👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 👑
✍️Alƙalamin Nusaiba Ibraheem Rimi (Nusy bee)
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Marubuciyar 👇
Matar khalees
Barrister Hibba
Siraɗin uƙuba
Ƙaddararmu ce ta zo a haka
And now; MASARAUTAR KAIZUR
بسم الله الرحمن الرحيم
Littafin MASARAUTAR KAIZUR ƙagaggen labari ne,komai da ke cikin littafin nan ƙirƙira ne,kama daga mutane,labari zuwa gari,ko da wani abu ya yi karo da rayuwar wani a zahiri,to a yi min afuwa,a rashin sani ne🙏
GARGAƊI!!!
Labarin MASARAUTAR KAIZUR mallakin Nusaiba Ibraheem Rimi (Nusy bee)ne,ban amince a canja labari ko a juya min ta wata fuskar ba sai da izinina
Ban amince a karanta min shi a YouTube channel ba sai da izinina
SADAUKARWA;
Na sadaukar da wannan littafin ga shugaba,ƙawa,kuma ƴar uwa Zainab Shehu Abdullahi (Zee kumurya) alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke bright pens 🥰
Da fatan mun yi Sallah lafiya 🥰 Allah ya karɓi ibadunmu, yasa muna daga cikin ƴantattun bayi a wata mai alfarma 🙏
Daga jiya zuwa yau na samu mutane da yawa da suka yi min tuni,(Nusy bee gobe ne fa😁yau ne da😊 I really appreciate it😍na ji daɗi sosai da kulawarku a gare ni,kuma ina matuƙar godiya, Allah ya bar zumunci 🙏
CHAPTER ONE
*TSOKACI*
*DAULAR KAIZUR*
"Ya'aƙub! ya'aƙub ka tashi!! masarauta babu lafiya,muna cikin masifa da bala'i"da sauri wanda aka kira da ya'aƙub ya ɗago yana kallon mai yi masa magana,a kiɗime ya ce"me yake faruwa ne Zayyad?"
"Ba'a ga YARIMA SAHAL ba,ana kyautata zaton sace shi aka yi aka fitar da shi daga masarautar nan,sarki Mu'iz da sarauniya Amna tuntuni sun fito bakin fada,gaba ɗaya kowa hankalinshi a tashe yake"
Shiru Ya'aƙub ya yi yana bin Zayyad da kallo cikin kaɗuwa,an sace Yarima Sahal!magajin masarautar Kaizur,wannan wanne kalar ibtila'i ne ya afka musu haka?don tabbas ya san ba'a ci banza ba,don sarki Mu'iz baya yafiya
Jiki a matuƙar mace Ya'aƙub ya dubi Zayyad ya ce"to ina su Umayr da Urwa da suke kula da shi?"
"Umayr ya tsere,amma an kama Urwa,sai dai yana ta rantsuwa daga shi har Umayr basu da laifi,ba su san yadda hakan ya kasance ba,sarki dai ya ce a wuce da shi da sauran yaranshi a bincike su "Ya'aƙub bai sake magana ba ya miƙe yana gyara zaman tufafinshi,ya nufi hanyar fita daga ɗakin nasu, Zayyad ya biyo shi jiki yana tsuma
A bakin fada ya ga jama'a sun taru,a nutse ya ƙarasa cikin mutane kanshi a ƙasa, Kamar yadda ya san al'adar masarautar,idan har Sarki yana magana ba'a kallonshi
Bayanan Sarki sun firgita mutane matuƙa,sarki Mu'iz ya juya ya koma cikin fadarshi ba tare da ya saurari uzurin kowa ba, gimbiya Amna da ke tare da shi ta rufa masa baya
Cikin saɓulewar jiki kowa ya fara zarewa da ɗaiɗai da ɗaiɗai bisa umarnin babban hadimin Sarki,wanda shima a take ya juya ya bar wajen,mutane suka fara watsewa suna ƙusƙus,kowa yana mamakin dalilin da ya sa aka sace ɗan Sarki Mu'iz, da hanyar da aka bi duk da tsauraran tsaro da ke masarautar
Shima Ya'aƙub wucewa sashen su ya yi zuciyarshi cike da fargaba kamar kowa,da tsananin mamakin wanda ya aikata wannan ɗanyen aikin cikin wannan talatainin daren
💫
Da tsananin gudu dawakansu suke keta manyan dazukan masu cike da ababen tsoro da matsananciyar duhuwa,su uku ne, dukkansu sanye suke da baƙaƙen kaya,hatta fuskarsu rufe take da baƙin fuske,ɗaya daga cikinsu ne yake riƙe da wani ɗan ƙaramin buhu wanda da alamu akwai abu mai ɗan girma a ciki
Sai daf da asuba suka iso masarautar Jasus,na gabansu,wato wanda yake ɗauke da buhun nan ne ya fara jan linzamin dokinshi don tsayawa,hakan ya sa sauran ma suka tsaya
Juyowa ya yi yana kallonsu,cikin dakakkiyar muryarshi irin ta gwarazan mazan fama ya fara magana
"Nan da kowanne lokaci daga yanzu asuba zata iya yi,hakan kuma yana nufin fitowar mutanen cikin garin JASUS don yin Sallah,kuma idan muka shiga da wannan kayan ina da tabbacin asirinmu zai iya tonuwa, kun san dai yadda MASARAUTAR KAIZUR take,to masarautar Jasus sun fi mu
Su bala'i,don haka za mu yar da shi a nan kawai,akwai muggan namun daji, cikin ɗan lokaci ƙalilan za su iya gamawa da shi,amma ya kuka ce?"
