SHA'AWA DA JARABA (Love and Romantic story) 💋💋💋 Mom Islam Page 11-12 Kafin ya furta wata kalma suka ruga da gudu bedroom ɗinsu suka yiwa ƙofar key, ƙwafa yayi ya fice. Sai dare yayi sosai, sannan suka leƙo suka tabbatar da baya nan, kana suka shige kitchen suka yi girkinsu, bai ƙarasa nuna ba suka sauke suka wuce bedroom, Kowacce na mayar da numfashi, san sun san idan har ya damƙesu tabbas sai sun sha baƙar wahala. Washe gari, tun bayan da sukayi sallahar Asbha suka fito aka fara gyare-gyaren gida, kasancewar dady zasu dawo yau, sun gyara ko ina tsaf sai ƙamshi ke tashi, daga nan suka wuce part ɗin Hajiya Mariya, suna kiranta da Umma, da sallama suka shiga, suka samu tana zaune ita da autanta Abdul yana wasa a saman carpet, zama sukayi kana suka ce "Umma munzo gyara miki gidane, tunda yau Abba yana hanya" Cikin fara'a da sakin fuska tace "aiko ina maraba daku wlhi, saboda dama aiyuka sun yimin yawa" Da bedroom ɗinta suka fara, kana suka wuce kitchen ɗinta suka gyara tsaf sannan suka wuce dinning table suka goge, kana suka saka turaren wuta mai ƙamshi, sukayi mata sallama saboda su ɗin ba ma'abota son yin girki bane bare suce ta kawo suyi mata, Part ɗinsu suka wuce, basu tsaya a parlor ba suka wuce bedroom, Diyana ce ta fara shiga wanka, bayan ta fito Fateemah ta shiga, Fateemah na fitowa ta zauna a gefen bed tana goge gashin kanta tace "Diyana wane irin kaya ya kamata mu saka?" Diyana tace "abayar da Abba ya siya ma lokacin da sukaje Egypt da Daddy" Diyana ta Ciro musu abayar, kala ɗaya ce komai iri ɗaya Black color ce sannan tasha adon duwatsu golden da ja, mayafan abayar sunada ɗan girma, bayan sun gama shafa mai sukai makeup wanda ya sake fito da ainihin kyawunsu, gasu dama farare tass, Kowacce tasa tata, sukai rolling Vail ɗin sosai sukai kyau, ga wani uban sarƙa da ɗankune da suka saka da zobe da warwaro, Masha Allah, parlor suka fito lokacin 9:am Momy ta gama breakfast takai dinning ta ajiye, suma suka wuce dinning ɗin suna yi mata sannu da aiki, suna zaune ya Muzaffar ya shigo, yana sanye da dakakkiyar farar shadda sai sheƙi take, ya ɗora hula a saman kansa, hular ta sake fito da ainihin kyawunsa, hannunsa sanye yake da tsadajjen agogo ga wasu kyawawan zobuna a yatsuntsa na tsakiya, Masha Allah yah Muzaffar yayi kyau sosai, "Momy Barka da safiya" Ya faɗa yana wucewa dinning table ya zauna, Momy tace "Barka ya aiki" "Lpy" ya amsa a taƙaice. Diyana ta kalli Fateemah, suka gwalo idanu yanzu dai babu halin guduwa dan haka ko wacce ta saita tunaninta, ɗaya bayan ɗaya suka gaishe sa, bai amsa ba sai can momy ta zuba masa faten dankalin turawa da yaji hanta da kifi, bayan ya zare spoon a bakinsa yace "lafiya kun gama gudun?" Suka wani zazzaro idanu, cikin haɗa baki sukace "dan Allah kayi haƙuri bazamu sake ba" Bashi da isasshen lokaci, dan haka bai wani bi ta kansu ba, sakamakon kiran gaggawa da akai masa, a gurguje yai breakfast ɗin ya miƙe yana cewa "momy sai ya dawo" Fatan nasara gami da Ubangiji ya tsareshi tayi masa ya fice, Diyana ta gyara zama tana cewa "kaii Masha Allah gidan har yayi ni'ima" Momy ta ware idanu tana