_Bossladieswriters_
_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don karanta littafin daga farko, da kuma abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_
https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_
_ZAINAB BATURE_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 20
Wararen ƙarfe ukkun rana Fahad ya dawo gidan hajiya, don bayan gama gasar ɗazun wanda da shi aka yi ta gida ya wuce ya shirya don sun yi da Deen da yamma zai je kai ma manyan garin ziyarar gaisuwa, sosai ya yaba da sabuwan motan Deen da ya iske an kawo, a ɗakin Deen suka zauna suka ɗan ƙara hutawa, ana gama sallar la'asar suka yi shirin tafiya, wani ɗanyen farin voile ne Deen ya saka da ya matuƙar amsar jikinsa, da ƙananun kaya zai saka hajiya ce ta kawo masa kayan ta ce manyan kaya yakamata ya saka, kansa ya faka sumarsa baya ba tare da ya saka hula ba don takura masa take yi duk da hajiya ta nemi ya sa hulan ya ce mata sai sun isa, shima Fahad farar shadda ce a jikinsa ya yi kyau sosai sai sakin ƙamshi suke yi, harabar gidan suka fito da wasu abokan su guda biyu da za su je tare , motoci ukku ne jere da za su yi tafiyar da su, ɗaya Deen da Fahad suka shiga, sai mota ta biyu ta abokan nasu ce, sai ta ƙarshe wasu daga cikin manya ne a harkar ƙwallon garin tare da ƴan jarida da suka zo da su, daga ƙarshe motar jami'ai ce da za su yi escorting na su, a jere motocin suka fita daga cikin gidan suka hau hanya duk idanun mutane a kan su, farko gidan ɗan majalissar jaha suka fara zuwa wanda yake a gari ya zo weekend, daga nan gidan chairman ɗin garin suka je, daga ƙarshe suka wuce fadar sarkin maskan Katsina hakimin Funtua, wanda da mahaifin kakansu ambasada da mahaifiyar hakimin yaya da ƙanwa ne, sannan hakimin shine mahaifin mommynsu Fahad. Duk in da suka je sun samu kyakkyawar tarba tare da nuna jin daɗin ziyarar ta Deen, sun yi hotuna tare da bashi lambobin yabo, shima kuma ya ba wasu kyautar jersey daga bisani suka dawo gida, nan da nan hotunan ziyarar tasa suka karaɗe shafukan sada zumunta, mutane na ta yabon halin kirkin Deen wasu kuma suna roƙon yaushe zai kawo masu ziyara suma.
Bayan sallar isha su Salma na zaune a tsakar gida da yake yau bata yi awara ba, suna cin abinci da ita da innarsu da su Imrana,
_"Duniyar nan sai da kuɗiii.. Allah Ka bamu kuɗɗiii...."_ Muryar Sagir ce ta karaɗe tsakar gida ya shigo yana rera waƙa, "Sallamar ke nan Sagir?" Innarsu ta tambaya, sai da ya zauna a bakin tudunkar baranda ya ce, "Bari innarmu, an gama tashin kaina ne qur'an, Allah dai ya yi mana arziƙi wllh dole tsiya ta ji kunya." Tana murmushi ta amsa da Amin Allah Ya bada arziƙin mai amfani, bayan ya amsa da Amin ya ce, "Wato wata arniyar mota ce Nuree Jnr ya faso da ita ɗazun, motar avatar ce wadda ake ma caji, wato innarmu sai kin ga motar nan...Innalillahi! Wallahi tallahi arziƙi ya yi, duk kuma wanda ya ce bai yi ba munafuki ne, idan ba aikin arziki ba an ce ɗazun nan aka kawo mashi motan, kuma wllh ta yi kusan miliyan ɗari." Da mamaki innarsu ta maimaita miliyan dari! Sagir ya gasgata mata haka ne. "Amman da ka ce caji ake mata kamar wai yadda ake ma waya caji?Sagir ya ce, "Eh mana, caji ake mata, dama ai an yi keke mai caji da mashin yanzu ga mota ma an yo." Imrana ya ce, "Innarmu bana baki labarin mashin mai caji ba wanda aka siya ma wani ɗan bokon mu, wllh nima ina son a siya mani irin mashin ɗin."