Na farkon ya ce"ah!hakan ya yi sosai,babu matsala,mu aiwatar da hakan"babu musu suka jefar da buhun,shugaban yana kallonshi yana murmushi ya ce"to Magaji!
Sai na ce sai haɗuwa ta gaba?"ya kaɗa linzamin dokinshi,sauran ma suka kaɗa nasu,suka canja hanya
BAYAN SHEKARU ASHIRIN
*DAULAR TAYYAR*
Tun daga nesa dakarun da ke tsaron babbar ƙofar shiga alƙaryar Tayyar suke jin kaɗe-kaɗe da bushe bushe,wanda hakan alamu ne na nasarar yaƙin da suka fita zuwa gawurtacciyar daular matsafa,kuma azzalumai wato daular BARUDA,inda Sarkin wannan daula,kuma gagarumin matsafi wato SARKI AKAAL yake mulki
Tsawon shekaru goma sha ɗaya kenan suna ƙoƙarin yaƙar daular ta Baruda,amma hakan ya gagara, sakamakon tsananin ƙarfi da izza irin ta mayaƙa da matsafa a ƙasar,sun addabi manyan garuruwan da suke maƙwabtaka da su
Farin ciki mai yawa ya bayyana a fuskokin dakarun nan,shugabansu,wanda ya kasance mai shela a yayin da mayaƙan suka fita yaƙi,a yayin da jama'ar gari suke dakon jin sautin busa cike da fargaba
A yau dai sautin ya bambanta da wanda aka saba ji a duk lokacin da aka fita zuwa gagarumin yaƙi irin wannan, musamman da daular Baruda,a maimakon sautin kukan mikiya da ya saba tashi wanda yake nuni da ba'a yi nasara ba,yau sautin sarewa, wanda yake bayar da tabbacin nasara daga wannan gagarumin yaƙi shine ya tashi
Cikin ɗan lokaci ƙanƙani garin ya kaure da sowa da farin ciki, kaɗe-kaɗe da bushe,tuni mata suka fara ɗora girke -girke da harhaɗa ababen sha na alfarma,hatta yara ƙanana cike suke da farin ciki
Cikin lokaci ƙalilan mayaƙan da suka dawo daga yaƙin suka ƙaraso,an samu shahidai mutum ashirin da bakwai a cikin mayaƙa dubu uku da suka fita,sannan an samu ribar yaƙi har mutum hamsin da uku,ciki har da gawurtaccen mayaƙi,kuma matsafin nan wato KAZUZI
Sanannen abu ne cewa duk wanda ya yi karo da shi sai dai ya amsa sunan gawa, saboda tsananin ƙarfi da tsafi da yake da shi
Kazuzi shi kaɗai ya tarwatsa runduna guda da suka tunkari Baruda da yaƙi a lokaci ɗaya,a kowanne lokaci kazuzi a shirye yake don yaƙi,duk girman runduna da ƙarfin mayaƙa ba sa ba shi tsoro,an taɓa ƙarar da rundunar Baruda,amma shi ɗaya ya yi nasarar yaƙin ya gama da rundunar abokan hamayya ya gurfanar da sarkinsu a gaban sarki Akaal
Kai tsaye aka gabato da dakarun yaƙi guda hamsin da biyu da aka kama waɗanda aka ɗaure su da wata doguwar igiya ɗaya a bayan ɗaya, jama'ar gari sai ihun murna suke yi,kiɗa da busar da ake yi ta ƙaru,karo na farko kenan a tarihi da aka taɓa cin nasara akan daular Baruda a tsawon ƙarnin, kasancewarta daula mai tsananin ƙarfin jarumai da ƙarfin tsafi
