👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 2
Cikin jimami sarki Mu'iz ya kaɗa kanshi, lokaci guda kuma ya buɗe wani ɗan ƙaramin abu mai kama da akwati,take wasu taurari guda uku suka bayyana ƴan ƙanana,sai dai sun yi jawur da su
Yarima Zaffar ya ɗan bi taurarin da kallo cikin fargaba,idan ya fahimta hakan na nuni da cewa Yarima Sahal yana cikin tsaka mai wuya kenan,to a wanne hali yake ciki?kuma a ina?kuma me ya same shi?
A taƙaice ma dai a ina ya rayu tsawon waɗannan shekarun amma suka kasa gano shi duk irin yawon da suka yi?
Kallon sarki Mu'iz ya yi wanda ya damuwa ta gama bayyanar masa a fuska, cikin sanyin murya ya ce"to yanzu shugaba na menene abin yi?
Ya zamu yi?"sarki Mu'iz ya girgiza kai ya ce"nima bana ce ba,bana son sarauniya ta san da wannan batun,don ban san yadda zata yi ba,kullum ina gaya mata cewa ɗanta lafiya yake,amma a wannan karon ban san yadda zata ɗauki wannan maganar ba"
Kai tsaye yarima Zaffar ya ce"kar ka gaya mata ya shugaba na,ina fatan in sha Allahu watan watarana Yarima zai dawo cikin masarauta,har ma ya karɓi ragamar da take jiranshi tsawon shekaru"
Sarki Mu'iz ya dafa kafaɗar ƙanin nashi, cikin raunin murya ya ce"ina fata fatan haka ɗan'uwa"
Jiki a saɓule suka fito daga cikin ɗakin,sarki Mu'iz ya sake kwanciya a turakar tashi,yayin da Yarima Zaffar ya fice daga turakar cike da jimamin wannan abu
*DAULAR TAYAAR*
lokaci ƙalilan baya,ƙasa da sa'a guda da aka sallaci gawarwakin waɗanda suka yi shahada a yaƙin da suka fita da daular Baruda,an raka su zuwa gidajen su na gaskiya cikin aminci, zuciyoyin masoya da yan'uwa cike da alhini da jimami,daga nan an dawo fada,don sauraren kiran sarki da jawabin da zai gabatar
Ba'a ɗauki lokaci ba sarki IYAAD ya bayyana cikin shigar ta alfarma,fadawanshi da suke tare da shi suka nunawa mutane wajen zama,mutane suka zauna,fada ta yi shiru suna jiran abin da sarki Iyaad zai faɗa
Tsawon wasu daƙiƙu ya ɗan yi shiru, kafin ya yi gyaran murya cike da salon izzar mulki,ya yi sallama cikin wani amo mai jan hankali,wanda yake tattare da mazantaka
Gana ɗaya fadar aka amsa,cikin nutsuwa da kamala ya fara bayani
"To alhamdulillahi!
Bayan tsawon lokaci Allah mai kowa mai komai ya cika mana burin mu
Kamar yadda muka sani Daular Baruda daula ce da ta ɗauki tsawon lokaci tana rainon azzaluman mayaƙa, waɗanda suke tarwatsa dukkan wani gari da suka gani da aminci
Daular Baruda bata tsaya iyaka nan ba,tana yaƙi da Muslunci da musulmai, kusan na ce daula ce da aka yi amfani da zalunci da ƙarfin tsafi aka gina ta don a rusa musulunci
To amma da yake Allah shine mai iko a bisa komai a yau ya ba mu iko mun durƙusa daular azzalumai ta Baruda"take ilahirin fadar ta ruɗe da kabbara da muryoyi mabanbanta,wasu har da kukan farin ciki
Sarki Iyaad ya cigaba da bayani "bayan mun yi nasarar lalata wannan azzalumar daula,mun yi nasarar hallaka sarkinsu,da sarkin matsafan wannan daula,da duk wani badakare da ake amfani da shi ake cin nasara akan musulunci "take aka sake ruɗewa da kabbara,da ƙananun ƴan maganganu ƙasa-ƙasa da ke cike da farin cikin faɗar ra'ayi,sai da aka nutsa sarki Iyaad ya ɗora da bayaninshi
"Nasararmu bata tsaya anan ba,har sai da muka kama babban badakaren da ya mayar da yaƙi tamkar wasa,sadaukin da idan bai ɗauki rai ba baya jin daɗi,jarumin da kisa tamkar maƙon ruwa ne a wajenshi,wanda duk girman runduna bata ba shi tsoro,duk ƙarfin runduna baya razana shi, duk shiri da tumbatsar runduna a ɗan ƙankanin lokaci zai iya tarwatsa shi komai yawanshi,jarumin da yaƙi da ɗaukar rai tamkar wasan yara ne a wajenshi,wato Sadauki KAZUZI!"
