*★MATAR DAMISA★*
By Asmeetah writer
PAGE 6
Tana cikin nazarin duniya kamar wacce aka zabure ta ta yi falo da gudu kamar wanda ta ga abun tsoro, daga nan ta haura upstairs ta shige d'akin Junaid, da sauri ta je gabansa ta tsaya tana ajiyar zuciya! Still a yanda ta barshi anan ta dawo ta same shi, lokaci guda taji wani irin tausayinsa ya kamata ta wani 6angaren kuma tarin tsanar sa ne a cikin kwayar idanunta, ba ta kaunar ganin fuskarsa, sunkuyar da kanta 'kasi tayi tana tariyo lokacin da ya buge mata mahaifiya da kalar wulakancin da ya yi mata itama yaso ya rabata da duniyar a lokacin, zazzafar hawaye ne yake gangaro mata ta d'ago da manya- manyan idanuwanta wad'anda sukayi jawur lokaci guda, kallon tsana takeyi mishi tana maganar zuci
"Saboda mahaifiyata zan taimake ka, ba don haka ba ba abunda zaisa na ceci rayuwarka a halin yanzu sai dai ka hallaka! Allah yasa ka mutu"
a halin yanzu mutuwar Junaid shine farin cikin Ayushh.
Rufe idonta tayi sosai ta d'ago da hannayenta biyu zata jawo shi, wani irin murya ne mai ban tsoro ya daki dodon kunnen ta
"KEE AYUSH KADA KI KUSKURA KI TAƁA SHI, UMARNI NAKE BAKI, KAR KI KARYA MUN DOKATA, YANA CIKIN UQUBA TA"
Nan fa ta bara jin kukan namun daji da na mujiyoyi 🦉 cikin firgici da tsananin tsoro yasa ta rungumi Junaid ta 'kan'kame shi cikin rashin sani,
(Ita da ake bata dokar kada ta ta6ashi amma tsananin tsoro yasa ta rungume shi gaba d'aya)
dogon numfashi yajaa tare da d'ago kansa sama ya bud'e jajayen idanuwansa wad'anda suka canza launi tsabar azaba, wani irin sanyi yaji a cikin zuciyarsa kamar wanda aka watsa masa ruwan sanyi, sakin shi akayi daga sama ya tafo luuuu ya fad'a kan Ayush atare suka fad'o 'kasan lallausar carpet, 'Kara Ayush tayi saboda jin yanda Junaid ya fad'o akan ta ga ciwon breast d'inta da ya fame mata shi!
Shi kuwa sai 'Kara narkewa yake ya 'kara 'kan'kameta, shi yasan kalar nutsuwar da ya ke samu daga gareta ba tare da yasan ko ita wacece ba, haka yake maida numfashi sama-sama!
Guri kuwa yayi tsitt ba alamar motsi sai numfashin da suke ja a tare...
(Ayush itace samun nutsuwar Junaid, itace kuma samuwar warakar sa indai ta samu rauninsa wanda yake jikinta, in har ta kusanci yanda Junaid yake to babu wani abun cutarwar da zai sameshi, a yanzun mah itace ta ceceshi daga azabar da ake gana masa, domin su ma kansu Aljanun tsoronta suke,
Ita d'in dai itace AYANAR JUNAID 🧚♀️🧚♀️ ).
Dakyarr Ayush ta tattaro iya 'karfinta ta ture Junaid gefe tana mai da numfashi duk ya kashe mata jiki, ta d'ago zata mi'ke ta nufi yanda yake kwance da rarrafe ta Isa, waro ido waje tayi tana 'kare shi da kallo abun mamaki duk ciwon dake jikinsa babu shi, jikinsa ya koma normal kamar bashi ne wanda akaita azabtarwa ba babu tabo ko 'kurzune d'aya sai tarin gargasar dake kwance saman kirjinsa,
Abun ba ƙaramin bata mamaki yayi ba, a ranta take fad'in
"Anya ba Aljani bane, nashiga uku nayi gamo" a tsorace taja da baya zata gudu yayi caraf ya ri'ke hannun ta, a hankali yake bud'e idanuwansa yana ganin Dishi-dishi har idon ya washe, nan ya sau'ke kyawawan idanuwansa akan ta idon ya washe ya komo fari soll, a hankali yake lumshe ido still hannunsa yana ri'ke da nata.....
