༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ
_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_
Unexpected and Surprising 🔥💥
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
Page 9&10
♡ ♡ ♡ ♡
ꨄ Wannan fuskar da ba zata taɓa mancewa da ita ba, ita dai wannan fuskar data mata fyaiɗe ta kuma wargaza rayuwar aurenta. Ta raba da da daraja da kuma kimarta, don haka bata san lokacin data saki Scissors ɗin dake hannunta tana zare glass ɗin ta jefar a ƙasa, tare da handglovs da hannunta ke ciki, bakinta ta toshe da duka wannuwanta tana fitowa daga ICU ɗin, idanunta na ƙoƙarin rufewa ko ganin gabanta bata yi, saboda dishi dishin da take kalla, kanta na mata wani kalan masifa da bala'in bugu na ƙafar ya zazzago ƙasa, ganin yadda ta koma lokaci guda ne ya saka nurses biyun dake tare da ita saurin mara mata baya suna tambayar lafiyanta kuwa?, Komai ƙin ce musu tayi har seda ta danga da lafiyayyun kujerun dake center na asibitin, irin na zaman jiran marasa lafiyar nan, babu jimawa sega Dr pooja (Aysha) ta bayyana a wurin tana cewa "Lafiya kuwa Maanol, meke shirin faruwa haka?, naga ma har kin cire uniform ɗin tiyatar?" Idanunta da take suka sanja launi ta ɗago tana kallar pooja ɗin tace, "Sabo da bazan taɓa iyama wannan mugun mutumin tiyatar bane...." Ɗan ja baya Dr pooja ɗin tayi ta ce. "Sabo dame Maanol?" A matuƙar tsawace ta ce. "Sabo da shi ne mugun mutumin daya min fyaiɗ....... Bama ta ƙarasa ba sabo da tsabar yadda ta sarƙe har numfashinta na kamar zebar gangar jikinta... Ga idanunta daya fara ja baya yana lumshewa kamar zata sume... "Subhanallahi Dr Meenerl!!!........... Ɗaya daga cikin Dactor's ɗin ta faɗa don babu wanda ya lura da yanayin sanjawa yanayin nata, don haka Dr pooja tayi saurin tallafota amma tana zamewa ta ma mike ta shige wani daki ta bugo wani kalan masifar kuka na taso mata, akan wani gadon marasa lafiya ta faɗa kukan na kufce mata da tari wanda tarin na fitowa sega jini ya faɗi gudul, zuciyarta ta danne gefenta da hannunta tana ambatar. "Hasbinallu wani'imal wakeen ³" babu jimawa sega Dr pooja ɗin ta sake biyota riƙe da wayarta a hannunta, miƙa mata wayar tayi tana saka ta a handsfree, kamar sauƙar aradu haka taji saukar muryan Ahmad yana bata umarnin Lallai lallai tayi aikin nan, "Wallahi bazan yi ba Ahmad, ba zan iya ba...." Daga ta ɗauka wayar nata tana dokata da ƙasa ta tarwatse kuwa take, zama Dr pooja ɗin tayi tana tallafota ta ce. "Haba Dr Maanol!, kiyi hakuri mana ki fara ceton lafiyarsa, ya kike abu kamar wacce baki san dokokin asibitin nan ba?...". "Wllh babu wanda ya isa ya saka ni yin wannan tiyatar da dai nayi masa ya sama lafiya yaci gaba lalata auren mutane ƙara ya mutu ko babu komai an rage mugun iri." Takai ƙarshen maganar nata zata miƙe, saurin dawo da ita zaune Dr pooja tayi tana sake furta. "Haba mana Maanol yanzun idan ya mutumin nan ya mutu kuma fa?, kin san iyayen yaron nan zasu iya kaimu ƙara kotu fa...." A ɗan zuciya tace "To bazan yi ba, na gaya miki bazan mai aikin nan ba, SO duk ku rabu dani sabo da ba'a dole...." Suna cikin haka sega shigowar wata Matashiyar mata a ɗan burkice, kallo ɗaya zaka mata ka gane cewar bata a hayyaci da nutsuwarta sosai. Har ta zarta su ta dawo tana me furta, "Ina ne inda ɗana yake?...daga yanayin yadda hankalinta yake a tashe ne ya saka su gane cewar uwar yaron ce, don haka kai tsaye nurses ɗin dake gefe da ita tace "Nan ne...." Tana mata nuni da ɗayan ɗakin dake ta bayansu ta glasses,don ɗakin da suke ta fado kai tsaye. Babu jimawa kuma se gata ta dawo tana balbala masifa da bala'in...