Ɗif fadar ta yi, tamkar babu wani mai numfashi a cikinta ba don komai ba sai don ambaton sunan kazuzi da sarki Iyaad ya yi, sarki Iyaad bai damu ba ya cigaba da jawabi
"Don haka muna cike da murna da farin ciki na wannan Gagarumar nasarar, wadda muka tabbatar da cewa ba wayon mu ko ƙarfin mu bane ya bamu,sai iko da buwayar Ubangijin talikai,muna mai miƙa godiya a gare shi"
Gaba ɗaya mutanen fadar suka ruɗe da kabbara,har da waɗanda suka firgita da wanzuwar Kazuzi a cikin Tayaar,sarki Iyaad bai damu ba,ya cigaba da jawabin farin ciki da suke ciki,a ƙarshe ya ƙara da faɗin"muna yi wa iyalan shahidanmu gaisuwa, musamman ma jarumi WALEED,wanda shine ya sauƙaƙa mana hanyar da muka samu nasara akan azzalumi Kazuzi,duk da cewar da kuskure a hakan
A ƙarshe ina mai farin cikin sanar da ku cewa za'a yi babbar liyafa ta wannan nasarar da muka yi a bakin fada,zuwa gobe da hantsi,na sallami kowa"
Haka taron fada ya tashi,mafi akasarin mutane suna cikin matuƙar farin ciki,yayin da wasu daga cikinsu suke cikin fargaba saboda wanzuwar Kazuzi a cikin Tayaar,wanda sanannen abu ne a wajen jama'ar garin,ba ma su ba,har da maƙwabtansu na yadda yake da haɗari
💫✨
Sarki Iyaad ya dubi wazirinsa da yake zaune kusa da shi,ya ce"waziri!
Allah ya yi,mun yi nasara a yaƙin nan da daular Baruda,har ma mun kawar da damuwar da ta addabi gaba ɗayanmu, wato Kazuzi,yanzu ya kuke ganin za'a yi da shi?"
Waziri ya ɗago kanshi a nutse, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na babu abin da ya rage sai a sake laƙana masa kalmar shahada,idan bai karɓa ba kawai a kashe shi kamar yadda aka yi wa sauran yan'uwan shi"
Sarki Iyaad ya dubi sauran fadawan ya ce"to kun ji,ki me kuke gani?"Sarkin yaƙi ya girgiza kai ya ce"wannan ba mafita ba ce ya shugaba na
Abu ne sananne a wajenmu cewa Kazuzi ba zai amshi addini a haka ba,kuma muna buƙatar mutane irin Kazuzi a wannan garin,ni da nake cewa mai zai hana mu ja shi a jiki,mu fahimtar da shi musulunci, idan ya so ba ma sai an yi masa dole ba zai shiga da kanshi?"
Sarki ya jinjina kai ya sake mayar da dubanshi ga waziri, kafin ya kai ga magana sarkin fada ya ɗaga hannu,sarki Iyaad ya ba shi damar magana,Sarkin fada ya gyara zama yana duban Sarki Iyaad, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na,da alamu su Sarkin yaƙi sun manta wanene Kazuzi!
