👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
https://chat.whatsapp.com/Is0HqhjNITL3VZIagV42u7?mode=gi_t
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 3
Sarki Mu'iz ya daka mata tsawa da cewa"ba ki da bakin yi min wani jawabi Munaya!
Ke kika ɓatar min da ɗa,ki yarda da hakan,amma ba ki da wasu kalamai da za ki kare kanki daga hakan,za ki cigaba da karɓar hukunci har zuwa lokacin da za ki bayyana ɗana,ko kuma ki bar duniyar,ke azzaluma ce tabbas,amma zaluncin zai rufto miki"ya miƙe a fusace ya fice daga wajen, Munaya ta bi shi da kallo ba tare da ta iya cewa komai ba
Masu tsaron lafiyarshi ba su yi mamakin ganinshi a haka ba saboda kusan duk lokacin da ya ziyarci Munaya hakan ce take kasancewa,suka rufa masa baya don komawa fada,kamar yadda suka saba har suka fice daga wajen babu wanda ya iya magana
*MASARAUTAR TAYAAR*
Da tsananin farin ciki take shiryawa,kuyanginta suna taya ta,a yau tana cike da tsananin farin ciki irin wanda bata taɓa tsintar kanta a ciki ba,ba komai bane ya faranta mata sai kame azzalumi Kazuzi da aka yi,wanda a yau ya dawo bawa a masarautarsu
Zata iya cewa a duniya babu wata halitta da ta tsana,tsana mai muni irin Kazuzi,shine ya kashe ɗan'uwanta ɗaya tilo da take tsananin so fiye da rayuwarta,wanda a dalilin rasuwar shi ne zuciyar mahaifiyarsu ta buga itama ta bar duniya,yanzu daga ita sai mahaifinta suka rage a raye,a dalilin Kazuzi Sarautar da suka gada zata bar gidansu suna ji suna gani
"Ya shugaba ta ga abin kama gashin"a cewar wata kuyangar ta,bata yi magana ba sai murmushin da ta yi,ta sanya hannu ta karɓa,ta kama gashin,sannan ta miƙe ta shiga gaba,su kuma suka biyo ta a baya,suka fice daga sashen nata
Sai da suka hau ƙawataccen keken doki wanda ya kai su har bakin ɗakin da aka ajiye Kazuzi,babban ɗaki ne wanda aka gina shi da zallar dutse da jan ƙarfe, ɗaki ne wanda ake kai duk wani taƙadarin gagararre a cikin Tayaar
Dakarun da suke gadin ƙofar suka bi su da kallon mamaki,saukowa ta yi daga keken dokin,kai tsaye ta tunkari ƙofar ba tare da ta yi magana ba,babban badakaren ya ƙaraso gabanta ya rissina yana faɗin "Barka da wannan lokaci ya shugaba ta"
Kallonshi ta yi fuska a tamke,kafin ta yi magana cikin izza
"Ina so na yi magana da dakaren da aka kamo a yaƙin Baruda"
Muryarshi har rawa take yi wajen furta "ranki ya daɗe su hamsin da uku ne ai,kuma....."
"Ina nufin Kazuzi,babban badakare a Baruda"
Cirko-cirko dakarun suka yi suna kallonta a matuƙar tsorace,ganin haka ta fusata ta ce"ko ba zan samu damar bane?
Ban isa a buɗe min shi ba?"