Kawunansu a ƙasa suke wucewa, mutanen gari da suka jeru suna kallonsu kowa da abin da yake faɗa cikin farin ciki, dakarun da suka shigar da su suka rufa musu baya,kai tsaye aka nufi ƙofar fadar masarautar Tayaar
Daga nan keken doki na alfarma shigo,wanda yake ɗauke da mutane ashirin da bakwai da suka yi shahada a wannan yaƙin,kalamai na nuna tsantsar alhini suka fara tashi daga bakunan mutane,wasu kuma suna ƙarfafa gwiwa da kasancewar sun yi gagarumar nasarar da ba su taɓa yi ba a kowanne yaƙi, ballantana yaƙi a Daular Baruda
Ƙaton toron giwar da ya fara shigowa cikin ƙasaita ne ya katse cecekucen mutane,wajen ya yi tsit tamkar ruwa ya cinye ilahirin dubban jama'ar da ke bakin fadar
A saman toron giwar an ɗaure wani madaidaicin keji,wanda ake iya ganin mutumin da yake cikin kejin,amma ba'a iya ganin fuskarshi, sakamakon dogon gashin shi da ya sauka har kafaɗarshi,ya zubo ta gaban kanshi ya rufe fuskarshi, kasancewar ya sunkuyar da kanshi, hannayenshi da ƙafafunshi ɗaure suke da wata ƙatuwar sarƙa, irin wadda aka yi amfani da ita aka ɗaure kejin da yake ciki
Babu wanda ya ƙara ƙwaƙwƙwaran motsi sai da toron giwar nan ya shige cikin daular Tayaar,daga nan mutane suka fara watsewa ɗaya bayan ɗaya,da yawansu a razane suke duk da tarin nasarar da suka yi, musamman waɗanda suka yi karo da shi suka san wanene ainihin KAZUZI
Daga nan kuma kallo ya koma sama, maganganu suka rinƙa tashi na mamakin yadda kazuzi ya yarda ya shigo hannu, inda wasu suke ganin kawai nasara ce daga Allah,wasu kuma suke ganin lamɓo kawai ya yi, hakan wata dabarar yaƙi ce don ya cimma nasara akan abokan gaba, saboda sanannen abu ne a wajen duk wanda ya san wanene kazuzi,baya taɓa yarda a yi nasara akan shi
Cikin ɗan ƙankanin lokaci mai shela ya fara yekuwar sanar da al'ummar garin kiran da Sarki yake yiwa ilahirin al'ummar garin bakin fada,don a sallaci shahidan da suka riga mu gidan gaskiya a yaƙin nan,sannan kuma zai yi muhimmiyar sanarwa,da haka kowa ya wuce gida don shirya amsa kiran sarki
*DAULAR KAIZUR*
Kamar yadda aka saba Rabee'a ne ya ja sallar azahar da aka yi a farkon mukhtarinta,kamar yadda sarki Mu'iz ya ba da umarni,yau gaba ɗaya masarautar a firgice take saboda yadda yanayin da sarki Mu'iz ya tashi da shi, kaɗan daga aikinshi ne ya huce ta hanyar raba wani da ranshi
Kai tsaye turakarshi ya wuce bayan an idar da sallar azahar,kallo ɗaya za'a yi masa a gano tsananin tashin hankalin da yake ciki saboda yadda fuskarshi ta kaɗa ta yi jawur
Da sallama sarauniya Amna ta shiga turakar, ba tare da ya waigo ya kalle ta ba ya ce"da wani abu ne sarauniya?"
Cikin girmamawa ta ce"dama batun abinci ne ya shugabana!
