RAGAYAR DUTSE.
Nana Haleema
Official Thriller
A 2026 Novel.
Daga marubuciyar, KWANTAN ƁAUNA, BAYA DA ƘURA, KIRAN RABO, MAI ƊAKI....
"Are you out of your mind? Duk bathrooms ɗin da suke apartment ɗin nan, you could'nt find one to use except the public one in the main palour?. What kind of nonsense is this?."
Islaha ta ɗago ta kalle sa jin yadda yake yi mata magana cikin kaushi da zafi, bata taɓa jin muryarsa a haka ba, bata taɓa ji ya yi magana mai ƙarfin wannan ba. Ko yaushe magana yake yi cikin steeze, yana yi yana basarwa. Amma yau ta ji akasin haka, har yana shouting.
Bata motsa daga inda take ba, duk kunya ta gama mamaye mata idanunta ta ce, "don Allah ka bani waje in shirya, bana so kana shigowa inda nake anyhow. Ka san dai ni ba muharramar ka bace, zuwa inda nake without permission haram ne."
Tsabar takaici bai san ya riƙo hannunta ya miƙar da ita tsaye ba. Bata yi zato ba zai yi hakan ba ko kaɗan, ta yi saurin riƙe towel ɗin jikinta, jin zai kwance.
Ya ce, "baki ji me na ce miki ba? Ina yi miki magana akan shirmen da ki ka yi kina yi min maganar na shigo ɗaki without permission?."
Islaha ta bi sa da kallon mamaki, ita dai bata ga abin ɓacin rai haka daga wajansa ba, ita ta yi tunanin bazai ji haushi ba, ita ce zata ji haushi, tunda jikinta aka gani ba nasa ba. Meye dan wani ya ganta tana wanka zai ɗaga hankalinsa haka, kamar ya ga matarsa ko wata ƴar uwarsa?.
Ita kunya take ji ta rufe ta, daga ita sai ƙaramin towel a tsaye, ga kanta ko ɗankwali babu. Ta ɗan juya baya da nufin ta ɗauko hijjab, ya finciko hannunta ya dawo da ita ta baya.
Kafin ta ce wani abun ya ce, "dan kin saba yin hakan a wani wajan, shiyasa za ki yi a nan?."
Bata yi niyar tanka masa ba, amma jin abinda ya ce sai ta kawar da duk abinda take ji, ta danne duk wata kunya da firgici ta ce, "tunda ka san na saba meye na zuwa ka same ni kana yi min shouting? Yau wani ya saba ganina ina wanka, ko ka manta har ta ya ni wankan ana yi?."
Duk da babu haske sosai a ɗakin, tana iya ganin yadda fuskarsa ta canja kamar ba shi ba. Ita wallahi mamaki yake bata, ko ina ruwansa oho.
Ta cire hannunsa da ya riƙe hannunta ta ce, "kar ka sake riƙe hannuna na faɗa maka, ka daina ƙoƙarin taɓa jikina. Ina ruwanka dan ya ganni ina wanka? Kai ya gani kana wankan, ko matarka ya gani, ko ƙanwarka ya gani da zaka damu har haka?."
"Na ga dai Islaha ya gani tana wanka ba kai ba ko, to meye na damuwa har haka?. Ai ba yau na saba ba, ka manta na saba zama dashi, ko ka manta kafin shi akwai maza da yawa da suka ganni a irin yanayin da ya ganni?."
"Meye naka, abu ne da na saba wannan ba komai bane a wajena. In na ga dama zan kwance towel ɗin jikina in fita kan titi, rayuwata ce ba taka ba, jikina ne ba jikinka ko na matarka ba. Kaf mutanen duniya in na yi niya zan iya nuna musu jikina, kuma bai shafe ka ba, tunda ba aurena ka ke yi ba."
Ka bani waje don Allah, ka kuma daina yi min ihu. Babu ruwanka da duk abinda zan yi, rayuwata ce ai ba rayuwarka. Ka je waje!" Ta faɗa bata yarda sun haɗa ido ba, tana nuna masa ƙofar da zai fita daga ɗakin.
Gabaɗaya ta kashe masa baki, ya kasa magana sai kallonta da yake yi. Bai san abinda ya saka yake jin zuciyarsa tana zafi akan kalamanta ba, ya san dai gaskiya ta faɗa, ta saba wanka da maza, shi shaida ne akan hakan, amma bai san dalilinsa na jin haushi ba.
Daƙyar take iya jurewa take komawa mara kunya a gabansa, tunda a haka yake kallonta bata so ta canja masa tunani, shine ya saka ta zama haka ta ƙarfi da yaji, bata so ta canjawa mutum tunanin da yake yi a kanta. Tunda ita ƴar iskace a idanunsa, aje a hakan.
Maganarta ce ta dawo da dashi daga duniyar tunani, ya ta ko ya zo kusa da ita daf da daf, yana kallon fuskarta ta ƙaramin hasken ɗakin ya ce, "mazan kan titi zasu iya ganin ki, haka ki ka ce ko?."
Yadda ya yi maganar sai da gabanta ya faɗi, gashi ya matso kusa da ita daf da daf, ga shi daga ita dai towel. Ta ɗan ja baya kaɗan ta ce, "zasu iya, kowa ma zai iya. Babu ruwanka."
