Matar Damisa Page 5 Complete na Asmeetah Writer

Matar Damisa

*★MATAR DAMISA★*


> By Asmeetah writer 

PAGE 5


Mommy faɗuwa tayi sumammiya ganin halin da Junaid ya shiga, tin da uwarta ta haifeta ba ta taɓa ganin wannan al'ajabin ba sai yau akan d'anta wanda ta haifa...

Junaid ne a manne da jikin bango an ɗaga shi sama  yayi cross kamar yanda aka yi wa Jesus Christ,    jikinsa yayi jawur sai tabo-tabon 'kunar wuta  ga shatar bulala a jikinsa duk ya faffashe,  babu kaya a jikinsa sai jageren wando wanda baije gwiwarsa ba,  kansa a sunkuye wuya ya karye kamar wani matacce  ko numfashi ba ya yi, sai gumin da yake gangaro mishi daga cikin sumar kansa..  
             
Abunda ya faru da shi shine 👉.    Naushin AYUSH da yayi a rashin sani shi ya jawo masa wannan bala'i,    domin naushin ba iya ita kad'ai ta ji ciwo ba,  hatta mahaifinta sarkin matsafan duniya sai da ya jijjiga da wannan  naushin! hakan yasa ya turo mutanensa wato Manya-manyan Aljanu guda uku don su hukunta shi..
      
Allah sarki bawan Allah yana cikin baccinsa yaji sau'kar bulalar kaca wacce aka ciro ta daga cikin wutar su na tsafi,  duka d'aya fatar jikinsa ya fashe   a razane ya tashi yana waiwaye amma bai ga kowa ba,   su kuma suna tsaye a kansa,  cikin fushi babban aljanin cikinsu ya yi wurgi da shi sai da kansa ya bugi jikin gini, kafin ya ankara an sake d'agashi sama aka buga shi a 'kasan tiles,  haka suka cigaba da buga shi da 'kasa,    tsabar wahala ko kuka ya gagara yi balle ihu,  har sai da yayi jina-jina  suka d'aga shi kamar tsumma ko motsi ba yayi sai numfashi sama-sama,       suka d'aure hannunsa d'aya da kacar wuta  haka d'ayan hannun,    wannan aljanin ya ri'ke hannun dama  shima wannan ya ri'ke na 6angaren hagun   sawayensa suka had'a biyu suka d'aure guri d'aya, a manne da jikin gini....

     Cikon na ukun kuma bulala ya fara zabga masa        shi kuwa hatsabibin uba wato Ayush father  watsa masa garwashi ya fara yi a jiki ta cikin madubin tsafi,  ana jibgarsa kuma ana watso masa garwashi,   haka jikinsa ya koma ba dad'in gani  jiki duk ya farfashe    suna cikin gana masa wannan azabar wuyansa ya karye ba alamar motsi,   shi Ogan yasan bai mutu ba doguwar suma yayi  domin tsafin Damusar su bazai bari ya mutu ba sai dai yasha iya wahalarsa..

(Innalillahi wannan ai gwara mutuwarsa).

Haka  *BOKA* *ZALIMU* ya bada umarni a cigaba da hukunta shi har na tsawon kwana uku 👌  

Farin Bafulatani mai Ba'kar Zuciya, Sarkin Matsafan Duniya (Boka Zalimun) Baban AYUSHH

Shi a fad'ar sa daka ta6a Ayush gwara ka ro'ki mutuwarka,
Domin duk duniyan nan ba wanda yake so sama da d'iyarsa Ayush,  ko cinyaka ce ta cije ta saiya zaro hannunsa ta cikin madubi ya mur'kushe ta 😳😳

(Anya kuwa d'aukar fansar Junaid zai yu akan d'iyar Bara'atu kuwa 🤔).

___________________________
Ihun da Mommy tayi ne ya jawo hankulan kowa na gidan,   
Ayush tana cikin cusa abinci sai da ta razana  daga zaune ta mi'ke tsaye,  sarkin tsoro har jikinta ya Fara 6ari   tayi cikin toilet da gudu ta danna sakata!

