ACikin Rayuwa page 17 Complete na Zainab Bature

 


_Bossladieswriters_

_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don karanta littafin daga farko, da kuma abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q

  *_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

   _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ 

_ZAINAB BATURE_

   _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._

17

Washe gari da wuri Fahad ya wuce wurin aiki, misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi Deen ya saukko ƙasa ya shirya cikin t-shirt da wando jeans sai faman baza kamshi ya ke, yadda rigar ta ɗan kama shi ta bayyana ƙirar ƙirjinsa dake a bude, yana ƙarasa saukowa suka haɗu da momy ɗin su Fahad da ta nufo hanyar benen, da murmushi ta furta, "Good morning my son." Shima murmushin ne akan fuskarsa ya ce, "Morning Momy..."


   "Hope you slept well?" Ya bata amsa da, "Yea, Alhamdulillah." ta sake cewa, "Ai da yanzu nike niyyar zuwa in taso ka ka yi breakfast kada yunwa ta kama mana baƙon turai, duk da na san dama ba lalle kana yin breakfast da wuri ba, kai ya ɗaga yana murmushi ya ce mata ba da safiya sosai yake cin abinci ba sai dai idan zai je wani wuri, jinjina kai ta yi tare da yi mashi nuni da dining area ta ce an shirya mashi table bari ta turo Sadeeya sai ta yi serving nashi, ya yi mata godiya ta wuce. Ba da jimawa ba Sadeeya ta shigo cikin falon tana sanye da ƙananun kaya riga da skirt kanta ta saka hula, wurin Deen dake zaune saman kujera yana latsa waya ta nufa, "Good morning bru." Ɗago fararen idanunsa ya yi tare da sakar mata murmushi, ya ce, "Morning my lil sis.." Ƴar harararsa  ta yi ya ɗage gira ya ce ko tana da ja kan hakan, da sauri tana girgiza masa hannu ta ce, "Ni dai ai baka ji na ce wani abu ba ko, balle ka ji daɗin yi mini mugunta dama ga shi daga ni sai kai a cikin falon." Ƴar dariya ya yi ba tare da ya ce wani abu ba, ta ce mashi su je ya ci abinci ya miƙe suka nufi dining area.


    "Ina Basma budurwarka ko in ce wife to be ɗin ka?" Sai da ya cinye abincin bakinsa ya bata amsa da tana can tana lafiya, Sadeeya ta sake cewa, "Yaushe ne za mu sha bikin to? Amman dai a nan za a yi shagalin bikin ko?" Amsa ya bata da sai ta ƙarasa gama karatu yanzu tana a year 2, ta ce,  "To ba kawai sai a yi bikin ba sai ta ci gaba da karatun a gidan ka" Ɗan murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya kai chips ɗin da ya ɗebo da fork baki, shiru Sadeeya ta yi tana zaune a saman ɗaya daga cikin kujerun wurin, a kaikaice ta ke satar kallon Deen ɗin a cikin ranta tana raya sam Deen bai dace da auran yarinyar ba, a yadda yake tubarkalla kamata ya yi ya auri mace da ta amsan sunan mace, ita fa a da ma tana crushing nasa da ta ji cewa yarinyar zai aura ta cire shi a ranta dama ba wanda ya san da hakan, tana cikin kallonsa ba tare da ta ankare ba ya ɗago idanunsa suka haɗa ido, da sauri ta wayance ta shiga yin ƴar dariya ta ce haka ya iya loma ashe shiyasa ya koma jibgege tubarkalla, murmushin gefen baki ya yi ba tare da ya kawo komai ba a ransa ya ce dama dalilin da ya sa ta zauna ke nan don ta yi masa kallon ƙurulla, sipping tea ya yi bayan ya shanye ya kalle ta ya ce, "Ya baki je school ba, or have you already graduated?”


 Amsa mashi ta yi da a'a tana dai a final year sun samu hutu ne, ya ce, "Sai aure ke nan idan kika gama?" Ɗan juyawa ta yi gefe ta juyo ta jinjina mashi kai alamar eh tare da kanne masa ido,  dariya ya yi har haƙoransa suka ɗan bayyana ya ce, "So you're very eager to get married right?" Ɗage masa gira ta yi tana dariya, ya dan girgiza kai kafin ya sake cewa, "Wannan soldier ɗin da kika turo mani picture na shi da shi za a yi auren, miye ma sunan shi?" 