"Kowa ma zai iya!" Ya furta yana cize bakinsa, cikin wani irin yanayin da bai taɓa jin irinsa ba.
Ya ɗan girgiza kai yana kallonta, kafin ya yi ƙasa da muryarsa, cikin soft vioce ya ce, "tunda kowa zai iya ban ga amfanin rufe jikinki ba. I can also see you without a towel" ya faɗa yana zagawa da hannunsa bayanta, ya asaka hannunsa a inda ta ɗaure towel ɗin ta baya, ya ja shi da ƙarfi ya zare shi gabaɗaya.
*******
Ya ce, "Yauwa. Za ku kawo kuɗin ko mu kashesa? Baza mu ƙara mu ku lokaci ba, in dai ba a kawo kuɗin nan ba, sunan ɗanku gawa!."
Baffa zai yi magana Islaha ta firgita ta fizge wayar, cikin kiɗima da tashin hankali ta ce, "Kar ku kashe sa, zamu kawo mu ku in sha Allah. Kar ku kashe Hamma. Ku ƙyalesa zan nemo kuɗin na kawo."
Islaha ta cillar da wayar, jikinta yana rawa kamar wacce aka jonawa wutar lantarki.
Ta gyaɗa kai tana kallon Baffa ta ce, "Baffa zan nemo kuɗin, zan yi komai saboda Hamma."
Baffa ya riƙe kafaɗunta ya ce, "ba ki da hanyarsu Islaha, ba naira dubu tamanin aka ce ba, ba dubu ɗari takwas aka ce ba, ba miliyan takwas aka ce ba. Miliyan tamanin suka ce. Miliyan ɗaya sau tamanin, baki da hanyar da zaki samu. Ki karɓi ƙaddara kawai. Ba a kansa aka fara kashe mutane ba, shima ki bari su kashe shi ya fi alkhairi."
"Bazan iya ba Baffa, zan nemo kuɗin a ko ina ne, na yarda zan yi ko me ye indai zan samu kuɗin fansar rayuwar Hamma!" Ta faɗa tana fita a guje.
Baffa ya ce, "Sadik bi bayanta don Allah." Da sauri ya bi bayanta, ya samu zata fira daga gidan, ya yi sauri ya cimma mata. Ya ce, "ina za ki je?."
Murya tana rawa tana kuka ta ce, "zan je na samo kuɗin ne."
"A ina zaki samu? Baki da hanyar da zaki samu wannan kuɗin."
Sai ta fashe masa da sabon kuka ta ce, "haka zan bar Hamma kenan a kashesa a banza, haka zan bari Hamma yana neman taimako na ƙyalesa?. Ni bazan iya ba, wallahi bazan iya ba" ta faɗa tana rufe fuskarta da hannunta tana kuka sosai.
Sadik ya ce, "haƙuri za ki yi, babu abinda za ki iya a kai"
Bata ce komai ba sai kuka, sai da ta ga ji sannan ta ta kalle sa ta ce, "ina da mafita, ban sani ba ko za ka bani goyan baya akan hakan." Ya kalle ta ya ce, "indai hanyar bata saɓawa addini ba zan amince, ina jinki." Ta ja numfashi ta sauke, ta rufe ido ta buɗe tana kallonsa cikin jin nauyin abinda zata ce.
********
Jikinta rawa yake yi, ga sanyin a.c da ya yiwa yanayinta yawa, ta cure a waje ɗaya tana kuka mai tsuma zuciya.
"Na shiga uku, na shiga uku. Ina zan saka kaina, me na aikata haka, ya aka yi na bari hakan ya faru?......" ta sake fashewa da kuka, ta riƙe bedsheet tana ji kamar ta shige ciki saboda rashin sanin abinda zata yi, ta juya kai ta ce, "My dignity gone for no reason. My life is a mess already, my life is scattered.......me na yi, me na aikata, What i have done to deserve all this, Why!" Ta faɗa tana kuka sosai wanda sautinsa yake fita.
Wani irin juyi take yi tana kuka, zuciyarta tana bugawa sosai.
"Na yiwa Hamma alƙawari, na ce zan riƙe masa kaina, amma kasa cikawa, na kasa. Ka yi haƙuri Hamma, ka yi haƙuri! Ba a son raina bane. Na yi duk saboda kai, saboda kai ne Hamma!" Ta kuma faɗa kamar yana gabanta tana kuka mai tsuma zuciya.
*******
Daidai lokacin da hawaye ya sakko daga idanun Islaha, muryarta tana cracking ta ce, "Hamma!."
Ya lumshe ido yana jan numfashi daƙyar, ya buɗe ido ya sake kallonta ya ga tana kuka sosai hawaye wani yana bin wani.
A hankali ya ja da baya, zai rufe ƙofar ta yi hanzarin tarewa ta hana shi rufewa, tana girgiza masa kai ta ce, "Hamma ka tsaya ka saurare ni, kar ka yanke min hukunci cikin fushi. Ka tsaya ka ji abinda zan faɗa maka, na san na ɓata maka rai amma ka tsaya ka ji uzurina, na tabbatar zaka fahimce ni. Don Allah Hamma ka dakata, kar ka riƙe ni a ranka. Wallahi saboda kaine, saboda ceton rayuwarka ne!."
