Karshen Kaddara Page 7&8 Complete by Ammey Laylerh - Abokiyar Hira Novels


༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*

𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢  𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

 _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

Unexpected and Surprising 🔥💥 

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. 

Page 7&8

♡ ♡ ♡ ♡     

ꨄ.... Sunfi ƙarfin 30 minutes tsaye a wurin kafin Ya Sadeeq ya lalubo hannun Baffansa cikin nasa tafin, cikin dauriya da son danne raunin dake son taso masa game da ƙanwar tashi yace. "Muje gida Baffa!" Don ya lura da yanda jikin Baffan nasa ke rawa, ganin hakan ya saka Baffan kallon Shareefah shima yace da ita. "Muje gida!" Kanta ta girgiza masa wanda taji kamar ze faɗo ƙasa na tsananin damuwar da take ciki, da kuma yunwar dake ƙoƙarin illatata ba tare da sanin taba,don ita samm a babin yau ɗin nan komai mancewa tayi dashi bare wani abinci da ta gama ɗaukarsa ƙaramin alhaki. "Zan tsaya anan Baffa!, Yaya Meenal zata iya farkawa a koda yaushe likitoci zasu bukaci wani nata a kusa!, kuje gida ni ina nan tare da Yaya Meenal...." Ta faɗa idanunta a soye don jin ƙaddarar yayar tata take kamar tata ce, "Kuje gida Shareefah ke macece kuma yarinya ƙarama, zan kula da ameenatou kuje....." Haka duk su ukun suka tsinkayi muryansa, wanda a kallon farko baka isa cewa shi ne yayi maganar ba, daga yanayin yadda fatar bakinsa take a bushe raƙayau, babu kuma wata alamar da zata nuna maka cewar shi ne yayi maganar... Taku ɗaya ana biyu ta ƙara tana tsaiwa a gaban mijin Yayar nata tace. "Kai ne zaka tafi ka barni, domin Ni nafi chanchanta da kulawa da Yayata...." Ba kallonta yake ba sema baya kaɗan da yana yana sake harɗe hannunsa a ƙirji yace, "Ni nafi chanchantar kulawa da ameenatou Shareefah, kina da buƙatar kaɗaicewa ki sama nutsuwa haka nan kema...."  Idanunta da suka sake cika taf da hawaye tace "Ni babu inda zana je, sabo da ni macece ƴar uwarta zanfi bata kulawan da tafi buƙata!" "Ni kuma Mijin tane ni ne zanfi kowa bata kulawar da kowa be isa bata ita ma Shareefah!" Daga ya kamo hannun Ya Sadeeq da suka jima da zama status shi da Baffa yana tsaida shi gabanta yace. "Ku tafi........" Ya Sadeeq ɗin ne tamkar wani gunki ya ɗamko hannun Shareefah ɗin ganin yadda take jujjuya masa kai alamar ya barta. Babu yacce ta iya, babu kuma yacce zata yi dole yaja hannunta suka tafi, ta tafi tabar Yayar tata a cikin wayuyacin halin da take a ciki. A cikin rai da ruhinta tana ayyana ba laifin yayarta bane, laifin wulaƙantattun wasu mazan irin ƴan iskan garin nan, ba laifin shigar dake jikinta bane, ba laifin ta bane, ba laifin ta bane, laifin  wasu mazajen ne masu son zuciyoyinsu, in banda haka daga ganin mace a hanya shikenan seku haike mata?, dolen dole laifin ba nata ba ne, ko tashi sayayyarsa ALLAH yayi mazan ze kama... Haka take ta jujjuya maganganun ita da zuciyarta. Tin da suka bar wurin Ya Ahmad ya sake jingina da jikin ginin wurin se a lokacin wani abu me kama da dawowa hayyaci ya same shi, wani kalan rumtse rinannun idanunsa da soye yayi ƙafafunsa na fara rawa, ya fara bi yana dafe bangon dake ginin wurin,  jikinsa da gaɓoɓinsa na kamar ana ruru musu wuta ne ata jikinsu, isowar Dr Bilal ne ya temaka masa, sabo da Dr pooja da tayi waya dashi ta labarta masa yacce ake ciki, amma bata faɗa masa ainihin abinda ya faru da Meenal ɗin ba ta ɓoye hakan a iyaka zuciyarta, se kuma Sir MAJEED da tayi kuskuren sanarma wa, wanda yace daya saka tsarkakan hannuwansa ya duba ta shima ya kwashi nashi rabon tagomashin zunubin, ƙara ya barta ta mutu, da uban wa yace karta kare martabar aure da addininta... Shi ne fitowar nan da yayi yana ta balbalin bala'insa har Shareefah ta gansa.  Shi da kansa ya temaka ma Ahmad ɗin ya miƙa shi ɗakin jinya ya kwantar dashi, tare da auna jininsa da yaga yayi mummunar hawa, drip ya fara ɗaura masa da masa alluran bacci zuwa can dare ya gani, idan har be sama pain Relief ɗin da ake buƙata, se a san yacce za'a yi dashi, bayan ya masa wasu allurai. Ga jikinsa da har wani hucin zafin yake fitarwa tsabar yadda yake amsar kidan dake sake rikita jiki da zuciyarsa, ga daga cikin kansa ji yake kamar ana masa bikin mahaukatan aljanu a cikin tsakiyar kan nasa, sannu a hankali tunaninsa ya fara janyewa yana nesa nesa dashi alluran da aka masa na fara rinjayar kai da tunaninsa, wani wahallen barcin da har a cikinsa mafarkan Meenal ɗin ne kawai a cikinsa, Meenal ɗin da yake ɗaukarka a matsayin DUNIYARSA, se gashi sama ta ka ta meda wannan Duniyar tasa ba komai ba, domin ta gama rugujeta tass babu komai a cikin ta se tarun wasu ababuwan da bai gama tantance ko sanin ko meye su ba....


