ACikin Rayuwa page 21 Complete na Zainab Bature


 _Bossladieswriters_






_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don karanta littafin daga farko, da kuma abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q



WhatsApp group


https://chat.whatsapp.com/Cw99mqDlyMpKRhkRMnHqWZ?mode=wwt




  *_✨A CIKIN RAYUWA✨_*



    

   _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ 



_ZAINAB BATURE_



   

   _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._





21



Washe gari da safe Salma ta fito bayan ta gama yin shirin tafiya islamiyya, a bakin baranda ta tsaya tana yi ma innarsu sai ta dawo, fitowa innar ta yi tana murmushi ta ce, "Za a tafi?" Kai ta ɗaga mata alamar eh, da yake lokacin da suna yin karin kumallo Salma ta ba innarsu labarin wayar su da aunty Kubra jiya da daddare hakan ya sa innarsu ta ce, "Idan kika dawo sai in taya ki ki kwance kan ki je a wanke makin ko?" Ƴar dariya Salma ta yi ta ce to, sai kuma ta ce, "Ya maganar zuwa kasuwar? Ko ki bani kawai da an tashi sai in wuce ba sai na yi wahalar dawowa ba." ɗan jimm innarsu ta yi ta ce, "Ko dai a bari sai bayan kwana biyu sai a yi awaran?" Da sauri Salma ta ce, "A'a innar mu kawai ki kawo a siyo waken, shike nan don an bamu kuɗi sai mu daina yin sana'a? Ai kuɗin za su ƙare ko." Kai ta gyaɗa ta ce  to bari ta bata, ɗaki ta koma bada daɗewa ba ta fito tana riƙe da kuɗi ta bata, bayan ta faɗi mata abubuwan da zata siyo ta ce mata sauran kuɗin ta yi amfani da su ta siya abun da take so, da sauri Salma ta ce, "A'a innarmu ki bar su, ai aunty Kubra ta ce zata turo mani kuɗi, ki yi amfani da waɗannan, na san ma duk a hidiman gida za su ƙare." Yar hararar wasa ta yi mata, "Ke ni ki amsa, na Kubra daban nawa daban, kuma bake kika samo mana su ba." Ƙin amsa ta yi tana noƙe kai tana ce mata ta bassu don Allah, Sagir ne ya shigo har zai nufi hanyar banɗaki ganin su ya fasa ya nufo su, 


"Wai Salma wasan da nike yi dake ne ya sa kika fara raina ni? Ya ina baki abu zaki ƙi amsa, kuma dama ba kin ce zaki siyo fara ba ki soya, to ba sai duk ki haɗa ki siyo ba." Innarsu ta faɗa da ɗan daure fuska, yamutsa fuska ta shiga yi tana marairaice mata tana faɗin ai tana da kuɗin da za ta siyo farar, 


"Ah lalle yarinyar nan gatan da kike samu ya yi yawa wllh, wato kuɗi ma ake baki kina ƙin amsa. Ni innarmu don Allah ki bani ina so..." Janye kuɗin ta yi ganin ya miƙo hannu ta ɗan ɗaure masa fuska, ya sake cewa, "pls innarmu wllh ina cikin buƙatan kuɗi, kuma dama baki bamu salalarmu ba a cikin kuɗin da Nuree jr ya bada." Wani kallo ta masa ta ce, "Ku da kuka ci gasan kana nufin baku samu komai ba a wurinsa?" 