"Where Are You The Dactor's?, kina ina?, tana ina?, me kike nufi ne?, so kike ki kashe min ɗa ne?, shin dama ba biyanki ake ba?, ko kuwa ba aikin ki bane?, to maza ki tashi yanzun ki duba min yaro!!!, Dan wllh² idan ya mutu sena nuna miki irin ƙarfin ikon da muke dashi a ƙasar nan, kin ji ko maza ki tashi kije ki duba min yaro....." Gaba ɗaya tin da ta fara maganar nata da hargowa take, gaba ɗaya bata cikin hankalinta....... Tsaye Meenal ɗin ta miƙe ta saka idonta cikin tsaƙiyar na matar bayan ta nuna ta da yatsa tace, "Bari kiji in gaya miki indai akan wannan dabbar ɗan naki ne!, to ba zan masa aikin ba!, in kuma anayi doke to bismilla ki sani inyi mu gani?...
Wani ihun daya kusan cika harabar wurin tayi tane me furta.
"Ƙarya ne!, Ɗan kwara ɗaya ya mutu? Wllh ƙarya ne kuna ina.....ina....ina...ina me asibitin yake?, yana ina Wllh sena sa an ɗaureku idan ɗana ya mutu baku duba shi ba...." Tafiya zata yi tayi hanzarin shan gabanta kamar za tayi kuka kuma ta ce. "Dan ALLAH kiyi hakuri ki duba min shi, shi ɗaya tal ne dani...." Wasu hawayene suka zubo mata tace bazan taɓa iya duba ɗan ki domin shi ne ya ruguza yardar dake cikin aurena, ya lalata min gobe na!, ya kuma illata rayuwata,illar da bata da ƙarshe har gaban abada..... Hannun Meenal ɗin matar ta kama tana shirin kaiwa tsugunne amma Meenal ɗin tayi hanzarin fizge jikinta daga gare ta, cikin ɗaga murya matar tace. "Don ALLAH baiwar ALLAH ki fara duba min yaron nawa!, in yaso in warware ko....ko...kome kike so se...se....se.... Ayi Don ALLAH kiyi hakuri......" Takai ƙarshen maganar nata ta na zubewa ƙasa tana ci gaba da kuka, se ga fitowar wani Dactor nan yana share zufar dake zubo masa, kansa matar tayi da gudu tana me furta, "Ya farfaɗo?, kun duba min shi?..." Kansa yake girgiza mata kafin ya furta. "IS GONE MA'AM, Sedai muce ALLAH ya masa raham..... Ai tin kafin ya ƙarasa maganar nashi ta wani fasa uban ihun da kaff asibitin seda ta ɗauka, ta zube ƙasa tana kururuwar sun kashe mata ɗan ta, kafin kuma kamar wacce aka zabura ta lalubo wayarta kai tsaye ta saka ƙiran numbern mijinta, wanda ƙasar ma, sedai dirarsa ƙasar kenan dake dama yau ɗin ze dawo. Ya a daga wayar ta fasa masa wani uban kuka tace... "Asi....asi....asibitin....4&4 sun kashe mana shi!!!!, sun kashe mana Sameer ɗin mu, sun rabamu dashi, sun ki masa aiki, sunki kulawa dashi har ya mutu Alhaji...."