kallonsu, kafin tace "bazaku tabbatar da gata ake yi muku ba sai zuwa nan gaba" Fateemah ta turo baki kafin tace "wlhi ina tausayawa wacce zata auri yah Muzaffar shifa kowa bai ƙyale ba har abokansa inda kasan wani sarki ko yarima" Momy tace "ya isa haka, da ace yana nan ƙwaƙwaran tari babu mai yi, da yake kunga baya nan shine bari kuyi gulamrsa ko?" Sukai shiru suna dariya, Diyana ta kwaɓe fuska kana tace "Momy dan Allah ki bari muje gidan Granny wlhi mun kwana biyu bamu jeba, bazamu daɗe ba muna gaisheta zamu dawo saboda muga dawowarsu Abba da dady" Momy tace "Allah ya kiyaye hanya, idan ma kun daɗe wlhi babu ruwana, dama cewa take wai nice nake hanaku zuwa gurinta, amma ku gama cin abincin" Godiya sukayi mata kana suka fice kowacce ta ɗauki hand bag ɗinta, suka dawo parlo, momyn bata parlor suka wuce bedroom ɗinta, da sallama suka shiga, momy ta kallesu gami da yin murmishi tace "ƴan matana kunyi kyau sosai" Fateemah tace "momy bamu da kuɗi..." Daga faɗar haka ta sunkuyar da kanta ƙasa, momy ta ɗaga ƙasan pillow ta ɗauko kuɗi ta ƙirga 5k ta bata tace su raba, suka yi mata sallama kana suka wuce, bayan tayi musu Allah ya kiyaye, Kai tsaye suka parking space, Diyana ta ƙwalawa driver kira, ya taho da sauri bayan sun gaisa suka ce ya kaisu gidan Granny suka shiga mota, backside, Bayan ya shiga yayiwa motar key suka bar gidan, tunanin abinda zasu siya mata suka farayi saboda idan sukaje hannunsu babu komai sun san sauran, Sunyi nisa sosai sukaga mai kifi a bakin hanya irin wanda suke sawa a ciki glass, sukace driver ya tsaya, Fateemah ta fita ta siyi na 3k ta dawo da kifin suka wuce. Cikin ikon Allah suka iso gidan Granny, driver yai horn a ƙofar gidan mai gadi ya buɗe masa get ya shiga, bayan yayi parking suka fito, ciki suka wuce suna tafe suna hira suna dariya. Babban gida ne, sai dai bai kai girman nasu ba, anyi masa shuke-shuke irin na turawa mai ban sha'awa irin na gidansu Diyana, Ƙofar parlor a buɗe take Kai tsaye suka shige bakinsu ɗauke da sallama, zama sukayi a saman lallausar Sofa tare da zubawa TV idanu, Cikin ɗaga murya Diyana tace "Granny ina kika shiga.." Ta fito da sauri tana sanye da doguwar rigar Atamfa ta mugun kere tsayinta sai tattare rigar takeyi, suna ganinta suka kwashe da dariya, saboda har ga Allah wannan shiga ta Granny dole ta bawa duk wani mai kallonta dariya, "Au ashema iskanci kuka zo yimin to ku tashi ku koma bana buƙatar ziyarar" Diyana ta kamo hannun Fateemah kana tace "ki ajiye kifin a mota nima ga ninan" Ba shiri Granny taje ta tare bakin ƙofa tare da cewa "babu inda zaku ai anan zaku zauna, kafin nan dai kuje kitchen ku ƙarasa yimin dambun shinkafa" Kowacce ta zaro idanu, Fateemah tace "meye kuma dambun shinkafa..?" Granny tace "mamanku ta fini sanin ko meye mtswww" ta wuce kitchen taci gaba da aikinta har sai da ta kammala sai zuba ƙamshi yakeyi, ta zubo musu a plate suka wani yamutsa mata fuska, ajiye tayi tare da fizgar ledar hannun Fateemah ta koma saman kujera ta zauna, a plate ta juye kifin ta fara gyarashi, Diyana tace "Granny kinsan da cewar Bama son ƙarni ko?" Mom Islam
Tags
Sha'awa Da Jaraba
