Abu A Duhu Page 2 by Fadeela Lamiɗo - Abokiyar Hira Novels


https://chat.whatsapp.com/GAA1Q2IaTTBJwFUguUIBtM?mode=gi_t

ABU A DUHU

ADABI WRITER’S ASSOCIATION

Page 2

Da sauri Magaji ya juya ya nufi kofar gidan adaidai lokacin da ta dauki ledan ta take kokarin shiga gidan, cikin kaukausar muryan sa yace  "Ke!"

     Babu alamar ta jisa yaga ta daga kafarta tashi gidan.

   "Ina miki magana kina tafiya?, Ko kina son ki nunamin baki da  tarbiya ne kamar yadda na ke tunani" Ganin da yayi ta kule cikin gidan dole yasa shi yin shiru yayin da bakin ciki ya cika masa zuciya, kasa komawa yayi jin ana sawa gidan sakata.

Daker ya iya juyawa ya koma  motar ya shiga ya zauna tare da kauda idon sa daga gefen da Moddibo ke zaune, Moddibbo ne ya kalle sa yace, "Ta yi magana?" Batare da Magaji ya kalli Modibo ba yace, "Aa, batace dani komai ba"

   "Ka mata tsawa ne ko?" Moddibo ya sake jefa masa tambayar" Kawar da Ido Magaji ya sake yi sannan yace "A'a" Jimmm Modibo ya sake yi sannan ya sake cewa, "Ka koma ka buga gidan, lallai ko wanne hali ake ciki yau ina son in ganta anan a gabana" Batare da Modibo ya gama maganar ba Magaji ya fita a motar, babban rigar sa ya gyara tare da daidaita zaman hularsa sannan ya koma kofar gidan.

Tun kafin tafara jin bugun kofar turaren sa ya fara mata sallama, zaune take bakin kitchen tana kokarin daura girki, cikin sauri ta mike, a cikin ranta take fadin, "Mutanenan ne na ranar nan, me suke nema wurina, me yasa suke bibiya ta" Gaba daya jikinta rawa ya fara, tana jin yadda yake buga gidan, zuwa can taji shiru dan haka ta fara takawa a hankali ta isa zauren sannan tasa hannunta akan kofar tare da zura idonta ta kafar kofar, wasu maza matasa ta hanga zaune bayan motar su biyu, fararene sosai wadda su kafi kama da larabawa, sai dai shadda ce lafiyayya a jikin su babban riga wadda akayiwa ado da aiki irin na zamani, mutun biyu kawai take hanga wadda suke zaune cikin farar shadda, saidai ganin su take tamkar mutum daya ne saboda tsabar kamar da suka yi, magana suke wadda  bata jin me suke fadi, shagala tayi da kallon su bata an kara ba saigani tayi motar ta wuce.

Cikin gidan ta koma ta zauna, gaba daya ji ta yi jikin ta ya mutu, babu wani karfi a jikinta, fuskar mutane nan guda biyu kawai take iya tunawa, cikin ranta take tunani, sudin suwaye? Kuma daga ina suke haka, kuma me suke son ce mata? Iri irin wannan tunanin taita yi har ya dauke ta dogon lokaci dan haka ta kasa girkin, tattara kayan tayi ta ajiye sannan tai alwala ta nufi daki.
Gaba daya yau ta rasa sukunin, komai ne baya mata dadi, fuska iri daya guda biyu sun tsaya mata azuciya, rasa abun yi ya sa ta fara zubar da hawaye Koda dare yayi daker bacci ya iya daukan ta, cikin ikon Allah washegari ta tashi da sauki, duk aikace aikacen gidan ta yi sannan tayi abun karyawa ta kwanta, kasancewar yau juma'a babu islamiya, baccin da bata samu jiya ba shi tayi wannan a lokacin.

Misalin daya ta shi, nan ma sallah ta yi sannan ta zauna tsakar gida, yau daya ta farajin zaman gidan ya dame ta, sosai take sha'awar tayi hira kamar yadda take jin mutane nayi, saidai tana tuna gargadin Innawuro.

Washegari ta kama asabar dan haka ta nufi islamiya domin shi kadai ke debe mata kewa tun bayan data kammala secondry school bata dawowa sai yamma liss, wannan ya matar da ita tunanin data fara sawa ranta akan samarin guda biyu.

                 *****

Yauta kama alhamis dan haka tun safe take dakon zuwan Dada amman ba ita tazo ba sai misalin biyu da rabi ta ji ana buga gidan tare da fadin, "Unaisa taho bude min."

 Jin Muryan Dada ya sata runtumowa da gudu har jikinta na bari ta bude kofar tare da fadawa jikinta.

Rungumeta Dada ta yi cikin nuna so da kauna tace, "Nasan kina ta zuba ido ko?"