Ɗif ɗif ɗif
Haka ƙarar datse ƙirar da aka yi daga ta can ɓangaren me wayar, cikin abinda be gaza 30 minutes ba sega jiniyar ƴan sanda da sojoji sun gama karaɗe ilahirin asibitin, gaba ɗaya jami'ai suka ma hospital ɗin ƙawanya kamar irin za'a kama mutum dubu ɗin nan masu laifi, Cikin mugu mugun tashin Dr Aysha ta ƙira Bilal take sanar masa halin da suke ciki, cikin mugun tashin hankalin da yake jin kaf rayuwarsa be taɓa shiga bane yaji ya shiga a lokacin, gashi baya ƙasar baki ɗaya, ga MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin ma da yake da tabbacin shima baya ƙasar, don haka ƙirar Daddyn MAJEED ɗin kai tsaye ya saka yana sanar masa abinda ke faruwa, wanda daidai lokacin da Dr Majeed ke ƙoƙarin cire sau cikin dake ƙafarsa da sauƙarsa kenan a ƙasar, shigowarsa kuma ƙasar kenan, don haka ya dakata cak shi be cire ba shi kuma be saka ba, wani Gwauron numfashi mahaifinsa ya sauƙe yana ce dashi shi kawai ya huta bara yaje yaji da matsalan, kansa ya girgiza masa yana zira sawu cikin nasa, kai tsaye ya sake fita cikin wata lafiyayyar motarsa ta *LAMBORGHINI* wacce ba'a fiye samar kalarta a Nigeria ba, sabo da kuɗin masu nauyin da motar ke lasa, gata wata a wani shafe, wacce ni kuwa AMMEY LAYLERH nace ehhhh lallai yaci a ƙira ta da sunan Lamborghini ɗin,domin kuwa a lamgwamen take, kalarta ma daka kalla kasan ta daban ce ba irin sauran motocin daka saba gani bane, irin su jeef, marcadez benz, toyota highlander, dadai sauransu to wannan ba kalarsu bace....
Tin daga kan yadda yaga an zagaye asibitin nashi ransa ya sake masifan ɓaci na ƙarshen ƙarshe, dan haka da wani mugun gudu ya danna kansa cikin ainihin compound na asibitin, jami'an dake tsare asibitin duk suka yo kansa, sedai bayyanuwarsa akan diga digan sane ya saka su ja baya da alamun mamakinsa me girmar, Me kuma ya kawo *BILLIONAIRE MAJEED DAWOUD ISHAQ?* Wannnan asibitin a cikin irin wannan lokacin?, kallo ɗaya ya musu kai tsaye yana kutsa kansa cikin ainihin ginin asibitin. Dr pooja kai tsaye ya ƙira ya tambayeta tana wanne room ne, cikin rawan jiki ta sanar masa room ɗin da suke, don dama rufe su ne tayi don gaba ɗaya jami'ai sun gama kewaye wurin, don ma sa'ar su ɗaya ƙofar bluetfroof ce, shi ne taimakon da ALLAH ya musu, amma in ba dan haka ba da tuni an gama bandarsu nama ɗanye, gaba ɗaya kusan Dactor's ɗin a ɗakin, don haka ya nufo room ɗin drectly... Bayyanuwarsa ya ankarar da jami'an dake zagaye da wurin, da da farko har sun nufo shi sedai suma ganin nasa ne ya saka su jan birki daga inda suke, shi kuwa Alhaji Kabeee mahaifi ga yaron daya rasu suna can shi da Matarsa Hajiya Madinah suna aikin kuka, sun saka shi a tsaƙiyarsu babu abinda suke se kuka. Da wani spire key yayi using ya buɗe ƙofar, kuma ya barta buɗe in yaso me shigar ma ya shiga.
Dr pooja ce ta gama koro masa duk abinda ya faru, har kan case na fyaiɗen da mutumin ya ma Meenal ɗin bata ɓoye ba, don baya da wata mafita kuma a yanzun daya wuce fadar gaskiya. Tana gama bashi jawaban ya wuni juyo ga Meenal ɗin yana zuba mata shegun idanunsa masu kama dana mayu,lolz inji Meenal ba inji LAYLERH.....
★..
"WHO IS SHE'S??"
Shine kawai abinda ya fara tambaya kafin komai.... "You..." Wata daga cikin nurse da jikinta ke rawa ta sake nuna masa Meenal ɗin a karo na biyu bayan bayanin da Dr pooja ta masa...
