yace ta kula da Ayla. Kai tsaye ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa, zuciyarsa na masa bugun da bai san kona minene shi ba, Sedai yana zuwa yaga bata nan, ya jima yana ta dube duben inda zai ganta amma be gani ba, duk da zurfin cikinsa amma se da ya magantu ya tambaya wata nurses, "Mr MAANAL FA?...." Da farko da nurses ɗin daburcewa tayi don bata san wacece kuma Mr MAANAL ɗin ba, har seda ya dafe goshinsa kana yace... "Dr ameenatou...." Jikinta na ɗan rawa da bakinta tace. "Mijinta ya zo ya tafi da ita...." Rumtse idonsa yayi yana rike kansa dake ɗan sara masa yana soma haɗa hanya ya fice a room ɗin.  Drectly office nashi ya wuce  yana zubewa saman doguwar kujera, Kai tsaye wani hawaltaccen bacci nayin gaba da shi, masu cike da kalan wasu surkullen mafarkai marasa kan gado....

Wajajen sha biyu ya farka a firgice  sakamakon wani irin mummunan famarkin da yayi,  Rumtse Idanunsa yayi gamm tare da ƙara ƙankame jikinsa wuri guda,a ƙalla ya ɗauki sama da minti uku zuwa biyar kafin ya saki  ajiyar zuciya. Amma  baiyi motsin kirkiba balle kuma ya iya furta wata kalma. Sosai mafarkin  ya firgita shi, in banda tsuma babu abinda jikinsa ke faman yi sai uban zufar dake yanko masa ta ko ta ina. Idanunsa da suke a lumshe ya ware tare da ƙurama wuri guda ido tamkar Anan ne za'a faɗa masa fassarar mafarkin da yai. Kafin ahankali ya riƙe kansa da hannuwansa biyu da yake jin tabbas yana gaf da samun matsala, indai har zaici gaba da shiga irin wannan attack ɗin. kwanciya yayi daga jikin sofar  don gani yake daya  koma ɗin mafarkin da yai zai kuma maimatuwa ne. "Ya Rabb" ya faɗa yana ci gaba da adda'o'i cikin ransa... Ya dau lokaci zaune a hakan kafin ƙarar shigowar ƙira cikin wayar nasa ya sanya shi buɗe idonsa da suka gama  galabaituwa sosai, Ahankali ya janyo wayar tare da shafa screen nata, take kyakkyawar Pics na Ayla ya bayyana.  ganin sunan Dr Bilal ne ya sanya shi 

ɗaukan wayan ba tare da yace komai ba yayi shiru. Kamar da 3 minutes ya janye wayar daga kunnen bayan ya furta. "Karka dawo ka tabbata a airport ɗin indai se nazo ɗaukar kane...." daga nan ya  shige bathroom babu jimawa ya fito ɗauke da alwala, kai tsaye yana fita zuwa masallacin da ake daf da shiga sallar ma. Bayan idar da sallar ya nufa ɗakin da ya kwantar da Ayla, yana tafe yana duba  Rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa  a nutse, don ƙa'idar sace yin komi akan loƙaci tamkar yanda ya gama  gindayama kansa, don aganinsa bashi da loƙacin ɓatawa lokaci lokacinsa, komi yana yinsa  ne akan loƙacinsa  ba tare da wani ya shiga cikin woni ba, donshi mutum ne  mai tsananin bin kowacce ka'ida acikin dukka lamuransa da taka tsantsan, kai tsaye har an zare mata jinin da aka sa mata an gyara ta harda wanka,  ɗaukanta kawai yayi bayan ya furta ma Dr pooja ɗin "Thanks!" A samar lips nashi ya fice da ita, be ko bi ta kan office nashi ba ya wuce wurin motarsa. Seda ya fara kwantar da ita dake bacci take har yanzun be gama sakin taba, ya zaga ze shiga driver sit kenan sega Bilal nan ya nufo wurin yana masa tsiya, "Banza da wani bauɗaɗɗen halinsa, da baka ɗauko ni ba gani na kawo kaina se ka mutu...." Ko kallar inda yake bai yi ba ya faɗa cikin motar yana mata reverse yabar wurin. Kansa kawai Dr Bilal ɗin ya girgiza a ransa yana cewa. _ALLAH ya taro ka ABDOUL-MAJEED...._   daga nan yayi cikin asibitin.....

   ★..