Kasa rufe ƙofar ya yi, ya lumshe ido yana jin yadda take magana cikin kuka da rawarta tana murya.
Ya buɗe ido bai kalle ta ba, ya sake ƙoƙarin kulle ƙofar ta buɗe ƙofar da ƙarfi, ta shiga ta tsaya tana kallonsa.
Ta haɗe hannayenta guda biyu ya ce, "na san na yi kuskure, na san kana jin zafi a ranka, amma don Allah ka yi haƙuri, ka tsaya ka ji abinda zan faɗa maka, na tabbatar zaka fahimce ni."
"Ba na faɗa miki ki bari su kashe ni ba, meyasa ki ka sadaukar da rayuwarki a kaina, Islaha!."
"Bazan iya bari a kashe ka ba Hamma, zan iya sadaukar da raina a matsayin a kanka! Shiyasa...shiyasa..shiyasa...kawai na amince.....na karɓi.....kuɗin......"
"Babu abinda za ki ce min Islaha! Kin ɓarar da yarda da na yi miki, kin lalata amincewar da na yi a kanki! Ki fita ki bani waje, bana son ganinki!" Ta faɗa cikin murya mai amo yana nuna mata hanya.
Safeera ta goge idanunta, ta dafa kafaɗarta ta ce, "tashi tsaye Islaha."
Ta miƙe a hankali ta kalli Safeera ta ce, "Na faɗa miki daman ni ba ƴar halak ba ce, jikina yana bani a......"
Safwera ta rufe mata baki ta ce, "kar ki ƙara faɗar haka. Allah ya san zuciyarki, nima na san silar abinda ki ka aikata, Sadik ma ya san dalilin yin. Mu mun san rayuwarki ki ka sadaukar saboda Saheer, shima kuma zai amince ki, amma na faɗa miki sai ya nutsu sosai."
Islaha ta kwantar da kanta a kafaɗar Safira ta ce, "Ko magana yaƙi ya yi min, yaƙi ya kalle ni. Na yi dansani ya fi cikin kwando Safeera."
Ta ɗan tapping bayanta ta ce, "ki yi haƙuri, ki daina kuka. Allah yana tare dake."
Ta goge hawayenta bata ce komai ba, ta ɗauki handbag ɗinta, sai kuma ta dafe kanta saboda yadda ya sara mata. Ta ce, "Kaina yana ciwo, mumfashina baya fita daidai."
Safeera ta ce, "babu lafiya kam. Tun ƙarfe bakwai da rabi tana unguwar nan, ta zo wajan Saheer amma ya gaza fahimtarta."
Sadik ya ce, "Islaha Saheer bazai fahimce ki yanzu ba, Saheer ba a nutse yake ba kwata-kwata, yana buƙatar lokaci kafin ya gane abinda zaki faɗa. Abu ɗaya yake kallo a yanzu, kin ci amanarsa, kuma su Mama suma sake ɗora shi akan hakan. Dole sai kin sake haƙuri na wani lokaci. Ke kin san halinsa, na tabbatar zai amince dake da zarar ya nutsu yadda ya kamata."
Safeera ta ce, "amma ni ya bani mamaki, ai ya san wacece ita ko? Ya san duk a kan karɓo shi daga hannun masu garkuwa da mutane ta aikata abinda ta aikata."
"Ba goyan bayansa nake yi ba Safeera, amma ina so ki tuna abinda ta aikata saboda shi. Yana jin zafi a ransa, yana jin haushinta, ni dake ne kaɗai muka san abinda yake faruwa shi bai sani ba. Ku bashi dama ya huta tukunna, in ya huta zan yi masa bayanin komai daki-daki."
*******
Baƙin ciki ya mamaye mata zuciya, ta miƙa masa wayar, ta miƙe tana zaga falon cike da tunanin mafita. Ta rasa yadda zata yi da Rehaan, kuɗin da ya kamata ace ƴaƴanta ne suka yi shine yake mallakarsu. Hakan yana taɓa zuciyarta, yana sakawa mata baƙin ciki da hassada.
Mama ta ce, "ya aka yi haka yake faruwa, Ya aka yi abubuwa suke jagule mana ne Sameer?. Rehaan fa, kai kanka ka girmesa da shekara ɗaya. Ya aka yi yake samun ɗaukaka, bayan ku ne manya a cikin gidan nan?."
Sameer ya ce, "wallahi zamansa a england babbar illa ce a gare mu, ni ban yarda ba dukiyar Abba ce a hannunsa ba. Ta ya yaro ƙarami ace ya mallaki abinda mahaifinsa bashi dashi, Hamma Zayyad da yake babba bashi dasu, mu ma da muka biyo baya bamu dashi. Kina jin wannan kin san haɗawa aka yi, gabaɗaya dukiyar Abba tana hannunsa, mu muna nan an haɗa mu da ƙananun abubuwa na banza. Babu damar mu yi magana sai ace ai shi a nan ya girma ba, shi a a can aka haifesa, a can yake kasuwancinsa da sauran shirme. Mama in muka zuba ido, kaf dukiyar Abba da take can zata zama haram a gare mu."