    "Captain Junaid.." Ta bashi amsa, ya ce Allah Ya nuna masu ta amsa da Amin, ɗaga fork ɗin hannunsa ya yi kaman zai jeho mata ya ce ita bata da kunya ne, ta duƙe tana dariya ta ce shi ne za ta ji ma wani kunya. Bayan ya kammala yin breakfast ɗin ya ce ma Sadeeya yana son zuwa gidan hajiya ko akwai motan da zai yi amfani da shi, ta bashi amsa da akwai ya ce ok, kafin ya sake tambayarta dad na nan ya je su gaisa ta ce mashi eh, tare da ita suka nufi bangaren dad, bayan sun gaisa ne Sadeeya ta yi mashi maganar Deen yana son motan da zai je gidan hajiya, dad ya ce mashi ba zai jira zuwa anjima ba idan suka yi sallan juma'a sai ya tafi, Deen ya amsa mashi da to sai kuma dad ɗin ya ƙara cewa ko da yake ya san ba lalle zaman gidan ya yi masa daɗi ba tun da abokin nashi baya nan, makullin mota ya bashi Deen ya yi masa godiya, lokacin da zai miƙe har dad ɗin na tambayar wai zai iya tuƙin saboda titunan nan ba kamar na can ƙasar su ba, da murmushi ya ce masa eh lafiya lau ko jiya ma shi ya kawo su nan daga Zaria, dad ya yaba masa kan hakan duba da yana daɗewa bai yi tuƙi a nan ba. Bayan sun dawo cikin falon ya je ya yi ma mom sallama suka fito tare da Sadeeya ta rako shi har bakin mota ta ce ya gaishe mata da hajiya tana nan zuwa within the weekend yanzu don za su yi online group discussion da ta bi shi, tana tsaye har ya ja motar cikin ɗaga murya take faɗin, "Ka kula sosai my lil bru." Ya sakar mata horn tana dariya ta juyo ciki.



Hajiya zaune a falo ta yi gayun juma'a tana sanye da doguwar rigar shadda ruwan toka da aka yi ma aiki mai kyau, falon ma ya sha gyara sai ƙamshi ke tashi, jin sallama ya sa ta kai idanunta kan ƙofa, ganin Deen ta saki murmushi ya nufo ciki a nutse, a gefen ta saman kujera mai mazaunin mutum biyu da take kai ya zauna yana murmushi ya gaishe da ita ta amsa, ta ce, "Ai ban yi zaton ganin ka ba yanzu, na yi tunanin sai zuwa bayan sallan juma'a." Kwantar da kansa ya yi jikin kujera ya ce mata haka nan ya taho ya zo ya ganta." Murmushin jin daɗin maganar ta yi ta ce to ta gode ga ta ya gan ta, tambayar ta tashi lafiya ya yi ta amsa mashi da lafiya lau Alhamdulillah, tare da tambayar suma sun tashi lafiya ko, 


    "Ya iyayen naka da ƴan'uwanka duk suna lafiya?" Ya bata amsa da lafiya lau, hajiya ta ce, "Sai suka ga ka yi masu zuwan bazata." Ya ɗaga mata kai yana murmushi ya ce sun ji daɗin ganinsa sosai, hajiya ta jinjina kai tana murmushi.


   "Za ka ci abinci a shirya maka ne?" Kai ya girgiza ya ce mata bai daɗe da ya yi breakfast ba sai dai zuwa anjima ta amsa da to, ya faɗi mata saƙon gaisuwar Sadeeya.


   "Ai jiya da daddare ta kira ni suna son awara, na ma isar da saƙon nasu wurin mai yi, na san zuwa yanzu ma ƙilan ta kusa gama masu." Labarin yadda aka ci awaran jiya ya bata tana dariya ta ce, "Ahaf, dama ni na san sai an yi rikici kan awaran in dai suka gani, dama ita haka take abun marmari ce, ai gata nan za a yi masu har ta tiya ɗaya sai su ci su ƙoshi. Fahad yana wurin aiki ne?" Amsa ya bata da eh ta ɗaga kai, kafin ta sake cewa, "Ko kana son awaran a sake yi maka?" Hannu ya kai ya shafo sumar kansa da murmushi ya ce idan akwai yana so ya ji daɗin shi da ya ci ta jinjina kai, bayan ɗan lokaci ya miƙe ya ce zai shiga ciki, har ya fara tafiya ta dakatar da shi ta hanyar sanar da shi cewa ta saka an gyara mashi part ɗin shi na can 6angaren su ko zai yi amfani da shi, ya yi mata godiya kafin ya wuce, wayarta ta ɗauka ta kira layin Innar su Salma, bayan sun gaisa cikin girmamawa innar ta ce mata ai ga aikin awaran nan ana gaf da gamawa, hajiya ta ce to in an gama za su aiko daga can gidan a amsar masu, kafin ta sake cewa dama tana son wata ta rabin tiya ne idan za a samu, baƙonta ya ji daɗin ta jiya shi ne za a ƙara yi mashi, cikin fara'a Innar ta ce mata eh lafiya lau za a samu dama da ta sauke wannan za ta ɗaura wata, hajiya ta ce to shike nan ba sauri take ba ko zuwa yamma ne idan an gama a ba Salma ta kawo, ta amsa mata da to suka yi sallama. 


