https://whatsapp.com/channel/0029Vb4VdFSDjiOgtgu6uz3T
ABU A DUHU
ADABI WRITER’S ASSOCIATION
PAGE 1
Bismillahir Rahamanir Rahim.
Manyan motocine guda guma zafafa ke shigowa cikin unguwar, banda kyalli babu abun da motocin ke yi, yayin da suke tafe cikin nutsuwa.
Sannu a hankali take tafiya cikin babban hijjabinta tare nikaf dinta, yayin da hijabinta ya kasancen kalar sararin samaniya, karan motocin da ta ke ji ne yai masifar gigitata, yayin da yai sanadin gushewar hankalinta, diriricewa ne da dimuwa ya same ta lokaci guda wadda ya haifar mata da rawan jiki tare da gushewan hankali harya kaita da curewa guri guda.
Hayaniya ne ke tashi bisa kanta, cikin yanayin firgici ta ke jin muryan maza saman kanta suna fadin, "Sannu ba ki ji ciwo ba dai ko?"
Wata muryan ta ji cikin fada a na fadin, "Ai gara ta ji ciwon ko yaya ne, tun da musamman ta shigo ta tsuguna saboda tana son tajawa mutane bala'i to Allah ya fiki, idan mutuwa kike nema dan ubanki ki je ki tari tanka, dallah tashi ki bamu waje" Cikin tsawa ya ke magana, kokarin tashi take ta hangi wasu ƙarafuna wadda kan zamarwa mara lafiya ƙafa suna tahowa gareta.
Sandunan karfen ta bi da kallo batare da tabi tsawon sadar ba, lumshe ido ta yi a lokacin data hangi wata kyakyawar kafa fara sol cikin cikin wani tsandanden takalmi, kallonta ta maida kan daya kafar wadda sai a wannan lokacin ta kula da ita, daure take tam da dauri irin na wadda ya samu karaya ko wata mummunan matsala, dan an nade kafar tunda kan tafinsa har ya wuce kaurin sa.
Yajima tsaye a gabanta saidai ta kasa dagowa ta dobe shi, yayin da ta kasa cire idon ta a kan daya kafar sa me lafiya, kuma ta kasa mikewa gabadaya.
Ahankali ta ji yayi gyaran murya kadan, wata irin murya ta ji me cike da kasaita yana fadi ahankali, "Tashi in gani babu wata matsala da ta same ki ko?" Ko motsi batai ba yayin da idon ta ke iya hangen kafafuwan su, zasu iya kaiwa kimanin mutum ashirin, kuma duk maza ne cikin kayan alfarma da takalma masu tsada, wani abun mamaki a da dukkan nin su magana suke cikin hayaniya, amman wannan me rike da karfin na fitowa gurin yayi tsit.
Kamar daga sama ta sake tsintar irin wannan muryan ta na sake fadin, "Ina magana dake ne fa" Wannan lokacin ma bata tankashi ba yayin da take ji ajikinta kallonta ya ke yi, saidai ita bazata iya kallon nasa ba.
"Ke baki ji ne a na miki magana dan rainin hankali kin yi banza da mutane? Tashi ki bamu waje, Idan nasame ki a wurin nan taka ki zan yi" Wani dake can gefe ke fadin haka cikin tsawa da hargagi, tsintan muryan mutumin dake tsaye agaban ta yi yana cewa, "Magaji bita a hankali"
Ba ta sake jin muryan wani ba duk suna tsaye yayin da kadan daga cikin su suka koma mota suka zauna, shi kuwa matashin dake tsaye a gabanta kyawawar kafar ta ya zubawa ido sannan ya koma kallon idon ta dake cikin nikaf, kasa cire idonsa ya yi a kanta tsawon lokaci duk da cewa shi ba mutum bane ma'abucin kallon mata amma a wannan karon sai ya zama tamkar wawa wajen kallon idon da be taba ganin mai irinsa ba a Duniya, har aka dauki tsayon lokac ya kasa cire idon shi a nata, sosai idon nata ya burgeshi har baya iya misalta wa, tare da kasa cire idonsa akan nata, acikin ransa yake fadin "Ban taba ganin idon da yai kyau da ni'kabi kamar wannan idon ba" Sosai ya ji yana son ganin fuskar mamallakiyar idon.