Mama ta girgiza kai ta ce, "ya aka yi hakan yake faruwa, ya aka yi abubuwa suke lalace min ne?. Meyasa na kasa ɗaukar mataki akan Rehaan, meyasa yake shigar min hancina na kasa fato shi?."
Sameer ya ce, "dole a san abinda za a yi, bazai yu kina babba a gidan nan, muna manya a gidan nan, ace komai yana hannun Rehaan ba, dole ki san yadda zaki yi ya dawo nigeria, in ba haka ba wallahi muna ji muna gani komai zai fi ƙarfin mu."
"Ƙarya ne wallahi, yadda ku ka kasance manya a gidan nan babu wanda zai samu ɗaukaka sama da ta ku, dole a dakusar da ɗaukakar Rehaan, dole Rehaan ya dawo ƙasar nan.."
"Ɗaukaka ta nawa kuma Mama? Sunan Rehaan da labarin Ray ina ne bai shiga ba a faɗin ƙasar nan?. Sai dai a kiyaye gaba, amma wannan ya riga ya faru. Kai tsaye ki samu Daada da wannan maganar, dan ita kaɗai ce zata zama silar dawowarsa ƙasar nan har abada."
Ta girgiza kai cike da gamsuwa ta ce, "yanzu nan zan je na same ta, indai a kan ganin bayan ɗaukakar Rehaan ne babu abinda bazan yi ba Sameer, zan iya sadaukar da duk abinda na mallaka dan ganin Rehaan ya dawo ƙasa, ku kun hau sama."
Sameer ta miƙe ya fita cikin gamsuwa sa kalamanta. A ganinsa ta ya ya suna manya a gidan, ƙaraminsu wanda ya zama shine namiji ƙarami a kaf gidan, ya zo ya fi su ɗaukaka.
Mama kuma ta dafe kai cikin rashin mafita, a bayyane ta ce, "Rehaan! Rehaan! Rehaan! Ka shiga rayuwata, ka hanani sakewa Rehaan, ka hanani cika burina....."
Ta girgiza kai ta ce, "Baka isa ba wallahi, baka isa ɗaukakarka ta disashe ta ƴaƴana ba, yadda na kasance gaba da kowa a matan gidan nan, dole ƴaƴana su kasance gaba da kowa a yaran gidan nan. Babu wanda ya isa ya sha gabansu, su ɗin su za a kalla aje ace su bayar, ba kai ba. Tun kana yaro ka ke bani wahala, amma a yanzu bazan barka ba Rehaan, bazan taɓa barin ka ba."
******
Maimakon ta bashi amsa sai ta fashe da kuka.
Baffa ya ce, "ki bar kuka Islaha."
"Baffa ni ban san yaushe aka yi min video ba, wallahi ban san an yi ba."
"Ki daina kuka, Hamman ki ya faɗa min an shigar da ƙara, za a nemo wanda ya yi wannan aika-aikar."
Hawaye ya zubo mata ta ce, "kowa maganata yake yi, ana ta tsine min Baffa. Kowa ya ga tsiraicina a duniya, kowa a fanko yake kallona Baffa. Zuciyata zafi take yi min."
"Ki yi haƙuri Islaha, ki daina kuka, Allah yana tare dake a ko yaushe. In ma an yi wannan abun da a tozarta ki Allah bazai bari ki tozarta ba, zai baki kariya in sha Allah."
"Baffa ai na tozarta, an gama tozarta ni a duniya. Baffa ji nake kamar na kashe kaina na huta, so nake na daina numfashi ko zan ji daɗi Baffaaaa!" Ta ƙarasa faɗa tana jan sunansa cikin kuka.
Hamma da yake kusa da Baffa ya ce, "Islaha ki nutsu, komai zai warware. Ni na tabbatar ba ke bace."
Ta ce, "Hamma ni ce, ni ce fa Hamma. Ni na san wannan jikina ne, ban san yaushe na aikata zina har aka yi min video ba. Shikenan an gama wulaƙanta ni Hamma, an cuce ni Hammaa!."
"Ya isa haka, ki daina faɗar wannan kalaman babu daɗin ji. Ki nutsu, zuwa nan da gobe komai zai zo ƙarshe."
Islaha ta ce, "Safeera nuna min video nan don Allah."
Safeera ta ce, "babu amfanin ganin Islaha, zai sake ɓata miki rai ne."
"Ina so in gani, ki bani."
"Bazan bayar ba, ki zauna."
Islaha taƙi zama ta ce, "In kina ƙaunar Allah ki bani."
"To meye abin gani a video?."
Cikin murya mai rauni ta ce, "ina so in gani."
Safeera ta sauke numfashi ta haska mata, ta karɓa tana kallo, sai ta rufe bakinta da hannunta ta zauna tana juya ido akan wayar.
Babu abinda ya banbanta da ta jikin video, komai irin nata sak da sak. Hatta abin hannun da Hamma ya bata akwai. Gata nan tsirara ana aikata alfasha da ita.
Ta girgiza kai ta ce, "Safeera ni ce, wallahi ni ce" ta faɗa hawaye yana sauka akan screen ɗin wayar.
