https://whatsapp.com/channel/0029Vb4VdFSDjiOgtgu6uz3T
ABU A DUHU
ADABI WRITER’S ASSOCIATION
Page 3
Gaba daya motocin ne su ka tashi lokaci guda, bayan ta su ke bi a hankali, ita ko Unaisa ko waige bata yi gudun ta kawai take tamkar wadda kura ya biyo ta.
Layin su na da tsawo sosai, ga hanyar babu kyau dan haka sannu a hankali motar ke tafiya yayin da su ke iya hangen yadda yariyar ke falla gudu a gaban su.
Magaji ko ajiyan zuciya ya ke saukewa, domin ya gamsu da gudun da yariyar ke yi a yau lallai ta ji a jikinta ya kuma fanshe walar da taita bashi, kallon mugunta ya ke ta binta da shi, shikuwa daya matashin ban da dariya babu abun da
ya ke har yanxun, yayin da Modibo ya daure fuska idon sa akanta, zuwa can ya yi wa driver Umarni daya tsaya domin wannan lokacin motar su ce a gaba.
Dan tsayawa su ka yi kadan yariyar ta kara nisa sannan yace "Mu je."
Magaji ne ya bi Moddibo da kallo, cikin nutsuwar sa ya ga yana bin yariyar da kallo dan haka shima ya juya ya kalli yariyar da ta yi nisa da su sai arta gudu take, Modibo ya sake kallo yayin da ya ga sai shafa gemon sa yake tare da shafo kansa, sunkuyar da kansa ya yi yai murmushi sannan ya dago ya sake kallon Modibo yace, " Modibo!" Lumshe ido ya yi sannan ya juyo ya kalle shi. "Na ce yariyar nan kodai mahaukaciya ce?" Lumshe ido ya sake yi akaro na biyu tare da fadi ahankali, "Lafiyarta lau" Ganin tasha kwana suka kara gudun motar, suna saka hancin motar akwanan sukaga ta shige wani gida ta rufo kofar.
****
Matsanancin hakin da take yasa Dada rikecewa, kara shigewa cikin jikinta take tamkar zata shige ciki tare da haki babu kaukautawa.
"Unaisa mene ne?, Gayamin me ya ke faruwa?"
Shid'ewa ta yi gaba daya, yayin da Dada ta kara rudewa, girgizata ta ke tare da kiran sunanta, ganin babu alamar numfashi ya sa ta zame ta, ruwa ta dauko a guje ta dawo ta shafa mata a fuska sau uku sannan ta ji ta ja dogon numfashi, zama ta yi sosai ta kara daurata jikinta tare da rungume ta sosai, tsayon lokaci tana rungume a jikin ta, ajiyan zuciya kawai take saukewa, sai da Dada ta tabbatar ta samu nutsuwa sannan tace, "Mene ne ya ke faruwa Unaisa, gayamin mene nr ya firgita ki haka?"
Hawaye ta share ta na manne jikin Dada, a hankali ta ce, "Wannan bakin na Malam Baba ne su ka tare min kofar shiga gida"
Jim Dada tayi sannan ta ce, "Akan wani dalili?"
"Bansani ba Dada, har biyo ni su ka yi da mota."
Shiru Dada ta sake yi, sannan ta mike ta leka kofar gidan, ba ta jima ba ta dawo tana fadin, "Kin dai tsorata ne Unaisa, amman babu wadda ya biyo ki, mayafinta ta dauka ta sake fita, tsawon lokaci sannan ta dawo tana cewa, "Na je har layin naku babu kowa inajin sun wuce." Ajiyan zuciya Unaisa ta yi mekyau sannan ta dauki nikaf dinta ta daura, ita ko Dada gaban murho ta isa ta na kokarin daura girkin dare, yayin da hakan yayi daidai da shigowan wanni Dattijo, ganin Unaisa ya sashi yaja ya tsaya tunda nesa yana fadin, "Tun da kin a jeta annan ni bari na koma"
"A'a Malam shigo mana, firgita ta yi ne yau, abin da ban taba ganin ta yi ba, shiyasa hankalina ya tashi har ka ganta anan."