.....Fin sama da 5 minutes kenan da suka zuba juna idanu, suna kallon tsaƙiyar idanun junansu babu ko ƙyaftawa, yayinda sauran Dactor's ɗin kowa ke sake shan jinin jikinsa daga yanayin kallon tsana da ƙamar da yake jifarta dashi, da wani kalan ɗan iskan salo ya wani juya mayan oily ayes ɗinsa dake kanta masu matuƙar haske da kyau, kafin ya wani kauda fuskarsa gefe yana mai furzar da wani irin hucin ɗumin da zuciyarsa ta ɗauka, Sai kuma ya sake dawo da idanun nasa a kanta cike da barazana da isa da basarwa ya furta, "WHO ARE YOU?" Yi tayi kamar bama tasan ALLAH yayi ruwansa a wurin ba, sakamakon tsohon miƙin da aka famo mata na daga cikin rayuwarta. Cikin ihu ya wani buga mata tsawa yana sake furta... "Who are you? Tell me who you are, answer me who you are?..." Haka yake ta famar nanatawa don ganin kalan renin hankalin da take son zuwar masa dashi. Ita kuwa a nata ɓangaren duk da yacce yake maganar nashi cikin tsawa be sa ta ɗago ba, bare yasa ran zata tanka mishi. Sema sake riƙe kanta da tashi tana jin duk wasu hargagi da kalamansa ɗaya bayan ɗaya suna mata wani irin amsa kuwwa da tartsatsi a cikin kunnenta, har kan nata na kamar ze rabe gida biyu ko ya fashe mata haka take ji, domin gaba ɗaya komai da take gudun ya dawo mata sabon ne ya dawo mata. Ga wani irin zafin lokaci gudan daya game ilahirin gwaɓɓan jikinta, yana narkar nata da duka wasu gwaɓoɓin dake jikinta da ƙasusuwanta tamkar zasu narke....
"You won't answer me?..."
Ya sake faɗa cikin gizago da tsawataccen sauti mai cike da fusatuwa, har yana bugar desk ɗin dake gabansa. Wanda ya sakata miƙewa tsaye tana sauƙema fuskarsa zazzafen marin da yazo masa a matuƙar bazatar da ya saka kowa rufe bakinsa dake wurin, musamman ma Dr pooja da tafi kowa dake wurin sanin irin ƙarfn iko da matsayin da yake da. Jikinta wani irin rawar zafin dake cigaba da ratsata tun daga saman kai har yatsun ƙafafunta, duk da yanayin da take ciki da kuma yadda jikinta ke fitar da wani kalan hucin masifar zafi seda ta bude lips nata, cikin wata irin dakiya da jarumtar da ta aro ma kanta ta shiga nuna shi da hannu tace....
"Idan baka san daraja da martabar mace ba to lallai kayi gaggawar zuwa ka koyo!, Kai waye da akan wannan dabbar mutumin har kaka cira min sauti?, Ba mace ba ce ta haife ka?, ko kuwa baka da ƴan uwa Matan ne?, yanzun idan da ƙanwar kace a cikin irin wannan halin da nake ciki zaka mata haka? Uyhmmmm zaka tambaye ta akan me yasa taƙi duba mutumin daya wulaƙanta mata rayuwa, Ni nasan daraja da kuma mutumcin kaina, wannan ma na baka warning ne don gaba ka kiyaye...." Tin da ta fara maganar a karo na farko kenan daya wani kauda kansa gefe guda. Kafin kuma ya wani ɗan yamutse fuska da ɗaureta yana maida hankalinsa a kan sauran Dactor's ɗin da sukai jugum-jugum suna kallar ikon ALLAH. Se kuma ya sake ɗauke kansa daga kallonsu ya sake dawo da kansa gare ta, kafin yayi taku ɗaya ana biyu ya wani tsaya nesa da ita yana wani huhhura hanci sama. Se kuma ya wani kaɗa yatsun hannunsa biyu ya ce.
"Da kyau! ai ban san kin iya wa'azi har haka ba, da tuni na yi magana an baki loud speaker sai ki faɗawa jakuna irin ki cewar zaki shelanta musu kin iya wa'azi....amma ba *ABDOUL-MAJEED DAWOUD ISHAQ BAAAA...* Domin shi tin kafin a san za'a yi halittar ki a cikin duniyar ya gama sanin DARAJAR MACE da kuma kimarta, Amma ba wai wake wake wata ba, Duk inda aka ce MACE, to ana nufin kamila wacce ta gama sanin DARAJA da KIMAR kanta, ta hanyar suturta jiki da kare martabar addinin Musulunci, da bin duk yacce tsarin Addininta ya gama shar'anta mata wannan ita ce MACE, ba wa sauran dabbobi irin ki masu fakewa a cikin rigar musulunci suna cin dunduniyarsa ba!!!...."