Ta ce, "komai irin nawa ne. Yaushe na sha giya har aka yi video nan ban sani ba? Ni dai na san ban taɓa aikata zina ba balle na ce ko an yi min video."
Safeera ta ce, "Don Allah ki nutsu, ki daina wannan koke-koken."
"Dole in yi kuka, ni ce a ji ki Safeera, wallahi jikina ne. Yanzu shikenan kowa ya san ya jikina yake ko, kowa ya daina ganina da suttura sai tsirara?."
Safeera ta ce, "don girman Allah ki daina wannan kukan, ki nutsu."
Ta dafata ta ce, "Islaha meye kuma ya sake faruwa, dare ya yi yanzu sosai."
Ta kalli Safeera ta ce, "za ki iya yi min wani taimako?."
Safeera ta ce, "me zai hana, faɗa min ko meye ina jin ki."
Islaha ta motsa tana riƙe da kanta, ta ce, "ina zuwa." Ta faɗa tana shiga kitchen, ba jimawa ta dawo ɗauke da sabuwar wuƙa sai ƙyalli take yi.
Ta miƙawa Safeera ta ce, "Don Allah ki kashe ni, ki kashe ni na huta Safeera. Bana so na mutu kafira, shiyasa bazan kashe kaina ba, amma da kafin ki zo nan na kashe kaina."
Safeera cikin tsoro da mamaki ta ce, "Islaha kina cikin hankalinki kuwa, me ki ke faɗa haka?."
"Safeera ya zan yi, ni kaɗai na san abinda nake ji a zuciyata. So nake in mutu, ki kashe kawai."
"Safeera hotunan tsaraicina ne suka yawo a duniya, ga wani abinda da akace na sake yi. Ance na gayyato namiji har nan, kuma bani da bakin kare kaina, dan kowa ya ganni. Safeera ina ji in ban mutu ba bazan samu sassauci ba."
*******
Suna zaune a babban falo, sai wata babbar mace a zaune tana kallonsu tana murmushi. Ta ajjiye wayar hannunta ta ce, "bakwa burin zama a irin wannan gidan don Allah?." Suka yi shiru basu ce komai ba, ta sake yin dariya ta ce, "ku saki jikinku, babu abinda zai faru a nan. Na san kun ji daɗin kuɗaɗen da ake baku ko?."
A tare suka ɗaga kai alamun eh, ta ce, "To kun gani. Da kuna gidan marayu kuna rayuwa kamar ta bayi, abinci ma ba wani mai kyau ake samu ba. Ku kalli yadda ku ka canja, ku ka yi kyau kamar ba ku ba. Ni kaina yanzu na tabbatar muna da ƴan mata kyawawa, da an dakusar daku a waje ɗaya."
Gyaran murya suka ji, ta yi musu alamu duk su miƙe suka miƙe tsaye. Babban mutum ne ya shigo sanye da shadda fara harda babbar riga. Kana ganinsa ka ga alhaji, wanda kuɗi ya zauna yake shigowa. Ganin ƴan matan sai ya yi murmushi yana binsu da kallo, ya kaɗa kai ya ce, Kai! Kai! Kai!!. Daman haka mu ke da kyawawa ƴan mata a garin Yola kamar haka?. Zulaiha aikin ki yana yin kyau."
Ta yi dariyar farin ciki ta ce, "Godiya nake yallaɓai." Ya murmusa ya ce, "ku zauna ƴan mata adon gari." Suka zauna gabaɗayansu, ya bi su da kallo yana murmushi. Kafin ya kalli Zulaiha ya ce, "waɗanan sun yi."
Ta ɗan rusuna ta ce, "Godiya nake yallaɓai."
"Ina fatan komai daidai."
"Komai daidai yallaɓai, komai zai tafi yadda ake so. Dukkansu babu matsala, na yarda dasu ɗari bisa ɗari."
Ya kalle su ya ce, "ai daga ganinsu, wayayyu ne basu da duhun kai. Kuna ji ƴan mata?."
Duk suka kalle sa, ya gyara zama ya ce, "Za a kai ku inda zaku samu cigaban rayuwa. Yin karatu a babbar makaranta, hawa mota, riƙe waya mai tsada, kwana a waje mai kyau, da komai za ku zamu. Abinda mu ke so da ku, bama son yawan surutu, ku yi shiru da bakunan ku. Ba ku da iyayen da zasu takura mu ku, abinda ku ke so shi za ku yi."
Zulaiha ta ce, "in ku ka yi haka, za ku samu abinda baku taɓa tunani ba. Fita ƙasar waje, da komai ma za ku samu. Kun amince?."
Dukkansu suka ɗaga kai alamun sun amince. Ya yi murmushi ya ce, "ku shiga ciki, akwai mai dafa abinci, ku faɗa mata duk abinda ku ke so za a yi mu ku. Akwai driver a waje, in kuna ƙwaɗayin kayan ciye-ciye duk za a baku." Suka miƙe suka shiga inda ya nuna musu, ya bisu da kallo yana murmusui har suka ɓace.
Ya kalle ta ya ce, "daɗin harka da yaran gidan marayu kenan, babu mai nemansu balle a ɗaga mana hankali."
