_Bossladieswriters
_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don karanta littafin daga farko, da kuma abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_
https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_
_ZAINAB BATURE_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
18
Salma na ganin waɗanda suka shigo ta yi saurin maida idanunta ƙasa, ƙirjinta ya hau bugu da ƙarfi, ta shiga zullumin abun da zai biyo baya ganin Fahad, sam ta kasa ɗaga kai ta sake kallon saitin ƙofar yayin da suke shigowa ciki, ƙamshin turaren su ne ya karaɗe ilahirin cikin falon, cikin washe baki hajiya ke kallon Fahad da Deen da suka nufo inda suke, "Ma sha Allah angwayen hajiyar ambasada, wannan wanka dai ya yi min na yaba gaskiya." Ta faɗa tana bin su da kallo, jin furucin hajiya ya sa Salma ta ɗan ɗago kanta a hankali ta kalle su aikuwa idanunta suka shiga cikin na Fahad, ganin yadda ya ɗaure fuska ya sa ta yi saurin janye idanunta, sam ta kasa dauke idanunta daga kan Deen don ba ƙaramin kyau ya yi mata ba,
"Wannan na san bai wuce aikin Fahad ko?" Hajiya ta faɗa tana ta murmushin jin daɗin ganin yadda jikokin nata suka fito, Deen ya bata amsa da shine ya kawo masa kayan, ta ce, "Amman kuwa sun matuƙar amsar ka. Kana ma saka kaya haka kuwa a can?" Ya bata amsa da ya daɗe, "Aikuwa ka rinƙa sakawa don ba ƙaramin burge mutanen can zaka yi ba." Da ɗan murmushi ya ce mata haka daddy ya faɗa, ƙoƙarin zama ya fara a kan kujera mai mazaunin mutum ɗaya, Fahad kuwa wucewa ya yi ciki Salma ta bi bayansa da kallo, maido idonta ta yi kan Deen suka haɗa ido, shi tun da ya shigo ma bai kalle ta ba sai yanzu ya ganta, a hankali ta sauke kanta ƙasa bayan ɗan lokaci ta sake ɗagowa lokacin idanunsa na akan wayarsa, "Ina wuni..." Ta faɗa da siririyar muryarta, sai da hajiya ta ce masa ana gaishe shi ya ɗago suka sake haɗa ido, a ɗan daburce ta sake gaishe da shi ya ɗaga mata kai ba tare da ya amsa ba, daga haka ya ci gaba da latsa wayarsa ita kuwa ta bi sumar kansa dake fake a ƙasa da kallo, bayan ɗan lokaci ya ɗago kansa yana kallon abun da suke kallo a tashar arewa 24, shi rabon da ya kalli channel ɗin hausa ma har ya manta, hajiya ta kai idonta kan sumar shi da ya juyo kansa ta ce, "Amman dai ba haka ka je sallar juma'an ba da gashi a ƙulle kaman mace." Juyowa ya yi fuskarsa a sake kaman zai yi murmushi ya ce mata haka ya je, "Wannan ai sai ka ɗauke ma mutanen dake salla a kusa da kai hankali tun da ba abu ne da suka saba gani ba namiji da gashi a ƙulle." Murmushi mai ɗan faɗi ya yi ya ce ai ya saka hula yana mota ne ya cire, Fahad ne ya fito suka maida kallon su kan shi, "Ba dai har zaka tafi ba?" Hajiya ta tambaya, ya bata amsa da eh ya samu kiran gaggawa ne daga private hospital ɗin da yake aiki a nan zai je ya duba wasu marasa lafiya, hajiya ta ce, "To amman zaka dawo ko, don kun zo ko abinci baku ci ba." Ya bata amsa da ya gama zai dawo ya ce mata a ƙoshe suke sun ci abinci a gida ta gyaɗa kai, kallon Deen ya yi ya bashi hannu suka yi sallama, Deen ya ce mashi sai ya dawo Allah Ya bada sa'a ya amsa da Ameen kafin ya wuce, hajiya itama ta yi addua'ar Allah Ya taimaka ya basu lafiya, bin bayansa Salma da ko kallon 6angaren da take bai yi ba ta yi da kallo, Deen na kallonta yanayin fuskarsa kamar zai saki murmushi don ya fahimci a tsorace take da Fahad sai ka ce ba ita bace mai tsaurin idon nan.
