_Bossladieswriters_
_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun littafin daga farko, da kuma abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_
https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_
_ZAINAB BATURE_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
19
Da tsananin mamaki innarsu Salma ke juya kuɗin da ta kawo mata wanda rafar yan dubu dubu ce guda biyu. "Yanzu kika ce haka nan ya zo ya baki wannan uban kuɗin ya ce ki kawo?" Ta tambaya idonta a kan Salma dake tsaye a gabanta bakin baranda, kai ta ɗaga ta ce, "Wllh innarmu yadda na faɗa maki." Hannu ta kai ta riƙe haba ta ce, "To amman ya akai ya san nan gidan har ya zo?" Ta tambaya da mamaki a kan fuskarta, Salma ta ce, "Ni ma wllh abun da nike ta mamaki ke nan innarmu, kuma na faɗa maki ai maganganun da muka yi da hajiya ɗazun sam shi bai ma saka baki ba lokacin da take mani maganar tuyan awaran." Gyaɗa kai innar ta yi ta ce, "To wataƙil dai daga hiran taku ne yana sauraro, kuma ƙilan bayan kin taho ya tambayi hajiyan har ya san in da kike yin tuyar shine ya zo. Dama Sagir yana ta faɗin irin uban alkhairin da yake ta yi ma mutane, an gode Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi ya ƙara masa ɗaukaka. Idan kuka sake haɗuwa sai ki yi masa godiya sosai." Amsawa Salma ta yi da to, tana shirin juyawa innar ta tambaye ta ina zata je ta ce mata za ta je wurin awaran ne, "To ku ƙarasa soya sauran sai ku rabar ma mutane tun da haka ya ce, ki ba Hamza ya kai gidansu Habu." Amsawa ta yi da to cike da jin daɗi ta nufi hanyar waje, ci gaba da juya kuɗin innar tasu ta yi tana mamakin irin kirkin Deen, haka nan ya ɗauki kuɗi masu yawa lokaci guda ya ba su! tabbas shi ɗin na daban ne ta ayyana a ranta tare da juyawa ta nufi ɗaki. Bayan Salma sun dawo gida suka zauna cin abinci har da su Sagir da suka dawo, suma sun yi mamaki sosai bayan da innarsu ta sanar masu zancen kuɗin da Deen ya basu, Sagir ya ce ai wannan ba wani abu bane a wurinsa, ya shiga basu labarin irin abubuwan alkhairi da yake ta yi ma mutane, gaba ɗaya suma su Auwalu sun yanke cewa maganar da Salma ta yi da hajiya ce ta sa ya zo ya bata kuɗin, sai dai sun yi matuƙar mamakin yadda ya iya takowa ya zo ƙofar gidan nasu, Sagir ji yake inama sun haɗu da shi. Bayan Salma ta gama cin abincin banɗaki ta wuce ta yo wanka, dama ta yi sallar isha tun lokacin da Deen ya zo aka ce tana cikin gida to salla ta je yi, sam bata wasa da salla da lokacin ta ya yi take barin abun da take yi ta je ta yi, shiryawa ta yi da doguwar rigar bacci ta saka hula a kanta jikinta na ta ƙamshin humra da ta shafa, littafinta ta ɗauko don ta yi karatun test da za a yi masu, sai da ta yi addu'a kafin ta kwanta a saman ɗan gadonta da ya sha shimfiɗar wankakken zanin gado, musamman babanta ya haɗa mata gadon da ɗan mirror har da ƴar wardrobe mai gida biyu, hannunta ɗaya riƙe da wayar innarsu keypad ta kunna torch tana haska littafin, sai dai tana fara yin karatun zuciyarta ta ƙi bata goyon baya ta hanyar jan akalar tunaninta zuwa faɗawa tunanin Deen, sai ma ta rinƙa ganin fuskarsa a jikin littafin, ƙarshe dole ta ajiye shi a gefe ta ci gaba da ba zuciyarta goyon baya, abubuwan da suka faru tsakaninsu yau ta shiga tunanowa tana sakin murmushi kamar wata zautatta, komai na shi ba ƙaramin burge ta yake ba, ba ƙaramin tafiya ya yi da ita ba lokacin da ya yi ma kansa kitson nan, ko ina ma kitson? ta raya don ba alamun shi lokacin da ya zo ƙofar gidansu, wata zuciyar ta bata amsa da ƙilan ya kwance da zai fita waje, jinjina irin kirkin sa ta shiga yi yadda har ya iya takowa kofar gidan nasu ya bata kuɗi, Fahad ne ya faɗo mata a rai nan take ta yanke hukuncin Deen ya fi shi kirki nesa ba kusa ba, a ranta take raya tabbas duk wadda ta aure shi wllh ba ƙaramin dacewa ta yi ba. Tana ta tunane-tunane a haka bacci ya yi awon gaba da ita.