Tun da ya ɗauko ta daga Asibitin ta rufe kanta a ɗaki take kuka, kuka irin wanda   ke gasa da soya zuciyar me yin sa, kukan baƙin cewa wai ita AMEENEERH SHEHU USMAN yau ƙaddara ta tsara mata ke ɗauke da ciki!, cikin wanda ya mata fyaiɗe tin da ganan watan cikin huɗu da kwana biyar ɗin da abin ya faru, ta gwada paisoning ɗin kanta yafi sau uku, idan ta tuna ko ta mutu bawai ta huta ko ta tsira bane,  Wannan dalilin yasa ta gama tsarama kanta za ta tsaya ta fuskanta rayuwar, tayi gwagwarmaya ta jure ta daure ta cinye duk wani maɗacin da duniyar da abinda ke cikinta zata basu, ta gode ALLAH da tin da abin ya faru  ko sau ɗaya Ahmad ɗin be taɓa koda kwatankwacin kusantarta bane, Idan kuma ta tuna cewar zasu rabu ne a duk lokacin da cikin jikinta ze bayyana tana jin kamar ba zata iya jurema hakan ba. Ahmad ɗin da tunda ta rufe kan nata yake ta famar Safa da Marwa kamo ɗakinta kamo ɗakinsa, yana cewa ta buɗe masa don ALLAH!, ta buɗe ze yafe mata komai, ze dawo suci gaba da gudanar da rayuwarsu irin ta baya, ze manta komai, ze shafe komai kamar komai ɗin kuwa be taɓa faruwa ba. A lokacin da maganganun nasa ke dukar cikin kofofin kunnenta kuwa kukanta tsananta yake, tana jin ta gama yafe kanta ta kuma haramta daga gare shi, yin Duniyar yayi ta buɗe masa amma ta ƙi ya, Dole ya kira Ya Sadeeq yazo har gidan amma taƙi saurar kowa daga cikinsu, Ina samm bata jin zata iya buɗe musu wannan ƙofar, ko kuwa so suke ta buɗe tace musu ciki ne da ita?, cikin da ba na mijin taba?, haba abin yayi munin da bata jin zata taɓa buɗe musu wannan ƙofar a dai daidai wannan lokacin ɗin.Suna tsaka da wannan danbarwar sega ƙarar jiniyar ƴan sanda nan ta gama karaɗe ilahirin gidan baki ɗaya, wanda jiniyar gaba ɗaya ba ƙaramin tasar hankulansu yayi ba,se dai banda ita. Don jima tayi kamar an yaye nata dala ne bisa kanta, tasan zasu tafi da ita ne bisa mutuwar mutumin da tasan ita ce sanadin hakan.  A ruɗe Ya Sadeeq da Ya Ahmad ɗin suka isa ga harabar gidan, Suna zuwa wani baƙi murjejen ɗan sandan da kana kallonsa kasan babu imani tattare da shi yace. "Ina mai laifin kisan take?"  Wani kalan mugun shock ne ya ziyarci Ya Sadeeq da bai san da zancen komai ba. Don haka ya duba Inspector ɗin tare da furta. "Ƴallaɓoi ko dai kun yi ɓatan kai ne?"  Jajayen idonsa Inspector ɗin ya zaroma Ya Sadeeq ɗin yace. "Ba nan ne gidan AMEENEERH SHEHU USMAN ba?, Matar AHMAD IBRAHIM SHAREEF?" tin da ya kama hasalin cikakken sunanta Ya Sadeeq ɗin ya gama sallama wa, Kafin ya juya ga Ahmad ɗin don yana buƙatan ƙarin haske dangane da maganar kisan da tazo masa a matuƙar bazata kwatsam lokacin guda.  A takaice Ahmad ɗin ya bashi labarin abinda ke faruwa daga jiya zuwa yau, har musabbabin ƙiran da ya masa ɗin kuwa. Jikin Ya Sadeeq ɗin ne ya fara wata kalan rawan tashin hankali. Kafin ya kalla Inspector ɗin yace. "Ƴallaɓoi zaku iya tafiya dani, domin wacce kuka zo wurin nata bata da lafiyar da ko fitowa da kanta ba zata iya ba, amma ni yayan tane, zaku iya tafiya dani duk hukuncin daya kama nata a min ciki kuwa koda rataya ce...."  


  "Gani nan da lafiyana Sir!, ni zaku kama domin kuwa ni ce mai laifin!!!..." 