"Wai kuwa ka ga mutanen dake ta son ganin ka tun ɗazun a bakin gate." Hajiya ta tambaya, ya bata amsa da eh sun yi magana sai zuwa dare zai yi ƙoƙarin ganawa da su.
"Su kawun ka ma Hamida ɗazun sun zo nan suka ce sun ji labarin zuwan ka, na sanar da su kana can gidan baban naka. Yakamata ka samu lokaci ka kai ma ƴan'uwa na nan ziyara ku gaisa za su ji daɗin hakan sosai." Amsa mata ya yi da in sha Allah zai yi hakan. "Ko a shirya maka abinci ne?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, ta sake cewa, "Ga awaran ma da ka ce kana so can Salma ta kawo Balaraba na haɗa maku." Kai idonsa ya yi kan Salma suka haɗa ido, sam ta kasa janye nata sai ƴan kame-kame da ta shiga yi tana kikkafta idanu. "Su suke yin shi ne?" Ya tambaya bayan ya maida idanunsa kan hajiya ta bashi amsa da eh, bai ce komai ba ya mayar da kallonsa kan waya, can ya miƙe ya nufi ciki Salma nata kallonsa, ita a wurin ta ganin shi da take yi hakan ba ƙaramar alfarma bace a wurinta, don in ba haka ba to ina zata samu damar ganin mutum mai kyau da ɗaukaka irin wannan? Ci gaba da kallon ta ta yi don ta san ko ta koma gida a lokacin ba wani abun da zata yi, dama ɗazun ƙarya ta yi ma innarsu cewa assignment take, kawai don bata son zuwa ne kada ta haɗu da Fahad, to ƙarshe ma sun haɗun ya nuna da ita da bola duk ɗaya.
Motsin da suka ji ya sa duk suka kai idanunsu kan Deen da ya dawo cikin falon, ya canza kaya zuwa ƙananu na shan iska riga mara hannuwa da wandonta gajere dukkan su kalar ruwan ƙasa mai haske da ta hau da fatarsa, kayan na ɗauke da tambarin Louis Vuitton, "Jama'a ku taya ni kallo, mi nake gani ne a saman kan Deeni?" Hajiya ta tambaya tana kallon saman kan nasa da mamaki akan fuskarta, wadda za ta bata amsa bata wuce Salma ba tun da su biyu ne kawai, sai dai itama gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan Deen ɗin da yanayin al'ajabi take kallon saman kan nasa, nufar kujeran da ya tashi ya yi ya zauna fuskarsa da ɗan murmushi don ya san abun da hajiyan ke ma mamaki, "Wai miye a kan ka Deeni kamar kitso?" Hajiya ta tambaya har lokacin da mamaki shimfiɗe a saman fuskarta, ba don bata ta6a ganin kitso a kan nasa ba, ta san yana yi musamman idan suna ƙwallo, to amman mamakinta waye ya yi masa kitson yanzu? hannu ya kai ya shafi kan nasa ya bata amsa da kitso ne, ta ce, "Ikon Allah! Waye ya yi maka kitso cikin ɗaki? ko kuwa shima kitson an yo injin da ke yin sa ne tun da Bature dai ba zai gaji da kashe mu da abubuwan al'ajabi ba?" Murmushinsa ne ya ɗan faɗaɗa jin zancen hajiya, ya ce, "Nah, ni ne na yi shi." Ya yi maganar yana jingina kansa da kujeran, "Kana nufin yanzu kai ne ka zauna ka kitse kan ka haka?" Kai ya jinjina mata ya ce eh, kafin ya ɗaura da cewa zafi ya yi yawa a nan gashi ya saka manyan kaya sun ƙara masa zafin, hajiya ta ce, "To ai dama ka san yadda weather ɗin tamu a nan take, a haka ma da sauƙi tun da damuna ta fara don ma dai ruwan bai zauna ba sosai. To mi zai hana ka aske gashin kawai ko kuma ka rage shi sai ka fi samun sauƙin jin zafin a kai, idan sumar kake so sai ka bari idan ka koma ka ƙara tara wata tun da gashin bai maka wuyar taruwa." Shiru bai ce komai ba sai ɗan murmushi da yake yi, Salma dai ta kasa ɗauke idonta akan nasa, al'ajabi ne bayyane a saman fuskar tata don ita tun da take bata ta6a ganin namiji da kitso a zahiri ba sai yau, gashi abun da ya fi ɗaure mata kai shine jin cewa da ya yi shi ya yi ma kan sa kitson, dama akwai mazan da suka iya kitso? hakan take ayyanawa a ranta, ko Sagir da take roƙa wani lokacin ya taya ta tsifan kanta bai ta6a jaraba cewa zai yi mata kitso ba, jin bai ce komai ba bayan hajiya ta yi masa maganar aske sumar ya sa ta ƙara