Washe gari Asabar, misalin ƙarfe tara saura na safe su Salma na zaune a ɗakin innarsu, wanda ba laifi ɗakin babba ne, akwai gado mai kyau da dressing mirror da side drawers ɗinsa, sai wardrobe mai gida biyu, daga farkon shiga dakin a gaban gado akwai kujeru mai mazaunin mutum biyu da masu mazaunin mutum ɗaya guda biyu, Salma na zaune a saman kujera mai mazaunin mutum ɗaya, yayin da Imran da Hamza ke zaune a tsakiyar kujerun saman ɗan madaidaicin carpet dake a saman ledar tsakar ɗakin, gaba ɗaya suna sanye da uniform ɗin islamiyya, kowannan su kofi ne a hannunsa suna yin karin kumallo,
"Faka-faka, ina abun karin kumallo na?" Sagir da ya faɗo cikin ɗakin ya faɗa, ƙafafunsa na sanye da dogayen safuna sai wandon ƙwallo hannunsa na riƙe da rigar bai kai ga sakawa ba, duk suka kalle sa, zama ya yi a saman kujera kusa da Salma, "Innarmu ina nawa?" Tana kallonsa ta tambayi saurin mi yake yi haka? Amsa ya bata da, "Wllh gasa ce zamu yi gaba ɗaya team ɗin ƙwallon garin nan, a cikin waɗanda suka yi nasara Nuree Jr zai zabi ƴan wasan sabon club ɗinsa mai suna 'FT STRIKERS." Kai Innarsu ta jinjina alamar ta gane,
"Tare da shi zaku yi ƙwallon?" Salma da ta kur6i kunu ta tambaya, ya bata amsa da a'a amman a gabansa za a yi gasar yana kallo, bayan an zuba masa kunnun ya ɗauka yana sha tare da ƙosai, ba tare da 6ata lokaci ba ya miƙe innarsu ta tambayi har ya gama ya ce mata eh, ta tambayi ko a ƙara masa ya ce mata a'a bai son ya cika cikinsa sosai ya kasa yin abun kirki,
"To ni zan tafi innarmu ki yi mani addu'ar nasara, dama baba tun da muka je sallar asuba na sanar masa shima ya yi mani addu'a." Tana murmushi ta ce, "To Allah Ubangiji Ya baku sa'a Sagir." Da sauri ya amsa da Amin yana ƙoƙarin saka rigar kwallon, "To ni ba zaka ce in yi maka addu'ar ba?" Salma ta faɗa tana wurga masa yar harara,
"Ke dalla wake ta wata addu'arki, ga mai kankat nan wadda da ta yi an kar6a ba shamaki." Gyaɗa kai Salma ta yi ta ce to shike nan, Innarsu dake murmushi ta ce, "A'a Sagir, wannan yarinyar tawa fa yar baiwa ce Allah, kada ka raina addu'arta don Allah na amsa mata addu'ointa." Bayan ya gama saka rigar ya kalli Salma yana ƴar dariya ya ce to ta yi masa addu'an,
"Ban yi!" A fusace ta faɗa, hannu ya kai ya kama kanta yana dariya ya ce,"Haba my lovely sis, ni da ke ai bata 6aci kin san wasa nike maki ina buƙatar addu'ar ku ƴan'uwana." Tana murmushi ta ce masa Allah Ya basu sa'a, amsawa ya yi da Amin tare da sakar mata kai, sai kuma ya ce, "Da kar ki yi mini addu'ar ki ci na jaki." Harara ta wurga masa tare da faɗin, "Kamm! To na ma janye addu'ar tawa." Nufar ƙofa ya yi yana dariya yana faɗin ta baya ta rago, su Imrana suka ɗaga murya suna yi mashi Allah Ya bada sa'a ya amsa lokacin ya fice.
Bayan Salma ta gama karin kumallon, ɗakinta ta koma ta sako hijab a saman kayan jikinta don tafiya islamiyyar hadda da suke yi asabar da lahadi kawai don ta yi sauka, "Innarmu zan tafi." Ta faɗa a daidai saitin ɗakin innar tana gyara hijab ɗinta, ɗaga labule ta yi ta fito da murmushi ta ce mata, "To, sai kin dawo Allah Ya bada sa'a." Ta ce, "Amin, yauwa ba kin ce kina son waken suya ba? Ko ki kawo idan aka taso sai in wuce bakin tasha in siyo." Ɗan jim innar ta yi kafin ta ce, "Je ki kawai a siyo ko gobe." Salma ta ce, "To wanda za a yi amfani yau fa?"