*Meenerl*


"DON ALLAH DA DARAJARSA KU ƘYALENI, KU RUFA MIN ASIRI NI....NIE MATAR AURE CE, KARKU AIKATA HAKA GARENI NA HAƊAKU DA GIRMA DA ZATIN DA MAHALICCINMU YAKE DASHI....!!!"


Da sauri ta wani kalan dafe kanta  tare da ƙoƙarin son ganin ta motsa idanunta ko yaya ne, amma hakan na ƙin faruwa sakamakon abubuwan da suka faru da ita ne kawai keta famar dawo mata a sabbin su....


  "ALLAH ba zai taɓa ƙyale kaba, ku sani har da ku da kuka bashi goyon baya, zaku hulaƙanta!, za kuyi dana sani, ƘARSHENKU ba zai yi kyau ba, domin kun keta kima da darajar addininsa...."

  Ta sake faɗar kalmomin domin ita a tunanin ta har zuwa lokacin a hannunsu take, "Kin makaro Ƴan mata, domin rising naki be amsu ba, uban wa ze ganki da shigar dake jikinki ya yarda ke *MATAR AURE CE?*, to ki sani idan ma ke MATAR AUREN CE se mun keta haddin ki, tun da shigar dake jikinki ita ce ta rinjayi ra'ayina a kanki har na kware miki, dole inyi abinda na gama ƙyasa shi a cikin zuciyata, dole ne in kwashi ganima yau...." Kalmar mutumin da fuskarsa ba zata taɓa goguwa a cikin idanunta ba ya faɗi hakan, yana fara yayyage kayan dake jikinta, dukansa da yaƙushinsa ta fara amma ba abin komai ba..... Da ganan sak komai nata ya tsaya shikenan nan wannan shi ne MAFARIN.....