Bibbiyu idanunta suka fara gani, saboda wata ƴar banzar juwar da taji tana nemar kai ta kasa, wata shiryayyar ciwon zuciya kuma na nemar illata rayuwarta ta raba da numfashi da gangar jikinta. Goshinta ta dafe idanunta na ci gaba da lumshewa duk yacce take son sake gasa da yaɓamar wata baƙar maganar amma tunanin ta be rinjayi hakan ba. Se ma tafiya da tayi luuu baya zata faɗi, Zaro ido Dr pooja tayi tana isa gabanta da sauri ta tarota jikinta tana ɗan dukan fuskarta tana me furta "Are you Okay kuwa Maanol?" Cikin fusgar numfashi da wahala ta buɗe bakinta dake karkarwa tace. "No...no I'm feeling fine is an Fever headache headache headache..... Haka taci gaba da ambatar headache ɗin idanunta na sake lumshewar,
"INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN ³ Sorry let Me tell for Husband" tayi maganar tana ƙoƙarin miƙewa tsaye don ɗauko wayar Meenal ɗin ta ƙira mijinta, amma se ta saka hannunta ta riƙo hannun pooja ɗin tana ɗan girgiza mata kai, kafin cikin ƙarfin hali ta tattaro jarumta ta ce "No I don't call him. Leave me alone.Pleaseeee......." wani numfashi mara sauti ya fita daga bakinta taja ijiyar zuciya shikenan....
Daidai nan kuma jami'an da MAJEED ɗin daya jima da fita ya basu damar shiga suka faɗo room ɗin, Idon Hajiya Madina akan Meenal da bata motsi ya fara sauƙa, don haka cikin ihu tace su ɗauke ta gata nan. Ita ce ta kashe musu Ɗa, duk yacce Dr pooja ke basu bakin akan su barta su ƙyaleta amma bata numfashin itama ƙiyawa sukai, kattan majiya ƙarfin jami'ai biyu su kayi kanta da niyar ɗauka amma uwar tsawar da aka daka musu ta dakatar dasu, shi ne daya dawo ɗaukan car key nashi ya tarar mazan na shirin daukarta ya dakatar dasu ta hanyar buga musu tsawar da ba iyaka jami'an ta razanar ba har da sauran jama'ar wurin. "All of you get out of here. I don't want to see anyone like you in my hospital again..." Wannan tsawar daya sake buga musu ne ya saka su fara zare jiki ɗaya bayan ɗaya, kafin ya taka a hankali zuwa inda take kwance jikin pooja ya zari car key nashi da cikinta ya fice. Se da yakai daf da ƙofan fitan ya ce. "Follow her" yana ƙarasa ficewar kai tsaye. Gadon marasa lafiya Dr pooja tare da wata nurses suka ɗora ta suna fita da ita zuwa ɗakin da tasan can ya nufa, sedai ga tarin mamakinta baya nan ɗin kuma, duk inda ta san zata ganshi bata gan shin ba, dole ta dawo ita da sauran Dactor's suka fara bata taimakon gaggawa.
Dr Majeed ɗin kuwa yana fita kai tsaye babban office ɗin sa da sunan DR MAJEED DAWOUD ISHAQ, ke rubuce a jiki ya budeyya shige ya kuma rofo, ta yacce baka isa shiga ko gane yana ciki ba. Yana tsaƙiyar room ɗin wayarsa na fara ringing ta hanyar flashlight ɗin dake motsi yana kunna kanshi da kashewa dan wayan na silent ne, wani zaro wayar yayi a matuƙar fusace zai jifa da ita, sai dai ganin sunan me ƙiran ne ya saka sa saurin amsa wayan ganin Mahaifinsa ne, kunnensa yakai wayar cikin sese ta natsuwa da yanayin sa yana Daddyn nasa sallama cike da girmamawa. Ta can ɓangaren a natse shima mahaifinsan ya amsa yana tambayar sa yacce ake ciki, se da ya fesar da wata iska daga bakinsa kafin yama mahaifin nasa bayanin duk abinda ke faruwa, har zuwa tafiyar da jami'an suka so yi da yarinyar, se da ya sake fesar da wata iskan kana ya ce.