Misalin ƙarfe ɗaya Fahad ya zo nan gidan hajiya dawowarsa ke nan daga aiki ya ɗauki Deen suka koma gidan su don su je sallar juma'a, bayan sun je Fahad ya ba Deen kayan da zai shirya wanda sabbabi ne a cikin leda ta brand din kayan, bayan ya saka kayan wanda shadda ce sky blue riga da wando da aka yi masu aiki kalan na ƴan gayu, tubarkallah sosai kayan suka amshe shi, shi ma Deen ɗin murmushi ya shiga saki yayin da yake kallon kan sa a madubi bayan ya gama saka kayan, shi ma Fahad shiryawa ya yi cikin shadda ruwan toka irin ɗinkin ɗaya da na Deen suma kayan sababbi ne tare ya siyo masu.


 "Kayan ya yi kyau sosai." Deen ya faɗa yana gyara zaman hular da ya saka wadda take mahaɗin kayan ce itama sabuwa ce sai salƙi take, "When last ka saka kaya irin wannan?" Fahad ya tambaya yana ɗaura agogo a hannunsa, amsa Deen ya bashi da ba zai iya tunawa ba don an daɗe rabon da ya saka manyan kaya. Bayan sun gama shiryawa suka nufi ƙasa sai baza uban ƙamshi suke, idan ka gan su sun fito a zaratan samari  tamkar ka sace su.


    "Wow, ma sha Allah, ƙanina wannan wanka haka!" Sadeeya dake zaune cikin falo ta yi gayun juma'a da jan lace ta faɗa tana nufo su, "Yaya Deen ka yi kyau sosai!" Binafa ta faɗa tana washe baki, tambayarta ya yi da gaske ya yi kyau ta ce eh wllh,  hannun Ayden ya kamo yana masa murmushi don jiya da ya zo basu haɗu ba ya yi bacci, yana ta kallon Deen ɗin don bai saba da shi ba sosai.


   "Tubarkallah ma sha Allah, son ka ƙara matuƙar kyau cikin kayan nan." Mom ɗinsu Fahad ce ta yi maganar yayin da take nufo inda suke tana sanye da doguwar rigar shadda ta yi ɗauri mai kyau, godiya ya yi mata yana murmushi, haka sauran mazan da duk suma sun yi gayun juma'a duk suka yaba gayun Deen, dad ne ya shigo cikin falon ya sha manyan kayan farar shadda, nufo su ya yi yana tambayar su Sadeeq duk sun shirya ko don sun kusa makara, yana ganin Deen ya yi faffaɗan murmushi tare da faɗin, "Ma sha Allah yarona, kayan nan sun matuƙar amsar ka. A can ma kana saka kaya irin wannan?" Amsa ya ba dad ɗin da yana da su amman yana daɗewa bai saka ba wannan ma Fahad ne ya kawo masa, 


"Amma gaskiya sun yi maka kyau sosai, yakamata kana saka irin su ko a can don za ka burge mutane sosai." Godiya ya yi ma dad ya ce zai rinƙa sakawa in sha Allah, hoto Sadeeya ta ɗauke shi tana faɗin dole ta watsa wankan nan daga haka suka tafi masallaci.




Zaune take a saman tabarma cikin baranda tana cin abinci, bata daɗe da dawowa daga makaranta ba ta yi wanka tana sanye da riga da skirt na atamfa, daga gefen ta su Imrana ne suma suna cin abincin su basu daɗe da dawowa daga sallar juma'a ba duk suna sanye da yadi mai kyau kala ɗaya, daga can saman tudun baranda yayansu Auwalu ne zaune shima yana cin abincin yana latsa waya, 


    "Ina zaka je?" Innar su ta ɗaga kai tana tambayar Sagir da ya shigo gidan ya nufi hanyar kicin yana sanye da wandon yadi ya cire rigar sai farar singlet. "Zan ɗan ƙaro abincin ne ban ƙoshi ba ni da su Aliyu muka ci." 