Kanta ta riƙe ahankali taci gaba da    processing farkawanta na farko!, da sumewar data ringa yi haka komai ya shiga dawo mata daki daki cikin kanta, wani kalan rumtse rinannun idanuwanta da suka kasa buɗuwa tayi, ga zuciyarta dake mata wani kalan zogi da ɗacin da ita kaɗai ce tasan iriyar ukubar da take amsa daga hakan,  yanzun shikenan hakan yana nufin sun gama da ita kenan? Sun keta hijjaban dake lulluɓe da igiyar AURENTA kenan?, Yanzun shikenan Ya Ahmad rabuwa  da ita zeyi  kenan?, shin yana inama?, a wanne hali yake yanzun?, tasan duk inda yake baya ƙalau wllh, shi take son gani!, so kawai take ta gansa. Kanta taci gaba da jujjuyawa tana riƙe da kanta muryanta a kasa can sosai take wasu maganganu... Ƙarar tsoki taji an saki, kafin wata fusatacciyar murya ta biyo baya ta hanyar furta kalmar *"IDIOTS"*  Bata san murya ko fuskan me maganar ba, don haka ta tattaro duk wani sauran kuzarin da take da tare da ambaton sunan ALLAH, tana buɗe idonta da a disashe suka ƙarasa kalle mata baya da gilmawar inuwar koma waye ɗin, bata zurfafa ko cilasta kanta ba, ta sake jan idanun nata ta kulle wasu zafafan hawaye su biyo bayan hakan. Sosai take ƙoƙarin dannar zuciyarta kasancewarta macece ita me dauriya, da shanye ko wanne irin ciwo da raunin dake cikin zuciyarta idan taso,don haka ko a yanzun ma take ƙoƙarin ganin ta danne hakan saboda ta taso yaƙi hakan. Wani kalan rumtse rinannun idanuwanta tayi a karo na babu adadi tana lallasar zuciya da gangar jikinta dake son bijire mata. Ita da kanta ga shiga bama kanta ƙwarin zuciyar shanye hakan ta fuskanta rayuwar da kyau, ta kuma yi gwagwarmaya tukuru wajen gyara rayuwa da gobenta. Don haka tayi luff idanunta lunshe, A yayin da ruhi da zuciya da gangar jikinya suke samun nutsuwa da hutu, mizanin yadda numfashinta ke sauƙa akan tafukan hannayenta tana tarar ruwan hawayen ƙarshen da In Sha ALLAHU ta gama zubar dasu kenan akan ƘADDARAR data afka mata, Kai bama iyaka ƙaddarar yau ɗin taɓa  da duk wata sabuwar da zata zo mata  cikin wannan duniyar zata jure, ta kumyi gwagwarmaya da yakar hakan, tafukan hannayenta dake riƙe da fuskanta da hawayen ke ci gaba da bi ta gefe da gefen fuskarta  suna sauƙa a cikin tafukan hannayen ta rumtse, wanda take jinsu kamar ɗigar dalma a  cikin zuciyarta, haka zafinsu ke ƙara birkita kanta da tunanin ta suna ci gaba da zana mata tabon ƘADDARAR da take kallar kamar ita da kanta ta sema kanta hakan. Wanda  kai tsaye idan da ace wani zai iya tambayarta miye sanadin ƘADDARARTA?, Da kuwa kai tsaye zata ce dashi ita ce, wanda rashin bin dokoki da ƙa'idojinsa suka jaza mata, wanda taurin zuciya da zafinta da rudin zamani suka bi suna  haɗawa duka waɗan nan abubuwan wuri guda su cakuɗe mata, harma  suka mata taron dangin daya jata zuwa ga ƙaddarar ta, tabbas ta yarda ta kuma amince ita ɗin tamkar *MISALI CE* da ALLAH ya bar ma ƴan baya a kanta, tamkar kuma *IZINA CE* gamai hankali da tunani. Wannan yasa da wani kalan gudun ceton rai da fitar numfashi  take ƙoƙarin danne zuciyarta daga son faso ƙirjinta da take son yi ta fito, wanda tama kanta alƙawarin cewa IN SHA  ALLAHU ba zata taɓa barin hakan,  ya zama shi ne  destiny ɗin ta  ƙaddarar data yi wa rayuwarta dabaibayi wajen fitar numfashinta na ƙarshe ba. Wanda zuwa lokacin wajen  ƙarfe biyu  na  dare ne, Amma har yanzu hawaye bai daina zubowa daga Idanunta ba,kamar yadda lokacin ke wucewa haka hawayenta ke ƙaruwa maimakon raguwa ma.... Wannan hali da take a ciki ne ya sake haddasa bugun zuciyarta ya karu wani zazzafan zazzaɓin kai tsaye na kai mata farmaki, hakan ya saka Dactor's biyun dake duty saurin ƙarasowa gadonta suka danna mata allurar bacci, wanda da farko fin ƙarfin allurar nasu tayi ma, har seda wata data kasance musulma ce ta taimaka da tofa mata wasu adda'o'i kana baccin ya ɗauke, sedai masu cike da wasu muggwan mafarkai wa rayuwar... 


 Ƙarfe goma a cikin asibitin tama su Baffa dukansu tare da gwaggo Sadiya da Bilkisu, sedai basu faɗin musu hasalin abinda ke faruwa da Meenal ɗin ba, kawai sun ce bata jin daɗi ne, wanda se da ƙyar gwaggo Sadiyan ma ta yarda ta biyo su, don da cewa tai bata zuwa jinyar lallauyi dai kowa tana kansa, se ita ce dan raki da lalacin tsiya daga fara laulayin zata fara tara ma kanta jama'a da mutane. Se kawai suka bita a hakan suka taho, don su duka ukun suma kansu alƙawarin bisne hakan a iyaka zuciyoyinsu IN SHA ALLAHU. Zuwa lokacin kuma Alhamdulillah ta dawo daidai ɗin ta sakamakon kwarin gwiwa da zuciyar da ta ringa bama kanta.  Har ma an dawo da ita normal room da kowa ze iya shiga ya ganta...

  Shigowar Baffanta da Yayan ta da ƙanwarta dasu gwaggo Sadiyan ne ya saka ta binsu da rinannun idanuwanta tana kallarsu kamar wasu sabbin halitta,  zama daga ƙafafunta Shareefah tayi a natse tana  dafa kafaɗar Yayar tata ahankali, wanda ya sata ɗagowa a sanyaye  ta juyo tana  kallon  Shareefah'n da jajayen idanunta da suke rine sosai har lokacin, Shareefah'n bata ce bata ce komai ba  har na wani ɗan lokaci suna zazzaune a hakan, kafin Gwaggo Sadiya ta miƙe tana me furta. "To Ameenatou ALLAH ya sauwaƙe, dan tafiya zanyi, ni ban san a gidan makoki muke ba mun zauna munyi jigum jigum kamar wasu masu damuwa ko wanda iftila'in rayuwa ya afkawa... Bilkisu taso mu tafi dan zamu biya ta gidan Inna Marka mu dubata...." Da wannan Bilkisun ta miƙe tana kallar Meenal ɗin don da zuciya ɗaya take ƙaunarta tace "ALLAH ya sawwaƙa Yaya ya baki lafiya..." 