"Eh shiyasa zan baku waje ai, idan ta firgice dake lokacin zaki gane abun da ake gaya miki, na gaya miki batun yau ba bana son ganin yariyar nan a cikin gidana, amman mu je zuwa duk wadda ya bari sauran tuwo ya kona shi shiya so."
"Malam karka min baki, hakuri zaka yi da yariyar nan , abin duk da ka ga ya koro bere ya fada wuta to ya fi wutar zafi, ka tausayawa yariyar nan Malam, tana tsananin son kulawa."
"Tun da kina tausaya mata kin dauke mana, ban da batan basira ta yaya za'a ce yariyar da kowa ya ki ta ke daya ki makale mata, duk dangi kowa ya ki ta saboda bakin naci kina nan da ita."
"Amanar Innawuro ce Unaisa a gareni Malam, ko duk duniya za su ki Unaisa ni bazan ki ta ba, Unaisa dolena ce." Shikenan Allah ya baki sa'a amma ni bana son na dawo na same ta agidan nan, komai na iya faruwa idan na dawo na same ta" A fusace ya fita, Dada kuwa ci gaba ta yi da aikinta ranta bace.
Mikewa Unaisa ta yi ta isa gaban Dada, cikin muryar ta kasa kasa ta ce, "Dada zan tafi." Batare da Dada ta juyo ba tace, "A nan za ki kwana." Sunkuyar da kai ta yi kasa tare da fadin, "Ba zan iya kwana ako ina ba idan ba'a dakin Innawuro ba Dada." Da sauri Dada ta kalli Unaisa sannan tace, "Ba in da za ki, idan su ka dawo cikin dare suka miki wani abin fa?"
"Ba za su dawo ba, na kula duk sati suke xuwa tun da sun tafi nasan ba za su dawo ba sai wani alhamis din." Jimm Dada ta yi sannan ta ce, "Ina zuwa toh bari na xo na raka ki." Bayan Dada ta gama daura girkin har gida ta raka Unaisa, acikin ranta take tsananin tausayawa rayuwar ta, fitowa ta yi tana tafiya tana hawaye, bakin cikin yadda mutane suke gudun Unaisa ko shege ba'a masa haka, Unaisa kuwa yau kuka ta ci ta na nade akan gadon Innawuro.
Tun da ga wannan ranar duk alhamis gidan Dada take wuni, Dada ke lekowa har sai ta taga wucewan motocin sannan ta koma gida.
Islamiya kawai ke fitar da ita bata zuwa ko Ina sai gidan Dada wadda daman duk alhamis ta na zuwa, sai dai yanzun zama take har yamma sannan ta koma gida.
Akwana a tashi a sarar mai rai, yau sati hudu kenan ba ta sa motocin a idonta ba, dan haka hankalinta ya kwanta, a yanzun ba ta jin fargaba ko tsoro, sai dai acan cikin zuciyar ta lokaci bayan lokaci ta na tuna maza biyu data hanga zaune bayan motar masu kama daya, ranar juma'a kuwa ko kofar gida ba ta zuwa tana cikin gida arufe.
Yau asabar tun misalin goma tafito cikin Shirin makaranta, fararen kaya ne ajikinta tass har hijjabin, sai bakar safa da ke kafarta tare da bakin nikabi, sosai kayan su ka karbi jikin ta, tafiya tafara sannu a hankali harta fita daga cikin unguwar ta isa titi, adaidaita sahur ta tare tahau tare da fada masa sunan makarantar su, bakin makarantar aka sauke ta yayin da ta ciro kudinsa ta mika masa ta nufi cikin makaran tar, da Sallama ta shiga ajin su sannan ta isa kujerar ta ta zauna, kasancewar mutum daya ke zama, saidai har aka tashi batai magana da kowa ba baya ga daukan karatu.