"Anya a yi awara yau, a dai bari ko gobe idan Allah Ya kaimu, kada shi mutumin da ya bamu kuɗi ya gan ki kina yi yayi tunanin mun cika son kuɗi." Ta ƙarasa tana ƴar dariya, itama Salma murmushi ne akan fuskarta ta ce, "To ai neman halak ne, kuma da ya bamu bai ce kada mu yi ba." Kai innarsu ta ɗaga alamar haka ne ta ce amman dai yau ta huta, sallama suka yi ta wuce innarsu ta bita da kallo tana murmushi, tana kai wa bakin ƙofa zata fita ta juya ta yi ma innar tasu bye bye tare da yi mata alamar kiss, murmushin jin daɗi ne akan fuskar innarsu ta furta, "Ina son Salmata. Allah Ya raya mani ke ya albarkaci rayuwarki." Amsa mata ta yi da, "Amin uwata da babu irinta.." Daga haka ta fuce innarsu ta ɗan girgiza kai tare da juyawa ta koma ɗaki.
Misalin ƙarfe sha biyu da rabi na rana su Salma duk sun dawo daga islamiyya suna zaune a tsakar gida, baka jin muryar kowa sai ta Sagir da ta karaɗe wurin yana basu labarin yadda gasar su ta wakana, jikinsa ko riga babu sai wandon ƙwallo daga gefensa takalman kwallon da ya cire ne tare da safar ajiye, Salma dake ta murmushin jin daɗin jin Sagir ɗin na cikin waɗanda aka za6a yau, ta ce, "Amman Sagir har da shi kuka yi ƙwallon?" Tambayarta ya yi wa? ta ce shi jikan hajiya da ya haɗa gasar, Sagir ya ce, "Farko bai shiga ba kallo ya yi, sai bayan da aka gama za6ar waɗanda suka ci zagayen farko na gasar muka buga tare da shi...kuturun uba! Kai, wanda ya iya dai ya huta wllh, ai duk yadda muke ganin mu nan ƙwararru ne gurin ƙwallo a garin nan ƙur'an duk sai da muka raina kan mu...wai kun ga yadda mutumin yake sarrafa ball kuwa....!" Dakatawa ya yi ya ɗauki wayarsa dake a saman cinyarsa ya ɗan lallatsa, miƙo ma Salma ya yi ya ce ta kalla ga wani video nan da ya yi lokacin da suke bugawa tare da second team da suka ci, da sauri ta yunƙuro ta zo ta amsa ta koma saman tabarmar da take zaune tana kallo, innarsu da su Imrana ma duk suka sako kai suna kalla, Deen na sanye da jersey ɗin club din su na gida, sosai kayan suka amshi jikinsa sun ƙara fito masa da hasken fatarsa, murmushi ne akan fuskar Salma yayin da take kallon ƙwallon, a cikin ranta ta raya ke nan sake yin kitson ya yi don ta ganshi akan sa yanzu, kamar innarsu ta san mike a ran Salmar ta ce, "Wai kamar kitso nike gani a saman kansa ko?" Ta ɗago tana kallon Sagir, ya ce, "Eh kitso ne mana, ai dama yana yin kitso. Ni ma indai na shahara a ball sai na rinƙa yin kitso tun da ai ba haramun bane." Yana rufe baki Salma ta ɗago da alamun mamaki ta ce, "A wannan kan naka kamar goruba ne zaka rinƙa yin kitso." Daƙuwa ya yi mata ya ce, "Eh don ubanki, shegiya, dama ni ne da irin gashin ki, ni na rasa yadda aka yi ma komai naki ya fi namu kyau, koda kike mace ai yakamata muma mu ɗebo wasu abubuwan irin naki, amman daga ke sai Hamza duk aka tara ma abubuwa masu kyau." Ƙyalkyale masa da dariya Salma ta yi tare da yi masa gwalo, innarsu na murmushi ta ce, "Ai kuma ma sha Allah ba munana bane." Imrana ya kai hannu ya shafi sumarsa ya ce, "Amman dai gara gashi na da na yaya Sagir wllh..." Da sauri ya yi shiru ganin Sagir ɗin na niyyar rarumar takalmin ƙwallonsa ya san kuma yana iya jefo masa. Bayan salar Azhar Deen ya shigo cikin falon kamar ko yaushe jikinsa sanye da kayan shan iska don ba karamin jin zafin yanayin da ake ciki a Nigeria yake ba, a haka ma wai ruwa ya fara sauka kuma koda yaushe yana a cikin Ac, hajiya na zaune ta ɗaga kai ta