A hankali yake motsa 'karamin lips ɗinsa murya Ciki-ciki yake fad'in
"Wace ce ke?"
Murya na kakkarwa ta ce
"Ni ni ni ni" ta rasa mai zata ce tsabar tsoro kuma lokaci guda yayi mata kwarjini ga wani shakkar sa da take ji! Tana cikin motsa baki ba tare da yasan mai take fad'i ba ya katsar da ita "please can you carry me to go inside bathroom?"
Yayi maganar da harshen turanci, waro Manya-manyan idanuwanta tayi waje tana binsa da kallo, seriously taji abunda ya ce! Duk da batayi karatun boko ba amma ta iya turanci sosai ta koya a gurin mahaifiyarta domin Umanta sai da ta zo Nigeria sannan ta koyi Hausa amma yarenta daga Ghananci sai turanci ta kuma iya yaren French, haka itama Ayush duk ta iya yaren sai dai yaren mahaifinta ne bata iya ba wato fulatanci.......
Ita dai ba za ta iya maida masa da amsa ba sai dai tayi magana da zuciyarta
"How comes Zan iya d'agaka kana nam gardi da Kai, amma sai dai kyakykyawa ne mutumin"
tana cikin maganar zuci taji ya ri'kota zai tashi ai tunin ta fad'a jikin shi 'karfinsa ya ninka nata sau goma 😄
Shima komawa yayi ya kwanta yana bin ta da kallo, d'agowa tayi a hankali suna fuskantar juna, numfashin su yana dukan na juna, ido cikin ido suke kallon juna! Dakyar Ayush ta iya cewa
"you're a strong man, I can't....... Kasa 'karisa maganar tayi sakamakon Breast d'inta dake mata ciwo ga wani feeling da yake shirin kawo mata ziyara duk ya kashe mata jiki shi kuwa babu wani abunda yake ji babu sha'awa a ransa an gusar masa da shi,
Gaba d'aya jikinsa ne yake masa ciwo, shi bai San meya faru dashi ba a tunaninsa duk abunda ya faru dashi mafarki ne saboda ya duba jikinsa babu alamar ciwo...
"I need bath, please ɗagani mana ko na zama gadon kwanciyarki ne"
yana magana ne a lokacin da yake shirin tashi...
A kunya ce Ayush ta tashi daga kansa, ita dalilin da ya sa ta cigaba da kwanciya masa rad'ad'in da Nononta keyi mata ne yasa ta kifar da kanta saman kirjinsa hakan yasa yayi mata magana...
Tashi yayi yana tafiya a hankali zuciyarsa kuwa cike tam da tambayoyi
"Shin meya same ni haka bana jin dad'in jikina, and than who is dis girl? And what is she doing in my room at this midnight? still ni da nake kwance on my bed me ya kaini 'kasa?".
Haka ya shige cikin toilet yana wannan tunanin!
Itama tashi tayi tana maganar zuci
"Tabbas wannan shine ya sha'ke mun wuya bayan ya buge mun mahaifiya da mota, Anya kuwa yanada lafiya kuwa, Ina tantama akansa wannan ba mutum bane, na ganshi a wani mummunan hali yanzu kuma Gashi lafiyarsa klau ba ciwo a jikin shi, Anya ba mafarki nake yi ba..? Shin meye silar faruwar haka..? A lokacin da ya raunana mun breast na bar d'akin normal amma kuma bayar faruwar haka meya faru..? Zanyi bincike akan wannan al'amarin......"
Nufan hanyar fita tayi taji an tsayar da ita
"where are you going....?"