Sagir ya ce, "Tabb, lallai yaro waye zai siya maka wannan mashin ɗin da ya yi kusan miliyan ɗaya, idan ba kuɗin shinkafar da ake siya mana muna ɗan yi ma talauci barazana kake son a tattare a siya maka ba." Tura masa baki Imrana ya yi, innarsu da ke murmushi ta ce Allah zai buɗa a siya masa,
"Ka sha kuruminka Imrana, ka taya ni addu'a in sha Allah na zama nurse na fara aiki in dai ba a siya maka ba ko ya kai nawa ni zan siya maka." Kai ya ɗaga ma Salma da ta yi maganar, Sagir ya ce, "Sai ka ce zama nurse ɗin wata tsiya ake samu zaki wani cika ma mutane baki, ni zuwa lokacin in sha Allahu ai na sha kwana, irin mashin ɗin fin guda goma ma sai na siya masa, amman ko da ina da halin ma ba zan siya ba tun da ya iya yi ma mutane rashin kunya don uban shi." Wani kallo Imrana ya jefe masa bai dai ce komai ba, a haƙiƙance Salma ta ce wllh in dai har ta fara aiki matsayin nurse siyan wannan mashin ɗin ba zai gagare ta ba, innarsu dai nata bin su da murmushi sam basu gajiya da shan chapter. Bayan sallar isha Deen da Fahad suka fito da hajiya don su zaga gari a sabuwar motan, daga baya suka wuce gidansu Fahad, daidai lokacin da Deen ya faka motan a cikin gidan sai ga daddynsu da sauran yara maza sun dawo daga masallaci, cike da farin ciki yaran suka tarbi kakarsu haka ma daddynsu ya ji daɗin ganin mahaifiyar tasa sosai, bayan sun gama gaisawa hajiya na murmushi ta ce, "Sabuwar amarya Deeni ya yi shi ne aka fito da ni ɗani." Kai daddy ya jinjina gaba ɗaya idanunsu na akan motar tun bayan da suka shigo dama ta ja hankulansu, "Ma sha Allah son, motar ta yi kyau sosai. Kamar avatr ko?" Kafin Deen ya bashi amsa Khaleel ya yi saurin cewa ita ce, hajiya ta ce, "Ni ai ban ma san motan ba, sai yau na fara ganin irinta." Daddy na murmushi ya ce mata ba a daɗe da aka fara yayin ta ba a nan, hajiya ta sake cewa, "Yayin masu kuɗi ko, don na ji ba laifi motan akwai kuɗi, a haka ma Deeni ya ce wai ba mai kuɗi bace wannan sosai." Daddy ya ce amman ya san wannan bata rasa yin hundred million koma ta fi, hajiya ta ce kusan haka don miliyan tamanin da biyar Deeni ya ce ya siya, gaba ɗayansu suka jinjina kai, "Congrats bro, ta yi kyau sosai. Allah Ya tsare " Khaleel ya faɗa yana murmushi, Sadeeq ma ya ce, "Ya Deen Allah Ya sa alkhairi Ya tsare." Da murmushi ya amsa masu da Amin, Daddy ma ya yi mashi addu'ar Allah Ya sanya alkhairi ya tsare, Sadeeq ne ya ce bari ya je ya kira su mommy da yaya Sadeeya su zo su ga sabuwan motan yaya Deen ya ruga cikin gida, ba da jimawa ba sai ga su sun fito sun nufo wurinsu, da gudu Binafa ta nufi hajiya tana faɗin, "Oyoyo granny..." Tarbe ta hajiya ta yi tana murmushi ta ce, "Oyoyo ƙawalliyana..." Fuskar momy da murmushi ta yi mata sannu da zuwa, Sadeeya ta rungumo kafaɗar hajiya tana mata sannu da zuwa,
"Wow, what a fabulous car!" Sadeeya ta faɗa bayan ta saki hajiya ta nufi motan tana kallo, "Kamar avatar ko?" Fahad ya bata amsa da ita ce, ta shiga shafa jikin motan tana zuba santi, momy dake murmushi ta ce, "Ma sha Allah son, motan ta matuƙar yin kyau sosai. Allah Ya sa alkhairi ya tsare ya ƙara arziƙi mai albarka." Duk aka amsa ma momy da Ameen, sakin hajiya Binafa ta yi tana kallon motan ta ce, "Ya Deen wannan motan mai kyau ka siya!" Kafin ya bata amsa hajiya ta ce ba tashi bace ta ta ce ta siya, wani kallo ta yi mata ta ce, "No na san ba taki bane, ai ke tsohuwa ce, ta yaya Deen ce." Jawo ta hajiya ta yi tana faɗin, "Zo nan ki gaya mini shi tsoho bai hawa mota mai kyau." Ta maƙe kafaɗa tana kyalkyala dariya haka sauran mutanen wurin,