"ba a taɓa samu team mai kyau kamar wannan ba, kin yi haɗi yadda ya kamata. Kuma da alama dukkansu lafiyayyu ne, za a samu abinda ake so."
Daɗi ya kamata, ta ce, "sai da na zauna sannan na zaɓa, na fiddo su."
Ya ce, "na san za ki iya. Amma ina yarinyar nan da na gani?."
Ta ɗan sauke numfashi sannan ta ce, "Hafsa ko?." Ya ɗaga kai ya ce, "ita. Ai na faɗa miki ina so a haɗo da ita, wannan da kaina zan ajjiyeta ba wani wajen zan kai ta ba."
"Hafsa da Zainab bana son taɓa su ko kaɗan, saboda yaran nan sune na hannun daman Islaha."
Ya bita da kallon mamaki ya ce, "Islaha kuma, ba mun gama da case ɗinta ba?."
"Mun gama Yallaɓai, amma ita bata gama damu ba. Daga ranar da ta buɗe ido babu ɗaya daga cikinsu, zata fara yi mana shige da fice a kan lamarinmu. A haka ma dan muna da maganinta a hannu ne, da ba mu san irin ɓarnar da zata yi mana ba."
"Ba an ce saurayinta ya jima da ɗauke ta daga gidan ba?."
"Ta jima bata nan."
"Wai wacece Islahan nan da mu ka kasa ganin bayanta?."
*********
Dpo ya ce, "mu ga lambar."
Ba musu ya basa lambar, ya saka a wayarsa sannan ya yi danne-danne ya saka a kunne ya ce, "Na turo maka wata lamba, a bibiye ta yanzu nan" ya faɗa yana kashe wayar.
Ya kalli Sadik ya ce, "ya ku ka yi dasu?."
Saleem ya ce, "sun tabbatar mana da tana hannunsu dan har maganar ta mun ji, sannan sun ce in mu ka saka ku a ciki sai sun kashe ta."
Ya ɗaga kai ya ce, "na san zasu ce mu ku haka daman, zasu faɗa muku abinda zaku ji taoro lokaci ɗaya. Nawa suka nema?."
Sadik ya ce, "miliyan ashirin."
Da mamaki dpo ya ce, "miliyan ashirin?."
Sadik ya ce, "eh."
"Sun taɓa kiran ka ne kafin yau?."
"Basu taɓa ba."
"Kuma kai tsaye suka nemi miliyan ashirin?."
"Haka ne."
Ya ɗan yi shiru yana tunani kafin ya ce, "ya kira ka a yau kuma har ya faɗi kuɗin da suke so, naira miliyan ashirin bayan ya saka maka muryar Islaha. Ya ce zai kira ya faɗi inda za a kai kuɗin, duk a yau..."
ya ɗan daki table ya ce, "ƴan garkuwa da mutane basa taɓa neman kuɗi ƙasa da naira miliyan ɗari, kai tsaye suna iya cewa suna neman naira miliyan ɗari biyu ko ɗari huɗu. Kuma ba sa fara faɗar kuɗin kai tsaye, suna kira su tabbatar maka ca mutum yana hannunsu sannan daga baya su kira su faɗi kuɗi. Amma wannan kai tsaye ya neme naira miliyan ashiri kacal!."
Ya ɗan kwanta akan kujera yana tunani kafin ya ce, "ba ƴan garkuwa da mutane ne suka ɗauke ta ba, tabbas an yi garkuwa da Islaha, amma ba garkuwa irin wacce aka saba ba. Wannan shirya ta aka yi, tsarawa aka yi kuma ba a yi tsarin mai kyau ba."
Sadik ya ce, "amma ranka ya daɗe sune da kansu suka kira ni."
"Na sani Sadik, na faɗa maka an yi garkuwa da ita, amma ba ƴan garkuwa da mutane bane. Tsarawa aka yi, ana sane aka sace ta. In ka tuna ta yadda aka sace ta zaka tabbatar da wannan plan ne."
Saleem ya ce, "yanzu ranka ya daɗe me ake ciki?."
"In sun kira ku ku cigaba da magana dasu, da zarar sun kira ku ɗaya ya kira ni a waya a turo min lambar, ni kuma a lokacin zan bibiyi kiran
dan na tabbatar da abinda nake zargi. Tabbas in ba yarinyar nan Ummi ce ta saka aka sace ta ba, akwai wasu a gefe da suka sace Islaha. Ko kuma wasu sun yi amfani da sace ta ɗin da aka ce an yi, suka kira ku dan su samu kuɗi."
Sadik ya ce, "babu wani cigaba a maganar.
Amma ɗazu wasu sun kira mu suna neman kuɗin fansa, kuma sun saka mana muryar Islaha mun ji. Sun ce mana suna buƙatar naira miliyan ashirin, in ba a bayar ba zasu kashe ta."
Saheer ya ce, "kafin a kashe ta ni ka ke so ka kashe Sadik, meyasa baza ka aiko da mutane su harbe ni a nan kawai na huta ba. Yanzu ka san da irin wannan maganar ka yi min shiru? Ka san hakan ya faru ka ƙi ɗaukar wayata? A ina ka ke so na saka raina, ka san a yanayin da nake zaune a ƙasar nan kuwa."
