Sha'awada Jaraba Page 9&10 By Mom Islam - Abokiyar Hira Novels


SHA'AWA DA JARABA*

    (Love and Romantic story)

          💋💋💋



          Mom Islam 



Page 9-10


Duk saurin su gurin ganin sun kammala girkin da wuri hakan bai yiwu ba, lokacin da suka kammala ana kiran sallahar magriba harda juice ɗin, kowacce idanunta yayi jajir tsabar kuka, suka fito da abincin a warmers biyu manya, Dinning area suka kai suka ajiye kana suka wuce ɗakinsu, kowacce zuciyarta na ƙuna, alwalah sukayi kana suka kabbara sallah a tare, bayan sun idar, Diyana tace "Sis Teema wlhi Yah Muzaffar azzalumi ne baya ƙaunar yaga mutum ya huta.."


Fateemah tace "nifa hatta muryarsa naji sai zufa ya tsatsafo min saboda tsananin tsoronsa da nake ji, suna cikin gulamrsa ya kirasu cikin ɗaga murya yana zaune a parlor shi da abokansa biyu, dawowarshi kenan daga ɗauko Momy daga gidan biki, suka kirashi wai sun iso ya fita ya tarosu, 

Kowacce tana sanye da hijabi suka fito, suka durƙusa a gabansa, "kun kammala komai?"


"Eh" suka ce,


Yace "ku ɗauko ku kaimin ɗakina"


Cikin bin umarninsa suka wuce kitchen suka ɗauko kyakkyawar warmer ɗin sai sheƙi take da spoon da Plate da Glass jug da kofunansa, kasancewar lemun abarba da kankana sukayi, kai tsaye ɗakinsa suka kai kana suka fito suka ce masa sun kai, yace "good" tare da miƙewa, suma abokan nasu suka miƙe kowanne idanunsa na kan Fateemah da Diyana,

Bayan shigarsu ɗakin ya haye lallausan Royal bed ɗinsa tare da ɗaukar system ɗinsa, "ku ci abinci ku ƙoshi.."


Doctor Muzaffar ya faɗa yana saka gilashi a idanunsa, 

"Ikon Allah Muzaffar gaskiya kazo ka zuba mana.."


Cikin isa yace "duk shegen da bazai ci ba ya barshi inhar nine zan zuba muku abinci"


Dole dai ɗaya ya ɗauki ragamar zuba abincin suka fara ci suna hira, shiko hankalinsa sam baya gurinsu, 


Ɗayan mai suna Abubakar yace "Muzaffar Please ƴan matan da na gani ƙannenka ne..?"


"Yea mai ya faru?"


Muzaffar ya amsa masa a taƙaice,


"Ina ciki ne idan babu wanda ya rigani.."


Doctor Muzaffar yace "aiko ba zaka samu ba saboda dukkansu ba yanzu zasuyi aure ba karatu sukeyi."


Khalil yayi dariya, kafin yace "idan ban da abinka Muzaffar ai cewa kana son budurwa ba shine zai hana ta yin karatu ba"


"Okay abinda ya kawoku kenan?, to ku tafi mun gode nace basa tsayuwa da samari ko ana dole?"


Abubakar dai bai sake magana ba, sai Khalil da yace "Allah ya huci zuciyarka"


Ba suci abincin da yawa ba, suka fara shirin tafiya, Muzaffar ya sauko daga bed, ya rakasu har compound inda motarsu take, ido biyu sukayi da Diyana da Fateemah sun fito daga garden kowacce hannunta riƙe da abin fifita,


Abubakar da Khalil suka zuba musu idanu, idanun Muzaffar ne ya sauka a kansu ya kalli su Abubakar sannan ya kalli Fateemah da Diyana da suke tafiya a hankali basu ma san Muzaffar ɗin na kallonsu ba, cikin daka tsawa yace "daga ina kuke" ba ƙaramin gigicewa sukayi ba, suka ƙara da gudu basu bashi amsa ba, Abubakar da Khalil suka shiga mota sukayi masa sallama, dan ko bari su gaisa da momy da ta shiga Sallah beyi ba, ya ɗaga musu hannu motarsu tabar gidan,

Cikin ɗaga murya yake ƙwala musu kira tun daga ƙofar shigowa parlor, basu fito ba suna bedroom ɗin Momy sunata haɗata da Allah akan ta bawa yah Muzaffar haƙuri bazasu sake fita ba,


Momy tace "kunsan halinsa mai yasa ba zaku dinga kiyaye duk abinda zai zame muku matsala a tsakaninku dashi ba"


Suka ce "bazasu sake ba"


Momy ta fito parlor ta sameshi yana zaune a saman Sofa mai zaman mutum ɗaya, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya fuskarnan tasa babu wani annuri, Momy ta zauna kafin tace "Doctor Dan Allah ka rage zafin zuciya yara nan ba wani guri suka je ba, garden suka je dan Allah kayi haƙuri irin haka sai su dinga tsoronka.."