Suka fita daga ɗakin ya rage se iyaka su, Suna fita ta buɗe idonta da suke jajir tace "Baffa ka yafe min, kaga abinda ya faru da rayuwata ko?, don ALLAH ka yafe min Baffa...." Be kalleta ba yace. "Ai ba yafiyana ya kamaci ace kin nema ba Ameenatou!, domin kuwa ba ni ne kikama laifin ba, yafiyar mijinki da ubangijin ya kamaci ace kin fara nema, domin kuwa su kika saɓamawa..."  Shareefah ce ta miƙe tsaye tana isa ga mahaifin nasu, har gaban ta kai ɗurƙushe ta ce "Don ALLAH ka yafe mata Baffa wllh ba zata iya ɗaukar waɗan nan abubuwan ba...." 


Seda ya danne tuƙiƙin dake ƙoƙarin taso masa kana yace.  "Zata iya mana, tin da ita ne ta saya hakan da kuɗin ta..." Yaya Sadeeq ne yace.


" Zata gaza ɗauka Baffa zuciyarta me rauni ce..." 


Tsaye ya miƙe don kar suga abinda ke son ciko idanunsa yace.


"Dole zata iya ɗauka mana, domin duk  tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa kan doka, Ta san da ba zata iya ɗaukan bane har ta  murzawa idanunta toka tayi fatali da dokokin ubangiji da kuma Mijin ta?..."  Yadda Baffan  ke maganar kaɗai ya isa  tabbatar maka da cewar  baƙin cikin da tashi zuciyar take ciki me girma ne, Meenerl dake kwance daga saman gadon marasa lafiyar kuwa, wani lumshe  idanunta  a hankali tayi , wasu zafafan hawayen data bawa damar sakkowa ya shiga sauka saman fuskarta, wani iri nauyi zuciyarta ke sake ɗauka da fitinannen ciwo, wani irin abu take ji me zafi da raɗaɗi,  ji take  dama ace ana iya meda hannun agogo baya da ta dawo da hasalin rayuwarta ta da can bayan nan, sedai lokaci ya gama nasa alƙalancin sedai batun tuba da miƙa lamura ga ALLAH kuma.