kalle sa tana murmushi, wurin da take ya nufo yana zuwa ya miƙa mata hannu ya ce ta taso su je waje zata ga wani abu, kama hannun nasa ta yi ta miƙe tana faɗin Allah Ya sa ta ga alkhairi ya amsa da Amin yana murmushi, wajen part ɗin suka fito hajiya nata wurga ido ko zata ga wani baƙon abu, wurin parking space ya nufo da ita sai lokacin idanunta suka ga wani mutum dake a tsaye gefen wata rantsattsar mota fara sol sai uban sheƙi ta ke, kana gani ba sai an faɗa maka ba ka san sabuwa ce, mutumin na ganin Deen ya shiga washe baki, suna ƙarasowa ya ba mutumin hannu suka gaisa tare da yi masa ya hanya cikin washe baki mutumin ke amsawa, daga baya ya gaishe da hajiya har da ɗan russunawa ta amsa masa a mutunce, bin motar Deen ya yi da kallo mutumin ya ce ko a buɗe masa ya ƙara gani ya jinjina masa kai, buɗe cikin motan ya yi wanda ya matuƙar tsaruwa, nuna masa abubuwa mutumin ya shiga yi yana ƙara yi masa bayani, fuska a sake Deen ke ɗan jinjina kai alamar yana fahimtar bayanin, duk da dama ya riga ya san abubuwa da suka danganci motan, hajiya dai ta zuba ido itama tana kallon motar da sauraran mutumin, bayan ya gama yi ma Deen bayanin ya ce shi zai wuce, Deen ya ce masa ba zai tsaya ya huta ba ya ci abinci, cikin washe baki ya sanar da shi tare suka zo da wani abokin kasuwancin su shima ya kawo wata mota Zaria za su haɗu ne suna son su koma Abuja yau kada dare ya yi masu, bayan sun yi sallama mutumin ya tafi don dama tuni sun gama duk wani ciniki da boss ɗin su, shi ma kuma mutumin lokacin da ya kira Deen ya sanar da shi shine zai kawo masa mota ya tura masa kuɗi masu yawa.
"Ya kika ga motan, ya yi kyau?" Ya tambayi hajiya idonsa akan motar, kai ta shiga jinjinawa ta ce kyau ma ai ba a ma magana ita bata ma ta6a ganin irin motan ba, yana murmushi still holding her hand ya ce mata Avatr EV ce, wato motan da ake ma cajin lantarki, cike da al'ajabi hajiya ta ce, "Ikon Allah, yanzu nan sai a yi mata caji lafiya lau a yi amfani da ita?" Amsa ya bata da sosai, ta ɗan ta6e baki ta ce, "Bature dai ba zai bar mu mu huta da abubuwan al'ajabi ba, saura kuma jirgi mai caji shi ma na san ba wani babban aiki bane a wurin su." Yar dariya Deen ya yi ya ce mata ai wannan ba daga turawan bane daga yan China ne, hajiya ta ce ai dai duk taron su ne masu jan kunnuwa, zagayawa ya yi da ita ya buɗe mata ɗayan bangaren ta shiga da bismilla a bakinta, shima ya zagayo driver seat ya shiga yana ƙara kallon cikin motar, kai kawai hajiya ke jinjinawa tana ƙara yaba tsaruwar motan, screen ɗin dake a kusa da steering motan ya ɗan tatta6a kafin ya kalli hajiyan ta ciki ya ce mata, "Hi Sweety!" Hajiya ta gwalo ido cikin rashin fahimta, dariya ya saka ya yi mata playing vedion da mamaki ta ce wai camera ce a jikin screen ɗin ya ce mata eh, bayan ya rufo motan ya tashe ta suka fara zagayawa a cikin harabar gidan, su officer dake bakin gate duk sun leƙo suna ta kallon motan cikin washe baki sai kace bakunan nasu za su yage, tambayarta ya yi ko su fita su zaga gari ta ce a'a ya bari ta shirya tukun ko zuwa dare, bayan sun gama zagayawa ya dawo da su wurin parking, suna fitowa su officers suka ƙaraso cikin washe baki suka shiga yin santin motan tare da yin Allah Ya sa alkhairi, bayan su officer sun bar wurin hajiya ta ce, "Yanzu ita wannan motan amfani zaka yi da ita ne da ka siya?" Amsa ya bata da eh ya zo ba mota shi yasa ya siya ya yi amfani da ita a