"Gaskiya yaron nan ka samu duniya!" Sadeeya ta faɗa tana murmushi tare da jinjina kai, "Lahira ma zai samu in sha Allah." Daddy ya faɗa duk suka amsa da in sha Allah, Deen ya ce ma Fahad ya yi testing nasu ya amsa da ok, Fahad ne ya shiga driver seat daddy na other side, baya Sadeeya da Khaleel da Sadeeq sai Binafa suka shiga suna ta santin tsaruwar cikin motar, cikin harabar gidan ya shiga zagayawa da su, Deen ya kira Fahad a waya ya ce mashi ya fita da su mana suka fita gate, after a while suka dawo itama mommy ta shiga aka zagaya da ita cikin harabar gidan, ba abun da suke sai yabo da son barka bayan sun gama ɗana motan, daga baya suka shiga cikin gidan, Fahad ya wuce part ɗinsa tare da Deen, a bakin gado Fahad ya zauna shi kuma Deen ya ɗan kishingiɗa tare da dafe forehead ɗinsa, Fahad na kallonsa ya ce ya gaji sosai ko don yau bai huta ba, yana murmushi ya bashi amsa da ai gajiyan ku san tare suka yi shi, "Yanzu zuwa wane lokaci ne za a yi launching club din?" Hannu Deen ya kai ya shafi sumar fuskarsa ya bashi amsa da shine yake son su zauna su tsara komai lokacin da yake da time, Fahad ya ce yana ganin ko zuwa gobe tun da ba aiki, Deen ya ce ok goben idan sun gama morning training zai zo, ya sake cewa "Ka ga da kaima kana harkan football sai ka zama manager ko kuma corch." Murmushi Fahad ya yi ya ce shi ai ba abun da ya haɗa shi da ƙwallo da dai abun da ya shafi bangaren lafiya ne, "Yauwa, ya maganar private hospital ɗin da kake so ka gina? Mun fara maganan baya..." Deen ya tambaya idonsa akan Fahad, gyara zama Fahad ya yi ya ce mashi maganan na nan yana son ya ƙara shiryawa ne sosai, "Amman already daddy ya baka plot so wani shiri yanzu ya rage?" With a smile on Fahad's face ya ce,"Kasan harkan gini yana bukatan a yi mishi shiri financially, idan ba haka ba sai ka ga abu ya zo yana delay." ɗan jinjina kai Deen ya yi alamar gamsuwa, sai kuma ya ce, "Idan wannan ne let's collaborate on it and get it done faster. Ka ga kai you provided the plot ni kuma sai in ɗauki nauyin aikin ginin" Wani kallo Fahad ya jefa masa sai koma ya janye fuskarsa gefe da ɗan murmushi, ya gama fahimtar Deen wato ya san idan ya nuna zai bashi kuɗi ba lalle ya amince ba shine ya 6ullo mashi ta hakan, kamar Deen ya san abun da ke a ran Fahad ya sake cewa, "Ka san nima I have the intention of building a hospital here, bari kawai mu yi amfani da wannan daman." Kallonsa Fahad ya yi da ɗan murmushi ya ce,"Amman ka san filin ba siya na yi ba?" Ɗan buɗa masa ido Deen ya yi ya ce, "But daddy ne ya baka,so ya zama naka ne ai." Fuskantarsa Fahad ya yi sosai, a nutse ya ce, "Deen, ka san aikin gini ba ƙananun kuɗi yake ci ba, ba kamar ginin asibiti dake buƙatan abubuwa da dama, ina ganin lissafin bai yi daidai ba a ce na bada fili kai kuma ka ɗauki nauyin ginawa." Ƴar dariya Deen ya yi don ya gane Fahad ɗin ya gane wayonsa, "Ba