Haka baki ɗayansu suka tsinkayi muryan Meenal ɗin data fito da fuskanta duk abin hawaye ya gama bushewa, idanunta tsabar kuka kuwa sun zurma sunyi ciki.  Ahmad ne yayi hanzarin shan gabanta yana me furta. "Wa ya baki umarnin ki fito?"  Kai tsaye tambayar da ya fara cilla mata kenan, "Sabo da ni aka zo nema!, kuma ko da ace ban fito ɗin ba dole zasu fito dani........" Ta sake faɗi tana ƙoƙarin nufar kwalawan. Kyakkyawar Garkuwa Ahmad ɗin ya bata ta hanyar tare gabanta da yayi daga shirin miƙa kanta ga kwalawan da dake, Zuciyarsa harya fara tafasa yace "Zaki koma ne ko se na saɓa Miki?" Ya sake faɗi daidai janye san da wani police yayi daga gabanta. Ya Sadeeq ne ya iso gabansu yana sake shiga tsaƙiyar police ɗin da ita. Cikin ɗan yanayin fusata yace."Na ce muku da nine wanda zaki tafi ba ita ba amma" Ganin renin hankali da wasa da aikinsu da duka su biyun ke yi ne ya saka Wannan ƙaƙƙarfan police ɗin buga musu tsawa, yana me furta "I like that..."  Daga haka yama macen dake tare dasu inkiyar ta kama Meenal ɗin, hakan kuwa akayi ta kamo hannunta tana zira mata Onka. Wani irin rinewa idanun Ahmad yayi zuciyarsa na ƙoƙarin masa bindiga. Kafin ya isa gabanta ya ce. "Abin da kike zaɓa kenan?, kariyar da muke shirin baki kika ture Meenal?, Kika zaɓa tozartamu da ƙasƙantar damu a idon duniya?...." Ya faɗi hawaye na zubo masa. Hannayenta duka biyun dake cikin onkar ta sa tana goge nata kwallar da ya ciko nata idon, kafin cikin ƙarfin gwiwwa da yaƙi ni tace. "Ko da ace ban yi hakan ba bazan taɓa tsira ba Ya Ahmad, dole gaskiya tayi halinta, dole komai ya bayyana, Me bi wannan ita ce zata iya zama magana ta ƙarshe da kai Ya Ahmad, domin kuwa na san koda na fito bayan gaskiyar komai ya gama bayyanuwa doke zaka rabu dani, domin abinda ke ɗauke a jikina da kasancewar sa ɗan duma ko an ɓoye se ya bayyana. Abinda kawai nake buƙata daga gareka shi ne Adda'a da fatan Alkhairi, tare da Adda'ar zaɓin  abinda shine mafi Alkhairun mu garemu. Tabbas dukkan ayyuka suna tabbata ne da niyya,kuma Lallai ko wanne mutum yana samun  sakamako ne na abinda yayi niyyar, Ubangijii ALLAH yana gani kuma shi ne wanda zai bani kariya, karka ji komai, domin nie a yanzun babu abinda nake jin ɗin kuwa... Face na bayyana gaskiyar abinda yake akwai ciki kuwa harda bayyana cikin dake jikina daya kasance na wannan dabbar ne...." Ji da ganinsa ne suka nema ɗaukewa lokaci guda, me take nufi da cikin jikinta?, tana nufin ciki ne ke ɗauke a cikin cikin nata irin na haihuwar ɗan mutum dai?,  me ya sa shi da ita bata taɓa fada masa ba?, me yasa be taɓa lura da hakan ba da suna zaune gida guda har cikin yayi wannan watannin a jikinta be sani?, Haba No wonder ranar yayi ta kallarta, ramar tayi yawa, zafgewar bici ace ta iyaka damuwar da take a cikinta bace, shi kuwa me yasa be tsaya ya fuskanta matarsa ba, me yasa fushinsa gare ta har ya bari yaja lokaci haka?..... Kansa ya riƙe yana ɗan jujjuyawa   yana ambatar Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un a cikin kansa.  