Tsayon lokaci suka diba babu me cewa komai zuwa can taji an bude motar sannan ta ji ance, "Modibo ka zo mu tafi dan Allah, muna da abun yi fa, sannan akwai tafiya me tsayo agaban mu."
"Ta kanta za mu wuce ne? Ba ka ganin ta zauna a hanyar?" Wadda a ka kira da suna Maddibo ya fada yana nuna masa yariyar, Jin haka ya kara fusata Magaji ya karasa gabatan cike da tsawa ya ce, "Ke Dallah tashi ko na latse ki da motar!"
Tsawan da Moddibo ya buga ya sa Magaji ya kallesa a furgice, yatsarsa yaga yasa a bakinsa "Shiii, ka koma ka zauna harsai lokacin data tashi."
Wani irin mugun kallo Magaji ya bi Moddibo da shi tare da nanata maganarsa a kasan zuciyarsa a fusace ya juya ya yin da wurin ya sake yin shiru tsawon lakaci zuwa can ta dafa kasa ta mike batare da ta iya daga ido ta kalli kowa a wurin ba, ta koma gefen hanya tana karkade hijjabin ta, bayan ta gama ta kara komawa can gefe sosai ta fara tafiya.
Gaba dayan su kallo suka bita da shi sannan suka shiga motar suka fara tafiya, koda su ka zo saitin ta kallo wadda aka kira da suna Modibo ya bita dashi, har suka wuce ta yana waigen ta.
Magaji kuwa kallo ya bishi da shi sosai, hakan ya zamar bakon al'amari ga Modibo, sai da su kai nisa sosai ta yadda ko alamar yariyar basa gani sannan Modibo ya dawo da kansa yana kallon hanyar da suka dosa, tafiya me nisa suka yi sannan suka iso wani madaidaicin gida, bayan sun faka motocin su ne suka fara fitowa tare da saurin bude motar da Moddibbo ya ke, cike da kasaita ya sauke kafarsa me lafiya, sannan suka tsayar da sandan karfen bayan ya sako daya kafar, sandar ta shiga tsakanin hakarkarinsa, dakin dake kofar gidan suka nufa mutum biyu ne a bayan sa, sallama suka yi bakin kofar daga cikin dakin aka amsa sallamar tare da fadin, "Kun iso kenan, ku shigo sannun ku da zuwa" Shiga suka yi bayan sun gaisa mutumin dake dakin ya kalli kafar Modibo yace, " Yaya kafar taka?"
"Alhamdulillah ba Kamar daba."
"Yauwa haka ake so." Matsowa mutumin yayi yana kallon kafar Modibo tsawon lokaci sannan yace, "In sha Allahu ya kusa zama tarihi" Mikewa yayi ya fara hado wasu magunguna tsayon lokaci sannan ya dawo gaban Moddibbo ya zauna, a hankali ya shiga warware nad'in da akama kafar, sai dai be gama warewa duk ba ya tsaya ya yana tofa addu'oi tsayon lokaci sannan ya bude wata roba yana shafawa kafar mgani, bayan ya gama sake nade kafar, ya yin da Modibo ke runtse ido, sannu yamai yayin da samarin da ke gefe suma suke masa sannu, dakai ya amsa, yayin da yai shiru kansa akasa kawai sai zufa ne ke karyo masa.
Tsawon lokaci ya dauka sannan ya dago ya kalli Malamin yace, "Baba maganin Yadikko ya kare, kuma Alhamdulillah tana samun sauki."
"Ma sha Allah" Malamin ya fada sannan ya kara da cewa "Zan baku wani ku kaimata, da yardan Allah zata samu sauki." Bayan ya gama hada duk magungunan, suka fito cikin girmamawa da mutunta juna.