Murya na rawa badakaren ya ce cikin girmamawa "ranki ya daɗe akwai haɗari a cikin hakan ne,ki yi min aikin gafara shugaba ta"
Kai tsaye ta ce"ina son a buɗe min shi idan har ina da ikon faɗa a ji a cikin birnin Tayaar"
Ba tare da ya sake magana ba,ya miƙe cikin rawar jiki, suma sauran dakarun suka miƙe,aka buɗe mata ƙofar, ba tare da ta sake kallon ko da sashen da suke ba ta sanya kai a cikin tangamemen ɗakin, kuyanginta suka rufa mata baya,suma dakarun huɗu daga cikinsu suka rufa mata baya,ya rage saura biyu a cikin guda shidan da suke gadinta
A can ƙurya suka hango Kazuzi a zaune,tun daga yadda aka shigar da shi cikin wajen har zuwa yanzu yana nan a zaune kanshi a ƙasa, idanunshi a rufe, abinci da ruwan da aka kai masa ma ko bi ta kansu bai yi ba
Har yanzu damtsenshi,inda marigayi sadauki Waleed ya sare shi yana ɗan zubar da jini,duk da cewar an saka masa magani a raunin
Daga baya kuyangin da dakarun suka tsaya,ita kuma ta ƙarasa gabanshi tana jefa masa wani kallon tsana,kafin ta bushe da wata iriyar dariya,tana dariyar ta ƙarasa gabanshi, ta sanya hannu ta ɗago fuskarshi,ta sanya hannu ta yaye gashinshi fuskarshi ta bayyana
Ya subhanallahi!samun kyakkyawan namiji kamar kazuzi abu ne mai wahala,komai na fuskarshi mai kyau ne da tsaruwa,tamkar wanda ya shiga gasar zana kanshi, gashinshi da ya sauka har gadon baya ya sake ƙawata kyau da sura da Allah ya ba shi,gashi namiji ne mai cikar zati da mazantaka,muradin ƴan mata a wancan lokacin
"KAZUZI!haka sunan yake ko?
Barka da zuwa daular Tayaar,a wasu shekaru baya sunan Kazuzi kaɗai idan mayaƙa suka ji yana kaɗa musu hanjin cikinsu, ballantana karo da shi a filin yaƙi,sau da dama mayaƙa suna yi maka laƙabi da ka fi dodo illa, saboda yadda kake ragargazar maza kana gamawa da su
A haka karambaninka ya kai ka ka kashe min ɗan'uwa na ɗaya tilo da mahaifiyata ta haifa,wanda sanadin hakan ya sa baƙin ciki ya yi silar barinta duniya
A taƙaice dai,ina yi maka kallon makashin mutum biyu, Yarima Nashwaar,wato yayana,da sarauniya Shahida, wato mahaifiyata
Ba sai na cika ka da surutu ba, yadda ka zo masarautar nan a matsayin bawa,na yi maka alƙawarin sai ka amsa hakan,sai na tabbatar maka da lokacin wannan ba lokacin da kake tashe bane,ka san shi tashe lokaci gare shi,kamar yadda naka ya zo kuma ya shuɗe
Sai na tabbatar da ka yi rayuwar ƙasƙanci a cikin masarautar nan,sai na tabbatar da dabba ma ta fi ka ƴanci da gata a cikin Tayaar
Da gimbiyar Tayaar wato HAYAAT kake magana!!!"tana kai wa nan ta saki fuskar tashi ta miƙe cikin takunta na isa da izza ta fice daga ɗakin ranta fes, kuyanginta dakarun suka rufa mata baya
Har suka ƙarasa ficewa daga ɗakin kan Kazuzi yana ƙasa kamar yadda suka zo suka same shi,a karo na farko,tunda ya rasa muradin ranshi ya ji ya kamata ya buɗe idanunshi don sake ganin wannan duniyar da ta yi masa yankan baya a lokacin da bai yi zato ba
Shi dai jarumi,mayaƙi,kuma sadauki KAZUZI IBN MURAAD shine wai aka kawo shi a ɗaure a sarƙa a matsayin bawa,bawan ma na wani birni da ya raina,ya raina jarumansa,duk menene sila?MALLI!