"Harna fara tunanin zuwa fa Dada"
"Toh ai gani mu je ciki"  kayan hannunta ta amsa tana kokarin juyawa ne ta hangi motocin yauma a kofar gidan  su ka aje wasu motocin.

Ganin in da take kallon motar Dada ta kalleta tace, "Daura aure ake ne a unguwar?"

"A'a Kamar dai bakin Malam Baba ne." Kallon motocin Dada ta sake yi akaro na biyu sannan tace, "Lallai kuwa Malam Baba kullum kara shahara yake, dubi irin wannan zuka zukan motoci haka, nan gaba ai bazai saurara aikin mu na yakubayi ba tunda irin wanna motoci na masa layi." Juya suka yi suka nufi gidan yayin da Unaisa ke fadin, "Dada waddan nan fah tare suke zuwa sukuma tafi tare, Ina tunanin mutum daya ne mara lafiyan."

 "Lallai kila wani babban mutum ne daya shara, cikin gidan suka shiga yayin da Dada ta cire gyalenta ta rataye kan igiyan shanya sannan ta nufi tabarman da Unaisa ta shinfida masu, abinci data taho dashi ta zuba sannan suka shiga ci tare cikin kwano daya, hira suke sosai suna daf da karasawa Dada tace, "Ina son nai wata magana dake Unaisa." Da saurinta Unaisa ta kalli Dada, Itama Dada tana kallon cikin idonta tace, "Magana ce akan aure..."
Bata kai ga rufe baki ba Unaisa ta juya bayanta tare da hada kanta da guiwa, Dada ce tacigaba da cewa, "Bansan me kike nufi ba, a duk lokacin da nai miki maganar aure sai ki juya min baya, ranar bana sake ganin walwalar ki, da ace Innawuro da Kawu basa zaman lafiya da nace kila wani mugun abun ki ga yanai mata, na fiki sanin halin su dan nafiki zama dasu, sosai nake son ki yi aure, abun dake daga min hankali mutanen unguwar nan, duk wadda ya zo koron sa suke, basa taba bari zancen yai kwari."

Cikin turo baki Unaisan tace, "Ni bakomai Dada taimako na ma suke." Yadda ta yi zancen kasa kasa yasa Dada tace "Me ki ka ce?"

      "Na ce taimakona suke yi."

    Jimmm Dada ta yi tsayon lokaci tana nazarin maganarta sannan tace, "Shikenan na ji, suna taimakon ki tun da suna kore miki manema, duk wadda ya zo yau gobe baya kara zuwa, hakan baya daga miki hankali, har kike iya cewa taimakon ki ake yi, shikenan saiki ta zama babu aure daga nan har a busa kaho, ki kare rayuwar babu miji tunda kina ganin hakan daidai ne." Hawaye Unaisa ke sharewa, kallon ta Dada ta yi tace, "In dai dan na yi miki wannan zancen ne ki barmin kuka, ni ina son naga kin yi aure ne kafin mutuwata kuma tana iya zuwa kowanni lokaci, amma tun da bakiso na bari, inna mutu saiki rayu ke kadai tunda hakan kikafi so"
Cikin shashshekar kuka ta ce, "Baza ki mutuba Dada tare zamu mutu." Dada kallon Unaisa ta yi cike da takaici zuwa can ta yi ajiyan zuciya tare da cewa, "Ba mu zo tare ba ai bare mu mutu tare, ni daya na zo, ni daya zan mutu, dan haka nake son ki kaunaci aure."

"In sha Allahu ni zan fara mutuwa kafin ki mutu, ta ya zanyi aure alhalin ban iya zama da wani ba, ban iya magana da wani ba Dada, bana hira da kowa, kwata kwata mutanen da suke min magana ba sufi a akirga ba, wlh Dada bazan iya magana da kowa ba"
 Lumshe ido Dada ta yi sannan tace "Ba zaki iya magana da kowa ba ko? Na fahimce ki, bazaki iya magana da kowa ba bare a je ga batun zama irin na auratayya ko?" Ba ta kai ga rufe baki ba Unaisa ta mike ta nufi a daki, cikin rufda ciki ta fada kan karamin gado,  bayanta Dada ta bi da kallo, sannan ta yi tagumi ta yi zurfi a tunani, shekaran Innawuro hudu kenan da rasuwa lokacin Unaisa na da shekara sha uku a duniya,  lallai ya kamata ta sauke nauyin dake kanta ta aurar da ita, sukar da mutanen unguwar ke kaiwa akan Unaisa babban abin da ke ,  cikin ranta, mayuyacin abu ne Unaisa tai aure a cikin garinnan, in dai so ake Unaisa tai aure dole ne a yi nisa da ita, tabbatarwan da ta yi tunanin beda wani amfani ya sa ta mikewa domin tasan Unaisa bazata taba yadda a kaita wani gari ba, a hankali ta cire tagumin da ta yi, tare da yin ajiyan zuciya sannan ta mike, mayafinta ta cira akan igiya ta yafa, cikin yanayin dake nuna fushi take tace ta yaye labulen dakin Unaisa ta ce "Ni na wuce." Mikewa Unaisa ta yi da saurin ta rajawo  nikabinta ta daura sannan tai saurin bin bayan Dada.