Sanannen abu ne tabbas ba zai karɓi musulunci ba ko me za'a yi masa,amma kuma ina ganin da kuskure a jan shi a jiki da za'a yi, saboda mu shaida ne,babu abin da jinin Baruda suka tsana kamar musulunci,duk wani wanda ya sha ruwan daular Baruda zai tashi da tsanar Musulmai da burin son ganin bayanmu,mai zai hana a yanke masa hukuncin shi kawai,kar ya yi amfani da yardar da muka yi masa ya cutar da mu?"
Girgiza kai sarkin yaƙi ya yi, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na,a dai duba magana ta,ban hana a sakawa kazuzi idanu ba,amma ya kamata a ba shi wata dama, tunda har muka iya kamo shi,abin da babu wata daula da ta taɓa samun wannan kwatankwacin nasarar,idan har ya gwada wata halayya muka ji ba mu yarda ba za mu ɗauki mataki akanshi kawai,amma a matsayin mu na musulmai,sannan manyan babbar masarauta bai kamata a ce mun razana saboda wani bawa da Allah ya ba mu nasara akan shi ba,amma ya kuka ce?"
Shiru fadar ta ɗauka,kowa yana nazari,zuwa can waziri ya katse shirun da cewa"to shikenan,a gwada shawarar taku,amma ni ina ganin a saka masa idanu sosai,sannan kuma a tsare shi,a yi duk mai yiwuwa don ganin an karya ƙarfinshi,yadda ba zai iya wani tasiri ba"
Sarki Iyaad ya ce"shiyasa muka bayar da umarnin a killace shi, kafin nan sai da muka tabbatar mun raba shi da duk kayan tsafi da surkullenshi"
Waziri ya sake rissinawa ya ce"ya shugaba na,an ɗauki matakin da ya dace, ragowar kuma sai mu bar wa Allah "
Sarki Iyaad ya ce"hakan ya yi,muna fatan yadda Allah ya ba mu ikon yin wannan jihadin muka yi nasara akan waɗannan azzalumai, Allah ya ba mu iko da nasara akan wannan babban shaiɗanin"
Fadawa suka amsa da "Ameen!"daga nan sarki ya rufe taro da addu'a,faɗa ta watse
💫✨
A hankali toron giwar yake zaunawa akan ƙafafunshi bisa umarnin dakarun da suke umartarshi,shugabansu ya kama ƙatuwar sarƙar da aka ɗaure kejin ya fara ƙoƙarin kwancewa cikin dakiya,sauran dakarun suka fara ƙoƙarin taya shi
Bayan gama warware ƙatuwar sarƙar tsayawa suka yi cirko-cirko suna kallon juna a ɗan firgice,duk jarumta da taurin zuciyar badakare ya san wanene Kazuzi, yanzu haka ma kallonshi suke yi, wanda shi duk abin da ake yi ko ɗago kai bai yi ba ballantana ya kalli wani,har yanzu kanshi a ƙasa yake,tunda aka shigo da shi cikin birnin Tayaar har yanzu babu wanda ya ga fuskarshi ballantana ya shaida a wanne hali yake ciki
Wani badakare ne ya yi ƙarfin halin fara ƙoƙarin saukar da kejin,sauran dakarun ma suka saka masa hannu,suna saukewa kuma shugaban nasu ya yi ƙarfin halin buɗe kejin
Yana buɗewa suka ja baya a ɗan tsorace,kafin ɗaya daga cikinsu ya yi ƙarfin halin matsowa yana kallon Kazuzi,da sai yanzu suka kula ashe duk abin da yake faruwa ma idanunshi a lumshe yake,babban dakaren ya saka hannu da nufin fito da shi, sauran dakarun ma suka saka hannu don fito da Kazuzi,amma duk ƙoƙarin su tamkar suna yunƙurin matsar da ƙaton dutse,ko motsi baya yi
Shiru suka yi,suka tsaya cirko-cirko suna kallon juna,kafin babban badakaren ya yi ta maza ya dubi Kazuzi ya ce
"Sadauki Kazuzi!