tuna sunan kawai sai da ya ji zuciyarshi ta girgiza,a hankali ya mayar da kanshi ya jinginar yana sauke numfashi da sauri da sauri, menene amfanin rayuwarshi da babu Malli a ciki? meyasa aka kashe masa Malli a gaban idanunshi?shin ta cancanci irin wannan kisan? Wanene silar mutuwar tata?shine
To indai haka ne bai ga amfanin rayuwarshi a matsayin wani mai galihu ba muddin babu Malli a duniya,ya gwammace ya mutu a matsayin ƙasƙantaccen bawa da ya rayu cikin farin ciki amma babu Malli a gefenshi,zai yi fatan waɗannan mutanen su yanke masa hukuncin kisa mafi wuya,ko zai rage masa ciwo da raɗaɗin wannan gangancin da ya yi har ya rasa abun da ruhin shi yake marari a kowanne lokaci na rayuwarsa
Malli ita ce farin cikinshi, walwalar shi, ma'anar rayuwarshi,fitilar rayuwar shi,kuma mahaɗin rayuwarshi,ji yake yi a rayuwarshi zai iya bayar da fansar ranshi akan Malli ɗinshi ta ji rauni duk kanƙantarshi
A yanzu jin shi yake yi a duk duniya babu wanda ya kai shi baƙin ciki,babu wanda ya kai shi shiga tashin hankali,babu wanda ya kai shi asara a rayuwarshi
"Ruhi na!ruhi na kana ji?
Yaushe za mu je ka kamo min irin wannan barewar da ka taɓa kama min kwanakin baya?ina son namanta,yana yi min daɗi sosai, musamman ma idan kai ne ka gasa min da hannunka,sai na ji wani ɗanɗano na musamman ya ƙaru"
A hankali ya mayar da kanshi ya jinginar yana sake lumshe idanunshi, ire-iren shiriritar Malli kenan a duk lokacin da suke cikin nishaɗi
"Ruhi na!
Menene dalilin da ya sa ba ka bar babana ya jagoranci tawagar yaƙi ba?
Ba shine Sarkin yaƙi ba?ko so kake yi wani abu ya samar min kai?"
Murmushi Kazuzi ya yi ya dube ta ya ce"au haka ne?
Wato shi matarshi bata san soyayya ba da zata bar shi ya fara afkawa ba ni ba?"
Ɗan murmushi ta yi tana yatsina fuska,ta zauna a kusa da shi ta ce"ka ga Ni da kai mun kusa aure,ba zai kyautu a ce angon wani abu ya same shi ba,don dai na san ka fi ƙarfin wata runduna wadda ta wanzu a duniya ma, ballantana a wannan nahiyar tamu"
Ɗan murmushi ya yi ya dafa kafaɗarta,ya ce"hakanan Sarkin yaƙi shima,ya girmi dukkan wata runduna,kar ki manta rundunar Baruda shine ya ba mu horo,har zuwa yanzu an rasa wanda zai iya tunkarar mu ya farmake mu,kai ko da ya iya hakan ma ba zai sha ba"ƴar dariya Malli ta yi ta kwanto da kanta gefen kafaɗarshi,ta lumshe idanunta tana murmushi ta ce"Duniya ta,kaine komai na,kaine dukkan buri na da cikar burina,ina matuƙar alfahari da kai"Kazuzi ya yi murmushi ya ce"nima ke ce farin ciki na,abin alfahari na, duniya ta,dukkan wani buri na,hasken rayuwa ta,ke ce komai na,sannan alfahari na"ƴar dariya ta yi ya miƙe tsaye tana karkaɗe ƙasar da ta taɓa mata tufafinta,ya yi ɗan murmushi yana taya ta kaɗewa,ta kama hannunshi,ya miƙe suka wuce cikin gari
Doguwar ajiyar zuciya ya yi saboda tunawa da ya yi wadda yake yin wannan tunanin da ita yana murmushi babu ita a duniyar,a karo na farko tun bayan da ya rasa ta ya iya buɗe baki ya yi magana
"Abin bauta!!!
Wanne laifi na yi da girma?me na aikata ka raba ni da rabin rayuwa ta? meyasa?shin na cancanci hakan ne? menene dalilin hakan?
Na zaɓi zama a matsayin bawa ƙasƙantacce,ko nima a raba ni da numfashi na kamar yadda ka bari aka raba ni da ƙawar zuciya ta"ya ƙarashe maganar cikin wani irin rauni da bai taɓa jin shi ba a tsawon rayuwarsa
💫
"Barka da shigowa ya shugabana!"da kai ya amsawa kuyangar sannan ya ba su iznin ficewa daga sashen da hannunshi,babu musu suka duƙa da girmamawa sannan suka fice daga sashen,ya mayar da kallonshi ga Hayat da ke zaune a bakin gadonta tana bin shi da kallon mamaki ganin yadda ranshi ya yi matuƙar ɓaci
"Barka da shigowa abbana!"ta faɗa tana rissinawa
"Me ya kai ki ɗakin hukunci Hayat?"