"Ai ba a gama ba gaba ɗaya, na san sai daga ƙarshe zamu samu kyaututtuka." ta ce, "To amman wace buƙatan kuɗi ce da kai? ina bada daɗewa ba ka zo ka ce in cika maka kuɗi zaka siya sababbin kayan ƙwallo da takalma na ɗauka na baka? Bayan su wace buƙata ce kake da ita? Koda ka ga ina bata itama na daɗe rabon da in bata kuɗi ta siya abun buƙata kuma ba tambaya ta take ba." Ɗan sosa kai ya shiga yi ya ce mata shi dai don Allah ta bashi ba sai ta ji buƙatan ba, Salma ta ce, "Innarmu kar ki bashi, yanzun haka wannan Fa'izar zai kashe ma su, kuma wllh wahalar banza kake yi don wannan yarinyar ba samunta zaka yi ba, su da suna gama makaranta gidansu ake yi masu aure, kuma mate ɗita ce nan da shekara ɗaya zata gama, ko kana tunanin zaka iya aurenta zuwa lokacin?" Hannu ya ɗaga zai make ta innarsu ta dakatar da shi cikin ɗaga murya ta ce kada ya sake ya ta6a ta ai gaskiya ta faɗa, "Ni dai innarmu ki bani don Allah, ƙarya take mani don ni wannan yarinyar tuni ma na rabu da ita." Ta6e baki ta yi ta  ciro dubu biyu ta miƙo masa ya amsa yana faɗin duka dubu biyu za a bashi, ta miƙo hannu tana faɗin, "Idan baka so to ka bani abu na, duk kuɗin ba a hidiman gida za su ƙare ba, babanku ma na bashi wasu a ciki." Tura kuɗin ya yi cikin aljihun wandonsa, ya kalli Salma cikin ɗaure fuska ya ce, "Munafuka yar hana ruwa gudu kawai, wllh saboda mugun halin ki har na fara ji na ƙosa ki yi aure ki bar gidan nan." Tana dariya ta ce, "Ka sha kuruminka man Sagir, bada jimawa ba ma ai zan tafi makaranta Kaduna." Yana hararanta ya ce, "Ai wannan still ba hutawa muka yi ba tun da za a rinka yi maki buƙatu kuma za ki rinƙa dawowa, amman idan kika yi aure shike nan ba ruwan mu da ke, duk nauyin ki ya koma kan mijinki sai kuma in kin kawo ziyara." Ɗan girgiza kai Salma ta shiga yi tana ɗan murmushi ta ce, "Allah Sarki Sagir, ka ga ni har zullumin abun da zai saka in rabu da ku nike yi, ba komai, amman ka rubuta ka ajiye wallahi duk ranar da na bar gidan nan da sunan aure sai ka yi kuka da idanunka." Tsoki ya buga ya nufi hanyar banɗaki yana faɗin Allah ya kyauta ya yi kuka don sun rabu da ƙaya, innarsu dake murmushi ta ce mata ta rabu da shi, da ƙyar Salma ta amsa kuɗin amman sai da ta rage ta mayar mata da wasu suka yi sallama ta tafi.