  "To ina ruwan wani da tare kuka ci, kowa kason shi aka zuba masa, saboda ma an san kafi kowa ci wanda aka zuba maka ya fi na kowa yawa kuma shine zaka zo ka kwashe sauran..." Salma bata ƙarasa ba ya nufo ta zai ƙwala mata cokali yana faɗin, "Ke wai uban mi yasa kika raina ni ne..." Da sauri ta 6oye a jikin innarsu, "Sagir kada ka sake ka buge ta, ai gaskiya ta faɗa, abincin da aka zuba maka ya fi na kowa, ba a hana ka ci da wasu ba, amman kuma ba zancen ka zo kai ta kwashe ma mutane abinci, idan kuma ya ƙare aka yi tuwo da daddare ka fi kowa yin tsegumin za a kashe ku da tuwo." Innar su ta faɗa da ɗan ɗaure fuska, ya ce, "Innarmu kaɗan zan ɗan ƙaro." Ya faɗa ya na nufar kicin, 


  "Kai dai ka sani, abinci dai har dare aka yi shi, idan ka kwashe ka nemi abun da zaka ci da dare, don ba wani abincin da za a ƙara dafawa." Bayan ya zubo abincin innarsu ta ce ya kawo ta gani, ya tsaya ɗan nesa da ita ya ɗan karkato mata da kulan yadda ba za ta gani ba sosai, 


"Kam! wllh innarmu cuko ta ya yi." Imran ya faɗa, da sauri Sagir ɗin ya fice yana dariya innar ta ce za su haɗe da dare ne. "Allah wanda ya rage mu za a zuba mawa da daddare ban da shi." Imrana ya faɗa yana tura abinci baki, 


"Su Imrana mala'ikun tauna..." Salma ta faɗa tana dariya. 


   

  "Habu shigo mana ya zaka lafe a nan." Gaba ɗayan su suka kai idanuwansu kan ƙofa jin maganar da innarsu ta yi, lokaci guda Imrana da Hamza suka ɗaure fuska ganin wanda aka kira da suna Habu, "Shigo mana mutumina." Salma ta faɗa tana masa murmushi, nufo ciki ya yi yana tafiya kamar mai jin tsoron shiga, yaro ne da ba zai wuce shekara bakwai ba, jikinsa yana sanye da wani koɗaɗɗan yadi da ba a iya tantance ainihin kalarsa saboda tsufa,  daga ɗan nesa da su ya tsaya sai da Salma ta sake cewa ya zo wurin ta sannan ya ƙarasa, nuna mashi gefen ta ta yi ya zauna, 


   "Har an dawo daga makaranta?" Salma ta tambaye shi, kai ya girgiza mata, a hankali ya ce, "Ba mu je ba." 


   "Saboda me baku je makaranta ba." Kan shi a ƙasa ya ce mata ai sun daina zuwa saboda kayan makarantarsu duk sun yayyage kuma basu da littattafai shi ne baban su ya ce su zauna gida sai ya samu kuɗi zai siya masu, ɗan girgiza kai Salma ta yi, har cikin ranta tana jin tausayin halin da yaran suke ciki na rashin wadatuwa, ba kamar a baya ba lokacin da mahaifinsu ke aiki yana kula da su bakin gwargwado, tun bayan da ya aje aikinsa na ɗan sanda kuma wurin biyan shi hakkinsa na gama aiki aka samu wasu azzalumai suka zabtare masa kuɗin aka biya shi ba yadda ya kamata ba shike nan silar shigar su wahala, gashi yana da iyali matansa ukku da yara sun kai sha bakwai, yana da wata ƴar gonarsa da yake nomawa sai kuma sauran ƴan buge-bugen da yake yi don bai da wata tsayayyar sana'a, ya yi niyyar idan kudin shi suka fito lokacin ya kama ƙwaƙƙwarar sana'a, har suma matansa ya basu babban jari to sai abu ya zo ba yadda ya zata ba, tun a biyan basussukan da ake bin su kuɗin suka tafi, ya dai samu ya canza tsohon babur ɗinsa ya siya wani da yanzu har sana'ar aca6a yake duk da manyanta da ya yi.