Security gidan kuwa suma da gudun gaske suka shiga cikin d'akin  direct d'akin Junaid suka nufa saboda sun san duk wani problem daga d'akin Junaid yake fitowa,
         Suna shiga cikin d'akin suka tarar da abun al'ajabi, zaro idanuwa sukayi waje sun firgita da ganin Junaid a haka  ga kuma mommy a shanye a 'kasi sumammiya, cikin zafin nama suka nufi gurin da Junaid yake Gadan-gadan  sun d'ago hannu zasu jawo Junaid  nan sukaji an had'a kayuwansu biyu aka gwara  kamar daga sama kuma basuga kowa ba,  ba 'karamin buguwa akayi musu ba  kwakkwalwarsu ne ya fara juyawa kafin nan kowannen su suka fad'i sumammu,  sauran two bodyguard suma ganin hakan yasa suka nufi gurin babu tsoro a fuskarsu  zasu sa hannu su finciki Junaid daga jikin gini  sukaji an sha'ko wuyansu  duk su biyun an d'aga su sama               kakaki suka farayi suna ri'ke wuyansu,      saiga mai gadi shima ya shugo da gudu cikin d'akin  abunda ya ganine yasa shi tsayawa cakk  ganin gardawa a sama suna lilo da 'kafafuwansu  kuma bai ga abunda ya d'agasu sama ba, nan take yasau fitsari a wando jikinsa ne ya hau 6ari,      
Su kuwa sai da numfashin su ya tsaya cak sannan aka wurgar dasu kan mai gadi  da yayi sumar tsaye,  sai yaraff duk su biyu akan mai gadi shima saida yayi asalin suma jin Manya-manyan gardawa a samansa.

                  Bayan 1hour   Ayush dai tana cikin toilet jin ihun da akayi yasa ta 6oye a gurin,   tana tsugune har ta gaji   jin babu komai yasa ta bud'e 'kofar toilet tana Le'ke-le'ke  cikin sand'a take tafiya  har ta sau'ko falo babu kowa,  
A hankali take 'kiran sunan "Aunty, Aunty, kina Ina ne"  taji shuru ba'a amsa mataba,  ta nufi kitchen tana bud'ewa taga wayam ba kowa
Anan fa ta fara rawar jiki  tsoro ne ya bayyana akan fuskarta,  "innalillahi wa inna'ilaihi raju'u, Allah yasa dai ba 6arayi bane suka shugo gidan, naji ihu kuma yanzu babu kowa"
Tana magana cikin kuka   hawaye ne sharaf-sharaf suka fara gangaro mata a saman kunci,    ta lalle'ka ko Ina amma bataga Mommy ba,   ta duba agogon saman bango  12:30 ne.

         Tayi hanyar waje ko zataga security hankalinta zaifi kwanciya,    
"May be an kirata ne a asibiti"  a cikin ranta take wannan maganar!
Abun mamaki ko dataje waje bata ga kowa ba hatta mai gadin sai haske Dara-dara ta ko Ina,
         Wani irin yawu ta had'iya  ga gumi kuwa daya fara tsirto mata, kakkarwa ta somayi  tana tunanin kar itama a sace ta
Da gudun gaske ta koma cikin d'aki  tana maida numfashi,
         Ta zauna a saman kujera 1seater  dafe kanta tayi ta fara rera kuka 
Ita kanta ta rasa shin kukan mai takeyi 
Shin na rashin ganin mutanen gidan ne ko kuma kukan tsoro ne,  tana cikin wannan halin ta tuno da Junaid!  Da sauri ta d'ago kanta idonta sun rine sunyi jaa   "Ina yaron gidan, ko shima an sace shi"  tana magana tana kallon upstairs d'in d'akin Junaid 
       Cikin rawar jiki ta mi'ke da sauri tayi hanyar d'akin Junaid  tana taka matakala da sauri-sauri kamar zata kife,
Tana zuwa daf da d'akin tasa hannu zata bud'e  naushin da Junaid yayi mata ne ya fad'o mata a rai, tsayawa tayi cak cike da fargaba ta fara tunanin "ya za'ayi na shiga d'akin wannan azzalumin  d'azu ya naushe ni yanzu kuma ban san wani muguntar zai 'kara mun b,   ta juya zata bar gurin ta koma falo sai wani tunanin ya sake fad'o mata  shin idan kuma shima ansace shi fa?  Inma ba'a sace shi ba ai zai fita ya nemo mutanen gidan!
                  