Wararen ƙarfe sha biyu saura Salma ta nufi kasuwa bayan ta taso daga  islamiyya, a nutse take tafiya a gefen hanya tana sanye da dogon hijab ɗin islamiyyarta, daidai lokacin da ta zo ƙarshen hanyar zata hau babban titi ta hango mota na tahowa ta hanyar da take, hakan ya sa ta dakata don motan ta wuce, lokacin da motar ta ƙaraso saitin ta sam Salma ta kasa ɗauke idanunta akan motar, bama ita kaɗai ba duk idanun mutane na akan motan, hatta waɗanda ke a saman ababen hawa kallon motar suke, a cikin rai Salma ke faɗin, "Wannan wata irin mota ce! Amman dai ta haɗu sosai...." Ita tun da take ma bata ta6a ganin mota irinta ba, ɗan gaba da ita motan ta tsaya da alama mai motan na jiran ababen hawa su gama wucewa ne ya hau kan babban titin, sam ba a ganin wanda ke a ciki hakan ya ɗarsa ma mutane mamakin waye mamallakin haɗaɗɗar motar wadda mafiya yawan mutanen garin basu ta6a ganin irinta ba, a maimakon motar ta tsallaka sai gani Salma ta yi ta ɗan yo baya hakan ya sa ta yi saurin ƙara matsawa gefe don ta ba motan wuri, sai da aka ɗan ɗauki lokaci sannan glass ɗin ta ya fara sauka ƙasa a hankali, bugawa ƙirjin Salma ya yi damm! lokacin da idanunta suka yi tozali da wanda ke a mazaunin driver, nan take ta dabarbarce ta shiga motsa baki don bata yi zaton shi zata gani ba, kallonta ya yi suka haɗa ido ta shiga kikkafta nata, da kai ya yi mata alamar ta zo, tamkar wadda babu laka a jikinta haka ta ɗan matsa sai dai bata yadda ta yi saiti da shi ba, "Ina..kwa...wuni." Ta faɗa cikin dabarbarcewa, kai ya ɗaga kawai ta sunnar da kanta ƙasa, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ta ji ya ce, "Where are you going to?" Da sauri ta ɗago ta kalle shi sai ka ce bashi ya yi maganar ba, da ƴar rawar murya ta ce, "Kasuwa aka aike ni..." Shiru ya ɗan yi tare da ɗauke idanunsa, ƙasa-ƙasa ta ji  ya ce, "Get in to the car.." Ta wani zaro ido sai ka ce wadda aka faɗa ma wani mugun abu, kokonto ta shiga yi na abun da ta ji ya faɗa haka ne ko kuwa dai kunnuwanta ne suka jiye mata ba daidai ba, after some seconds ya yi mata wani kallo ya ce, "Baki ji maganan da na yi ba?" Da sauri ta ce, "Cewa ka yi in shigo motan?" Kai ya ɗan ɗaga mata alamar yes, sumi-sumi ta zagayo ɗaya bangaren, sai da ta ɗan yi tunanin ina zata shiga tsakanin gaba da baya, ƙofar baya ta buɗe kafin ta shiga ta ɗan ɗago ta kalli mutanan dake a area ɗin, sai da gabanta ya ƙara bugu ganin gaba ɗaya idanun mutanen wurin na a kan ta, ruɗewa ta yi da ganin yadda ake kallonta da sauri ta kama handle ɗin ta ja ya buɗe ta shiga bugun ƙirjinta na ƙara tsananta tamkar wadda ta aikata wani laifi, wani irin ni'imtaccen sanyi ne tare da ƙamshi mai kwantar da zuciya suka tarbe ta, bin cikin motan ta yi da kallo at the same time al'ajabi ya bayyana akan fuskarta, ita dai ko a film bata ta6a ganin mota haka ba balle a zahiri, ɗaga kanta ta yi sama ta ɗan waro idanu ganin yadda take ganin kanta tamkar tana kallon madubi, tana cikin kalle-kallen ta sauke idanunta a kan madubin gaban motan karaf suka haɗa ido, da sauri ta sunne kanta ƙasa cike da jin kunya, duk yadda Salma ta so ta kama kanta ta kasa a hankali take ci gaba da bin cikin motan da kallo, tafiya suke suwet kamar ba a mota ba don ba wata ƙara ko irin gumin cikin mota da zaka ji wani lokacin haɗe da warin fetir, sauke idanunta ta yi akan screen ɗin da ke a kusa da sitiyarin motan, wani sabon mamakin ne ya kamata ganin duk abun da ke faruwa a bayansu ana gani ta cikinsa kamar vedio, "I don't know the place, zaki nuna mani..." Da sauri ta kai idanunta kansa jin ya yi magana sai dai bata ji abun da ya faɗa ba, daga yanayin kallon da ya ga tana mashi ta cikin madubi ya gane bata fahimci mi ya ce ba, haɗa ido suka yi ta madubin calmly ya sake faɗar abun da ya faɗa ta ɗaga mashi kai alamar toh, tafiya kaɗan suka ƙara suka zo roundabout, da sauri ta ce mashi da an ɗan wuce round ɗin ne wurin, bayan ya yi parking ya bi wurin da kallo, hannu ta kai za ta buɗe kofar saidai in da ta yi tunanin nan ne ake buɗewar ta ta6a amman kofan ta ki ta buɗe, juyowa ta yi da niyyar yi masa magana daidai lokacin shima ya juyo idanunsa suka shiga cikin nata ya ce mata, "But nan kasuwa ne?" Kikkafta idanu ta shiga yi ta ce, "A'a, amman da na ɗan ƙara gaba kasuwan take, a zagaye take mota bata shiga sai dai a aje a bakin hanya." nodding kai ya yi tare da juyawa, ganin bai gane ta kasa buɗe kofar ba ya sa innocently ta ce, "Ban san ya zan buɗe kofar ba..." Haɗa ido suka yi ta mirror ta yi saurin sunnar da kai, bata san ina ya ta6a ba kawai ta ji kofar ta yi wani ɗan sauti har sai da ta ɗan tsorata ta yi saurin kallon ƙofar ta ganta a buɗe, har zata fita ta juyo a hankali ta ce, "Na gode.." Kai ya ɗaga ba tare da ya kalle ta ba, tsaye ta yi bayan ta fito tana kallon motar ya ja ya tafi, sai da motar ta 6ace ma ganinta sannan ta ankare da irin kallon da mutane suke yi mata, da sauri ta juya ta fara tafiya ta gefen hanya, yayin da a cikin ranta take ta jinjina haɗuwar motar, ta raya a zuciyarta ba tantama ita ce motar da Sagir ya zo yana masu santi, ita cikin motar ya fi yi mata kama da irin cikin private jirgi da take ganin hoto , "Anya ba jirgi bane aka yi da suffar mota?" ta yi tambayar a ranta, ƙarshe zuciyarta ta yanke hukunci da alama ma hakan ne, maida akalar tunaninta ta yi kan yadda akai har ya ganta ya gane ta ya tsaya ya ɗauke ta, tunowa ta yi da screen ɗin nan dake nuna mashi komai dake faruwa a bayan shi ta raya ta san ta hakan ne ya ganta, tana ta tunane tunane har ta iso kasuwar. Bayan Deen ya isa gidansu Fahad ya yi parking motan, kai tsaye cikin gidan ya nufa, Sadeeya na zaune tana latsa waya ta hango shi ya shigo, miƙewa ta yi tana murmushi ta nufe shi tana masa welcome, hannunta ya kama bayan ya amsa suka dawo wurin kujerun, Khaleel dake kwance shima yana latsa waya ya miƙe zaune da murmushi ya ce, "Ya Deen sannu da zuwa." Da murmushi ya amsa mashi yana kokarin zama a saman 2 sitter Sadeeya ma ta zauna gefensa, tambayar su Binafa ya yi Sadeeya ta bashi amsa da suna islamiyya sai yamma, momy ce ta ƙaraso wurin su da fara'a ta ce, "Son, an shigo." Amsa mata ya yi kafin ya gaishe ta ta amsa tare da zama, "Ya hajiya da gajiyan ɗanin mota." Yana murmushi ya bata amsa da tana gida tana gaishe su, "Da jigunannar motar ka zo?" Sadeeya ta tambaya, ƴar dariya ya yi jin yadda ta kira motan ya ce mata eh, miƙewa ta yi tana faɗin bari ta je ta yi hotuna dama jiya don dare ne ya sa bata yi ba, miƙa mata makullan motan ya yi ta amsa da sauri tare da faɗin yauwa ta gode, kallon Khaleel ta yi ta ce ya zo su je ya yi mata hotunan ya amsa da toh tare da miƙewa, "Kafin ki tafi yin packaging ɗin ki fara samo mashi abun da zai ci." Momy ta faɗa tana murmushi, Sadeeya ta yi dariya tare da faɗin, "Kai momy, ai ba packaging bane tun da dai motan mallakinmu ce." Kallon Deen dake murmushi ta yi ta ce breakfast zata haɗo mashi kafin a gama abinci, ya ce mata no baya jin yunwa ya yi breakfast, ta ce to bari ta kawo mashi ko lemu shima ya ce ta basshi ta je, momy ta ce, "Son ka bari ta kawo maka wani abu mana kafin a ƙarasa abincin." Calmly ya ce mata yanzu baya jin yunwa a bari sai an gama abincin ta amsa da ok, bayan tafiyar su Sadeeya ya tambayi momy ko daddy na nan ya je ya gaishe shi, ta ce, "Eh yana nan, suna tare ma da Fahad a can part ɗin sa ina tunanin wani aikin suke yi." Miƙewa ya yi ya ce bari ya je part ɗin ya gaishe da shi ta amsa masa da ok, bin shi da kallo momy ta yi bayan ya nufi bangaren daddyn fuskarta da murmushi, tana son yaron saboda yana da hankali da natsuwa, duk da irin ɗaukakar da ya samu sam bai yada nasa ba ko ya canza masu, sam bai ɗauko ɗaya daga cikin halayen mahaifiyarsa ba, ta6e baki momy ta yi tunowa da irin munanan halayen mom Jameela, ba don ita ɗin tana da kyakkyawar zuciya ba ai ko kallon Deen ba zata yi ba balle ma ya ga murmushinta duba da yadda mahaifiyarsa ta yi maltreating mata yaro lokacin da yana wurin su. Da sallama Deen ya shiga  falon daddy, a tare suka kai idanunsu kan ƙofa, da murmushi suka amsa masa ya ƙarasa ciki, daddy na zaune a saman kujera mai mazaunin mutum biyu, Fahad na zaune daga gefensa a saman carpet, system ce a gaban Fahad da wasu takardu a gefe, "Barka da zuwa son." Daddy ya faɗa idonsa akan Deen da ya zauna a ƙasa gefen Fahad, da murmushi ya ce, "Yauwa daddy, ina wuni." Amsa mashi ya yi ya tambayi hajiyarsa, kallonsa Fahad ya yi yana murmushi ya ce, "Sannu da zuwa..." Ya ɗaga masa kai, bayan shiru na ɗan lokaci dad ya kalli Fahad ya ce, "Ka ce gaba ɗaya lissafin ya kama nawa?" amsa ya bashi ya ce, "Abun da ya bada 135m." Kai daddy ya jinjina sai kuma ya ce, "Ka saka har da na waɗanccan kayan da na fada maka?" Kai Fahad ya jinjina ya ce yes, daddy ya jinjina kai tare da komawa ya jingina bayansa da jikin kujera yana murmushin sa na dattako ya ce, "Alhamdulillah, saura mu ga abun da kuma wannan damunar zata kawo mana. Allah Ya saka mata albarka." A tare Deen da Fahad suka amsa da Ameen. "Son, ka zo muna ta lissafi, haka hanyar samun namu ya koma tun da yanzu ba aikin gwamnati, wannan ne ya koma aikin office ɗin nawa." Ya ƙarasa yana ƴar dariya, shima Deen faffaɗan murmushi ne akan fuskarsa ya ce, "Allah Ya ƙara sama nema albarka daddy." ya ce, "Amin my son, Ya saka ma nemanmu baki ɗaya. Dama haka abun yake kowa da kalar hanyar samun sa, ga ɗan'uwanka nan shi rashin lafiyar mutane ne tasa hanyar samun, sa6anin kai kuma nishaɗin mutane ne naka hanyar samun." Gaba ɗaya faffaɗan murmushi ne akan fuskokinsu, 