Waiwayowa tayi da sauri ta kalle shi, fuskarsa a d'aure ba annuri yana d'aure da towel a kunkumin shi alamun ya watsa ruwa ne a jikinsa..
Nufan wurin da take tsaye yayi har sai da ya 'karaso gurin da take GAF to GAF suna fuskantar juna ya ri'ke kunkumin sa yana mata kallon tuhuma..
Ganin kallon yayi yawa yasa ta sunkuyar da kanta 'kasa tana kallon carpet, hannu yasa ya tallafo haɓarta suna fuskantar juna ya ce "who are you...?"
Shuru tayi ba ta ce komai ba sai siraran hawayen da ya gangaro mata.
Sakin fuskarta yayi yana fad'in
"can't took to me..? Okay have a seat" ya nuna mata bakin gado, ya koma gaban mirrow yana milka jikinsa da cream mai shegen 'kamshi! Ayush zama tayi a bakin gadon kamar yanda ya umarce ta tana ta sa'ke-sa'ke a raanta cewa
"yanzu kenam yana nufin ya manta da fuskata..? Ya manta da matar da ya d'auki raanta...?"
Lokaci guda kuwa taji kamar ta sha'ke shi ta baya.. Tana bin duk surar jikinsa da kallo
"Gaskiya yana da ƙirar jiki mai kyau, ga tsayi ga faɗi ga ɗaurarran jiki ga kuma gargasa ta ko ina a kwance luff-luf gwanin sha'awa, sai dai kuma shi baya yabon mace kamar yanda mace take yabonsa bcox baya ra'ayin mace kwata-kwata, bai ta6a jin son mace ko sha'awarta ba haka yake zaune daga gida sai gida ko aiki baya zuwa yanzu....
Ayush fah ta kafa idonta akansa bata san lokacin da take sauƙar da murmushi ba,
Shi kuwa gaba ɗaya ya tsargu da kallon da takeyi mishi , a fusace ya juyo gareta, a kaci rashin sa'a jikin mirrow ya kama towel d'in dake d'aure dashi, ya zame gashi bayan towel babu komai a jikinsa...
Ayush tana ganin haka ta zaro ido waje wani irin ihu tayi tabi saman gadon yaraff ta fad'i sumammiya, ta ga abun da ba ta ta6a gani ba tinda uwatta ta haifeta....... Shi kuwa ihun datayi ne yasa ya bita da kallo, bai bi takan towel d'in ba haka ya tsaya zigidirrr yana kallon Ayush wacce ta suma akan gadonsa........
Tsaki yaja ya nufi yanda jerin kayan baccin sa yake ko sauraronta baiyi ba, haka yake taku tsindir ba kaya a jikinsa ga towel kuma a yashe a 'kasa,
Riga da wando ya zaro marasa nauyi sleeping dress milk colour ya sanya su a jikinsa ba 'karamin kyau kayan sukayi masa ba, sai hasken sa ya ƙara bayyana!
Ya feffeshe jikinsa da turare mai sanyaya zuciya, yana kammalawa ya nufi hanyar fita zai dubo mommynsa, kamar wanda aka dakatar da shi ya tsaya cak sannan ya dubi clock dake manne a jikin bango 3:30 na dare, fasa fita yayi a bayyanai ya ce
"nasan kinyi bacci yanzu, may God keep you safe my Mom"
Juyawa yayi ya nufi gurin bed d'insa, ya bi ta gefen Ayush ya kwanta, jawota yayi close him ya kashe light d'in d'akin sannan yaja musu mayafi rungumarta yayi suna fuskantar juna, da haka har bacci yayi awun gaba da shi! Itama Ayush daga suma ta wuce da yin bacci,
Asubar fari anata 'kiraye- kirayen sallah dai dain lokacin wayar Junaid ya hau ringing
Juye-juye Ayush ta fara yi tana mur'tsika ido tana 'ko'karin bud'e idonta taji an 'kan'kameta juyar da kanta tayi tana fuskantar Junaid wanda numfashin su yake gaurayuwa, a firgice ta zaro ido waje ga tsananin tsoro da ya bayyana akan fuskarta, a hankali take janye jikin ta daga nasa har ta samu ta zame kanta tana maida numfashi tare da dafe kan kirjinta tana kallon kyakykyawar fuskarsa shi kuwa sai sharar baccin sa yake lokaci guda tasau murmushi har saida dimple d'inta ya bayyano, haka kawai take jin nutsuwa a tattare da ita..