Knocking ta fara yi taji shuru ko motsi bataji ba  ta sake buga 'kofar still ba motsi 
Almost 30minute tayi a tsaye tana sa'ke sa'ke a raanta 
Daga baya ta yanke shawarar shiga kawai,  cikin rashin sa'a tana shiga tayi tuntu6e da mutum a gabanta, 
                  Juyowa tayi ta kalli gurin  ganin Mommy a kwance yasa taji fad'uwar gaba,
"Innalillahi was inna'ilaihi raju'un Aunty meya sameki" jijjigata ta somayi taga babu alamar motsi 
         Juyawar da zatayi taga mutane uku aguri d'aya  2 bodyguard da mai gadi ja da baya tayi cikin firgici da tsoro  tana waiwaya gabanta taga still 2 bodyguard  kwance ba motsi 
Daman bodyguard 4 ne a gidan sai mai gadi  

Bakinta ne ya soma kakkarwa ko magana ta kasayi  
Ga wani irin guminda yake yarfo mata 
Cikin fargaba da tsoro take bin d'akin da kallo 
  Karaff idonta ya sau'ka akan Junaid dake manne saman bango  rai a hannun Allah,   'Kara ta sau tare da toshe bakinta  kuka ne yaci ranta  yau taga abunda tinda aka haifeta bata ta6a gani ba.

Da gudun gaske ta nufi gurin da Junaid yake,  jinin da yake d'idd'iga daga jikinsa duk ya 6ata tiles d'in d'akin,
                   'Dagowa da kanta tayi ta 'kura wa fuskarsa ido  lokaci guda kuwa ta zaro Manya-manyan idanuwanta waje   bakinta ne yake motsi kamar maiyin magana, jikinta kuwa rawar sanyi ta soma,  cikin firgici ta jaa baya da sauri sai da ta fad'i 'kasi  still idonta akan Junaid 
            Da kyarr ta iya bud'e bakinta cikin kuka ta fara fad'in 
"Wayyo Allah nah Umma nah,  Kaine ka kashe mun Ummana bazan yafe maka ba, ka sanya ni cikin maraici! Saika tozarta a rayuwa, sai kayi mutuwar wulakanci kamar yanda ka kashe mun mahaifiyata" 
                     Gaba d'aya Ayush idonta ya rufe bata ganin halin da Junaid yake ciki,   kamar zautacciya haka take maganganu cikin fitar hayyaci,
Saida ta gama surutanta ta mi'ke da gudu ta fice daga cikin d'akin...

Shi kuwa Junaid duk abubuwan da yake faruwa bai saniba ,  baya cikin hayyacinsa, 
A halin yanzu taimako yake bu'kata 
Kuma Ayush ce kawai zata iya wannan taimakon,  in har ba itaba  ba Wanda zai iya ceton Junaid daga hannun azzaluman Aljanun nan da kuma mahaifinta.

Barin Ayush cikin d'akin falo ta nufa ta kwanta 'kasan carpet tana rera kukanta mai cin rai,  a halin yanzu ba mutumin da Ayush ta tsana kamar mutumin da ya kashe mata mahaifiya, 
Kuma saita d'au fansar mahaifiyarta akan sa, 
Wato JUNAID.........


