💋💋💋💋
*JIN DADIN RAYUWA*
(Romantic story)
Mom Islam
👉Idan baki da aure karni karantamin littafi na matan aure ne.
Join my comments section 👇
https://chat.whatsapp.com/KniyTO2M0rBE6IEUy7YVRW
Page 5-6
Zuhrah ta gyaɗa mata kai, kana ta fice taje ta ɗauro alwalah, kana tazo ta kabbara sallah, bayan ta idar Hajiya Halima suna kiranta da mama, ta ƙwala mata kira tazo ta daukar musu abinci, Zuhrah ta miƙe bayan ta amsa ta ɗauki abincin ta kawo ɗaki,
Tuwon masara ne miyar kuka, Umma taja dogon tsaki mtswww... Tare da cewa "Allah wadaran naka ya lalace, Zuhrah kinga rayuwa ko? nifa na fara zargin Halima tanada farar ƙafa dan tunda Alhaji ya aurota muka daina cin abu mai daɗi,
Zuhrah tace " Umma komai na Allah ne, talauci da arziƙi duk na Allah ne, sannan babu wani ɗan adam da ya isa yayi wa wani abu idan ba da nufin Ubangiji ba, kuma jarabawa ce Ubangiji yana gwada imaninmu ne wllhi"
"Dalla can rufemin baki, Shiyasa naga akan maluntarki kinyi baƙinjini kinƙi auruwa, babu wanda ya taɓa zuwa yace yana sonki"
Umma tayi maganar cikin hassala,
Zuhrah tayi shiru bayan ta janyo kwanon tuwon gabanta,
Ta fara ci a hankali, har ga Allah miyar babu daɗi ko kaɗan gata tsululu kamar an wanke kai, haka nan ta dinga tura tuwon tana da gwalar miyar,
Umma kam ko loma ɗaya bata kai bakinta ba, dan ba wani cin tuwon take yiba, a hakan tasha kwana da yunwa, baya wani basu wadataccen kudin cefane daga bayanan,
Bayan Zuhrah ta wanke hannu ta dawo Umma ta miƙa mata rubutun dake cikin gora, ta karɓa, zuciyarta cike da tararradin me Umma ta bata, duk da tasan a iya tsawon zaman da tayi da Umma bata taɓa tsangwamarta ko hararta ba, sannan babu abinda take nema ta rasa, dan Umma tana iya bakin ƙokarinta gurin ganin ta yi mata wasu abubuwan, matsalar Umma kwaɗayi da hangen nesa,
Shan rubutun tayi kai tsaye tare da bismillah, kana ta ajiye gorar bayan ta gama sha, Umma tace ta shafa a fuskarta, ta shafa kamar inda Umma ta umarceta,
"Zuhrah..."
Umma ta kira sunanta,
"Na'am Umma"
Zuhrah ta amsa tana sauraren Umman,
Umma tace "abinda nake so ki sani, ki bawa duk wani wanda ya nuna yana sonki dama ya dinga zuwa zance, kina ji kina gani sa'anninki zasu yi aure ke kina gida, ya kamata ace a yanzu kina taimakona, kina ganin halin da nake ciki,
Dan Allah Zuhrah karki dinga wulaƙanta mutane, ke ba abin sha'awa bane ki ga kin fi kowa aji da ado, ki duba kiga duk yawancin kayanki sunsha ruwa, babu wani mai kyau wanda zaki fita biki ko wani taro, dan haka nake so kema ki fito kamar kowace budurwa, kinga Shahida wannan yazo wannan ya tafi, wlhi haka samari suke yi mata layi, amma ke ban taɓa jin wanda yazo yace yana nemanki ba"
Sosai Zuhrah ta ɗauki shawarar Umma, dan itama abin yana bata sha'awa taga ƙawayenta suna fita hira, ko kuma idan sunje islamiya taga sun yi ƙarya zasuyi fitsari sai suje suyi waya da samari,
Hakan yana damunta bata taɓa furta wa ba, kenan Umma maganin farinjini ta bata,
Ta daɗe tana tunani, daga ƙarshe dai sukai sallahr isha'i, suna nan zaune Alhji Muktar yayi sallama,
Umma na daga ɗaki ta amsa tare da ɗaga kanta sama tana leƙe ko ya shigo da wani abun a hannunsa,
Babu komai a hannunsa, gashi rabon da ta mallaki dubu ɗaya nata na kanta har ta manta, hakan yasa take son ko ita bata samu ba, taga Zuhrah tana taimaka musu, dan ita kanta bawai tanada wadatar kayan bane...!
Mom Islam