 "Kasuwanci yana da daɗi sosai, musamman idan Allah Ya riƙe maka, ba don kasuwancin nan da muke yi ba watakil yanzu abun da muke samu matsayin pension ba lalle ya iya riƙe mana iyali ba a yadda rayuwar ta yi tsada..." Ya ɗan dakata su Deen suka jinjina kai alamar tabbatar da gaskiya ne zancensa, ya ci gaba da cewa, "Shi ya sa yana da kyau bayan aikin gwamnati mutum ya samu wata kasuwa yana yi, hakan na da amfani sosai musamman a lokacin da ba aikin. Idan kuma kasuwancin kaɗai mutum ke yi yana da kyau ya bullo da wasu hanyoyi da dubaru da za su inganta sana'ar tasa, ya zama a koda yaushe ana tafiya da shi...." Dakatawa ya sake yi yana shafa sumar gemunsa dake haɗe da ƴar furfura, "Son, na san bayan tamolan baka rasa wata kasuwar da kake yi ko, kamar yadda na ga yawancin yan ƙwallo zaka ga suna wasu kasuwancin daban-daban." Deen ya ɗaga kai with calmness ya ce,"Yes daddy, ina da hannayen jari da wasu kamfuna daban-daban, sannan akwai wasu hanyoyin da muke samu da so da yawa." Kai daddy ya jinjina, "Ma sha Allah..." 