Sadik bai ce komai ba Saheer ya yi shiru yana salati kafin ya ce, "yanzu ya ake ciki?."
Sadik jin muryar Saheer ɗin ta yi ƙasa kamar mai kuka sai ya ce, "kuka ka ke yi?."
"Ban cancanci in yi kukan bane?. Sadik mahaifina yana kwace babu lafiya, ga matata an sace ta, gashi ana batun kuɗin fansa alamun garkuwa aka yi da ita. Ni kuma ina nan wata ƙasa a kulle an hana shiga da fita, wallahi Sadik ji nake kamar zuciyata zata buga saboda tashin hankali, ni kaɗai na san irin abinda nake ji a raina. Baza ka taɓa hasashen yanayina ba tunda ba kai ne a cikinsa ba."
"Gani a raye amma na zama bani da amfani, gani da lafiya amma babu amfanin da zan yi. Matata tana wani wajen da ban sani ba, ni ina nan a kulle. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!. Sadik a daji suke ajjiye mutane, Islaha tana da asthama, a wanne yanayi zata kasance? A cikin bishiya suke ajjiye su, a wanne hali take ciki yanzu?."
Saleem ya ce, "Allah ya bayyana Islaha cikin aminci, Allah ya sa Islaha tana hannu na gari." Sadik ya amsa da amin suka ja motar suka bar wajan.
******
Rehaan ya miƙe tsaye, ya dafe kansa cikin tashin hankali. Ya kalle su ya ce, "in zaki faɗi waɗanda suka saka ki ki faɗa ki huta, in ba haka ba wallahi sai na ɗaure ki."
Hafsa ta sake fashewa da kuka, ya dafe kai cikin rashin sanin abinda zai yi, jikinsa yana rawa saboda rashin hankali, ya nuna ta da yatsa ya ce, "da ke, da Lawal, da ke" ya faɗa yana nuna Safeera da take kuka har lokacin.
"In wani abu ya same ta, wallahi babu wanda zan bari!. Dukkanku ban yarda daku ba, a tafi dasu a saka su a cell, a yi bincike mai ƙarfi!" ya faɗa cikin wani irin yanayin da shi kaɗai ya san me yake ji.
Jazy cikin damuwa ya ce, "Haba Rehaan! Me ka ke yi haka ne? Safeera ƙawar Islaha ce, ta ya za a haɗa kai da ita a sace ta?."
Ya nuna Safeera ya ce, "Meyasa ba a ɗauke su tare ba, meyasa ita ta dawo ita kuma bata nan?. Me wayarta take yi a hannunta a lokacin?. Ka dawo hankalinka Jazy, ka fahimci babu wanda zan yarda dashi a ɓacewarta, ko da kai ne!" Ya faɗa cikin fitar hayyaci yana nuna Jazy.
"Wa take dashi da zai ɗauke ta haka kawai, ƴar siyasa ce ita ko me?."
Cikin ɗaga murya shima ya ce, "Yar jarida, wacce aka yi ƙoƙarin kashewa a kwanakin baya, kowa zai iya ɗauke ta, saboda ta yiwa wani ba daidai ba
"Islahan dah daban da ta yanzu, ta dah ba tawa bace, ta yanzu tawa ce. Babu wanda zai ɗauke ta ya zauna lafiya. Wallahi akan ɓatan nan nata, zan iya tashi Adamawa gabaɗaya, zan hana kowa zaman lafiya, matuƙar ba a nemo min ita ba!."
Abba ya miƙe ya ce, "Rehaan ka nutsu."
Ya katse Abba ya ce, "ta ya zan nutsu, ana cewa an sace ta?. Meyasa da zasu fita ban sani ba, da ta ce su fita ba sai a kira ni a sanar dani ba?...." Ya girgiza kai ya ce, "Ban yarda da ita ba, duk su ukun bakinsu ɗaya. Ko su faɗa min inda take ko na saka a ɓatar dasu daga duniyar gabaɗaya. Kuma na ɓatar da banza!" ya faɗa yana sake nuna su.
Abba ya ce, "babu mai laifi a cikinsu, kowa yana na sa ɓangaren. In akwai abin zargi Hafsa ce, ba Safeera ba."
"Abba duka su ukun nake zargi, kuma wallahi bazan ƙyale ko ɗaya daga cikinsu ba. Sai sun girbi abinda suka shuka. Ko yatsanta aka yiwa wani abun, sai sun gwamace ba a haifesu ba!."
******
Safeera ta duƙushe ta riƙe ƙafarta ta ce, "Don Allah Umma kar ki yi mana haka, mun fi buƙatar ki sama da komai a rayuwar nan. Ni na yarda zanje, na amince zan je ba sai kin je ba."
Umma ta ce, "lokacin da nake lallaɓa ki ai iskanci ki ke yi min, dan haka ki sakar min ƙafa na wuce."
Baba ya ɗaga labulen ya shigo yana kallon ta ya ce, "Maimuna da gaske tafiya za kiyi?."
Ta kalli Baba ta ce, "yanzu na gama yi maka bayani fa."
"Duk abinda Yayanki ya faɗa miki daman baki ji ba?."