Idanunsa na dishi dishin lumshewa   yake ja baya yana cewa kar ta masa haka, karta yarda ta sako maganar cikin nan, nashi ne!, na shi ne!!, Ze amsa yana son ta yana son duk wani abu daya kasance tsatson tane.... Yana ji yana gani suka tafi da ita, tafiyar da ita ce farko da kuma ƙarshen rayuwa da duk wani farin cikinsa, tafiyar data tafi ta barshi na har abadan da dama ta riga ta gama ambata mishi, Kuka ya saki a wurin tamkar wani ƙaramin yaro yana buga kansa da jikin biyar settline ɗin dake tsakar compound ɗinsu, Ita kuwa zuwa lokacin idanunta sun gama ƙaiƙashewa  sun bushe babu alamar hawaye, domin zun riga da sun gama zubar da iyaka ruwan da zasu gama zubar wa ɗin, sun soye kuma yanzun sun ƙaiƙashe, bata jin kuma akwai abinda ze sake sakata kuka yanzun. Da kanta tana layi tana komai ta shige cikin motar suka buga suka bar gidan da ita. Ya Sadeeq ne yayi hanzarin yin kan Ahmad ba wai dan shima tashi zuciyar na cikin sauƙi da nutsuwa ba, sedan haƙurin daya gama bata ya jure ya taya ƙanwar tashi gwagwarmaya, ya taya ta yaƙin har se inda ƙarfinsa ya kare shi ma. Ciki ya shige da Ahmad bayan ya ƙira gidansu ya sanar da iyayensa abinda ake ciki, kafin kiftar ido sega mahaifinsa a gidan, wannan ne ya saka Ya Sadeeq ɗin tafiya shima domin ya fara binciken Inane inda aka kai ƙanwar tashi. Se dai duk wata HEADQUARTERS ɗin daya sani dake cikin garin KANO ya gama zagayesu, se dai babu ita babu me ko alamarta. Sosai hakan ya tashi hankalin sa goshin zuhr ya isa gidansu, Daga yanayin yacce mahaifinsa ya ganshi a jigace ne yasan cewar ba ƙalau ba, seda ya fara shan ruwan da Baffan ya bashi ɗan huta kaɗan kana yake tambayarsa ko lafiya?... Kora masa bayanin duk yacce ake ciki yayi, se dai ya ɓoye zancen cikin da yaji ta furta kuwa, tin da bai da tabbacin hakan ne koba haka ba, ALLAH sarki take Baffa shima ya shiga wani kalan zallar tashin hankalin da ba'a sa masa rana. Kafin ka me se gashi har ya haɗa kan almajiransa ya saka su sauƙar Alqur'ani me girma, cikin gidan ya wuce yake gwaggo Sadiya ta dafa shinkafa jallop kamar kwano uku, tana gunguni tana komai ta miƙe ta ɗora don wllh ita ta tsani wannan saka aikin na Baffan, da sai kana zaune kwatsam se ɓallo maka da aiki bayan kana murna ka kammala naka, gashi babu damar musu don duk tsiyarta tana shakkarsa ai, ɗan kwalin dake ƙoƙarin zame mata  ta gyara tana cewa. "Se ka bani kuɗin kayan miyar ai dubu uku..." Ganin kuma yana kallonta da kanta yasa ta tsargu don haka tace "To ai kowacce kwana kayan miyar dubu take ci, amma ba sai ka bada kuɗin mai da magi ba muna dasu...." Ta ƙare maganar da susar kan da kana kallarsa kasan bana gaskiya bane, don kar a gano ƙaryar data labta ne. Kansa kawai ya jijjiga ya fiddo ukun harda ƙarin ɗariya biyar yace ganan yacce zefi isa ma, yasa kansa ya fita. Yana fita ta ƙira Bilkisu dake daki  ta bata 1500 bayan ta zare dubu biyu, tace a mata malkaɗe bashi ɗaya kulli uku na  ɗari biyar biyar gida uku, iya zallar tattasai da da tarugu. Shimar nata ta koma ta ɗauko a cikin ranta tana ma Ummar nata fatan shiriya, don duk maganar da suka yi tana jin su. Fita tayi taga gidan har ga gota Baffan nata da sai da ta masa sannu ya ƙiranta, wanda se da ya saka gabanta faduwar ko tambayar ta baffan nasu zaiyi, duk da dai bawai hakan yake mata ba. Tsugunne takai tana cewa "Baffa gani!" Dubu ɗaya ya zaro daga cikin aljihunsa yace ta taho da ciyawan shayi ta ɗari biyar ta dafa mishi shayi me ɗan dama, bayan ya tambayeta ai suna da sugar tace ehhhh kana yace to ta riƙe ɗari biyar ɗin, godiya ta mishi tana miƙewa ta tafi aikar nata.