Gyara zama Deen ya yi ya ce, "Daddy idan ba damuwa dama ina son neman shawara a wurin ka." Ɗagowa daddy ya yi ya fuskance shi da kyau ya ce, "To Allah Ya bani ikon baka mai amfani." Amsawa ya yi da Amin kafin ya ce, "Ina son buɗe company ne a nan, shi ne nike son ka bani shawara abun da kake ganin zai samu kar6uwa kuma zai kawo ma mutane sauƙi." Jinjina kai daddy ya yi tare da yin shiru alamar yana nazari, after few minutes ya gyara zamansa tare da ɗan yin gyaran murya ya ce, "To a ganina cikin abubuwan da za su samu karbuwa idan aka bude companyn su akwai abinci, wato kamfanin da ya danganci sarrafa kayan abinci tunda shi wannan ba shi da wani lokaci da za a ce ba a tafiya da shi, saboda abinci abu ne wanda ake buƙatarsa sosai a koda yaushe. Sannan buɗe company da ya danganci abinci a nan za a samu sauƙin tafiyar da shi duba da yadda muke da albarkar noma a nan, akwai kamfuna da dama dake sarrafa abinci ciki da wajen nijeriya waɗanda a nan suke siyan kayan da suke sarrafawa. Ka ga dama an ce wai da arziƙi a garin wasu gara a naku, a nakun ma a cikin gidanku, idan namu ya buɗe kamfanin ai ba buƙatar siyar ma wasu kayan amfanin gona ke nan." Gaba ɗaya suka yi ƴar dariya, bayan shiru na ɗan lokaci ya ci gaba, "Sai abu na biyu da nike tunanin idan aka buɗe kamfaninsa zai samu kar6uwa shine kamar textile ko kayan sakawa, ka ga mu nan a arewa bamu da kamfuna irin haka, yawanci a kudu ake da su wasu kayan ma masu inganci sai dai a shigo mana da su daga ƙasar waje, kuma ka ga suma yawancin abubuwan da suke sarrafawar wasu duk a nan suke samun su, kamar auduga da sauransu. To ina ga cikin waɗannan biyun duk wanda aka yi zai samu karbuwa, kuma zai kawo sauƙi da ci gaba a arewa." Kai Deen ya jinjina alamar gamsuwa, Daddy ya ce "Sai ka natsu ka ga wanda ya yi maka, wanda kuma nauyin aljihunka ko in ce account ɗin ka zai iya yi." Ya ƙarasa yana ƴar dariya, Deen yana kallon daddyn da murmushi ya ce, "Zan duba duka in sha Allah." Dan waro ido daddy ya yi ya ce, "Duka son...!Hakan ba ƙaramin shiri yake buƙata ba musamman na kuɗi." Still da murmushi a fuskarsa ya ce, "In sha Allah ba zai gagara ba, ko ba duka ba a lokaci guda." Jinjina kai daddy ya yi, "Ma sha Allah, Allah Ya taimaka Ya tabbatar da hakan. In sha Allahu nima ba za a barni a baya ba zan bada duk wata gudunmawa domin tabbatuwar hakan idan Allah Ya nuna mana, kuma muna daga cikin masu saka hannayen jari, tun da muka ma saka ma wasu balle namu." Duk murmushi ne akan faces ɗin su, Deen ya dan rankwafar da kai ya ce, "Thank you daddy..."