wani damuwa in sha Allah ba wani abu da zai gagara." Ya ƙare tare da ɗage ma Fahad gira, kafin ya ce wani abu aka yi sallama, "Assalamu Alaikuum..." Duk suka kai idanunsu kan kofan shigowa, Sadeeya ce ta nufo su tana murmushi, "Barkan ku da hutawa..." Deen ne ya yi mata murmushi tare da amsa mata, "Dama daddy ne ya ce a yi maku magana ku zo mu yi dinner." Fahad ya ce mata a kawo masu abincin nasu nan, ta ce,"Da hakan za a yi but sai daddy ya ce tun da duk an haɗu har da hajiya a yi dinner ɗin tare." Kai Fahad ya ɗaga, kallon Deen ta yi ta ce, "Gaskiya lil bru yakamata idan zan koma school ka fasa da ni a sabuwar motan can taka, na san zan tashi kan mutane over." Yana murmushi ya ce mata ta nemi lil bru ɗin nata sai ya kai ta, dariya ta yi ta ce, "To yaya Deen..." Shima yar dariyar ya yi kafin ya tambayi yaushe zata koma ta bashi amsa da ranar talata, ɗan jimm ya yi kafin ya ce ok zai duba yuwuwar hakan don yana da schedules ranan amman idan ma bai samu kai ta ba sai Fahad ya yi using motan su tafi tare idan zai je wurin aiki" Ta yi masa godiya tana murmushin jin daɗi, daga baya suka fita zuwa yin dinner din. Bayan an rako su za su koma gida, Fahad ya ce ma Deen akwai wani aiki da yake son yi a daren da sun tafi tare, Deen ya ce masa ba matsala gobe zai zo nan ya wuni su ƙara tattaunawa.
Salma ta gama yin shirin bacci tana niyyar kwanciya saman gadonta wayar innarsu dake a hannunta ta fara yin ringing, duba mai kiran ta yi, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ganin sunan mai kiran, ɗauka ta yi ta kai wayar kunne a nutse ta fara magana, "Asslamu Alaikum..." Daga ɗayan 6angaren muryar mace ta amsa, "Wa'alaikumus salam, yaya Fiddausy barka da dare..." Yar dariya Salma ta yi ta ce, "Aunty Kubrah ba ita ba ce, baki gane muryata ba?"
"Ahh..wllh sam ban ɗauki murya ba, da yake itama ba wata babban murya ne da ita ba, ashe babynah ce.." Tana murmushi ta amsa mata da eh,
"Babynah ya kike? fatan kina lafiya."
"Lafiya lau Autynah, ina wuni ya aiki."
"Alhamdulillah, gani nan ban daɗe da dawowa ba ma, da yake evening na yi, gaba ɗaya na gaji yanzu nan na watsa ruwa gani nan na baje." Salma tana ƴar dariya ta ce, "Sannu Autynah.." Ta amsa mata da yauwa,
"Bari in kai ma innar wayar..." Katse ta ta yi, "No ba sai kin kai mata ba, dama kiran naki ne ina son in ji muryan ƴar babynah ne.." Still da dariya akan fuskarta ta ce, "To na gode Autynah mai kaunata, ina missing en ki sosai.."
"Allah Sarki my baby, in sha Allahu ai mun kusa mu kasanci a kusa da juna da zaran kin fara karatu a nan, yanayin aikin namu ne da mutum bashi da lokacin kansa sosai ina ta son nima in zo in gan ku...." Hira suka ci gaba da yi mai nuni da yadda suka damu da juna, daga baya ta tambayeta ko tana da wata matsala ta ce mata a'a,
"Babynah na san halin ki sarai da nauyin baki, in baki sanar da ni buƙatunki ba to wa zaki sanar wa?" With a broad smile Salma ta ce, "Allah Aunty Kubra bani da wata buƙata, ko kuɗin da kika turo mani last time suna nan ban siya komai ba." Da alamun mamaki a muryar aunty Kubra ta ce, "Lahh..ke da na turo ma su don ki siya abun da kike so shine kike ta ajiyar su?" ta ce, "To ai Aunty Kubra ba wani abu da nike so yanzu."