 Fitar Baffan ne ya saka kukan da take ta ƙoƙarin dannewa kufce mata, tana kuwa fasa shi da azabar da yake taho mata daga cikin ƙarƙashin tsakiyar ƙirjinta, saurin dawowa gare ta Shareefah tayi, tana tallafar kan yayar nata tare da soma karanto duk adda'ar da tazo bakinta, don ta sama sassaucin abinda ke zuciyarta ya ragu, Cikin iko da buwayar Ubangiji kuwa se gashi adda'o'in na ratsa ta  sosai tare da sanyaya zuciyarta. Kafin cikin natsastsiyar kalama da natsuwa Shareefah ta ce... "Ki sani! Babu wani abinda zai faru sai da izinin ALLAH mai girma Yaya!, Tabbas na yarda da ƙaddara kuma koda ace kina yawo da mafi girma a cikin sutturu ne tin da ya ƙaddara hakan a cikin kaddararki seta same ki, sedai sanadin kawai da kika faɗa tarkonsa na shaidan, wajen rashin ƙarasa suturta jikinki da rashin daraja ƙa'idojin da Ubangiji ya gindaya a cikin rayuwar aure. Kiyi hakuri Yaya Meenal, kiyi hakuri ki kuma yi joining wannan ƙaddarar,ki kuma roki ALLAH gafarsa ze kafarta miki, domin kuwa shi ya ce. idan wani lokaci mai tsanani da wahala ya zo a cikin rayuwarku,  kafin komai ku sani cewa ALLAH yana da manufa da dalilinsa na zuwan wannan al'amarin dake tare daku, kuma ku tuna cewa na ɗan ƙanƙanin lokaci ne abin zai zo ya wuce ɗin, tamkar ba'a taɓa yin saba.... Yaya Meenal I know da zan ci gaba da ce miki wani abu, domin duk kalmomin da zanyi amfani dasu kin fini saninsu, I know kuma  bana da  kalmomin da zan baki baki wajen  sanyaya zuciyarki a wannan lokacin!, Kamar yanda babu wanda zai iya kashe wutar da ke balbala acikin Rai da Ruhinki  sabo da But trust me, I can imagine your pain akan kaina, amma kuma babbar gudun mawar da zan baki a matsayina na Ƴar uwar da kika kasance Yaya kuma Uwa a gareni shi ne,   kawai zance ki dage da haƙuri da kuma dannar zuciyarki da fawwalama ALLAH  duka lamuranki. In sha  ALLAHU Lokacin da baki tsammani ba, Zai sauya miki damuwarki zuwa farin ciki mara iyaka. Tamkar yadda yake juya dare  izuwa rana....." Kukan dake ƙoƙarin kufce mata ta danne tana sake tallafar Yayar tata da take jin ta tamkar uwa a gare ta, Don haka cikin wata irin muryan kwantar da hankali ta ci gaba da faɗin. "Ina son  ki rungumi duka  ƙaddarorinki da zuciya ɗaya, Ki bar komai ga ALLAH domin kuwa shike maganin kowacce irin damuwa da matsala, kana ki yawaita adda'a ki kuma tsarkake imaninki tare da komawa gare shi baki ɗaya, kiyi kokarin cire komai daga ranki duk da nasan da wuya,amma ina son daga wannan rana me kama da haka ki dena ɓata hawayenki akan kaɗɗararki dama  ƙalubalan da zakici gaba da riska a gaba , kar kiyi kuka ki dena kuka Yaya domin kuwa ba'a ma ƙaddara kuka bata waje tayi aikinta ake, don kuka baya maganinta sedai karfin adda'a kan rage kaifinta, Bama da uwar da zata tsaya mana wajen dannar zuciyoyinmu, sedai muna da ALLAH shi tsai tsaya mana kin ji Yayata....."  Takai ƙarshen maganar nata suna rungume juna su sake sakin wani sabon kukan a tare, sedai na Shareefah'n yafi nata tasirintuwa, don ita nata se ka kasa kunne da kyau zaka iya jin sautin kukan nata,sautin da bashi da wani ƙarfi ko ƙarsashi da amo cikinsa ko misƙala zarratin,saboda rashin wadatacciyar garkuwar jikin da zata bata wannan damar,uwa uba kuma tayi kukan tayi kukan har batasan adadi ba,ta zubda hawayen har sai data daina sanin lokacin tahowarsu, har sai da idanunta suka fara gani dishi dishi tin a daren na jiya data raba kuka da kowa da numfashinta, wanda har daga karshe ta yanke tsammani daga samun dukkan ɗauki,ta kuma gama sallamawa ƙaddarar rayuwarta sedai a yanzun ƙanwar nata ta bata kwarin gwiwa sabuwa. Motsin taɓa ƙofar da akai ne ya saka ta buɗe jajayen idanunta, duk da cewar a hankali ne aka  buɗe ƙofar ɗakin,  haka nan zuciyarta ta bata tabbacin shi ne, Ya Ahmad ɗin tane, da jiya jiyar nan ta gama wulaƙanta aurensa dashi, amma yanzun wa gari ya waya?, ita ce, ita ce ta sani har gaban abada ita ɗin nan dai ce a ruwa. A hankali ta ɗaga kanta tana kuma sauƙe dubanta ga bakin ƙofar shigowar,duk da kuwa irin yadda gabanta ke  mummunar faɗuwa wahala da iftila'in daya gama afkama rayuwarta me gigita hankalin taya gama riskarta, kai tsaye kuwa idonta ya faɗa cikin nashin.

   Shi da ita suka zubama  juna ido kamar yau ce ranar farko da suka fara ganin juna,kowannensu da kalar kallon da yakema  ɗan uwansa. Wanda a kallon farkon daya mata yana kallar yadda tashin hankali ya gama dabaybaye kyakkyawar fuskar nan tata,  da har yanzun wani irin kyau na daban me matuƙar tasiri da fusgar hankalin da ya gagara gushewa shimfide saman fuskar tata,saidai kana kallonta kasan ba haka take ba,abubuwa da yawa sun canza wanna fuskar, tsakanin daren na jiya zuwa yau komai ya sanja lissafin fuskar nata, idanuwansa na a kanta ya fara takowa Mahaifinta na tako masa baya, raunin kalaman da Shareefah tayi na kamasu su duka, don suna tsaye sun kuma gama saurarar komai daga gare ta, wannan abu shi ya sanyaya duka jikkuna da zuciyoyinsu, kamar yadda suka gama ruguwa taurin zuciyar Ya Sadeeq ma anan ɗin, da yake zaune har lokacin ya gaza koda wanne kalan motsi, tabbas kalaman Shareefah haka suke kuma suna akan daidai, lallai duk abinda ya faru da bawa tin daga Rabbil Izzati ne yake, Koda ace kai ne ka fi kowa kare martabar da kimarka, idan har ALLAH ya rubuta hakan to kuwa se an samu ɓata garin da dolen dole su bata maka rayuwar a irin wannan gabar!, se dai kamar kuma yacce tace ɗin ne still, son zuciya da rudin zamani kan zama sila ko kuma ja gaba wajen bama shaidan damar afkuwar hakan.