  Babu jimawa ta dawo ta wuce ta bama Ummun nata markaɗen, kafin itama ta nema tukunyanta me kyau me ɗan girma ta ɗora, koda uwartata ta tambayeta me zata yi, tace Baffa ne ya sakata dafa masa shayi, yi tayi kamar tayi magana amma kuma ta fasa tana ɗaukan wata babban tukunya itama ta ɗora. Kafin kace me sega gidan ya ɗauki ƙamshin girkin gwaggo Sadiyan, ita kuwa tuni dama Bilkisu ta gama dafa shayin ta juye a wata babbar cooler. Ta nemi wankakkun ƙananun kofuna ta ɗora a kai ta ajje daga bakin ɗakin Baffan nasu ta shirya a gurguje ta wuce Islamiyya, ita kuma dama  Shareefah tana school dake Monday ce tana can ba kuma zata dawowa ba se Friday, weekend kawai take zuwar musu. Bayan  idar da sallar la'asar Baffa ya saka manyan almajirai fitowa da abinci da shayin da aka dafa, nan gardawan ciki suka ringa zuzzuba musu abincin da shayin, bayan sun kammala ci aka kuma taruwa aka yi adda'an ALLAH ya kawo musu komai da sauƙi...


★..


Tafiya yake cikin yanayin da kai baka isa ainihin gane masa ba, domin kuwa wannan moody face ɗin nashi  da kullum haka zaka ganta babu murmushi balle dariya, ita ba'a ɗaure ba ita kuma ba'a sake ba. Gaba ɗaya tin da ya kama kallar labaran maka yarinyar da tayi sanadiyar mutuwar ɗan gidan senator Garba Aliyu na Yaya a kotu, yaji hankalin sa ba'a kwance ba. Ya rasa abinda yake masa daɗi haka kawai kawai, a ransa tunani yake don me yasa ba asibitin zasu kai ƙaran ba?, ai ba iyaka yarinyar bace likita a cikin asibitin, me yasa basu kai kowa ba se ita? Sune jerin tambayoyin da yake tama kansa. Gaba ɗaya lissafinsa nemar kufce masa yake akan al'amarin, gani yake idan har be shiga cikin case ɗin ya kwatarma da yarinyar ƴan cin ta ba to shima yana da nashi kamisho ɗin zunubin ne. Wayarsa ya fidda ya saka ƙiran Dr BILAL lokacin da yake kaiwa zaune cikin motarsa, lokacin kuma wajajen tara da rabi ne na dare. Wayan nata ring baya ɗauka don haka kai tsaye kawai yama motan key ya fita daga gidansu.  Asibitin ya nufa directly, Lokacin da ya isan kuma goma saura, ganin motar Dr Bilal ne ya bashi tabbacin yana cikin asibitin kenan, kai tsaye office na Dr Bilal ɗin ya nufa ganinsa da yayi zaune gaban computer yana ta famar aiki ne ya saka shi jan tsuƙa, ya ƙaraso ya zaune yana janye computer ɗin dake gabansa yace. "Uban me kake da kana kallar ƙirana baka daga ba?"  Wani kallo Dr Bilal ɗin ya watsa masa yana furta. "Aikin daka aiken ɗan renin sense kawai, bani computer na woni aiki me muhimmanci nake, ƙirarka kuma ban gani ba ne Malam...."  Seriously ya dawo yana fuskantar Bilal ɗin, kafin cikin ɗan ƙaramin sautu yace. "Ƙarin bayani zaka bani game da ita...." Daidai nashi Dr Bilal ɗin ya dawo yana me furta. "Game da?..." Don shi ma bai gane ko waye yaje nufi a kai ba. "Ita yarinyar da case na su sen  Garba Aliyu ke kanta...."  Wani numfashi Bilal ɗin yaja yana me furta yanzun ma shi ne aikin daya riƙeni, don da magribar nan Yayanta yazo cikin asibitin yake tambayana game da ita, wai kwalawa sunje har gidan mijinta sun tafi da ita, kuma ya duba duk wata headquarters na ƴan sanda bai sama labarin taba, bayan tafiyansa nima nake kallar labaran kama ta ɗin da aka yi shi ne ma dalilin da yasa na yi busy kenan..."  Wata iska daga cikin bakinsa ya fesar tare da miƙewa tsaye, yana cewa "Kafin zuwa wayewar gari kayi gaggawar gano inda suka ɓoyeta,nd kuma shi ina banzar mijin nata yake da har zasu shigar masa har cikin gida su tafi da ita, da ba zai dakatar dasu ba...."  

 

 "Yayi duk yacce zeyi dan ya bata kariya shi da Yayan nata dana ce maka yazo, amma Ita yarinyar ne ta ƙi aminta har ta bayyana kanta gare su...." 


Kafaɗunsa ya ɗaga alaman bashi da damuwa ya fice, shi dai abu daya kawai yasan zai tsaya mata akai shi ne kare martaba haƙƙinta na wacce aka zalumta...

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215


Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post