A hankali ta ɗago kai tana kallonshi,zata iya cewa rabon da ta ganshi a cikin Irin wannan ɓacin ran ta manta, cikin sanyin murya ta sake rissinawa,ta ce"a yi min afuwa ya shugaba na,na yi wani alƙawari ne,shine na je na cika"
"Amma kin san cewa Kazuzi ya fi haɗari haɗari?kin san cewa Kazuzi ya fi shaiɗan?ya fi sharrin mayaƙan abokan hamayya dubu?
Kin san wanene Kazuzi da kika tunkari inda yake ke kaɗai ba tare da tsoro ba?
Yanzu da ace wani abu ya same ki fa?ko kin yi tunanin ya rissina ne saboda an kamo shi an kawo shi nan a matsayin bawa kawai?"
Hayat ya sauke numfashi, cikin girmamawa ta ce"ina neman afuwa abbana!
Amma tabbas na daukar wa kaina alƙawarin sai na ga ya durƙusa a gaba na,sai na bautar da shi na wulaƙanta rayuwarsa saboda a dalilin shi na rasa duniya ta, ɗan'uwa na magajin Sarautar Tayaar da mahaifiya ta, kana ganin na bar shi ya tafi a banza kenan?
Abby idan na yi haka bana jin na kyautawa ɗan'uwa na"ta ƙarashe hawaye suna zubo mata daga idanunta
Lokaci guda zuciyar sarki Iyaad ta buga sakamakon tuna wannan asarar da ya yi,amma sai ya dake,ya dube ta cikin tausasawa,da Muryar lallashi ya fara faɗin
"Ƴata!
Ki yi haƙuri da rayuwa,ki kasance mai yafiya da tausasawa
Mu masu jihadi ne, waɗanda suke yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah,ashe idan haka ne mutuwa rahama ce a gare mu
Raki ne,ko na ce kai ƙarar Allah,ashe a matsayin mu na musulmai sai mun yarda da cewa shahada a wajen yaƙi ita ma nasara ce sannan za mu cim ma nasara?
Ba mu faɗi ba, kamar yadda Allah ya faɗa a Alkur'ani ba mu rasa shahidanmu ba,ciki kuwa har da ɗan'uwanki
Hayat!wannan ba lokacin ɗaukar fansa bane, lokaci ne na godiya ga Allah,zuwa gobe za'a laƙana wa ribatattun yaƙin mu kalmar shahada,muna fatan gaba ɗaya za su musulunta,daga wannan lokacin za muyi musu Barka da shiga musulunci ne,ba fansa za mu ɗauka kamar yadda kika ce ba,in sha Allah"
Sake rissinawa ta yi,cikin girmamawa ta ce "ka gafarce ni abbana!
Tabbas na yi kuskure, don ban san da wannan tsarin da kuka yi ba,nima kamar ku ina farin cikin samun ƙaruwar musulunci,sai dai Abba ina neman afuwarka
Idan bai karɓi addini ba ya kamata a ƙaddamar masa da hukuncin kisa kamar yadda aka yiwa sauran ƴan uwanshi "
Dan murmushi sarki Iyaad ya yi,ya ce"ina fatan ya karɓi addinin ma, ƙaruwar musulunci yana sama da komai"ɗan murmushi ta yi ta ce"haka ne, Allah ya ba ka nasara abbana"
Dafa kanta ya yi yana murmushi ya ce"na bar ki lafiya ƴata"daga haka ya juya ya fice daga ɗakin, kuyanginta da ke tsaye suna jiran fitowar shi suka rissina,sannan suka koma zuwa cikin ɗakin
TSIBIRIN GAYUR,FADAR SARKIN ALJANU
Ƙaton tsauni ne,mai tsawo na tsawon mil biyu, faɗi kuwa ya kai mil huɗu a tangamemen tsibirin na gayur,inda fadar sarkin aljanu yake mulki,wato SARKI LAIMUS
#Nusy_bee
08125952284