     A wani kalan sanyin jiki dana zuciya ya ƙaraso gar gaban gadon yana kaiwa zaune inda Shareefah tayi gaggawar tashi ta bashi,ya zauna sosai yana fuskantarta haɗi da zuba masa idanunsa da suka janye sosai shima... Ganin hakan ya saka su Baffa fita dukansu amma kuma suna daga bakin ƙofar room ɗin, "Me kika yi haka ameenatou?, wanne kalar fentine ne haka kika gogama rayuwar aurenmu uyhmmmm?, kawai don biyema rudin duniya da zamani kika zaɓa lalata rayuwarmu mu duka biyun, da kuma ruguza yardar dake tsakaninmu!. Kina jin irin yadda nake ji kuwa a cikin ƙirjina?, ashe dama haka ƙaddarar take bata da sauƙi irin haka?"  Ya ɗinke maganar nashi ne saboda rawar da bakinsa ya fara da haƙoransa,  zuba masa jajayen idanunta dake a rine tayi kafin ta  lumsh su, ragowar hawayen da basu samu damar zubowa ba suka gangaro mata kana  ta buɗesu tarwai a kansa tace....


"Bana da tsumi ba kuma ni da dabarar hana faruwar hakan Ya Ahmad, Kamar yadda ban isa na fidda kaina daga gare kaba, nasan zuwa yanzun ka tsaneni ne Ya Ahmad, kayi hakuri kayi hakuri kayi ta yin haƙuri da bama zuciyarka salama, Ubangiji ya maka mace ta garin data fini nagarta!, da halaye masu kyau fiye dani, zanyi nesa sosai da rayuwarka kamar yacce kaima nasan za kayi nesa da tawa rayuwar!!!, Sedai ka tayani adda'ar koda ace bana raye, to ina son ka tayani da Adda'ar hana duk wanda yamin haka nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin rayuwarsa,Ya kuma  girbe fiye da abinda ya shuka min.... Saurin rufe bakinta  yayi da hannunsa yana jijjiga mata kai, kafin Yace...


"Ina sonki Meenoh!, bazan iya rabuwa dake ba, kuma banajin zan daina SO da ƘAUNARKI don wata ƙaddara ta gilma tsakaninmu, zan ci gaba da zama dake ameenatou!, kuma bana son wannan maganar ta fita ko ina daga mu se su Baffa, Sedai se kin yi hakuri kin kuma jurema zaman, don kuwa se na gama jinyar zuciya da kaina kafin komai ya dawo mana dai-dai gwargwado iyaka abinda naga naga zan iya, ba zan rabu dake ba INA SONKI ina ƘAUNARKI Meenal........"  Sosai ta buɗe ido da baki da hanci tana kallarsa da wani kalan yanayi, kafin bakinta na rawa ta ce...

  

"Har yanzun kana jin zaka iya ci gaba da zaman aure dani Ya Ahmad?, bayan na gama take aurenka dake kaina, wasu kuma sun gama wulaƙanta martaba da yardar dake cikin auren namu amma har yanzun kake jin zaka iya zaman auren dani?...." Kansa yake ɗan jujjuya mata kafin Yace... "Kifar taso da abinda ya riga da ya gama faruwa, ki ɗauka hakan a wani issue ne na daban daya shafi interest nawa  da kuma naki kawai, ki dena sako ko danganto wani a ciki domin zuciyata ba zata ci gaba da jure hakan ba...." Wani kuka ta saka tana ɗamke hannunsa dake cikin nata take furta. "Na gode!, na gode ALLAH, Alhamdulillah ko yanzun ALLAH ya ɗauki raina na gode masa...." 


 Rumgumeta kawai yayi domin bazai iya ci gaba da saurarar kukan taba, daga nan Dr pooja ta shigo ta sake dudduba jikinta ta haɗa mata magani ta basu sallamar da ita ce da kanta tace a basu, Sosai Baffa da Ya Sadeeq suka ta yima Ahmad ɗin godiya don duk dama zullumin hukuncin da zai yanke a kanta suke da tsoron kar ace ya rabu da ita,   Se da suka musu rakiya har gida kana Baffa ya sake jaddada godiyarsa ga Ahmad kana suka bar gidan....