Wayarsa ce ta sake ringing a karo na biyu, idonta na kan wayar batada niyar picking har sai da ya kusan katsewa sannan takai hannun ta kan wayar, Doctor Hasheem ta ga an rubuta picking tayi ta kara akan kunnen ta tana sauraron Wanda ya kira
"Hello Captain Junaid, mahaifiyarka tana cikin mawuyancin hali, sunanka kawai take ta ambato, please kazo yanzu har sai ta ganka kafin mu iya magance matsalar ta....! Shuru yaji anyi ba amsa, ya sake cewa
"Hello Captain Junaid kana jina kuwa...?" Katse wayar Ayush tayi ba tare da ta amsa masa ba, wani irin kuka ne mai cin rai yazo mata, tana cikin kukan taji wani 'kiran ya sake shugowa wayar, da sauri ta katse 'kiran tayi switch up d'in wayar gaba d'aya ba tare da tasan ina ta danna ba domin Ayush ko keypad bata iyaba balle wannan 'katuwar waya 'kirar iPhone 15...
Bud'e wardrobe tayi ta sa wayar cikin kayansa, t katse wayar ne saboda kar ya kai mata naushi again, tayi waje da gudu tana toshe bakinta da hannayenta kuka ne yaso ku6uce mata....
Bedroom d'insu ta nufa tana shiga ciki ta doku a saman gado, lokaci guda ta fashe da kuka tana fad'in
"innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, mahaifiyata ta tafi ta barni itama wacce take kula dani tana kwance rai a hannun Allah, Allah ka taimake ni ka bawa Auntyna lafiya, idan ta mutu bansan Ina zan sa kaina ba, wayyo niii"...
Bayan ta gama kukanta mai isanta ta tashi ta shige toilet jiki ba 'kwari Alwala tayi sannan ta tsayar da sallah tare da lafulfuli, Addu'o'i ta shiga karantowa, tayi Addu'a a mahaifiyarta tare da nema mata gafarar ubangiji sannan tayiwa momin Junaid Addu'ar nema mata lafiya...
Junaid yana kwance yanaji har an shiga sallah yanaso ya tashi yayi sallah amma dai dai lokacin aka shagaltar dashi da wani mafarki mai ban tsoro da kuma firgici....!
Gashi a cikin tsakiyar ruwan da bashi da iyaka, crocodiles ne sun kai goma suka nufo shi a cikin ruwan nan, yanata gudu a cikin ruwan ya kasa isowa karshen ruwan, su kuwa sunyi daf dashi suna bud'e manya-manyan bakinan su, wani 'karamin jirgin ruwane yazo ya tsaya ta gabanshi sai dai jirgin ya d'anyi nesa da shi wata kyakykyawar Yarinya ce mai sanye da fararen kaya dogi da suman gashin ta har gadon bayanta yarinyar farace soll ta ware hannayenta biyu tana fad'in
"Junaid taho, kazo gareni don ka tsira da rayuwarka...."
Tsayawa yayi cakk a cikin ruwan yana kallon kyakykyawar yarinyar dake masa magana, zazza'kar muryarta ne ya sake dukan dodon kunnensa "JUNAIDDDDD ka kula bayanka" kafin ya ankara har sun kawo masa hari, "JUNAIIDD ga wannan, ta cillo masa wata doguwar tokobi mai she'ki irinta sarakuna. .
Hannunsa yakai ya cafko wu'kar kafin yakai musu sara har sun rufa mishi ƙasin ruwa suka lumar da shi...