Misalin hudu ta iso gida cikin saurinta nufi kofar tare da lalibo mabudin ta cikin jakar makarantar ta, jimm ta yi jin karan karfe bayan ta, tamkar dai takowa ake da karfe, dan haka gaban ta yai wani irin mugun bugawa, nan da nan jikinta ya fara rawa yayin da ta kasa dago mabudin, banda rawan jiki ba abun da ta ke.
Hannu tasa ta rike hannun kofar, jin da ta yi kafar ta na son kayar da ita, a hankali ta ke jin karan na dad'a matsowa gare ta, har ta zo ta fara hango kafar karfen dake tahowa tare da wata farar kafa cikin kyakyawan takalmi, daya kafar kuwa daure ta ke, anan take ta tuna ta taba ganin wannan kafar, tahowa ya yi har ya ya isa jikin kofar gidan ya jingina bayan sa yana kare mata kallo.
Bata iya dagowa ta kalli fuskarsa ba kamar wancen karon, sunkuyar da kanta tayi kasa tare da rawan jiki abayya ne. Tsayon lokaci su ka dauka haka zuwa can yayi gyaran murya cikin wata irin murya ya ce, "Kowa ya hana ka dakin kwana da safe saiya ganka Idan har kwanan ka na ga gaba" Dan murmushi ya yi kadan sannan ya sake cewa "Ya ya sunan ki?"
Kara sunkuyar dakanta ta yi tsayon lokaci suna a haka.
Lumshe idonsa ya yi sannan ya bude a kan kyawawan gashin idonta yace, "Ina jin ki Antina ki min magana mana" Karashe maganar ya yi da a jiyan zuciya me karfi, sannan ya sake cewa, "Gudu da waiwaye fa shike kawo mugun zato yanmata" Yadda ya ke magana ya sata kara lumshe idonta, har cikin ranta ta ji zakin muryan tasa, sai dai babu wata kalma da zata iya furtawa.
Muryar sa ta sake ji cike da kasaita yana fadin, " "Meyasa ba za ki min magana ba? Gashi ni ina tsanin son in yi magana da ke." Lumshe ido ta sake yi yayin da ya zubawa gashin idonta kallo tsayon lokaci sannan yace, "Ke kadaice a gidan?" Wannan karon ma babu amsa, wani irin kallon ya ke mata wadda kusan shi kadai yasan ma'anar sa sannan yace, "To ba komai, kowa yaki tsotse hannun be ji dadin miya ba ne" Dago ya yi daga cikin kofar sannan ya gyra sandar sa ya taka gefe hankali.
Tsaye yayi a gefe yana kallonta yayin da Magaji ya ke bayan su yana jin duk yadda suka yi, ganin ya tashi a kofar gidan ta yi kokarin dawo da nutsuwar ta, sannan ta lalubi mabudi ta bude gidan ta shige.
Bayanta ya bi da kallo kafin ya ji tasawa gidan sakata, lumshe idonsa ya yi sannan ya kara kallon kofar gidan, gidane na marasa karfi amman gyare ya ke tsaf, yaji siminti tare da lafiyayyen kofa, "Modibo muje yamma nayi" Magaji ya yi maganar ya na kallon fuskar Moddibo, cikin sauri ya fara takawa yayin da Magaji yai saurin rikeshi "Modibo ka manta kafarka babu lafiya ko?" Tafiya ya ci gaba da yi yayin da Magaji ke binsa abaya har suka isa in da motarsu take, da taimakon Magaji ya shiga motar sannan shima ya zaga ya shiga wadda ke zaune mazaunin driver ne ya ce, "Kun rutsata ko?"
Magaji ne ya bashi amsa, "Ina fa, gata dai a tsaye amman ba zata yi magana ba saboda rashin da'a ba ta amsa kowacce irin magana koda kuwa sallama ce Muftahu, sai dai kaga tana karkada kwayar idon ta me kama dana mujiya"Batare da Modibo ya kallesu ba ya ce, "Wacce irin magana ce kake yi? Ga dukkan alama yariyar kurma ce, tana ji amman ba ta iya mayarwa." Kasa da murya Magaji ya yi yana dan murmushi sannan yace, "Kada ka yi tsammanin alheri, a inda baka ga haske ba."