Bayan tafiyar su Baffan sun jima zaune a wurin zaman kurame kafin tayi kundin balar sake nemar yafiyarsa gare ta, Komai bai ce mata sema tashi da yayi ya bar mata parlour ya shige bedroom nashi, don kansa wani bala'in ciwo yake masa, koda ta bishi taji ya rufe ɗakin kanta kawai ta jinginar da jikin ƙofar tayi kukanta me isarta a wurin, kafin taja ƙafafunta ta nufi bedroom nata, kwanciya tayi zuciyarta na wani kalan mata bugu da tafasa, ƙarfe biyu bayan tayi Sallah ta fito tayi girkin rana, ɗakinsa ta leƙa daga a rufe ta woje alamar ya fita kenan,  kaɗan ta ɗan cakali abincin itama ta ture ta koma tayi wanka ta ɗauki Alqur'ani tayi karatu,  har kusan yamma sosai tana nan zaunen kafin ta tashi taje ta meda na dare, bayan ta kammala tayi sallar magrib, ta sake karatun Alqur'ani tsakanin magrib da isha'a, wajajen tara taji alamun shihowansa gidan, tayi hanzarin fitowa jikinta da himar har ƙasa, daidai lokacin yake ƙarasa bayyana a cikin parlourn, sannu da zuwa ta masa ya amsata da hannunsa yana ƙoƙarin wucewa, cewa ta mishi ga abincinsa yace ya gode amma ya koshi, bata ji daɗi ba amma haka ta danne ta kyale shi, kana ta mara masa baya zuwa ɗakinsa, Sedai ya dakatar da ita ta hanyar ce da ita tayi haƙuri yana bukatar balance ne sosai, don haka ta dawo parlourn jikinta a matuƙar sanyaye, seda dare ya tsala sosai kana tabar parlourn, koda ta shige bedroom nata bata kwanta ba Alwala tayi ta fuskanta alƙibla, ta fara jero sallolin da bata san iyakar su ba, har aka ƙira asuba, A hankali ya turo ɗakin nata don tada ta tayi sallar subhi ɗin, Sedai ganinta a zaunen da yayi ne ya saka shi fita be ƙaraso ba, wajan shida ta fita ta ɗora musu brekfast.  Lafiyayyar Doya da kyau ta musu, da lemun kwakwa,  a gurguje taje tayo wanka kana tazo ta zauna cikin parlourn tana jirar fitowar sa, babu jimawa kuwa se gashi ya fito da brifcase nashi a hannunsa ta fita aiki, saurin miƙewa tayi tana isa gare shi yay hanzarin janyewa ya koma gefe guda, kanta ta sunkuyar ƙasa ta gaida sa, amsata yayi sama ²  tace dashi ga breakfast yace da ita ya gode zeci a woje. Kusan a wannan karon kam daskarewa a tsaye tayi, shin me yake nufi ne wai, ko dama shi ne haƙurin da ya ce se tayi? In sha ALLAHU zata yi za kuma ta jure da Ikon ALLAH... 


Tin tana kallar kamar zata iya jurema yanayin, har hakan ya fara fin ƙarfin tunani da kuma kanta, don takai ta kawo ko zama ya dena yi inda ta zaune, tayi kukan tayi adda'ar amma duk a banza, abinci kuwa dama tuni ta dena yi dashi, don ko tayi Sedai ta tayin asara tana bama getman ya rabama almajirai,   abinda ya sake bata mamaki kuma shi ne da sati ɗaya da faruwan abun ya zo mata da zancen zata iya ci gaba da aikinta tace ta dena ta haƙura har gaban abada,  komai daga haka be sake ce mata yaci gaba da rayuwarsa, har takai ta kawo gidan ma yanzun kafin ta tashi ya fita, lokacin da zai dawo kuma tayi bacci, inda sosai hakan ke damunta, har take jin ƙara kawai ya rabu da ita idan har hakan shi ne mafi alkhairinta, saboda da wannan matsalar nasu har Shareefah seda ta tuntuɓa da lamarin, kai tsaye kuma tace da ita ta ƙara hakuri akan wanda take yi, In sha ALLAHU komai zai wuce, gama hucewar ne be yiba. Tin Dr pooja na ƙirar ta har ta haƙura, inda daga ƙarshe take jin kyakkyawan labarin musluntar Dr pooja ɗin, wacce ta musulunta a hannun Baffansu a masallacin ƙofar gidansu, a yanzun haka tana amsa sunan AYSHA ne, tayi murna sosai da jin lamarin na musuluntar da tayi, Ta inda take sake godema ALLAH ma shi ne da bata da komai, idan kuma ta tsaya ta tsai da ranta rashin samun cikin da batayi ba a tin farkon Aurensu har zuwa yanzun kan damunta, se dai shima ta barma ALLAH lamarinta, haka sukaci gaba da gudanar da rayuwar Aurensu, ba tare data sake fuskantar kowa da matsalar ta ba, har kimanin 2 Months, gashi ma har suna kokarin shiga na uku...