cewa, "Ko ba a ko ina kake yin aski ba? Balle garin namu ƙauye ko?" Tana rufe baki caraf Salma ta ce, "Ai akwai wani wurin aski mai kyau a can bakin tasha, ƴan gayu masu kuɗi nan suke zuwa aski, ko wannan ɗan film ɗin na nan garin na taba ganin shi a can an masa ask..." Kasa ƙarasa maganar da ta ɗauko ta yi sakamakon ido da Deen ya ɗago ya yi mata wani kallo mai kama da kallon ni tsaran wasan ki ne? hajiya da ta lura da abun da ke faruwa a tsakanin su ta sa dariya, dama maganar Salmar ta bata dariya, cikin dariyan ta ce ma Deen, "To kai shike nan ma ka ji Salma ta san inda ake ma irin ku celebrity aski sai ta raka ka a yi maka." Maida idonsa ya yi kan Tv ba tare da ya ce komai, itama Salma tun da ta yi maganar ta sauke kanta ƙasa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi, yayin da zuciyarta ke tsawatar mata kan ita ina ruwanta da shiga maganar su! sosai ta ji rashin daɗin su6utar bakin da ta yi masu, kunya duk ta lullu6e ta tana jin kaman ta nutse a wurin, bayan ɗan lokaci da ƙyar ta miƙe hajiya ta kalle ta ta ce ina zata je, cikin ƴar rawar murya ta bata amsa da gida za ta tafi, hajiya na murmushi ta ce, "Kina yin kallon ki muna hira, ki zaman ki." Shiru ta yi tana ɗan wasa da yatsun ta,
"Deeni ka ga zaka korar mini baƙuwa." Kamar ba zai ce wani abu ba, slowly ya juyo idanunsa ya kalli Salma, janye idonsa ya yi ya mayar kan Tv tare da faɗin, "Ban kore ta ba. If I want to cut my hair, I have a clipper (Idan ina son aske gashina ina da abun yin askin)" Hajiya dake murmushi ta ce mata, "To kin ji, shi ba ruwan shi da ke ki zaman ki." A hankali ta ɗago kai ta kalle sa, daidai lokacin ya maido nasa kanta idanunsu suka haɗu, kawai sai gani ta yi ya ɗage mata gira tare da ɗan jinjina kansa alamar ta ji abun da ya ce? ɗan kikkafta idanu ta shiga yi tare da tsuke baki ta jinjina masa kanta alamar eh, ya kauda idanunsa daga barin kallonta, komawa ta yi ta zauna amman duk da haka ta kasa sakin jiki, after some few minutes ta sake miƙewa hajiya ta kalle ta, tun kafin ta ce wani abun Salma ta riga ta cewa, "Zan je in shirya ne, anjima zan fara tuyan awara." Da alamun rashin fahimta hajiya ta ce, "Dama ke kike tuyar awaran?" Kai ta ɗaga mata alamar eh, ta sake tambayar ta anan cikin gidan su? ta bata amsa da a ƙofar gida.
"Amman ba kina da ƙannai ba?" ta ce mata eh amman duk maza ne, tambayarta ta yi maza basu tuyar awaran ne, tana ɗan murmushi tare da wasa da yatsunta ta ce suna yi kawai dai ita ce ke son tana yi, hajiya ta ce, "Amman Salma baki gudun samarinki su gan ki kina tuyar awara?" Still da murmushi ta ce ai ita bata da saurayi, kallon ban yarda da abun da kika faɗa ba hajiya ta yi mata, "Ya za ai budurwa kamar ke, ga ki kuma tubarkallah ki ce mani baki da saurayi Salma?" Ƴar dariya ta yi kanta a ƙasa ta ce ai ita ce bata saurarar su,
"To saboda me?" hajiya ta tambaya tana kallonta da ɗan murmushi, cikin yar en-ina Salma ta ce, "I...idan na gama makaranta so nike in ci gaba da karatu shi ya sa." Kai hajiya ta jinjina alamar gamsuwa kafin ta ce, "Duk da haka dai idan akwai wanda ya zo da magana ta kirki mai nagarta, kuma kin ga ya yi maki yakamata ki saurare shi, saboda karatu baya hana ai a saurari saurayi, kuma ko da mace tana cikin karatunta zata iya yin aurenta ta ƙarasa a ɗakin mijinta. Ita mace akwai lokacin da zaki ga tauraruwarta ta haska samari sun yi mata caa har da masu son aurenta, to ya kamata ta yi amfani da damarta don wani lokacin in ta ce sai lokacin da ta shirya sannan sai ki ga samarin ɗibb babu su, duk da dai dama komai ya faru da bawa rubutacce ne. A dage a rinƙa yin addu'ar neman za6in Allah." Cikin muryarta mai tattare da natsuwa ta amsa da in sha Allahu.