Kafin yau kai ɗin jarumi ne, mai gata da dama,mai sharafinshi a wannan nahiya,wanda ya gagari kowa,amma a yau kai ba komai bane face bawa,don haka sarki Iyaad yana umartarka da ka fito daga kejin nan don a kai ka inda aka warewa bayi irinka"
Maganar babban badakaren ta razana ƙananan,don da alamu sun manta wanene Kazuzi,sai dai abin da ya yi tsananin ba su mamaki bai wuce ganin Kazuzi ya yunƙura ba,cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ya fito daga cikin kejin ya tsaya a gabansu,kuma har zuwa lokacin idanunshi a rufe suke
Da farko bin shi suka yi da kallo cikin tsananin mamaki da kaɗuwa,amma daga baya babban badakaren ya dake ya kama shi,kai tsaye suka wuce ɗakin da aka tanada don Kazuzi
Ba su kwance masa ko sarƙa ɗaya ba,daga ta hannu har zuwa ta ƙafa,suka tura shi zuwa ɗakin mai tsananin duhu,suka mayar da ƙofar da ta kasance ta wani nau'in ƙarfe mai nauyi suka rufe ta ruf
Kai tsaye wajen Sarkin yaƙi suka nufa, cikin girmamawa suka sanar da shi cewa sun kai Kazuzi zuwa ɗakin da aka tanada don shi,sarkin yaƙi Ra'uf ya kalle su yana murmushi ya ce"sannunku da ƙoƙari,yanzu sai a kai masa abinci"suka rissina, babban badakare ya ce"an gama ya shugaba na"
DAULAR KAIZUR
A hankali yake tafiya yana bin doguwar hanyar, dakaru uku da ke tsaron lafiyarshi suna take masa baya,yana zuwa daidai inda suke tsayawa suka tsaya ba tare da an umarce su ba, gami da juya baya,sarki Mu'iz ya cigaba da tafiya zuwa cikin duhuwar bayan ya ɗauki karan a ci bal-bal guda ɗaya da suke bakin ƙofar
Ƴar doguwar tafiya ya yi a cikin kogon kafin ya ƙarasa inda yake muradin zuwa, murmushi ya yi yana kallon dattijuwar matar da take durƙushe a kan gwiwowinta, ɗaure take da sarƙa mai matuƙar nauyi,tana sauke numfashi a wahale,kayan jikinta zuwa gashin kanta a hargitse
"MUNAYA!"ya ambata cikin wani irin amo mara daɗin ji, ɗagowa matar ta yi da kanta, cikin ƙarfin hali ta furta "Barka da zuwa ya shugaba na!"
Bai amsa ba,sai zama da ya yi a wajen da ya saba zama yana kallonta cike da tsana,bata damu ba,ta saba ganin irin wannan kallon daga wajenshi,har zuwa mutanen garin da suke kallonta a duk lokacin da aka fitar da ita daga inda take a kulle
"Munaya!
Tsawon shekaru ashirin kenan kina azabtar da zuciyarmu,akan abin da kika sani ba naki bane tun kafin wanzuwar shi a duniya, menene dalilin da ya sa ba za ki daina azabtar da zuciyoyinmu haka ba? menene dalilin da ya sa ba za ki huta ba mu ma mu huta?
Ki yiwa kanki adalci ki yi mana,ki bayyana inda kika kai ajiyar nan,daga nan za mu sallame ki kema ki huta"
A hankali Munaya ta ɗago kanta tana sauke numfashi, ba tare da ta kalle shi ba, cikin sanyin murya ta furta "a yi min afuwa ya shugaba na!
Amma abin da na saba faɗa dai shi zan maimaita,bani da masaniyar inda yake"
Shiru sarki Mu'iz ya yi yana kallonta zuciyarshi tana tafasa,da sauti irin na fushi ya ce"amma kin yarda da cewa da saka hannunki a ɓatan kadara mafi daraja a kaizur?"
Kai tsaye ta amsa da faɗin"tabbas haka ne ranka ya daɗe,ni na fito da shi,amma daga nan ban san komai ba,kuma ba zan iya komai don dawowarshi ba"
#Nusy_bee
08125952284
