💋💋💋💋
*JIN DADIN RAYUWA*
(Romantic story)
Mom Islam
👉Idan baki da aure karaki karantamin littafi na matan aure ne.
Join my comments section 👇
https://chat.whatsapp.com/KniyTO2M0rBE6IEUy7YVRW
Page 3-4
Doctor Zayn-Kareem ne zaune a cikin mota ƙirar Mercedes Maybach S-class, yana driving cikin ƙwarewa, haɗaɗden matashi mai ji da kyau kuɗi da kuma aji,
Doctor Zayn-Kareem fari ne amma ba can ba, yanada tsayi da faɗi, sannan yana yawan tara suma a kansa, sumar kansa sai sheƙi take ga wani ƙamshi da take fitarwa, baya yawan dariya koda wane lokaci a dake yake, yafi yin murmishi, sannan yanada kyauta sosai, kuma yanada tausayi, shine shugaba a hospital sunan hospital ɗin da yake aiki (Imperial Heart Specialist Hospital, Abuja)
Yana aiki da basirar da Ubangiji yayi masa gurin ceto ɗaruruwan rayuka masu kamuwa da ciwon zuciya da kuma waɗanda ciwon yake yi musu barazana, hakan yasa ya samu muƙami sosai da kuma Alkairai daga gurin manyan mutane, ta wani ɓangaren abokan aikinsa likitoci suna kawo masa farmaki har gida, sai dai basa samun nasara kasancewar akwai Bodyguard masu tsaronsa ciki da waje, bashi da mata ko ɗaya, haɗaɗden matashi kenan mai tashe, yana da tanƙasheshen gida a MAI TAMA Abuja, wanda aka bashi musamman saboda hospital ɗin basa ƙaunar ya matsa ko ina,
Wayarsa ce ta fara ringing, a hankali ya miƙa hannu ya ɗauko wayar idanunsa yana kallon titi,
Ji nayi yace "My Lovely Mom ya kike i Miss you wllhi"
"Miss you too my son, ga Farrah sai cewa take a kawota gurin brothernta nace soon kana nan zuwa"
Ɗan matsakaicin murmishi yayi, tare da shafar gashin bakinsa yace "hakane kam, amma har yanzu akwai ayyuka a gabana, Dady ya dawo ne?"
Momy tace "Zayn Dady kam ai sai mun gansa, kayiwa gidan ƙaura shima Dadyn yana can yana aikinsa bai dawo ba"
Zayn yace "to shikenen Momy ina driving ne idan na tsaya zamuyi waya"
Momy ta katse kiran, shi kuma ya mayar da hankali sosai ga tuƙi,
RUGAN JULI dake nan Abuja
Hajiya Baraka ce zaune a ɗakinta, ɗakin ya kasance babba an shinfiɗa carpet wanda ya rufe duka filin ɗakin, daga gefe kuma madaidaicin TV ne na bango, ga dukkan alamu baya aiki, sai kujeru idan nada dinnan sun kewaye palon, Hajiya Baraka tana zaune a ɗaya daga cikin kujerun, Zuhrah kuma tana zaune acan gefe hannunta riƙe da reza tana yanke farce,
"Zuhrah zo nan"
Hajiya Baraka ta kira sunanta tare da yi mata nuni da gurin zama,
Bayan Zuhrah ta zauna, Hajiya Baraka ta dafa kafaɗarta, cikin ƙasa da murya tace "idan an shiga sallar magriba kije gurin Malam mai almajirai ki karɓo ruwan rubutu kice masa inji ni kuma ki saka a hijabi karki babu kowa ya gani kuma karki nunawa kowa"
Zuhrah tace "to Umma baki da lafiya ne?"
Umman tace "eh to nidai kawai kiyi abinda na saki bana neman wani dogon zance"
Ana ƙwala kiran sallah Zuhrah ta miƙe, sai da aka shiga sallah ta fita, da fitarta ta samu malam ɗin yana nan zaune hannunsa riƙe da carbi, yana ganin Zuhrah ya ɗauko wata gora ya miƙa mata, ta karɓa kana ta juya ta koma ciki,
Zuhrah ta wuce ɗakin Umma da maganin, babu kowa a tsakar gida,
Umma na ganinta har ta tayar da Sallah ta yi sallama tana daga tsaye, kafin tace "ajiyemin shi can gefe, idan kinci tuwon dare karki sha ruwa da yawa kinji...!
Mom Islam