    "Salma je ki samu wuri ki zuba mashi abinci ya je ya ci shi da ƙannansa." Innarsu ta faɗa, amsawa Salma ta yi da to tana ƙoƙarin miƙewa, wani kalan tamke fuska Imrana ya yi jin za a kwashe masu abincin dare, Salma da ta kalle shi ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska ta nufi kicin tana mashi dariya. Bayan Salma ta zubo mashi ya amsa zai tafi, cikin tsawa Imrana ya ce, "Ba zaka ce an gode ba!" 

 

 "Imrana miye haka ne, kai ka basa abincin da zaka ce sai ya yi godiya!" Salma ta daka mashi tsawa, kallon Habu ɗin ta yi ta ce, "Je ka Habu." A hankali kamar zai yi kuka ya ce mata an gode ya tafi, yana haura tudun barandar zai nufi ƙofa Auwalu ya ɗaga kai ya kira shi, bayan ya je ya saka hannu a aljihu ya fiddo kuɗi dubu biyu ya bashi ya ce ya kai ma innarsu ya ce ta basu kuɗin aski a ciki, shima sai da ya ce mashi an gode sannan ya tafi, kallon Imrana ya yi cikin ɗaure fuska ya ce masa idan ya ƙara ganin ya hantari yaron sai ya zane shi, ya shiga kwatanta mashi kowa ma zai iya shiga irin halin da suke a ciki ba wai don Allah Ya fi son su bane ya sa su ya wadata su, idan Allah Ya buɗa ma mutum har da don ya taimaka ma wanda bashi da shi ne, Salma da innarsu nata jinjina kai cike da jin daɗin abun da Auwalun ya yi, innarsu tana alfahari da irin halin yaran nata na tausayin wanda bashi da shi, duk da irin rashin kirkin Sagir shima wani lokacin yana taimakon su da kuɗi, shima Imrana ta san har da yarinta ke damunsa.



Wuraren ƙarfe biyar na yamma innarsu ta gama aikin awarar da hajiya ta buƙata, ƙwala ma Salma dake a cikin ɗaki kira ta yi ta amsa tare da fitowa, 


  "Yauwa zo ki kai ma hajiya awaran nan." Turus Salma ta yi jin in da zata je, 


"Inna ko ki ba Imrana tun da ga su can suna yin kallo, ni wani assignment ne nike yi." Ta faɗa cikin rashin son zuwa. Innarsu ta ce, "Da shi zan aika, sai na tuna hajiya da kanta ta ce a baki ki kai, ai tun da ba wani nesa bane kawai miƙawa zaki ki dawo, je ki ɗauko mayafin ki." Bayan ta ɗauko mayafi ta ɗauki robar ta wuce, tun da ta tunkaro gate ɗin gidan ƙirjinta ya fara bugawa da ƙarfi, fargabarta kada ta iske su Fahad, ganin mutane a bakin gate ɗin ya ƙara saka mata fargaba don ta san wurin jikan hajiya ɗan kwallon nan suka zo da alama yana nan ke nan, bayan ta wuce gate ɗin ta nufi ciki tana ta saƙe-saƙen ko shima wannan ɗayan yana nan.


A bakin kofar shiga falon ta haɗe da hajiyar ta yo ma wasu magidanta su ukku rakiya da alama ziyara suka kawo mata, sai da suka gama yin sallama sannan ta dawo kan Salma da murmushi ta ce, "Salma..." 


  "Na'am hajiya, ina wuni." Amsa mata ta yi da lafiya lau ta ce su shiga ciki, bayan ta zauna ta nuna ma Salma kujera ta ce ta zauna, "Gashi innarmu ta ce in kawo." 


  "To, awaran ce an gama." Ƙwala ma Balaraba kira ta yi don ta zo ta ɗauka, bayan ta fito suka gaisa da Salma ta ɗauka ta wuce, "Salma ya makaranta, an dawo tun ɗazu ko?" Hajiya ta tambaya tana kallonta, ta amsa da eh tana wasa da yatsun hannunta, hajiya ta ji daɗin ganin yadda ta saki jiki dama saboda abun da ya faru jiya ya sa ta ce a ba Salmar awaran ta kawo, tayin abinci hajiya ta yi mata Salma ta ce mata ta ƙoshi yanzu nan ta gama ci, shiru suka yi gaba ɗaya idanunsu na akan tv, sallamar da aka yi ta sa duk suka kai idanunsu kan ƙofar shigowa........

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post