"Amman dai yakamata ki bar ma ƙannanki suna tuyar awaran nan, ko ba samari ba baki jin kunyar ƙawayen ki su gan ki kina tuyar awara?" Hajiya ta tambaya da zolaya, Salma ta yi ƴar dariya ta ce, "Ai ma duk ƙawayena sun san ina yin awaran, kuma ni bana jin komai tun da neman halak ne, ya fi ka je kana roƙon mutane." Da alamun burgewa a maganarta hajiya ta ce, "Wannan gaskiya ne Salma. Allah Ya ƙara rufa asiri." Ta amsa da Amin, duk abun nan Deen na saurarar su duk da ba za ka ce hankalinsa na a kan su ba don idanunsa na akan Tv, maganar Salma ta ƙarshe ba ƙaramin burge shi ta yi ba saidai ba alamar da ta nuna hakan. Bayan hajiya ta ƙwala ma Balaraba kira ta fito ta bata umarnin ta kawo ma Salma robar awaran ta ce ta zubo mata kayan itatuwan da aka kawo ɗazun daga lambu, after some minutes Balaraba ta kawo mata robar da lemu, mangaro, gwaba a ciki, hajiya ta ce ma Salma gashi nan su je su sha ta yi mata godiya, har za ta juya ta ji Balaraba ta ce, "Wai Salma ina fara ne, kwana biyu ko kin daina soyawa?" Tana murmushi ta ce, "Wllh anty Balaraba faran ne ta yi tsada sosai, idan na soya sai a yi ta cewa na yi tsada shi ya sa ma kawai na bari." Balaraba na murmushi ta ce, "Ai komai ma yanzu ya yi tsada abun sai dai addu'a kawai, amman idan kina fita ko ya ya ne kuma ana siya ai ya fi ki ci gaba da ki ce kin bari ɗin gaba ɗaya, tun da gaskiya kin iya soya fara ba ƙarya." Dariyar jin daɗin yabon ta yi, ta ce in sha Allah za ta ci gaba dama wasu na ta so, itama Balarabar ta ce to idan ta yi tana so ta kawo mata ta dubu ɗaya, hajiya dake sauraran su tana ta murmushi, juyawa Balaraba ta yi ta koma kicin Salma ta ƙara yi ma hajiya Sallama da godiya ta nufi hanyar barin falon, har ta kusa kai wa ƙofa ta juyo da niyyar satar kallon Deen kawai sai gani ta yi ashe idon shi na kan ta, da sauri ta juya ta tafi.