Yanzun ma d'in rike yake da sandunan karfen dake cikin hakarkarinsa, yayin da mutun biyu ke bayan sa, mutum biyu dake tsaye jikin motar su suka bude motar da Modibo zai shiga, wadda itace ta kasance a tsakiya. Sai dai suna kokarin rabashi da sandunan suka lura hankalinshi baya wajen shiga motar, daya daga ciki ne yabi inda idon Modibo yabi da kallo domin son sanin abun da yaja hankalin sa haka, wata yariya ya gani tana kokarin bude wani madaidaicin gida da mabudinta a hannun ta, kallon ta yayi sosai cikin yanayin irin na mai nazari, a hankali ya maida idonsa ya kalli Modibo sannan ya sake kallon yariya, matukar mamakine ya kamashi, yayin da duk aka gama shiga cikin motar amman Moddibbo tsaye yake ya kasa shiga ciki.
"Modibo mu je mana tafiya ce fa me nisa agaban mu." Lumshe ido yayi sannan ya shigar da kafarsa me lafiya yayin da aka taimaka mai ya zauna da kyau, adaidai lokacin da yariyar ta gama bude gidan tana kokarin tura kofar Modibo ya kalli wadda ke gefen sa yace, "Magaji ka kira min yariyar can" Lumshe ido Magaji ya yi sannan ya juya cikin azama, beji mamakin jin Modibo yace ai kiranta ba, saidai yadda yake kallon ta abun ya bashi mamaki.
Kokarin shiga gidan take wadda aka kira da suna Magaji yace, "Ke! ki zo ana kiran ki."
Ta cikin nikabi ta juyo kadan ta kalle shi, sannan tasa kai ta nufi dogon zauren nasu tamkar bada ita ake maganar ba
Daga Murya Magaji ya yi a fusace "Ke!! ni ne nake miki magana keke tafiya, wanni irin rashin tarbiya ne ke damun ki dahar zan miki magana ki kalleni ki wuce?" Ko kafin ya rufe baki ta idan shigewa gida, dan haka ransa yai mugun baci, sosai zuciyarsa ke masa zafi, a fusace ya juya yayin da Modibo cike da kasaita yace, "Me ta ce maka?"
"Batace komai ba asali ma kallona tayi ta watsar kasan talaka da fadin rai"
Lumshe ido Moddibo ya yi, sannan juya ya kalli gidan yace, "Naso in yi magana da ita kwarai Magaji."
"Ba girman ka bane Modibo, bata da darajar da zaka yi magana da ita, ni kaina dan dai kawai kai kace in je, har yanzun dai idan taimako zaka bata kabani zan koma nakai mata." Gidan Modibo ya sake kallo batare da ya cire idon sa agidan ba ya ce "Mu je kawai." Jin haka Magaji yayiwa driver Umarni batare da wani bata lokaci ba motar ta fara kokarin tashi, hakan ne yabawa Motocin dake gaba damar fara tafiya sannan ta Modibo ta tashi yayin da wasu kebin bayan tasu. Modibo kuwa babu abun da idonsa da zuciyar sa ke iya hango masa sai idon ta wadda ya hanga cikin ni'kabi tare da farar fatanta dake gefen idon ta sai kuma farar kafar ta me daukan hankali.
******
Zaune take adan madaidaicin tsakar gidan wadda ya ke share tsaf, kanta ta hada da guiwa tsayon lokaci, a kodayaushe idonta sun kasa daina ganin kafafuwan sa guda biyu, daya me lafiya daya mara lafiya, tsawon sati daya kenan ta kasa barin tuno kafar tasa, wannan dalilin ya fara sata hawaye dan ta kasa fahimtar me hakan ke nufi, daker ta iya yakece tunanin ta mike domin karasa sharar data fara, bayan ta kammala ne tai wanka, shiryawa ta yi tsaf kamar kowanne lokaci ta fita sannan ta fito ta jawo kofar dakin, gidan ta kallah komai tsaf dan haka ta ji wani sanyi cikin ranta sannan ta fice tare da sawa gidan kwado.