nan, hajiya na kallonsa ta ce, "Amman duk motocin dake a gidan nan Deeni? Idan ma na nan basu yi maka ba ai a can 6angaren iyayenka ba akwai wasu da bama amfani ake da su ba suna a lullu6e, in ma duk basu yi maka ba a can gidan ɗayan baban naku duk ba akwai motocin da zaka iya amfani da su ba kafin dai ka koma?" Murmushi ne akan fuskarsa ganin kallon da take masa mai kama da na tuhuma, ta ci gaba da cewa, "Ba laifi bane don mutum ya siya abun da ransa ke so, amman a rinƙa dubawa kada don an samu dama kuma a rinƙa yin almubazzaranci, tun da ai kana da motocin a Abuja da can ƙasar ma da kake, ai ina ganin su kala-kala a hotuna da video, har da wata mai suffa kamar ta wasan yara..." Dariya ya saka jin yadda ta fasalta motan ya kuma gane lamborghini ɗinsa take magana,
"....Akwai abubuwa da dama masu amfani da ya kamata a rinƙa yi wanda har da dalilin hakan Allah Ya bada wadatar, duk da na san ana yi sosai." Murmushi ne akan fuskarsa don ya fahimci akan abun da take magana, tambayarsa ta yi yanzu wannan motan zata yi nawa, ya bata amsa da 85m wato miliyan tamanin da biyar, har da ce mata ai ba wata babba bace sosai a cikin jerin avatrs, kai ta jinjina tana ƙara kallon motar ta ce ta ci kuɗinta amman dai a rage yawan son ƙyale ƙyalen duniya a fi maida hankali ga yin zubin da za a ƙwasa a lahira. Gently ya ce, "In sha Allah sweetienah, wannan ma zan ɗan yi amfani da shi ne amman ba nawa bane, Fahad na siya mawa na ga yana son irin motan." Da mamaki hajiya ta kalle sa ta maimaita Fahad ya siya ma wannan motan? kai ya ɗaga mata yana murmushi, wani irin farin ciki ne ya lullu6e ta, tana matuƙar jin daɗin yadda jikokin nata suka haɗa kan su suke kyautata ma junan su, yadda suke taimakon juna ko iyayensu ba su yin hakan, duk da kowanne a cikin iyayen nasu yana hali daidai gwargwado, amman mahaifin Deen ya fi na Fahad arziƙi saidai bai yawan yi masa alkhairi kamar yadda ɗan nasa ke ma ɗan'uwansa Fahad, sai dai ta san hakan na da nasaba da rashin dacen mata da ya yi wadda ta san har da ita ke hana shi yi ma makusantan shi alkhairi yadda ya kamata.
"Ban san ya zan misalta maka irin farin cikin da na ji ba Deeni, ina matuƙar alfahari da yadda kuke ƙaunar junan ku kuke taimakon juna. Allah Ubangiji ya ƙara haɗa kawunan ku ya sa ku ɗore da hakan ko bayan ba ran mu." Hannu ya kai ya rungumo kafaɗarta jikinsa yana murmushi ya amsa mata da, "Amin Ya Rabb. In sha Allah." Tana murmushi ta ce aikuwa ita zata yi ma Fahad wannan babban albishir ɗin, da sauri ya ce mata, "No, I wanna give him a surprise, ka da ki sanar masa cewa nashi ne yanzu." Ƴar harararsa ta yi ta ce, "Ke nan buƙulun goron albishir za ka yi mini." Yana yar dariya ya ce, "Idan wannan ne ni zan baki, ki faɗi duk abun da kike so." tana ƴar dariya ta ce, "To nima irin motan nike so."
"No problem, zan sa akawo maki naki." Sanin da gaske yana iya sakawa a kawo mata ya sa ta yi saurin ce masa, "Ni wasa nike maka, in yi yaya da wannan motan ni da ake tuƙawa, wanda ke a kwai ma sun isa." yana murmushi ya ce, "But yana da kyau ka canza zuwa sabon abu if you have the means, sai ki bada wani da kike da shi." Tana murmushi ta ce ai duk motocin da ake mata amfani da su ba su wani tsufa ba akwai ma wadda ba a daɗe da aka kawo mata ba, ta ce tun da dai ya siya ma angonta hakan ya wadatar an gode ta san kuma zata rinƙa hawa, bayan sun gama ganin motar suka koma cikin gidan.....
_1.jpg)