"The girl is pregnant..." Yayi maganar wani irin rauni na ziyartarn zuciyarsa, sabo da duk lokacin da zai ga mace mai ciki gani yake kamar zata mutu ne ita ma da Cikin dake jikinta irin AMEENATOU ɗin sa, a duk lokacin da zai ga mace da ciki wani kalan rauni kan zuciyarci zuciyarsa har ya gaza ɓoye shi wannan raunin nasa.... Saurin yanke wayar yayi jin yacce numfashinsa ke fara sama sama, duk yacce kuwa mahaifin nasa keta famar ambatar.. _Majeed kana lafiya² kana lafiya kuwa?_ saboda yasan duk inda yake ba'a daidai nashi yake ba. Bayan ya datse wayar mahaifin nasa ne ya jinginar da kansa da jikin ginin. Yana tuno rayuwar da suka yi da ameenatou ɗin sa cikin SO da ƘAUNAR junansu me tsanani, amma lokaci guda ta tafi ta barsa cikin lokacin da suka fi buƙatarta shi da Ƴarsu AYLA data haifa masa, tana shirin sake haifa musu na biyun ta mutu ita da cikin, ta tafi ta barsu cikin kewar da har yau basu sama wacce ta maye musu gurbin wannan kewar ba, ta barsu da ciwon rashin ta, wanda har yau ba'a sami wacce ta cike musu gurbin wannan ciwon ba. Ta barsu da tsoron da har a yanzun be gama barin su ba. Ta tafi ta barsu da ababuwa da yawan da har basu sama masu basu garkuwa daga waɗan nan ababuwan ba.... Musamman yaga mace da ciki hakan yafi komai daga hankali da tunaninsa. Adda'ar duk da tazo bakinsa ya fara karantowa yana jin lallai zai tsaya mata akan duk abinda ya tunkaro ta, ciki kuwa koda hakan na nufin ze jefa kansa cikin matsala ne. Sabo da kusan duk lokacin da suke zaune da ameenatou ɗin sa takan ce dashi.
_ABU AYLA!, a duk lokacin da zaka ga mace me ciki, abar a tausaya mata ce, domin duniyarta tana rabewa zuwa gida biyu ce, ƙafarta ɗaya na duniya, ɗayar kuma na lahira ne, a koda yaushe zata iya mutuwa ko kan cikin ya girma, ko kuma tana gaf da haifesa ta mutu ita da abinda take ƙoƙarin taga ta haife ɗinnn, Ina jin a jikina nima kamar ba zan kai labari ba!, domin kuwa ni kaɗai nake jin abinda nake ji a cikin jikina, idan na mutu abu na farko da zaka fara min, shi ne taimakon masu ciki a duk lokacin da zaka kalle su cikin matsala, abu na farko da zaka Duba a gare su to ni ce!!!, ka ɗauka cewar ni ce ke cikin wannan matsalar, sabo da wasu mazan basa da imani, a daidai gaɓar da ya kamaci ace suna tausayama mace idan tana da ciki, to wasu kuma a daidai ita wannan gaɓar suke samun damar ƙuntata mata saboda da basu ke ɗauke da wannan nauyin ba.... A duk lokacin da zaka ga mace me ciki a cikin matsala kwatankwacin wacce na lissafa maka to ni ce!, Ni ce!!, Ni ceee Abu Ayl....._ Wani kalan ƙara ya saki me tafe da salati yana katse tunanin iyaka haka nan. Don idan yace hannun agogon sa ze dawo dashi baya ababuwan da yawa suna da yawar da jumiri da lokacin ba zasu tsimaya ba... Bedroom ɗin dake office ɗin ya wuce yana sakarma kansa ruwa me sanyi sosai... Tsaye yake ƙarƙashin showern ruwan kuma naci gaba da dukan jiki zuwa kansa, domin ganin abin yake tamkar mafarki ne yake yi, gani kuma yake tamkar idan ya buɗe idanunsa zega a mafarkine ashe hakan ke faruwa. Ameenatou ɗin sa ba rasuwa tayi ba, zata dawo suci gaba da rayuwarsu kamar baya, Ruwan daya taro acikin tafukan hannayensa ya watsa akan kyakkyawar fuskarsa, lokaci ɗaya kuma ya saki wani irin ajiyar zuciya tare dajan dogon numfashi. Gaba ɗaya kuma kwantattun gargasan dake jikinsa na mimmiƙewa... Dafe jikin bangon bayin yayi yana yin wani irin shiru. Wanda shirun da yayi kuma wannan ɗin alamace ta samun