"Fahad kai ya maganar ginin asibitin naka?" Kallon daddy ya yi da murmushi ya ce, "Tana nan daddy, dama na bari in shirya sosai yadda aikin ba zai delay ba idan aka fara, but...jiya Deen ya ce we should collaborate on it." Kallon Deen ya yi ya ce, "Haka ne son?" Kai ya jinjina ya ce eh, daddy ya ce, "Hakan ya yi kyau, amman ka fara tuntu6ar iyayenka kan hakan." Shiru Deen ya ɗan yi a ransa yana raya ya san ko da mahaifinsa ya amince to mom ɗinsa ba zata ta6a amincewa da hakan ba, kallon daddy ya yi ya ce, "Daddy tun da kai ka sani ai duk ɗaya ne." Murmushinsa na dattako ya yi mai nuni da jin daɗin maganar Deen ya ce, "Duk da haka son, suma suna da hakkin ka sanar masu ko don ka samu sakawar albarkar su." Amsa masa ya yi da toh, kamar daddy ya san abun da Deen ya saƙa a ransa ya sake cewa, "Ka sanar da su before a fara gudanar da aikin don ka ji miye ra'ayin su a kai." Shiru Deen ya ɗan yi don a yadda ya yanke kawai sai bayan an gama gaba ɗaya aikin asibitin zai sanar da su, slowly ya furta"Okay daddy." 