  Masu iya magana sukan ce a duk lokacin da wani abu ya tunkaro ɗan Adam yana yi masa barazana da rayuwarsa, sai yaga kamar duk duniya babu wanda ya kai shi shiga tsananin rayuwa. Har takan kai wasu ƙarancin  imanin fara fafutar nemarwa kansu mafita ta kowacce siga ce kuwa domin kawar da ita wannan matsalar da yake fuskanta. Kamar yadda ya kasance a cikin rayuwar Meenal a ƴan tsakan kanin lokutan da suke wucewa a cikin rayuwar aurenta da Ahmad. Lallai ta sake yarda da wannan maganar da ake yawan cewa. Ciwon da ya addabi hannu idanu yake hanawa bacci. Idan ido bai yi bacci ba to lallai dukkan jiki ba zai huta ba. Jikin da rashin hutu ya yiwa sarƙa kuwa yana tattare da ƙarantar kuzarin kare kansa daga bullowar wasu cututtukan ne, Kamar yacce sannu a sannu wani irin ciwon da bata san ko ainihin na minene ba ke famar wajiga rayuwarta,  Ta kuma sake yarda da ake cewa idan bamu magance ciwon hannun ba, da sannu sannu shi dai wannan ciwon zai iya kama ragowar sassan jiki ko kuma ya bayar da ƙofar samuwar cutar da tafi ta hannu.  Sannu a sannu rayuwarta ke ci gaba da gudana cikin kunci a gidan Ahmad, ga ciwon dake ƙoƙarin kaita ƙasa amma tana gwada jarumtarta akan hakan, har tana  daukar hanyar wata guda kenan da wannan jinyar, wanda a zahiri na gaskiya ba haka hasalin lissafin yake ba,  wannan jinyar alamu ne bayyanuwar cikin haihuwa a jikinta, sedai tsananin kunci da damuwar da take ciki be saka ta fuskanta hakan ba, ko daga yanayin sanje sanjen da take samuwa daga wasu sassa na halittar jikinta, se dai idan aka ce tashin hankali to anan nufin gaba da komai kenan, don babu cikakkiyar nutsuwar da ya kamaci ace ta tsaya duba ko tantance yanayin da take a ciki ba...


 Ranar da ba zata taɓa mancewa da ita ba a cikin rayuwarta itace ranar wata LAHADI, ranar ta tashi ne kamar ba ta kai labari ba, gaba ɗaya tin daga kamo daren ranar har kamo la'asar ɗin ranar haka ta wuni a kwance ko ruwa kasa zama a bakinta yayi,  tana daga kwancen a yadda take ta fara ƙoƙari da yunƙurin miƙewa, da shigowar Ahmad sassan nata da rabon daya shigo shi har ta manta, gaba ɗaya ya gama fitar da ita daga cikin rayuwarsa tun faruwar wancan lamarin, ko zama kusa dashi be sake bari tayi ba. Kin kallar inda take kamar ko da yaushe, kamar yaga dogon zunubin da ze iya kifewa koya halakar dashi, haka ya dubeta yace tayi maza ya shirya ta fito yana jiranta a mota, tambayarsa tayi lafiya ina kuma zai kaita, wayarta yace ta duba Dr pooja (AISHA) tayi ta ƙiranta amma ta gaza taƙi amsawa, ƙoƙarin komawa kwancen data yunƙura ta tashi take, tana ce dashi.....


 "Babu inda zani Ahmad!, ai na faɗa mata bana jin daɗi ne, ko kuwa duk Dactor's ɗin dake cikin asibitin basu isa ba se lallai dole ni naje???, Haba Ahmad da wanne kake son inji, na baka hakuri kaki ka haƙura ka fita a cikin rayuwata, ka dena sakewa dani ka dena kusantata, komai daɗa lalacewa yake,  memakon ace samun sassauci nake, Bayan kuma na baka hakuri na baka hakuri, don girman  kayi hakuri mana..."  Tsaiwarsa ya gyara yana fuskantar da kyau yace.  "Wanene ya gaya miki ban haƙuraba?, Idan da ban haƙura ba da tin tuni kin jima da tafiya gida!, kinga yanzun dai wannan a matsayin umarni da kuma temakon rai zakiya, kasancewar weekend na babu yawaitar manyan Dactor's duk se ƙananu shi yasa suka biyo ta hannu nama, Dr Bilal ne yamin waya don shi ashe ma baya 9j ɗin ne.........

 Da kyar ta yunƙura tana shigewa bathroom, babu jimawa ta fito babu laifi kuwa taji ƙarfin jikinta sosai, don haka ta zira doguwar hijjabarta har ƙasa ta fito ta same shi cikin motarsa. Karatun Afid muhd taj ya saka musu, cikin ƙanƙanin lokaci suka isa asibitin, tin daga yanayin tsaron da aka bama hospital ɗin ta gane cewar lallai wani babban ne ko ɗan gidan wani kusar ne me jinyar, tana isa ta shiga wani room ta sanja kayanta zuwa na surgery, hannunta da handglovs idanunta da glasses fari ta nufi ICU inda nan ne me jinyar yake, Dactor's biyu ne suka mara mata baya ta shiga, tana isa  Dr Aysha dake kan majinyancin ta bata hanya, isa tayi gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta ta saka hannu kenan da niyar amsar tiyatar idanunta ya sauƙa akan...................

_To fa shin akan mene ko waye idanun Dr Meenerl ya sauƙa?..._ 

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215


Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post