https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 17 Novel
DISTENY LOVE STORY
1/ 04/2026
PG 2
SUDAN
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
TSOKACI
Rayuwa tamkar gona ce; abin da mutum ya shuka shi zai girba, wanda ya shuka mugunta, kada ya yi mamakin girbin nadama.
Giya da sha’awa suna ɗaukar mutum kamar iska mai ƙarfi, suna rufe masa idanu har ya manta da darajar rayuwa da mutuncin wasu. A lokacin da yake wasa da lokaci da dukiya, yana ganin duniya tamkar wasa ce. Amma wata rana sai ya farka ya tarar cewa abin da ya ɗauka wasa ne ya zama bala’i.
Sau da yawa mace marar laifi ce ke ɗaukar nauyin kuskuren namiji. Ita ce ke shan ƙunci, ita ce ke ɗaukar ciki, ita ce ke fuskantar zargin duniya, alhali laifin ba nata kaɗai ba ne.
Hakika, duk wanda ya lalata rayuwar wani saboda son zuciya, to lokaci zai zo da zai nuna masa cewa nadama ba ta dawo da abin da aka riga aka lalata.
Don haka mai hankali ya koyi darasi tun kafin lokaci ya kure, domin kuskure na ɗan lokaci kan iya zama hawaye na tsawon rayuwa.
AFNAN KINAN
PG 2
MARROCO
Rana ta fito da ƙarfi a garin Casablanca, inda tituna masu ƙanƙanci ke zagaye gida-gida, ƙara da hayaniyar kasuwa da yara ke ta wasanni. A ɗaya daga cikin unguwanni masu cunkoso, gidan su AFNAN tsaya a ƙananan bango na laka, ƙaramin fili, inda ƙaninta biyu ke tsaye suna wasa da ƙwallo, suna dariya mai ƙarfi.
AFNAN ta fito daga ƙofar gidan, tufafin ta sun kasance launin ruwan kasa mai ɗan tsufa, rigar da ba ta da kyau sosai, amma tsafta ta yi kyau. Kafaɗunta sun ɗan lankwasa saboda nauyin kayan wankin mutane da ta ɗauka,
AFNAN ta tsaya na ɗan lokaci, idonta na kallon ƙaninta biyu suna jefa ƙwallon ƙafa a cikin ƙananan filin, suna dariya da wasa zuciyarta ta ɗan ƙara nauyi, domin ta san cewa rayuwar su bata da sauƙi ta matso kusa da su, ta ɗaga muryarta da harshen Larabci mai ɗan tsauri:
“Ya ishe ku wasa, ku tafi makarantar allo yanzu! kada ku tsaya anan, ku tafe karatu kuna wasar banza mara amfani”
Ƙaninta suka tsorata, suka yi dariya amma suka san cewa ba za su iya yin watsi da umarninta ba. AFNAN ta kalla ƙwallon da ta yi wasa da su da ƙyar, sai zuciyarta ta ɗan tsinke , ta ɗauke ball in ta jefar a kwata ..
Ta ja numfashi mai nauyi, ta shiga gida da Yulin wankin ta ajiye zuwa dare zata musu gobe takai musu kafin a biyata haƙƙin ta . sannan ta fara tafiya zuwa Soleil International Guest Company, tana tunanin yadda rayuwar ta za ta canza… kuma tana sane cewa kowanne motsi na yau zai iya haifar da wani abu mai girma a gaba.
Tana tafiya cikin ƙafa, tana kallon titin da ke cike da sauran yara, mutane masu siyarwa da motoci, sai zuciyarta ta cika da ƙarfin hali. A ƙarshen titi, gidan “Soleil International Guest Company” ya bayyana: ginin na zamani, gilashi mai haske da fensir ɗin farar launi, a ciki ma’aikatan baƙi suna zagaye suna ɗaukar kayan abinci, ruwa da abinci da juice kowane ɓangare da aikin su Wannan shi ne wurin aiki na AFNAN, inda take zama karamar ma’aikaciya mai nitsuwa da kwarewa, tana daga cikin masu kula da baƙi ta hanyar basu abinci da ruwa ko wani buƙatar su a ɓangaren aikin ta duty every day mutum biyar ne maza ukku mata biyu wanda ya kasance sun ware ta a cikin su kasancewar bata shiga sabgar su ta son nishaɗi da yawan kai ziyara club domin shaƙatawa hakan yasa wani lokacin suke tafiya su bar mata aikin ba tare da sanin manager su ba , a hakan bata isa taye complain ba domin a banza wahalar da ita zasuyi da barazanar zasu tufka mata sharrin da sai an kore ta ba shakka tana tsoron su .