An gama haɗawa,a kawo ne?"ba tare da ya kalle ta ba ya ce "ba yanzu ba,za ki iya tafiya"ta sake rissinawa ta ce"ka huta lafiya ya shugaba na"ta miƙe don ficewa daga ɗakin
"Ki cewa yarima Zaffar ya shigo,ina son magana da shi"ta tsinkayi muryarshi
Sake rissinawa ta yi ta ce"an gama ya shugaba na"sannan ta nufi ficewa daga cikin ƙasaitacciyar turakar
A ƙaton katafaren masaukin baƙin da ke cikin gidan ta tarar da Yarima Zaffar da Yarima Jamal a zaune suna jiran fitowarta,ita kam zuwa yanzu ta daina mamakin duk abin da sarki Mu'iz ya yi, yadda yake ganewa a duk lokacin da Yarima Zaffar yake kusa da shi saboda tsananin ƙauna da soyayyar junansu
Kallonshi ta yi tana murmushi,ya rissina tana faɗin "Barka da fitowa ya shugaba ta!"
"Zaffar!
Yanzu mai martaba kuwa ya ce na yi masa magana da kai,ashe dai kana kusa,wannan ƙauna tsakanin ka da mai martaba dabam take"
Murmushi yarima Zaffar ya yi, cikin girmamawa ya sake kallonta ya ce"ranki ya daɗe ai tasirin jini ne kawai, kin san an ce jini ya fi ruwa kauri"
Sarauniya Amna ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce"haka ne!
To yanzu dai ka amsa kira, don kamar ma baya cikin yanayi mai daɗi"
"An gama ranki ya daɗe,ki huta lafiya"ya faɗa da girmamawa kamar koda yaushe,sannan ya miƙe ya nufi turakar Sarki Mu'iz
Yarima Jamal ya bi shi da kallo cikin takaici,a yayin da sarauniya Amna ta yi tafiyarta ta bar shi a wajen,ya miƙe tsaye cikin ɓacin rai,a ranshi yana jin dole ma ya karɓi kujerar daular kaizur bayan wucewar Sarki Mu'iz zuwa kushewa duk da kasancewar Yarima Zaffar ya girme shi,da wannan tunanin ya bar wajen zuciyarshi cike da baƙin ciki,da muradai kala-kala
Sarki Mu'iz ya yi masa iso daga inda yake kishingiɗe a kwance akan ƙawatacciyar kilishin da ke shimfiɗe a tsakar ɗakin, Yarima Zaffar ya ƙaraso ya rissina a gabanshi yana faɗin"Barka da wannan lokaci ya shugaba na"
Kallonshi sarki Mu'iz ya yi, lokaci guda ya miƙe tsaye,ya dubi yarima Zaffar ya ce"mu je Yarima!"ba tare da musu ba Yarima Zaffar ya miƙe,kai tsaye suka nufi wata kusurwa a cikin turakar
Kamar ba a cikin dakin sarautar ba,wajen da duhu sosai,sarki Mu'iz ya saka hannu ya taɓa wani abu da shi kanshi Yarima Zaffar ɗin bai san da shi ba,take wata ƙofar sirri ta buɗe,sai ga wani madaidaicin ɗaki ya bayyana
Ba yau Yarima Zaffar ya saba ganin ɗakin ba,shi yasa ya zama sanannen abu a wajenshi cewa duk lokacin da sarki Mu'iz yake cikin wani yanayi mara daɗi to yana da alaƙa da wannan ɗakin
Cikin rauni da sarewa sarki Mu'iz ya dubi ƙanin nashi Yarima Zaffar ya ce "Zaffar!
Ban san tsawon wanne lokaci zan ɗauka ina kuka da fargabar inda ɗana SAHAL yake ba
Kai shaida ne,tsawon shekaru ashirin kenan da ɓatan shi,amma ban ga wani canji daga taurarin shi ba,sai dai kewarshi da fargabar halin da kujerar kaizur zata shiga idan na bar duniya
A kullum ina ganin taurarin Sahal da haske tamkar walƙiya,amma a yau na ga abin da ya kaɗa hanji na"
Yarima Zaffar ya kalle shi zuciyarshi cike da fargaba, saboda wannan bayanin da sarki Mu'iz ya ɗauko akwai dalili, cikin fargaba ya ce"menene yake faruwa da Yarima ya shugaba na?"
*To jama'a ya kuka ji tafiyar MASARAUTAR KAIZUR?ba mu saba irin wannan tafiyar ba ko? tafiya ta musamman kenan,ku biyo ni kawai!!!*
#Nusy_bee
08125952284