Ayush! Ayush!! Ayush!!!   Cikin sassanyar murya ake kiran sunan nan,  ita kuwa Ayush tana kwance akan carpet kuka yaci ranta   taji ana kiran sunanta kamar daga sama,  dakatar da kukan tayi tana sauraron kiran da ake mata,  sautin zazza'kar murya ne yake dukan kunnenta   a hankali take d'ago da kanta   wani irin hajijiya ne yake d'iban ta a haka ta tashi zaune! 
Da dara-daran idanuwanta wad'anda sukayi jawur  ta d'agosu ta kalli yanda sautin sunanta yake fitowa,  cikin firgici taja da baya ta zaro manya-manyan idanuwanta waje  tsoro ne ya kuma bayyana akan fuskarta,  baki na kakkarwa ta ambaci  "Umaa"  abunda ya fito daga bakinta kenam  tana kallon gurin da            wata zankad'edd'iyar mata take tsaye, tana sanye da fararen kaya daga sama har 'kasa   ta rufe doguwar suman kanta da farin mayafi,  da murmushi a kan fuskarta...
 Ayush ce ta sake motsa baki tana fad'in "Umaanah"  tana kuka kuma tana had'awa da dariya  tayi farin cikin ganin mahaifiyar ta a wannan Daren misalin karfe 2:00
                        Itama Uman da murmushi a fuskarta cikin sanyayyar murya tace "Yarinyata nazo gareki ne domin na tunasar da ke abunda kika manta a baya,  ki kasance mai taimakon al'umma idan kika fuskanci suna cikin wani irin hali,  kada ki dubi girman laifin da mutum yayi miki  idan ya bu'kaci taimakon ki kawai ki taimake shi kema wata rana idan kika shiga wani hali Allah zai taimake ki, kada ki tsani bawa! kada ki cutar da bawa!! kada ki bari ata sanadiyarki a cutar da bawan Allah, Ayush d'iyata! 'Dan uwanki yana bu'katar taimakon ki kije ki taimake shi    kada ki damu Allah yana tare da mai hakuri,  kije ki, ki je ki taimake shi........!
Tana kaiwa karshen maganar ta 6ace 6attt.
               A firgice Ayush ta tashi zaune tana fad'in "Umaa! Umaana!! Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un,   mafarki Ayush tayi  kwanciyar da tayi tana kuka  ashe bacci 6arawo yayi awun gaba da ita,  zuwan da mahaifiyar ta tayi acikin mafarki ta zo mata.
Ta waiwaya ko Ina bata ga kowa ba   ga hawayen da ya bushe mata akan fuskar        "tabbas mafarki nayi, Uma tazo mun"  a lokacin ta fara tariyo maganganun mahaifiyar tatan  lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka,    Junaid ne ya fad'o mata a rai     "Uma  mutumin da ya rabaki da rayuwarki shi kike so na taimaka?"  Kuka ne ya kwato mata      sai wani tunani yazo mata a cikin zuciyarta take fad'in "Mahaifiyar shi ta taimake ni, ba don ita ba bansan Ina zan nufa ba, shin itama tana raye ne ko ta mutu?  Tabbas suna bu'katar taimako a wannan halin" ta mi'ke tsaye cikin sauri lokaci guda kuma ta tsaya cakk 
Alamar ta tsaya tunanin wani abu   "amma meyasa naga shi wannan mutumin a manne da jikin gini ba tare da an d'aure shi ba, kuma jikinsa a faffashe kamar ma ya mutu"...  'Kirjinta ne yayi wani irin bugawa ta zabura da gudu ta nufi hanyar d'akin       takawa d'aya biyu taji kamar an ri'ke 'kafarta  ta doku a 'kasi    danma carpet ne mai gashi da tunin taji ciwo,  
Tana shirin d'agowa   kunnuwanta suka jiyo mata kukan mujiya 🦉🦉  mai firgitarwa   a tsorace ta kalli saman cilling  yanda ta jiyo kukan kenam,  wutar nepa gidan ne ya d'age  sai duhun daya biyo baya ko hannunta bata iya gani   wani irin tsoro ne yabi jikinta,    kamar daga sama tajiyo wata 'katuwar murya ana cewa  "AYUSHHHH KADA KI KUSKURA KI TAKA 'DAKIN NAN,   WANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA ZAKI TAIMAKA?  TO LALLAI KEMA ZAI KASHE KI KAMAR YANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA,  KIYI TUNANI SHI BA MASOYINKI BANE MAKIYINKI NE, YANA NEMAN AHALINKU NE DOMIN YA GAMA DA RAYUWAR KU GABA DAYA  HAHAHAHA, HAHAHA, HAHAHAHA haka ta ringa jiyowa dariya marar dad'in ji,
               Jikinta ne ya hau 6ari  murya na kakkarwa tace "waye Kai?"
              "NIIII MAI BAKI KARIYA NE,  still ya 'kara  tintsirewa da razananniyar dariyar shi mai ban tsoro....
              Lokaci guda kuwa haske ya bayyana ta daina jin kukan mujiyan.
           "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'unnn wannan wani irin bala'i ne a cikin gidan nan,  Aljanu da mutane duk suna rayuwa a gidan nan"   zuciyarta ne ta soma magana kamar haka "Ayush kar ki manta wannan Addu'ar da malamin nan ya koya muku ke da mahaifiyarki"  anan ta tuno da Baba tsoho wanda yayi hijira zuwa dajin da suka zauna  yayi tsawon shekara biyar atare da su,  Babban malami ne na gaske  shi ya koya musu karatun al'qur'ani mai girma tare da addu'oi ya koya musu alwala da yanda ake sallah  su wankan janaba da haila ba abunda bai koya musu ba ta 6angaren addini, Ayush lokacin bata wuce 15yrs ba  ita kuma mahaifiyarta tana 'kara koyan karatun ne domin wad'annan karatuttukan mahaifin Junaid ya koyar mata su tin suna GHANA.
Damuwar dai Ayush ta samu ta koya duk da itama tana koya mata wasu abubuwan!!

Anan tayi firgitt ta soma jero manya-manyan addu'o'i....