Ita ko Dada tana saka kafar ta kofar gidan ta hada Ido da nawasu maza guda biyu zaune saman mota, ganin sun kalleta tai saurin dauke idonta tare da mayar dasu kan Unaisa ta na fadin "Koma abinki ban so rakiyar ta ki." Bude baki ta yi da nufin yiwa Dada magana itama suka hada ido da su, daya daga cikin su ne ta hangesu a mota shida wani irin sa sak, wani harara taga ya zafga mata me cike da zallah tsana dan haka ta maida idonta ga dayan shikam kallonta ya ke yana murmushi dan haka tai saurin sakawa gidan kwad'o sannan tai sauri ta zura hannunta cikin na Dada.

 "Dama baki fito ba Unaisa, domin bana son a dinga fahimtar ke daya ce agidan."

     "Ba komai Dada insha Allahu."

"Allah yasa amman duk da haka ki koma gida na gode." Sallama suka yi, sannan ta juyo, daman ba wani nisa tayi ba, matashin nan ne ta hango fuskarsa dauke da masifa yana sauka daga samar motan.

    Yi tayi kamar bata ganshi ba ta nufa kofar gida gadan gadan, ganin matashin ta yi ya rigata isa kofar ya tsaya, daga cikin nikabin take kallon shi sama da kasa, acikin ran ta take fadin, "Ban da a binka bata jikinka zaka yi, kana sanye da kayan alfarma me ya kai ka hawa dandamalin gidan mu?" Kallon ta bishi da shi, kafar sa sheki take hakama takalmin sa tamkar ba kasa ake takawa dashi ba, da ace tana da damar yi masa magana da ta tambaye shi me yake nima wurinta dahar yake kokarin bata kata kayan sa.

Daga can nesa taja ta tsaya ta cikin nikabi take kallon irin kallon wulakancin da yake mata, juya wa ta yi ta kalli motocin bata iya hango kowa sai mutun daya da shima ya sauko daga saman motar yanxun, cikin wani irin murya taji matashin yace, "Ki karaso kina bata mana lokaci, koda yake bayau kika fara ba." Ganin bata da niyar matsowa ya sashi ya sake fadin, "Wai ko dai kurma ce ke?" Wannan karon ma babu alamun zata amsa dan haka ya sake cewa, "Idan kika bari na iso wurin daukan ki zanyi cak in direki agaban shi." Zoro ido ta yi yayin da taga yana kallon cikin idonta sannan Yana tahowa gareta ahankali

       Shikuwa matashin  yana tahowa ne yana kallon gefen idon ta da yai tsananin nuna hasken fatar ta, tsintan kansa yayi dason ganin fuskar ta dalilin ganin kwayar idonta be yi kama dana hausawa ba, acikin ransa yake fadin, "Meyasa take boye fuskarta kodayaushe? Daga idon sa yayi ya hange Modibo yana zaune cikin mota idon sa akansu, meye sa Modibo ya nace sai ya yi maganq da yariyar, duk da kasaita irin tasa? Ganin babu me amsa masa ya sauke idon sa akan yariyar yana me ji a cikin ransa shi ba magana ya ke son yi da yariyar ba Fuskanta kawai yake son gani.

 Itako Unaisa babu abun da ke mata yawo akai  sai ji da ta yi yace zai dauketa ya  dire ta agaban shi, tunani ta shiga yi aranta "Shin waye shidin? Me zasu min ko me zai min?" Yin wannan tunanin yasa ta fara ja da baya, daga can bayanta ta ji wani irin murya me sanyin sauti tana fadin, "Magaji rike ta karka barta ta gudu' Jin haka yasa Unaisa ta kwasa a guje yayin da Magaji ya rufa mata baya, sai dai ya na tsallaka kwatar ya tsaya yayin da ya hangi yariyar har tayi nisa.

 Komawa cikin motar ya yi yana ya tsuna fuska, yayin da ya samu wannan matashi da suke zaune tare yanata dariya dariya.
Shikuwa Modibo da ke zaune a bayan motar tsaki yayi sannan ya duba agogo yana fadin, "Mu je, bi bayan ta karta bace mana." Wani irin kallo Magaji yaiwa Modibo ganin in da yake ciccin magani a hankali ya bama driver umarni dan haka suka tashi jerin motocinsu cikin kokarin bin bayan ta...

Fadila Lamido...✍️

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post