Bayan sallar magrib Deen ya fara ganin mutanen dake son ganawa da shi, yawanci duk koke ne kan halin matsin rayuwa wasu kuma abun da ya shafi ƙwallon ƙafa, a wurin parking space ya zauna ana shigo mashi da mutane a nutse da yake bakin gate ɗin akwai jami'ai, sai da aka fara kiran sallar issha ya dakata tare da ba waɗanda bai samu gani ba haƙuri ya basu lokacin da zai gan su, cikin gida ya koma wurin Fahad wanda ya dawo da magrib, tare suka tafi masallaci yin sallan issha, bayan sun dawo suna shigowa haraban gidan aka kira Deen a waya ya ce ma Fahad ya shiga ciki zai shigo idan ya gama amsa kiran, a wurin da ya zauna ɗazun da yana ganin mutane ya zauna, ya ɗan ɗauki lokaci yana yin wayar wanda wani babban abokinsa ne ɗan team ɗin su bature ya kira shi suke tattaunawa game da hutun da suke yi da kuma shirin da za su yi don tunkarar next season, bayan ya gama yin wayar zaune ya yi a wurin idanunsa na kallon wuri ɗaya kamar mai tunanin wani abu, motsin da ya ji a ta gefensa ya sa shi kai idanunsa wurin, Balaraba ce ta fito tana ruƙe da wata babbar roba ta nufi hanyar bayan gidan, juyo da kansa ya yi ya shiga latsa wayarsa, ba a ɗauki lokaci ba ya sake jin motsi ya ɗago kai, ita ce ta dawo zata koma ciki, har ta kusa kai wa ƙofa ya dakatar da ita ta hanyar yin alamar kiran ta, da sauri ta aje robar a wurin ta nufo shi, kafin ta ƙaraso wurin sa a cikin ransa ya shiga tunanin to mi ma zai ce mata da ya kira ta? Daga gefensa ta tsaya cikin ladabi ta gaishe da shi ya ɗan jinjina mata kai, shiru ya ɗan yi na wani lokaci sai kuma ya gyara zaman sa ya ce mata dama yana son tambayarta ne a kan yarinyar nan da suke yin awara a nan unguwan suke? Da sauri ta amsa mashi da eh, ta ce ai basu da ma nisa da an fita, layin da ke tsallake yana kallo bangaren nan gidan anan ciki suke gidansu ne na ukku daga dama, kai ya jinjina mata ya ce ya gode za ta iya tafiya, sam Balaraba bata kawo komai ba a ranta illa ta yanke taimakon su wataƙil zai yi ganin yadda yake ta taimaka ma mutane, bayan ɗan lokaci ya miƙe yana tafiya a nutse jikinsa sanye da ƙananun kaya ya nufi gate, ganinsa ya fito officers dake bakin gate ɗin suka shiga faɗin, "Barka da fitowa yalla6ai..." Bayan ya amsa masu, ganin yana kallon bangaren da aka faɗi mashi gidansu Salma yake wani cikin jami'an ya ƙara cewa, "Ko da wani abu ne yallabai?" Ya bashi amsa da a'a, tunanin ko ya kamata ya yi abun da zuciyarsa ke horan sa akan ya yi ya shiga yi, hannu ya kai cikin aljihun wandonsa ya fiddo takunkumin fuska, tafiya ya fara yi bayan ya gama sakawa, wani jami'i ya ce mashi ko yana buƙatar rakiya ya ɗan ɗaga masa hannu tare da faɗin ba nisa zai yi ba, suna ta mamakin in da zai je ganin yana ƙoƙarin tsallaka titi, yana shiga layin idanunsa suka hango masa wani wuri inda wuta ke ci ga wasu yara a tsugunne, daga yadda aka kwatanta masa ya fahimci nan ne inda take tuyan awaran, a nutse ya tunkari wurin fuskarsa a ƙasa, daga ɗan nesa da su ya dakata yana kallon wurin.
"Awara za a baka?" Ya ji ɗaya daga cikin yaran ya tambaya cikin ɗan ɗaga murya, hannu ya kai a hankali ya zame nosemask ɗin ganin wurin ba wadataccen haske, tambayarsu ya yi ina mai yin abun, yaron ya ce, "Yaya Salma ce ta shiga gida ta dawo, amman ko mu zamu iya saida maka." Shiru Deen ya yi daga yanayin zaƙin muryar yaron ya fahimci ɗan'uwanta ne, hannu Deen ya kai ya mayar da nose mask ɗin ganin wasu matasan samari sun nufo wurin, awaran suka siya bayan an sallame su yaron ya kalli Deen ya ce "Ka ji, ta nawa za a baka awaran?" Ɗan murmushi ya bayyana a kan fuskarsa ya ce masa bari ita mai abun ta dawo, miƙewa yaron ya yi da sauri yana faɗin to bari ya je ya kirawo ta, da ƴar sassarfa