"Ni fa ta dole zan tafi, ba dan son raina zan je ba."
"Yanzu dai sai kin je ɗin?."
"Jirana ma suke yi zamu tafi."
Baba ya girgiza kai ya ce, "kin zaɓi ki watsar da ƴaƴanki mata ki tafi wata ƙasar aikin gidan larabawa, kin zaɓi ki barsu a nan ki je inda baki da kowa saboda neman duniya?. Ki bar naki yaran, ki je ki yi bautar yaran wasu?."
Umma ta ce, "ga Safeera nan, meye baza ta yi musu ba? Ai ba lallai sai ni ba."
Baba ya bita da kallo dan bai ga alamun zata fasa ba, bai ga alamun tana jin tausayin ƴaƴan ba balle shi ta ji tausayinsa a matsayin mijinta.
Ya gyaɗa kai ya ce, "na faɗa miki baza ki bar ƙasar nan da aurena akan ki ba, anyi haka ko?."
Sai a sannan ta ji gabanta ya faɗi matuƙa, ta ɗago ta kalle sa ta ga ita yake kallo ta kasa cewa komai.
Baba ya daure ya ce, "tunda kin zaɓi tafiya a kan aurenki da ƴaƴanki ki je Maimuna, ki je ki nemo duk abinda ki ke ganin zaki samo a saudia."
"In kin bar gida nan ki taho da duniya gabaɗaya, ƙarewar arzuƙin da ki ke hangen zaki samu a aikatau. Kin zaɓi yin aikatau a wata ƙasa akan zama da yaranki. Ki tafi, amma ki sani na sake ki Maimuna!."
******
"Islaha!."
Cak ta tsaya, tana jin kukanta yana ƙaruwa, jinin jikinta yana tafasa, ruhinta yana rawa, numfashinta yana ƙoƙarin ƙwacewa.
A kafaɗarta ya ɗora hannusa ya ce, "bazan yi forcing ɗinki akan ki zauna dani ba, amma ina so ki sani, in ki ka tafi bazan iya rayuwa babu ke ba. Ke ce rayuwata, ke kaɗai nake so."
Ya ja numfashi, ƙirjinsa yana yi masa nauyi ya ce, "za ki iya yi min wata alfarma, alfarma ta ƙarshe?!."
Ta ɗaga masa kai alamun zai iya, ya juyo da ita ya ɗago fuskarta yana goge mata hawayen da suke ta gudu, yana girgiza mata kai. Ya lumshe ido ya ce, "can i....."
Ya ja numfashi mai ƙarfi, yana cize baki ya ce, "can i kiss you, for the last time?.."
Ta ɗago ido tana kallonsa, gabanta ya faɗi ganin kamar an canja shi. Kamar Hamma ba, kamar ba wanda ta sani ba. Gentle guy, mai taƙama da steeze. Ta sauke ido ƙasa ya ce, "plesase! I would never kiss you without your consent."
"Please!."
Bata san ta ɗaga masa kai ba, ya jawo ta jikinsa ya haɗe goshinsu waje ɗaya, lips ɗinsa suna rawa kamar mai son yin magana, idanunsa a rufe ya ce,
"thank....."
"You...."
"My....."
"Life...."
Ya faɗa a rarrabe, yana ɗora lips ɗinsa a kan nata, ya jawo ƙugunta ya haɗe da jikinsa, ya saka bakinsa a cikin nata yana kissing slowly.
Zafin jikinsa yana ratsa ta, yana shiga har cikin ƙwaƙwalwarta. Sai ta ji kamar ana yi mata allurar zazzaɓin jikinsa, yana shiga jikinta a hankali.
A hankali ya raba kansa da ita, ya kallevta ya ce, "Thank you so much, thank you for your time, Thank you for everything you've done for me. I love you so much."
Islaha ta juya tana kuka, sai kuma ta fita da gudu dan in ta tsaya baza ta yi abinda ta yi niya ba.
FIND OUT IN RAGAYAR DUTSE!❤️🔥
Release on 1st June 2026 in sha Allah.
_Mutanen amana, mutanen kirki, iyayen fita kunyar Nana Haleema💃🏻💃🏻 tafiyar Ragayar dutse tafiya ce mai tsaho, tafiya ce mai nisan zango, tafiya ce kashi-kashi, daki-daki, babu gaggawa. Akwai akasin tunani, akwai saɓanin tunani, akwai akasin zato, duk a cikin labarin._
_Kamar yadda muka saba book 1 free ne, book 2&3 paid ne akan naira 1k kacal. Wannan karon babu regular da vip group. Vip zai zo akan manhajar ArewaPen kaɗai, ga waɗanda basu dashi su yi gaggawa su sauke, dan tafiyar RAGAYAR DUTSE ta sha banban da tafiyar KIRAN RABO. Za a iya fara payment yanzu, za a biya dubu ɗaya a wannan account ɗin Sadiya Nuhu Mukaddas 5903999117 Moniepoint MFB. A tura shaida a 09030398006 ko 0701 809 8175. Tafiyar babu danasani in sha Allah, tafiya ce cikin nishaɗi da ɗebe kewa._
Nana Haleema✍🏻❤️
09030398006.