Gyaɗa kai kawai yayi ba tare da ya cewa momy komai ba, ya tashi ya fita, ta sani sarai haushi yaji, kuma gaskiya ta faɗa masa, cikin ɗaga murya Momy tace "Diyana Fateemah kuna ina?"


Suka fito da sauri suna leƙo ko Yah Muzaffar ɗin ya fita, ganin baya nan yasa su fitowa da gudu suka zo parlon suka zauna a saman Sofa suna kallon Momy kowacce tayi tsuru-tsuru da idanu, kuma ankare suke dan suna ganinsa rugawa zasuyi.


Momy tace "wlhi ku kuka da kanku ransa ya ɓaci, sakamakon faɗan nayi masa"


Shiru sukayi basu ce komai ba, Momy tace "ashe kunyi girki"

Nan suke bata labarin  birthday ɗin da aikinsa ya hana su zuwa dole sai haƙura sukayi,


Momy tayi murmishi kana tace "sai kunyi haƙuri, ya kamata tunda kuka san abinda baya so sai ku kiyaye"


Momy ta tashi zuwa yin sallar isha'i, suma suka wuce bedroom ɗinsu, sun rigata fitowa dan haka sukai saurin zuwa kitchen suka kwaso plate da spoon da sauran abubuwan buƙata gudun kar ya fake dasu yayi musu hukuncin da zai huce a kansu,


Momy ce ta fito daga bedroom ta nufi dinning area, ta ƙwalawa su Fateemah kira, amsawa sukayi kana suka ɗan leƙo suga ko Yah Muzaffar ya dawo, ganinsa sukayi yana zaune a saman kujerar Dinning table ɗin yana daddana waya, suka koma saɗaf-saɗaf suka kullo ƙofa,


Tunda momy taga  basu zo ba, ta ƙyalesu saboda tasan kwanan zancen.


Jawad yace "momy lafiya kuwa me yaranaki sukayi?"


Momy tayi murmishi kafin tace "hmm basa jin magana ne rabu dasu kawai"


Jawad na gama cin abinci ya fice shiko yah Muzaffar har yanzu ko loma ɗaya bai kai bakinsa ba, sannan gefe kuma farfesun da yasa su Diyana sukayi masa ne, koda Momy ta gama cin abincin, ta dubesa kafin tace "Doctor abincin zai yi sanyi ko a rufe maka ne?"

"No momy ina wani abu ne yanzu zan ci"

 Momy taja kujera baya tace "ni zan shiga ciki gobe dai Dadynku yana hanya"

Yah Muzaffar yace "Masha Allah Ubangiji ya dawo dashi lafiya"

Momy tace "Amin ya rabbi" ta shige ciki.

Yana zaune a gurin bai ci abincin ba har ƙarfe 9:30pm idanunsa na kallon screen ɗin waya, sai yanzu ya ɗauki spoon ya kawar da abincin sannan ya ɗauko warmer na farfesun kana ya zuba, ya fara ci a hankali, 

Acan ɗakinsu Fateemah yunwa ta addabesu, dama tsabar zumuɗin zuwa birthday yasa basu ci abincin rana ba, yanzu kam ko wacce ta fara raina kanta, gashi sun leƙo parlor sun hangoshi yana nan a zaune yanzu nema ya fara cin abincin, Diyana tace "Abu mafi sauƙi ko tea suje kitchen su haɗa"

Fateemah tace "kina ganin bazai ganmu ba, sannan tea dame zamu haɗa?"

Suka yanke shawarar zuwa kitchen su dafa indomie ko hungry man guda ɗaya ce, sun fito keman sukayi ido biyu da Yah Muzaffar yana shirin fita ya dawo da baya..!


Mom Islam

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post