Da ta shiga cikin ginin Soleil International Guest Company, AFNAN ta ɗan tsaya kaɗan don duba duk inda take tafiya, kowa na aikin gaban sa, raye sign sanan ta shiga apartment nasu tasa uniform masu na ma'aikatar masu kai abinci da amsa kirar masu buƙata abu a dakin su , tsayawa taye a gaban madubi tana ganin kanta cikin Skirt da rigar launin marron wanda ya mata kyau ta kafa cap nata , bazata haura shekaru sha bakwai ba, fara ce mai launin larabawa fuskar ta yayi dai dai da launin garinsu larabawan ƙasar Marroco Murmushi taye mai kyau har sai da farararen haƙoran ta suka bayyana " AFNAN " aka ambaci sunan ta da sauri tasa jakarta a loka ta fito da hanzari , Irfan ce ta ganta da cewa " kiye sauri mujee ana kirar mu a hall " nan suka taho zuciyar ta na bugu bisa ka'ida.
Oga Salman ya fito daga ƙofar babban court ɗin company, sanye da suit baƙi mai tsada, takalminsa na sheƙi yana danna ƙasa da ƙarfi, aka buga bell, nan take hayaniya ta lafa.
Duk ma’aikata suka tsaya layi-layi, kowa ya san matsayinsa, kowa ya san inda zai tsaya.
AFNAN ba ta rikice ba ta san layin da ya dace da ma’aikata masu matsayinta ta taka a hankali, ta tsaya inda ya kamata, ta sunkuyar da kai cikin nitsuwa.
Sai ga HAMLA — yarinya mai gadara, wacce take ganin kanta fiye da kowa ta matso kusa da AFNAN, ta ture ta da kafada, idonta cike da raini, sai ta faɗa da Larabci mai zafi:
“إبتعدي عني! لا تقفي بجانبي يا فتاة غبية!”
(Ki matsa daga kusa da ni! kada ki tsaya gefena ke wawiyar yarinya!)
AFNAN ta ɗan girgiza, ta kalli Hamla na ɗan lokaci, zuciyarta ta ɗan yi zafi… amma ba ta ce komai ba ta daidaita tsayuwarta, ta sake gyara cap nata ta sunkuyar da kai.
A ranta ta ce:
“Ba kowa ne yake buƙatar amsa ba… wasu rainin ma shiru yafi musu zafi.”
Hamla kuwa ta yi tsaki, ta juyo da sauri
Hamla ba ta tsaya gardama ba. Da kafada ɗaya ta ture AFNAN da ƙarfi, AFNAN ta rikice, kafafunta suka cakude, sai ta faɗi ƙasa a gaban kowa.
Nan take wasu ma’aikata suka juya suna kallo, wasu suka fara dariya a ɓoye, wasu kuma ba su ma ɓoye ba “Hahahaha!”
AFNAN ta zauna a ƙasa, hannunta na dama yana rawa. Ta miƙe a hankali, tana mirza hannun nata saboda zafin da take ji Irfan ce ta taimaka mata ta miki ba tare da tace kanzil na Fuskar ta ta cika da kunya, idonta ya cika da hawaye amma ta ƙi su zubo.
A nan ne Oga Salman ya ɗaga murya, tsawarsa ta tsayar da kowa cak ya kalli AFNAN da fuska mai tsauri ya ce da Larabci:
“أفنـان! إلى متى ستبقين بلا عقل؟!”
(Afnan! har yaushe za ki ci gaba da zama marar hankali?!)
AFNAN ta sunkuyar da kai cikin rawar murya ta amsa:
“عفواً سيدي "
(Yi haƙuri ranka ya daɗe…)
Ta ci gaba da mirza hannunta cikin tausayi, idonta na ƙasa, hawaye na taruwa amma ta danne su wasu na girgiza kai kamar abin bai dame su ba, AFNAN ta tsaya nan tsaye cikin kunya da zafi, zuciyarta na cewa:
“Wannan ciwon hannun… ba komai bane idan aka kwatanta da ciwon raini.
⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️