nutsuwar gangar jiki da kuma brain ɗin sa, na amsar rashin nata da yayi da hannu bibbiyu domin haka ƙaddararsu ta gama tsara musu ba zasu tsawon rayuwa a tare ba, Kafin ahankali kuma ya janye jikinsa daga gaban classic glass shower ɗin, ruwan da suka shigar masa ido kuma nasa wani abu ciccikowa a cikin idon. Wata nannauyar iska ya fesar daga bakinsa yana nemar kalmar ALHAMDULILLAH ya aza akan laɓɓansa, Jiƙaƙkun kayan jikinsa ya zare yana zarar wani sabon towel ya ɗaura, inda drower'n kasan yake ya nufa da yake da wasu kaya anan ɗin, wasu labcoat sky blue ya saka a natse cikin mutuwar da jikinsa ya gama yi, yana zirawa ya kwanta akan doguwar kujerar office ɗin take wani nannauyar bacci yayi awon gaba dashi, masu cike da mafarkan yarinyar da wannan shi ne gani na biyu daya taɓa mata, da kuma Ameenatou ɗin sa da take ce masa lallai ya kula da ameenatou don ita kaɗai ce macen da ze samu a madadinta.... A wani kalan mugun firgice ya farka sunan ALLAH ɗauke fal a bakinsa, wani gumin tashin hankali na tsatstsafo masa ilahirin gangar jikinsa. Time ya duba yaga bakwai har ta gota,don haka yayi hanzarin miƙewa ya fado bathroom ɗin ya fito ɗaure da alwala. Masjid ya wuce daga nan be dawo ba ya wuce gida.....
★..
Gudu sosai yayi a motar a ganinsa gudun ko shi ne zai rage zafin dake ƙoƙarin faso ƙirjinsa ya fito, saida yayi tafiya mai ɗan nisa kafin yayi parking motar agefen titi, hanunsa dake ɗan rawa ya sanya ya bugi steering motar, tare da furzar da wata iska daga cikin bakinsa me zafi, wata loca dake jikin motar ya jawo haɗe da ciro goran ruwa, ɓalle murfin goran yayi haɗe da kafa goran abakinsa, be ɗauke bakinsa ba har seda ya tabbatar da ya zuƙe ruwan dake cikinta kana ya zare gorar yana jifa da ita, Wani numfashi ya fesar Ahankali nauyin da ƙirjinsa yayi a da na ɗan raguwa, ɗago kansa yayi ya kalli madubin dake cikin motar, da sauri ya kauda kansa gefe saboda kamar gimlawarta ne ya gani, jiyayi zuciyarsa tayi wani irin karyewa har wasu abu na ciko idonsa, kifa kansa yayi ajikin steering motar, baisan ya zaiyi da rayuwarsa ba, haka kuma bai san baƙar ƙaddarar dake son sake kusanto kanta gare shi ba, Bayan Ameenatou yay wani auren. Ya auri Ramlah xiyar shaibah, ƴar hasalin Dubai, ita ma mutuwar tayi da cikin 7 Months a jikinta, ya zo ya auri Fareedah.... Ita ma ta mutu dai wajen haihuwar babu ita babu abin cikin, daga nan ya yafe Aure daga cikin rayuwarsa gaba ɗaya, sabo da be shirya sake fuskantar wani kalubalen ba, duk gudunsa da sauri da taka tsantsan ɗin sa, amma hakan be hana mataye har uku sun mutu a hannunsa ba, kula da zurfafa bincikensa akan hakan amma hakan kuma be sake hana rashin matayensa biyun da ya sake bayan ita ba. Shi yasa a duk lokacin da zai ga mace da ciki kallon wacce ta gama rayuwa yake mata ɗago kansa yayi yana zuba rinannun idanunsa akan jikin steering motar, idanunsa ne suka sakeyin ja kamar an watsa musu garin barkono, Ga tiririn da zuciyarsa keci gaba dayi a cikin rai tunanin sa yana jin bayajin cewa kuma zai iya zama da kowacce mace a cikin duniyarnan, Motar ya kunna yaci gaba da tafiya kai tsaye yana buga hong a babban get ɗin gidan su. Buɗe masa get man yayi shi kuma ya danna hancin motarsa ciki, tamkar me jinya haka ya fito a motan yana tafiya a hankali, A kuma hankalin ya saka zara zaran yatsun hannunsa ya murɗa Handledoor na kofar babban parlourn gidan, yana sanya kansa cikin babban parlourn ta tura kansa ciki.