👉.  "Allahumma laa sahla illaa maa ja'altahu sahlan wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlan"
                    (Yaa Allah! Babu wani abu mai sau'ki sai abin da ka sanya shi ya zama mai sau'ki, kuma Kai kana sanya tsanani idan ka so ya zama sau'ki)

"'Kadrul laahi wamaa shaa'a fa'ala"
(Kaddarar Allah ce, kuma abin da Allah ya so, shi ne yake aikatawa, domin da-na-sani tana bud'e 'kofar aikin shaid'an).

"Laa ilaaha illallaahul aziimul haliimu, 
Laa ilaaha illallahu rabbul arshil aziim, 
Laa ilaaha illallahu rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kariim"....

Bayan ta kammala addu'o'in ta      ta shafa ayatul kursiyu,    duk wani tsoro da fargaba da 'kuncin zuciya ya wuce mata   ta 'kwarin gwiwarta ta mi'ke tsaye ta nufi d'akin da ake bu'katar taimako!

Upstairs ta fara takawa a hankula har da iso bakin 'kofar d'akin tasa hannu zata ture d'akin...     
        Aka daka tsawa "kada ki kuskura ki bud'e"      amma kash duk wannan maganganun kunnen Ayush ya toshe bata jin maganar
Tana bud'e d'akin kuwa wani irin duhu ne a d'akin babu haske kwata-kwata    tana shiga d'akin haske ya bayyana  ta ko Ina,  still yanda taga mutanen nan a kwance haka ta same su 
Ta d'aga kanta ta kalli yanda Junaid yake a manne a jikin gini   ganinsa yasa ta tsorita      naman jikinsa duk ya farfashe   ciwon yanzu yafi na d'azu     hakan na nufin har yanzu basu daina  azabtar da shi ba,    
                Girgiza Kai tayi tana maganar zuci "bazan iya kusantar ka ba, ka rigada ka mutu".      Toilet ta nufa ta d'auko bucket da ruwa a ciki            duk bodyguard d'in da suke kwance ta bisu da ruwa tana kwakwkwara musu     cikin sa'a kuwa suka tattashi a firgice suna ajiyar zuci,  bayan sun dawo hayyacin su kowa rige-rigen fita yake daga cikin d'akin har mai gadin!
Ta dawo kan Mommy itama ruwa ta yayyafa mata,   ajiyar zuciya tayi tana Jan numfashi sama-sama tana ambaton "Junaid! Junaid my son,  ya mutu ko? Kamar wata zararriya haka take magana tana bin Ayush ta kallo,  mommy bata san waye akan ta kawai dai tana sambatu ne,        
Ayush ta tsaya tana tunanin aina ta ta6a jin sunan nan!
     Tana cikin wannan tunanin tajiyo kukan mommy ya tsananta sosai        tana kuka tana nuna gurin da Junaid yake da yatsanta,  kafin kace mai Mommy ta tashi da gudu tayi kan Junaid 
Da karfin gaske aka hankad'o mommy baya     da sauri Ayush ta tareta  badon haka ba fad'uwa 'kasi zatayi.
     Lokaci guda idon Mommy ya 'kakkafe ta dafe 'kirjin ta  tana shure-shure      ciwon zuciyar ta ta tashi,
Ayush ta tsorita sosai da ganin haka    da kyar ta iya d'ago Mommy suka fita daga d'akin  
Falo ta nufa       tana zuwa ta tarar da bodyguards duk sunyi cirko cirko kowa yaji jiki  sai ajiyar zuciya suke sau'kewa 
      Da sauri sukayi kan mommy 
'Daya daga cikin bodyguard ne ya d'aga mommy cakk yayi waje duk sauran ma binsa sukayi a baya  
Motor suka shiga  gaba d'ayansu    
Motor biyu suka d'auka  
Biyu suka shiga d'ayan motor and order car shima mutum biyu a ciki,
             Kafin one minute sunbar harabar gidan,       iya Ayush da mai gadi kawai aka bari a gidan,   da sauri Ayush ta nufi gurin mai gadi tana fad'in "Ina zasu Kai ta?"
             In short amsa mai gadi ya bata  "Asibity"  yana fad'an hakan ya shige cikin d'akinsa  zallar tsoro ne a tattare dashi...

"Anya kuwa ba Aljanu a cikin d'akin nan?   Junaid kuma? Uma ta ta6a bani labarinta akan Junaid,  a'a ba wannan Junaid bane,  to aina Zan samu Junaid d'in da Uma take so na taimake shi??
    Waye wannan Junaid d'in? Innalillahi wa ina'ilaihi raju'un shi na gani acikin mafarki na idon sa kamar na namun daji,
A'a sharrin mafarki ne bashi bane......
                        Haka ta rin'ka saƙe-saƙe a raanta!...

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post