"Junaaiidddd" yarinyar ce ta kwalla mishi ƙira sannan ta ce "karka bari suyi nasara akan ka, ka zamo jarumi na gaske, kayi yaƙi da su kamar yanda kake a filin dagaaa......" Bata 'karisa maganar ba ta ga jini duk ya malale ruwan, fashewa tayi da kuka tana fad'in
"why! Why!! Why!!! Meyasa zaka bar maƙiya suyi nasara akan ka Junaiid.."
Ji tayi an ri'ke jirgin da sauri ta le'ka 'kasin ruwan
Junaid ta gani ya d'ago da kansa duk ruwa ta ko ina a jikinsa, kallon juna suka tsayayi murmushi yasau mata itama ta mayar masa da martani..
Mi'ka mata hannu yayi ta ri'ko shi d'aya hannun kuma yana ri'ke da takobin nan ya haura cikin jirgin still bai daina kallonta ba itama idonta akansa..
Daga bisani ya soma motsa lips d'insa zaiyi magana tayi saurin katse shi ta d'ora yatsanta akan lips d'inta "Shhhhhhh 🤫🤫 you wanted to ask me who I am again...?"
Abun ya d'aure mishi kai a ransa ya ce
"wace ce wannan" kamar tasan abunda zai tambayeta kenam!
Murmushi tayi ta kanne masa ido d'aya 6atttt ta 6ace masa, a firgice ya mi'ke tsaye yana waiwaye baiga kowa ba....
Firgitt ya tashi daga baccin da yake duk gumi ya wanke masa jiki duk da A.C dake d'akin
Yana furta "Laa'ilaha ilalla, Muhammadu rasulullah S.A.W"
Agogo ya kalla 8:30 waro ido waje yayi
"A'Uzubillahi Mina shaid'anin rajin, The Fajr prayer has already passed.”
a gaggauce ya tashi ya shige toilet yayo alwala ya tsayar da sallah...........
Mommy kuwa tana kwance a gadon asibiti tana 'kiran sunan Junaid har numfashinta ya d'age cak oxygen aka sanya mata domin da sauran bugun zuciyar,
Likitoci sunyi ta 'kiran wayar Junaid switch up daga farko ya shiga amma daga karshe kuma switch, bodyguards kuwa suna kawo mommy hospital suka fece Junaid yafi karfinsu zai iya hallaka su wata rana...
Doctor Hasheem har gidan yaje dubo Junaid sai dai an'ki bud'e gate, shima mai gadi yana kwance zazza6i mai zafi ya rufeshi ko kwakkwarar motsi baya iya yi, hakan yasa Doctor Hasheem juyawa yayi tunanin babu kowa a gidan, shima kanshi ya shiga damuwa ganin Doctor Fateemah a wannan halin..
Yana tu'kin motor yana nazarin "shin meya faru da Junaid? Kodai ciwon shi ne ya tashi a wani gurin! Amma Ai Doctor Fatima bata shiga irin wannan tashin hankalin akan ciwon Junaid saboda ta saba dashi tin yana yaro..."
Haka ya ringa tunani har ya shiga cikin hospital.
Wata Nurse ce ta nufi gurin da Doctor ya parker motorsa tana fad'in
"Doctor baka samu Junaid bane? Zata iya rasa rayuwar ta indai bata sa Junaid a Idonta ba, bugun zuciyarta ya fara low! Doctor please we should help her.."
Junaid bayan ya idar da sallar baccinsa ya cigaba da yi
Allah sarki duk a tunaninsa momminsa na a cikin gidan....
Itama Ayush bacci ne yayi awun gaba da ita domin jiya bata samu isashshen bacci ba, duk ta mance da wayar da tayi da Doctor akan ana neman Junaid, amma tasan mommi tana asibiti sai datayi mata Addu'a kafin bacci ya d'auketa.........
> PLEASE FOLLOW MY CHANNEL TO VIEW MORE....