A hankali yake takawa zuwa ainihin ɓangarensa, ya kai ƙafarsa kenan kan stairs ɗin Benensa ya jiyo muryar uwar da tayi sanadiyar kawo shi cikin duniyar. Cak ya dakata yana dedeta yanayinsa kwarai se dai be juyo ma a samar laɓbansa ya furta. "Sannu da gida Ummieh!" Ya ce kawai yana shirin hayewa samar... Sedai ya dakata ne sakamakon muryar abu mafi tausayi da soyuwa a cikin duniyarsa AYLA... Da gudu ta isa gare shi tana rungume ƙafafunsa bayan ta jefar da ƴar Teddy'n dake hannunta ƙasan floor'n. Gaba ɗaya ya shanye duk yanayin dake tare da shi, kafin ya juyo yana rage tsawonsa daidai nata yana sakar mata murmushi yana kama fuskarta yace. "How is your night Baby AYLA?" Wani ɗan jujjuya ido yarinyar tayi kafin takai bakinta ta sumbaci goshinsa ta ce.... "THANKS GOD I'm fine..." Ɗan janye ta baya yayi yana kallar shigar ta, don wannan yana ɗaya daga cikin kamar aikinsa, sabo da lumonia ɗin da take ɗauke da ita. Wata ijiyar zuciya ya sauƙe ganinta sanye da wando da riga na sanyi, da takalmi cover sedai kan babu hula se gashinta dake rito a bayanta irin na uwarta, hannunta ma da safan hannu......
Ɗan murmushi ya mata kafin yace "Babyn Papa tana lafiya?" Ɗiɗɗige tayi tana sake kissing goshinsa ta ce...
"Today is not a happy day for me.."
Tayi maganar tana wani shagwaɓe fuskarta.
Dan zaro idonsa waje yayi yana me cewa. “Ohh Dear Papa what Happen?"
"PAPA is this good for you?"
Gefen kunnensa ɗaya ya ɗan kama yana me sake cewa. "Ohh to ni kuma ɗan Ummiensa mi ye nayi kuma?".
"Ka dawo ka sake tafiya ko kallarka ban yi ba!..." "Ohhh SO sorry na dena cutie " daga nan ya kama hannunta suna hayewa sama. Se da aka ƙira sallan isha'a suka fito tare da ya wuce masjid tare da Daddynsa. Koda ya dawo dinner ma sama sama yayi ya haye sama bayan ya musu sallama, yana isa bedroom ɗinsa kayan dake jikinsa ya cire tare da shigewa cikin bathroom, wanka yayi tare da ɗauro alwala kana yafito, dogon wando na bacci ya sanya babu da vest, kwanciya yayi akan makeken gadonsa tare da lumshe gajiyayyun idanunsa yana faɗawa wata duniya ta daban. Bacci barawo gaza ɗaukan sa yayi se daf da asba, amma hakan be sa ya makara sallar ba, yana dawowa ya sake komawa bacci me nauyin da be sama ma daren jiya na sake ɗaukarsa.
10:30am.
Ahankali yake buɗe kyawawan idanunsa masu ɗauke da zara zaran gashi asamansu, kai tsaye ganinsa na sauƙa akan agogon dake saƙale jikin bangon ɗakin, cike da nutsuwar daya samu ya zuro ƙafafunsa ƙasa daga kan gadon, bathroom ya shiga babu jimawa ya fito da alaman wanka ya yo. Tsab ya gama shirya kansa cikin wani lallausan yadi, ya feshe jikinsa da turarukansa masu ƙamshi da kama jiki, combat shoe ya sanya aƙafarsa haɗe da ɗaura agogon Apple a hanunsa na dama, sosai yayi kyau bana wasa ba, ahankali ya isa gaban mirror yana ɗora kyawawan idanunsa ya kalli kansa acikin madubin. shi kansa yasan cewar shi cikakken kyakkyawan Namiji ne mai aji da kuma ɗaukar hankali. Haka ya tsaya sosai gaban madubin yana kallar kansa, Kafin ahankali ya sauƙe idanunsa ƙasa yana nufar wayarsa me ƙirar Galaxy S50 ya jefa cikin aljihun kayan dake jikinsa, yana sa kai ya fice daga cikin ɗakin.....
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