"Allah Ya ƙara saka albarka a dukkanin abun da muka sa a gaba, nima da na ce ma Fahad filin da na bashi matsayin bashi ne idan komai ya kammala aiki ya kankama zai biya ni koda a hankali, a yanzu na janye batun bashin na mallaka maku shi kyauta matsayin tawa gudunmawar, sai ku yi haɗin gwiwa wurin aikin ginin, zuwa a kammala mu gani idan da gudunmawar da zamu ƙara baku." A tare suka haɗa baki wurin yi masa godiya da adduar Allah Ya ƙara girma da lafiya, bayan ya tambaye su ko akwai wani abu duk suka ce masa a'a ya sallame su, bin su da kallo ya yi yayin da suka nufi ƙofa, a ransa yana matuƙar jin daɗin haɗin kan su, suna tuna masa lokacin da suna matasa shi da mahaifin Deen, haka suke kansu a haɗe yake komai za su yi sai sun tambayi shawaran juna, sa6anin yanzu da komai ya canza a tsakanin su, duk da daddyn bai bari hakan ya zame masa damuwa ba, ya saka a ransa cewa kowa yana da iyalin da zai iya yin shawara da su. Bayan sun baro part ɗin daddy upstairs suka nufa zuwa part ɗin Fahad, suna fara taka staircases Sadeeya da ta shigo cikin falon ta kira sunan Deen, hakan ya sa shi dakatawa yana jiran ta ƙaraso, tana washe baki ta miƙa masa wayarta ta ce, "Duba ka gani don Allah yadda hotunan suka ɗauko, kuma packaging ɗin nawa ya yi, motan ta hau da ni sosai Allah..." Ta ƙarasa maganar tana dariya, Kallon hotunan ya shiga yi yana murmushi, da gaske sun yi kyau dama ga wayan tata iphone ce, bayan ya gama kalla ya ce, "Yakamata ai snapping naki ai kina driving yadda za a fi yarda naki ne." Ya faɗa yana ƴar dariya, ɗan waro ido ta yi ta ce bata yi gigin hakan ba don gani take kaman ba zata iya driving motan ba, miƙa mata wayan ya yi ya ce lafiya lau zata iya tuƙa ta mana ba ta iya driving ba, ta ce a'a gara dai idan ya fara nuna mata, ci gaba da hawa matattakalar ya yi yana faɗin ok idan ya fito zai nuna mata lokacin tuni Fahad ya wuce ya bi bayansa.....






       *_ZEELALUH_*✍️

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post