Cikin sauri Moddibbo ya runtse ido tsawon lokacin sannan ya bude ahankali, cikin muryarsa me dadin saurare ya ce, "Idon da ya ga sarki baya tsoron galadima Magaji, lallai Ina son nasan wasu abubuwa game da ita."
Muftahu ne yace, "Ta yaya zaka san wani abu game da ita alhalin ta na kurma ko bebiya?"
Modibon ya sake lumshe ido abkaro na biyu sannan ya ce, "Wannan ba matsalar ku bace." Ba su sake magaanr ba sai dai dukkan su ukun kowa da abun da ya ke sakawa cikin ransa.
*****
Unaisa kuwa tsaye ta yi jikin kofar har ta tabbatar da tafiyan su, ajiyan zuciya ta sauke sannan tai saurin shiga cikin gidan, cikin gudu gudu ta canza kaya sannan ta sake fitowa akaro na biyu, wannan karon gidan Dada ta nufa tana ta tafe tana waiwayen bayan ta.
Kamar da ga sama Dada ta ganta, iya sanin ta Unaisa ba ta zuwa wannan ranar dan haka ta tabbatar lallai akwai wani muhimmin abun da ya kawo ta, cikin sauri ta taho gareta ganin in da take waiwayen bayanta ya sata kallon kofar sannan ta juyo ta kalli Unaisa ta ce, "Unaisa meke faruwa?"
Batare da ta dauke idonta daga kallon kofar ba ta ce, "Dada sun dawo" Zaro ido Dada ta yi tare sa cewa "Su waye?"
"Dada mutanen nan ne da ke bibiya ta kwanaki"
Kofar Dada ta nufa da sauri yayin da Unaisa tai saurin fadin, "Sun wuce amma dada nafara tsoron karsu dawo." Yamutsa fuska sosai Dada ta yi, tare da fadin, "Me su ke nema ne Unaisa? Me su ke ce miki? Firgicin da kike shiga idan kin gansu ya na daga min hankali, wai daga ina suke?"
"Bansani ba Dada, amman kamar ba 'yan kasan nan ba ne, na ta ba ganin fuska guda biyu iri daya acikin su akusa da juna ba su da banbanci Dada, sannan wani jarababbe ke yawan biyo bayana yanai min mazurai kuma akwai mara lafiya akafarsa guda daya tare da tarin motoci da su ke zuwa dasu." Jimm Dada ta yi, zuwa can tace, "Narasa gane me su ke nema, Unaisa me suke ce miki.?"
"Dada ba na iya tunawa domin ba gane in da maganar su ta dusa nake yi ba" Kare mata kallo Dada ta yi sannan tace, "Ba zaki koma gidan nan ba Unaisa, maza shiga bandaki ki kama ruwa ki yi alwala ki zo ki shige dakina." Kamar yadda ta fada haka Unaisa ta yi, tana jin dawowan Malam mijin Dada bayan isha'i, misalin goma Dada taiwa Unaisa sallama ta wuce turaka tare da kara jadda mata karta yadda malam yasan tana gidan.
Misalin sha biyu da rabi Dada ta ji alamar zare sakatar dakinta, bude Ido ta yi da sauri tare da kara baza kunnenta, tabbas dakinta ne kuma harda alaman tafiya, tashi ta yi zaune batare data shirya ba, Malam ta kalla sai bacci ya ke dan haka tai saurin daukan buta ta zare sakatar dakin, Malam din ne ya motsa cikin fada yake fadin "Kullum ina miki gargadi ki dinga shigowa da robar tsuguno." Cikin sauri Dada ta fice ta na fadin, "Na mance ne Malam."
Gilmawan mutum Dada ta gani ta zauren gidan na su yayin da ta kalli kofar dakin ta dake bude, cikin sauri ta nufi zauren albarkacin farin watan dake sararin samaniya take ganin hanya, a hankali ta furta "Waye nan ?" Cak ta tsaya saboda tsananin kaduwa da rawa da zuviyar ta ta yi..
Fadila Lamido...✍🏻