ya nufi gidan Deen ya ɗaga ido yana kallon inda yaron ya nufa, a daidai bakin zaure suka haɗe da ita har suna yin karo, ta ce, "Lafiya Hamza ka taho haka?" Da sauri ya ce, "Wani mutumi ne ya zo siyan awara na ce ta nawa za a bashi amman ya ce sai kin dawo." Da alamun mamaki ta maimaita abun da ya faɗa, ɗan leƙa kanta ta yi ta hango shi saidai bata iya gane ko wanene ba saboda ba haske ta dai hangi mutum a tsaye, "Ka san shi?" Ta tambayi Hamzan, kai ya girgiza mata ya ce, "A'a ya rufe fuskan shi, amman dai yana ta uban ƙamshi." Juya maganar Hamza ta shiga yi a ranta tana ƙoƙarin tuno wanda ta sani mai zuwa siyan awara yana ƙamshin turare sosai, fitowa suka yi tana biye da bayan Hamza jikinta sanye da hijab mai hannu ta tsaya mata daidai gwiwa, da sallama ta ƙaraso wurin ta tsaya ɗan nesa da shi tana kallonsa sai dai ta kasa tantance wanene don tana ganin kamar bata ta6a ganin wani mai irin suffar jikinsa ya zo siyan awara ba, ga shi ta gaskiyar Hamza sai baza uban ƙamshi mai ratsa zuciya yake duk ya cika mata hanci, "Ina wuni..." Ta gaishe da mutumin duk da bata san wanene ba amman ya yi mata ƙwarjini sosai, ganin bai da niyyar yi mata magana koda ta gaishe shi kai ya ɗaga mata, ta ce, "Awara za a baka ne?" Ta tambaya ta tsare shi da idanu, ta cikin mask ɗin ta ji ya ce za su yi magana tana a nan ne? ta gane yana nufin ta yi masa nisa, sam bata gane muryarsa ba saboda rufe bakinsa da ya yi, ɗan matsowa ta yi kaɗan a ranta tana mamakin wanene wannan mutumin mai aji haka? Jin bai ce komai ba duk da ta matso ya sa ta shiga yin tunanin ko har yanzu ta yi masa nisa ne shiyasa ya ƙi cewa komai, ƴan kame-kame ta shiga yi ta ce, "Uh..mm jikina yana yin ƙaurin wuta ne ban so in matso ka ji..." Ita kanta bata san dalilin faɗin hakan da ta yi ba, wataƙil saboda yadda ta ji yana sakin ƙamshi ya sa ta kama kanta, steps biyu zuwa ukku ya yi shi ya matsa ta kafe shi da idanu, a hankali ya kai hannu ya zame nose mask ɗin fuskarsa, duk da bata ganin fuskar sosai sai da gabanta ya faɗi, kallon ƙurulla ta shiga yi masa tana son gane waye,
"Kina zama a kusa da wuta with this, ba ki tsoron ya kama wutan?" Ya yi maganan yana nuni da hijabin jikinta, damm! gaban Salma ya faɗi, ai ko a cikin magagin bacci ta ji muryarsa wllh sai ta gane, kokonton anya kuwa shine ta shiga yi, to mi zai kawo shi nan idan shi ne? Ya ma za ai ya san wurin? To amman kuma tabbas wannan muryarsa ce, tana cikin yin wasi-wasin wani mai mashin ya shigo cikin layin hasken babur ɗin ya haske mashi rabin fuska farar fatarsa ta bayyana, tabbas shi ne! zuciyarta ta gasgata hakan, ƙirjinta ya shiga yin bugu fat, fat, sai ta ji ma kamar ƙafafuwanta na barazanar kasa riƙe ta, ɗage mata gira ya yi ya ce bata ji abun da ya ce ba? ta shiga motsa baki da ƙyar ta tattaro kalaman bakinta ta ce mashi ai tana kula sosai, kauda kai ya yi ta ji ya ce It’s not safe to go near fire da dogon abu irin haka, kamar yar ƙadangaruwa ta gyaɗa kai ta ce mashi to ta gode za ta daina saka irin shi idan za ta yi tuyan, hannu ya saka cikin aljihun gaban wandon shi, miƙo mata abun da ya fito da shi ya yi ta matso ta amsa, lokaci guda ta gane kuɗi ne masu yawa, a dabarbarce ta ce, "Awaran bata kai ta haka ba, duka ma wadda ta rage bata da yawa." Ya ce mata ta raba ma mutane shi, daga haka ya maida mask ɗin, ganin yana ƙoƙarin juyawa da sauri ta ce, "To kuɗin sun yi yawa ai, duka awaran ma bata wuce ta dubu ɗaya ba idan ma ta kai..." A taƙaice ya ce ta kai kuɗin gida, daga haka ya yi gaba abun shi ba tare da ya tsaya sauraren abun da za ta ƙara cewa ba, tamkar rainon sakarya haka ta bi shi da kallo yayin da yake tafiya bakinta a buɗe tsabar mamaki.....
_1.jpg)