"Kina budurwa za ki ce ba abun da kike so, ina kika bar cosmetics? Su perfumes, roll on..." Cikin sigar shagwa6a Salma ta ce, "To ai Aunty Kubra duk ina da su fa cikin waɗanda kika aiko mani duk akwai saura." Salati Aunty Kubra ta saka, "Yau na bani..Salma ba dai jere kika yi da su ba baki using da su?" Da sauri ta ce mata wllh tana amfani da su,
"To amman yakamata a ce by now sun ƙare ai, kuma dama abubuwa irin wannan wa ya ce maki bari ake har sai sun ƙare sannan a siyo wasu? Tun da products din ko da yaushe cikin yin su ake kala kala, yakamata mutum na bincikawa idan ya ji wani mai kyau da inganci sai ya yi trying nasu ya ga ko za su fi wanda yake using da kyau. Sannan su gyaran kai da jiki....wai ma Salma kina zuwa saloon kuwa?" Kame-kame ta shiga yi tana ɗan sosa ƙasan gashinta ta ce, "To ai ni Aunty Kubra kin san bani yin saloon."
"Ina nufin kina zuwa wankin kai da su gyaran jiki, su lalle?" Ɗan zaro ido Salma ta yi ita yaushe rabon ta da yin wani lalle, kawai dai bata barin ƙumbunanta su yi fari fat, wankin kai kuwa dama sai idan ta je hutu Kaduna wurinta take kai ta amman a nan innarsu ke taya ta ta wanke "Kika yi shiru?" Amsa ta bata da a'a amman tana yin lalle sai dai ba akai akai ba,
"To fisabilillahi baby kuma sai ki buɗe baki kina cewa ba abun da zaki da kuɗi? bacin duk ga abubuwan da ya kamata ace kina yi amman ba kya yi, ai an ce ko kana da kyau to ka ƙara da wanka, idan baki gyara kan ki sosai ta ya zaki samo mana surukin kirki? Ko so kike ki kwaso mana kwashikwaraf?" Tana ƴar dariya ta ce mata a'a.
"To kuwa mace yanayin gyaranta yanayin mazan da za su rinƙa tunkararta. Daga yanzu karki ƙara wanke kanki a gida in ba so kike sumarki ta lalace ba, kina da gashi mai kyau tubarkallah, idan kina son ya ci gaba da bunƙasa to ba kowanne abu zaki na danƙara ma kanki ba wurin wanke shi, duk ƙarshen wata kije a yi maki wash and set da kuma ƙunshi, sai gyaran jiki ma duk bayan lokaci shima a rinƙa yi maki, zuwa da safe zan ƙaro maki kuɗi sai ki haɗa da wanda kika ce suna nan ki je a yi maki duk abun da na ce, har su kayan shafan ki je ki siyo ki daina jira sai sun ƙare, bari ma zan bincika maki skin care products masu kyau sai ki samo." Cike da jin daɗi Salma ta amsa mata da to tare da yi mata godiya,
"Ba godiya zaki mani ba, ki tabbatar kin yi duk abun da na ce kin ji ni?" Kai ta daga, "Eh, in sha Allahu I will do as you instructed auntynah." Murmushi Aunty Kubra ta yi tare da faɗin, "That's my baby girl. Allah Ya ci gaba da raya mana ke ya ƙara yi ma rayuwarki albarka."
"Amin Autynah, may Allah bless ur life too." Cike da jin daɗi aunty Kubra ta amsa mata, bayan sun ɗan ƙara yin hira daga baya suka yi sallama, Salma ta ajiye wayar gefe tana murmushin hirar tasu, don ma bata san cewa har yanzu tana yin awara ba ta san da sai ta yi mata faɗa, don tuni ta hana ta ta ce ta bar ma su Imrana suna yi to amman ita tana son yi, a ranta take raya Aunty Kubra tana matuƙar ƙaunarta ta san kuma don Allah bai ta6a bata haihuwa bane.....
_1.jpg)