Tafiya take gefen hanya sannu a hankali har ta isa wani gida na marasa karfi sosai, sallama ta yi cikin siririyar muryar ta tare da saka kanta acikin gidan. wata Dattijowa ce ta amsa fuskanta sake. Jikinta yariyar ta fada, tana fadin, "Sannu da aiki Dada."
"Yauwa sannu dai Unaisa, tun dazon nake ta xoba ido jiran zuwanki harnai tunanin yau baza kizo ba."
Cikin zazzakar muryan ta tace, " Zan zo Dada idan banzo ba ai banajin dadi."
Cikin yanayin tunani tsohowar da takirata da Dada tace, "Hakane, sannan wani al'amari yafara min yawo cikin kaina."
Da sauri yariyar ta kalli Dada tare da cewa, "Dada mene ne shi?"
Jimmmm ta yi zuwa can tace, "Yanzun matasa duk sun lalace, sa'anan duk unguwar nan kowa yasan da cewa ke daya kike kwana cikin gidan nan, gashi girma nata miki sallama" 'Karashe maganar ta yi tana kallon fuskar yariyar da takira da suna Unaisa.
Nan da nan idon yariyar ya cika makil da hawaye, yayin da matar ke cigaba da fadin, "A duk lokacin da nasa hakarkarina akan shinfidata bayan kin wuce gida fargaba ya ke mamaye ni, wani lokacin nakan raba dare, Unaisa ke bakijin tsoro?"
Kwallar da take makalewa ce ta zubo zuwa kan kumatun ta, yayin da tai saurin sa hannunta ta share tare da girgiza kai, "Bana ji Dada, Innawuro tace tabarwa Allah amanata, ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu babu abun da zai faru."
"Allah yasa Unaisa, tashi maza ki dauki kayan ki wuce, alhamis me zuwa basai kin zo ba zan kawo da kaina, ya makarantar kina zuwa dai ko?"
Dakai ta bata amsa sannan ta sauke nikabinta tare da nufa kayan ta dauka sannan ta mata sallama ta nufa kofar gida
Tana saka kafarta akofar gidan wani kyakyawan matashi na sawo kai, a hankali ta kauce ta bashi hanya yayin da ya dan tsaya yana kallonta, fuskarsa dauke da murmushi yace, "Unaisa"
Jimmm yarinyar ta yi sannan ta fara takawa a hankali batare da ta saurareshi ba, shi kuwa wannan matashin bebar fada mata wannan kalmar ba har saida tai nisa sosai.
Sosai ta kosa ta isa gida domin tsakanin gidan da gidan Dada akwai tazara, daf take data karasa gida ta hangi wasu jerin gwanon motoci masu kyalli da daukan hankali, motoci ne manya manya na alfarma jere kofar gidan Malam Baba Kamar yadda ake kiran shi cikin unguwan, shahararrene malamin gyaran karaya da duk wani maganin gargajiya, dan haka duniya tasan dashi, kofar gidan sa be rabo da baki a kowanni lokaci, saidai tun da take cikin unguwar bata taba ganin zuka zuka motoci har kamar haka akofar gidan ba, sai wancen satin daya wuce, sai kuma yau data take ganin kamar sunfi na ranar farko.
Cire idonta ta yi daga kallon kofar gidan Malam Baba sannan ta tsallaka kwatar da ke kofar gidan tahau kan dakalin.
Ledan dake hannunta ta sauke tana lalibo mabudin gidan.
*****
"Magaji duba can" Da hannu yai masa nuni da kofar gidan da budurwa ke kokarin bude kofar kallon yariyar yayi sannan ya juya ya kalli Modibo. Dauke ido Modibo yayi sannan ya ce, "Kamin magana da ita, kayi kokari ka kawota nan gabana, Ina son in ganta a nan gurin yanzun nan.
Fadila Lamido...✍️
