💋💋💋💋
*JIN DAƊIN RAYUWA*
(Romantic story)
Mom Islam
👉Idan baki da aure karki karantamin littafi na matan aure ne.
My comments section domin ganin update 👇
https://chat.whatsapp.com/KniyTO2M0rBE6IEUy7YVRW
Page 1-2
Madaidaicin gida ne mai ɗauke da ɗakuna biyar, ɗaya na Hajiya Baraka da na Hajiya Halima, su biyun amarya da uwar gida ne, Hajiya Baraka itace babba yayinda Hajiya Halima ta kasance amarya.
Sai kitchen da kuma banɗaki dake a waje, kasancewar basu da banɗaki a cikin ɗaki, tsakar gidan malale yake da siminti, hakama cikin banɗakin nasu da kicin duka an malaleshi da siminti, sai ɗakin mai gidan Alhaji Muktar, dukkansu sunje Makkah sau ɗaya, Alhaji Muktar yana kasuwanci, na siyar da kayan abinci dan babban shago ne dashi, ada yayi tashen kuɗi sosai, dan shine manager na gidan mai ɗin wani amininsa da Allah yayi masa rasuwa, tun daga nan ya ɗan tattara kuɗaɗensa ya fara sana'ar siyarda kayan abinci, tun yana saka tebur a anguwarsu har Allah ya albarkaci sana'ar tasa ya kama shago a kasuwa, duk rabin shekara yana biyan kuɗi,
Hajiya Baraka tanada yarinya guda ɗaya, wacce asalin uwar gidansu ta rasu ta bari, sunan yarinyar Zuhrah, tun tana bakin nono mahaifiyarta ta rasu, hakan yasa Hajiya Baraka ta shayar da ita cikin so da ƙauna, kasancewar sunyi zaman lafiya da mahaifiyar Zuhrah, a halin yanzu Zuhrah tanada shekaru goma sha takwas, kyakkyawa ce ajin farko sannan tanada manyan idano, tare da gashin ido wanda ya ƙarawa fuskarta kyau, fara ce amma ba can ba, zamu iya kiranta da wankan tarwaɗa, doguwa ce tanada ƙiba marar muni sannan tanada shape mai kyau, gata da gashi sosai, sannan tanada girman nonuwa masu shape ɗin Mango.
Hajiya Halima yarinyarta itama ɗaya ce, sai dai ba ƴar Alhaji Muktar bace, da ita mahaifinta daban, dan a bazawara Alhji Muktar ya auri Hajiya Halima,
Sunan yarta Shahida, a halin yanzu tanada shekaru goma sha tara a duniya, itama kyakkyawa ce, sannan fara ce tass kamar balarabiya, sannan bata da jiki sosai kuma ba irin siririyar nan bace, tanada nonuwa amma ba manya sosai ba,
Kullum Alhji Muktar yana iya bakin ƙoƙarinsa na ganin ya kawo musu abinda zasu sa a bakin salati, da safe suna dama kunun koko da rana kuma sunayin shinkafa ko taliya ko macaroni da dai sauransu, da dare kuma sunayin tuwon masara kullum, miya kawai suke sauyawa, yau suyi miyar kuka ko kuɓewa ko kuma miyar karkashi, dan basu cika yin miyar taushe ko tuwon shinkafa ba, tunda ya samu karayar arziƙi yace suyi haƙuri a inda suka samu rayuwa, ada kusan kullum sukanyi miyar dare da nama, haka kawai ma idan ya bushi iska yakan siyo musu ganda ko Tsire, yanzu haka shekara uku kenan da faruwar abin nama sai sallah duk da ya ɗan samu canji ba kamar da ba...!
08141799224
Mom Islam 🍷
